Thursday 9 May 2013

TAMBIHI


Wannan shafi na tambihi na maraba da ziyartarsa.
                                                          GABATARWA.
Da sunan Allah mai Rahma mai jin }ai, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah{T} ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta kuma cikamakon Annabawa,Annabi Muhammad da kuma alayensa tsarkaka.                                                                                                                                                                Bayan haka wannan shafi na Tambihi, rubuce rubuce ne da suka gabata a filin tambihi na jaridar Almizan.Filine da ake gabatar da Darussa  na wasu fannoni na ilimin Addinin Musulunci,kamar ilimin Akla},Fi}hu,Tarihi da kuma rayuwar Manzon Allah[SAAW] da Ahlul-Bayt[AS] da dai sauran Maudu’oi dabam-dabam. Saboda bu}ata da wasu sashen ‘yan uwa suka yi, na cewa rubutuk-tukan da ake gabatarwa da kuma wa]anda suka gabata a tattara su a bu]e masu shafi a Internet, domin tunatarwa da kuma fa’idantarwa da amfanuwa ga sauran mutane.                                                                                     Akan asasin haka aka bu]e wannan shafi .Kuma a halin yanzu yana da ~angarori guda hu]u sune:
Bangare na farko:DARUSSA DAGA RAYUWAR MANZON ALLAH {S.A.A.W} DA KUMA AHLUL-BAYT {AS}.Sune:
1.       Darussa daga rayuwar Manzon Allah [S.A.A.W].
2.       Darussa daga rayuwar Ummul-A’imma Fa]ima [AS].
3.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali [AS].
4.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan [AS].
5.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Husain [AS].
6.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali zainul Abidin [AS].
7.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Muhammad Al-Ba}ir [AS].
8.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Ja’afarus-Sadi} [AS].
9.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Musa-Al-kazim [AS].
10.   Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali Arridha [AS].
11.   Darussa 12 daga rayuwar Imam MuhammadAl- Jawad [AS].
12.   Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali Al-Hadi [AS].
13.   Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan Al-askari [AS].
14.   Darussa 12 daga rayuwar ImamAl- Mahdi [AS].
Bangare na biyu:DARUSSAN  AKHLA{.Sune:
1.       Darasi na 1 Bayani kan fannin ilimin Akhla}.
2.       Darasi na 2 Bayani kan muhimmancin ilimin Akhla}.
3.       Darasi na 3 Bayani kan hanyoyin samun kyawawan Akla}.
4.       Darasi na 4 Bayani kan Ruhin mutum.
5.       Darasi na 5 Bayani kan Tazkiyatun-nafs.
Bangare na ukku:DARUSSAN FI{HU.Sune:
1.       Darasi na 1 Bayani kan fannin ilimin fi}hu.
2.       Darasi na 2 Bayani kan Ala}ar limaman mazhabobin Ahlus Sunna da Imaman Ahlulbayt [AS].
3.       Darasi na 3 Bayani kan Azumi [1].
4.       Darasi na 4 Bayani kan Azumi [2].
5.       Darasi na 5 Bayani kan Ijtihad da Ta}lid.
Bangare na hu]u :DARUSSA DAGA MAUDU’OI, DABAM-DABAM.Sune :
1.       Alamomin bayyanar Imam Mahdi [AF].
2.       Rubuce-rubucen shehu [an Fodio akan Imam Mahdi [AF].
3.       Tarihi da kuma Darussa daga rayuwar sayyida Zainab [AS].
4.       Tarihi da rayuwar sayyid Abul-fadhal Abbas [AS].
5.       Ranar ghadir a mahangar shi’a da sunna.
6.       Ashura a mahangar shi’a da sunna.
7.       Imama a mahangar  shi’a da sunna.
8.       Gudunmawar mata a wa}i’ar  karbala.
9.       Arba’in ]in Imam Husain [AS].
10.   Darussa 12 daga rayuwar Imam Khumain [KS].
11.   Tarihi da rayuwar shahid Ayatullah sayyid Muhammad Ba}ir  sadr.
12.   Shekaru 60 masu albarka na Sayyid Zakzaky [H].             
13.   Darussa 12 daga rayuwar Sayyid Zakzaky [H].
14.   Ruhin Azumi da kuma Ayyukan watan Ramadan.
15.   Ban kwana da watan Ramadan 1432 A.H.
16.   Ban kwana da watan Ramadan 1433 A.H.
17.   Hanyoyin samun Ta}wa.                                                                                                                                        Kuma Insha Allah za’a dunga samun }ari a wa]annan ~angarori guda hu]u,lokaci bayan lokaci.Da fatan abubuwan da zamu karanta, Allah {T} ya amfanar damu,ya kuma bamu ikon aiki dasu. Allah {T} yasa su kasance haske gare mu duniya da lahira. Allah {T} ya kiyayemu kada su kasance duhu da nauyi akan mu gobe }iyamah.                                                                                                                   Daga }arshe duk wanda yake da wata shawara, ko neman }arin bayani, ko kuma tambaya  kan abubuwan da ya karanta a wannan shafi na tambihi.To  yana iya rubutowa ta wannan adreshi na emel  TAMBIHI@GMAIL.COM.
MUHAMMAD SULAIMAN KADUNA.                                                                                                       WAS-SALATU WAS-SALAMU  ALA  MUHAMMADIN  WA  ALIHI[  [AYYIBINA[  [AHIRIN.                                                                                           

RUHI DA KUMA ASRAR NA SALLAH.


Sallah tana da ~angarori guda biyu,~angaren ruhinta,wanda shine ba]ininta da kuma ~angaren jikinta,wanda shine zahirinta.Malaman Irfan ko Tasawwuf sun yi rubuce-rubuce da kuma bayanai dangane  da Ruhin sallah da kuma Asrar ]inta.Kamar yadda Malaman Fi}hu suka yi rubuce-rubuce da kuma bayanai dangane da zahirinta.

ASRAR DA IBADODI NA WATANNIN RAJAB,SHA’ABAN,RAMADAN.


Watannin Rajab,Sha’aban da kuma Ramadan,watanni ne masu gayar falaloli da kuma Asrar,domin a dukkan watanni 12 na musulunci babu watannin da suke da ayyuka na Ibadodi kamar su.Shi yasa bayin Allah[T] suke farin ciki da shau}in zuwansu.Haka nan kuma suke ba}in ciki da ma kuka idan sun zo }arshe.wato saboda yankewar da zasu samu na falaloli da darajoji da zau}iyyat da halawat da kuma ma’anawiyyat na Ibadodin da ake samu a cikin watannin,wanda babu irin haka a sauran watannin.

ASALIN SHI’A DA ABUBUWAN DA AKA JINGINA MATA.


                Asalin kafuwar shi’a da abubuwan da aka jingina mata yana ]aya daga cikin ababen da Malamai dabam-dabam na shi’a,suka yi rubuce-rubuce da bayanai dabam-dabam akai,saboda haka akwai littafai masu yawa a wannan fagen.

Darasin fikhu {7}.


A darasin daya gabata bayani ya gudana akan shakka a rakao’in sallah da kuma raka’ar ihtiya]i.An yi bayani akan cewa shakka a sallah ta kasu kashi ukku.1-shakka a rakao’in sallar.2-shakka a asalin yin sallar.3-shakka a ayyukan sallar.Na farko bayanin sa ya gabata,yanzu sai bayanin na biyu dana ukku.Bayan haka kuma sai bayani kan sujudi sahawi da kuma mas’aloli da suke da ala}a dasu.

Darasin Akhlak {7}.


                A darasin daya gabata wato darasi na 6 bayani ya gudana akan {AL’B wato zuciya,an kawo abubuwa guda 9 da suke da ala}a da ita,amma an tsaya ana shidda,sauran aka ce sai darasi na gaba insha- Allah.Sabada haka a yanzu za a tashi ana 7-Magance bushewar zuciya:Malaman irfan ko tasawwuf sunyi bayani dangane hanyoyin maganin bushewar zuciya

Tuesday 7 May 2013

Tarihi Da Kuma Darussa Daga Rayuwar Marubucin Mafatihul Jinan.


Bayani ko rubutu kan tarihi da kuma rayuwar Marubucin littafin Mafatihul-Jinan,wato shaikh Abbas Al-}ummiy wani fage ne mai fa]in gaske.Kuma sanin tarihinsa da kuma rayuwarsa yana da muhimmancin gaske,saboda zai yi wahala ka samu wani mabiyin Ahlul-bayt wanda bai da wannan littafi nasa na Mafatihul jinan,wani gidan ma kana iya samun mutum shi da iyalinsa kusan kowa nada nashi mafatihun