Tuesday, 7 May 2013

Tarihi Da Kuma Darussa Daga Rayuwar Marubucin Mafatihul Jinan.


Bayani ko rubutu kan tarihi da kuma rayuwar Marubucin littafin Mafatihul-Jinan,wato shaikh Abbas Al-}ummiy wani fage ne mai fa]in gaske.Kuma sanin tarihinsa da kuma rayuwarsa yana da muhimmancin gaske,saboda zai yi wahala ka samu wani mabiyin Ahlul-bayt wanda bai da wannan littafi nasa na Mafatihul jinan,wani gidan ma kana iya samun mutum shi da iyalinsa kusan kowa nada nashi mafatihun
.Haka nan a nahiyoyi ko }asashe na ‘yan shia,mutum zai ga a masallatai da kuma Husainiyoyi baya ga Al-}ur’anai akwai littafan mafatihul jinan da akan aje ga masu bu}atar karantawa.Ata}aice dai mutum zai iya cewa a wannan zamani namu,babu wani littafi da ya samu amsuwa da kuma watsuwa tsakan-kanin mabiya Ahlul bayt kamar littafin mafatihul jinan.Saboda haka wannan bawan Allah yana da ha}}i akanmu, a}alla na sanin tarihinsa da kuma yi masa addu’a.Kuma wannan addu’a tana ]aya daga cikin abin da  ya bu}ata ga duk wani mumini ko mumina,kamar yadda ya rubuta haka a mu}addamarsa na littafin mafatihu jinan.mutum na iya duba mafatihunsa a mu}addimar zai ga haka.Saboda haka yana da muhimmanci mutum ya kasance ya sanya shi cikin wa]anda yake yima addu’a,a kowane dare bayan sallar tahajjud ]insa,in kuma haka bai samu ba to a}alla kowane daren jumma’a.Haka nan Shaikh Abbas Al-}ummiy baya ga littafin mafatihul jinan ya rubuta littafai masu yawa,a}alla sun kai guda sittin ga mai bu}atar ganin sunayensu yana iya duba littafinsa mai suna Al-kuna wal Al-}ab.kuma wa]annan littafai nasa in mutum ya bincika zai ga suma sun samu kar~uwa da  watsuwa da kuma wanzuwa.Domin wa]annan abubuwa guda ukku da aka ambata wato kar~uwa,watsuwa da kuma wanzuwa a fagen rubuce-rubuce, baiwa ce wadda Allah[T] kanyi ma wasu daga cikin bayinsa.In mutum ya bibiyi tarihin malamai na wa]annan makarantu guda biyu wato na shia da sunna wa]anda suka yi rubuce-rubuce na littafai,zai ga akwai wa]anda Allah yayi masu baiwa da wa]annan abubuwa guda ukku,Zai ga wani malamin ya rubuta littafi shekaru ]aruruwa wani ma sama da shekara dubu,littafin ya wanzu har zuwa wannan zamani,ya kuma kar~u wato ana amfana dashi,kuma ya watsu wato a sassan duniya dabam dabam ta yadda kusan ko ina kaje zaka same shi.Shaikh Abbas Al-}ummiy littafan da ya rubuta sun sami irin wa]annan baiwowi da aka ambata,misali littafin mafathul jinan ya rubuta shi sama da shekaru 70 da suka wuce,amma mu duba yadda ya wanzu,kuma lokaci bayan lokaci da]a buga shi akeyi, a kuma sassan duniya dabam dabam.Tun yana raye ma irin amsuwar da mafatihun ya samu ba ka]an ba ne.wani misali anan shine,wata rana Shaikh Abbas Al }ummiy yana zaune a wani masallaci yana Azkar,sai wani sayyid yana zaune kusa dashi yana biya mafatihul jinan,lokacin yana sabon fitowa,sai shaikh Abbas ya tambayi sayyid ]in waye mawallafin littafin ? Sayyid ]in yace Shaikh Abbas Al-}ummiy,sai ya kama yaba masa yana cewa kai wannan littafi,wannan malami Allah ya saka masa da al-hairi da dai zantuka na yabo.jin haka sai shaikh Abbas al-}ummiy yace ma sayyid ]in,amma mawallafin littafin bai cancanci wannan yabon da ka keyi ba,saboda haka ka barshi,jin haka sai sayyid ]in ya fusata,da yake bai san mai tambayar shine shaikh Abbas al-}ummiy ]in ba.yace tashi kaba mutane waje kawai,to wani mutumi yana kusa dasu a wajen wanda shi yasan shaikh Abbas al-}ummy,sai yace ma sayyid ]in,to ai kai wannan shine shaikh Abbas al-}ummiy ]in.jin haka sai sayyid ]in yayi nadamar abunda yayi, ya kuma nemu afuwa a wajen shaikh Abbas al-}ummiy, har ma ya nemi ya sun banci hannun shaikh Abbas Al-}ummiy,amma bai yarda ba,sai shine ya sunbanci hannun sayyid ]in,yace masa ai kai sayyid ne.da yake yazo a tarihin rayuwar shaikh Abbas al}ummiy cewa ya kasance yana gayar girmama zuriyyar Manzon Allah[S] kamar yadda zamu ga haka nan gaba a wajen darussa daga rayuwarsa.Haka nan Shaikh Abbas al-}ummiy yana ]aya daga cikin malaman da Imam khumaini yayi karatu a wajensu,wato Imam yayi karatu a wajensa.Bayan wannan shimfi]a sai kuma abinda ya shafi Tarihinsa.
            An haifi shaikh Abbas Al}ummiy a Iran wato a binin }um,shi yasa ake yi masa la}abi da Al-}ummiy,an kuma haife shine a shekara ta 1294 wato bayan Hijira.Sunan mahaifinsa Shaikh Muhammad Ridha Al-karbala’iy,yazo a tarihin wannan mahaifi nasa cewa ya kasance salihine kuma mai Ta}awa.Haka nan mahaifiyarsa itama ta kasance saliha mai ta}awa,Shaikh Abbas al }ummiy yace dangane da wannan mahaifiya tasa  ta kasance ta kanyi sallolinta farkon lokaci.kuma yace lokacin yana shan mama wato jariri duk lokacin da zata shayar dashi in bata da alwala ta kan je tayi alwalar, saannan ta shayar dashi,shine har yake cewa muwafa}ar da ya samu a rayuwarsa yana komawane ga mahaifiyarsa.Shaikh Abbas al-}ummiy ya tashi a birnin }um kuma anan ya soma karatunsa,a wajen Maluma dabam dabam.Lokacin da yakai shekaru 26 sai ya bar birnin }um da niyyar zuwa }aro ilimi a birnin Najaf.A lokacin birnin Najaf itace babbar cibiyar ilimi a duniyar Ahlul-bayt dama duniyar musulmi baki ]aya,kamar yadda a yanzu birnin }um shine babbar cibiyar ilimin Ahlul bayt dama duniyar musulmi baki ]aya,ta yadda mutum zai iya dukan }irji yace a doron }asa baki ]aya a yanzu babu inda ake zuzzufar karatun addinin musulinci a kuma fannoni dabam-dabam kamar birnin }um.Kai hatta wasu daga cikin masana na }asashen yamma sukan zo birnin }um domin yin bincike dangane da addinin musulinci ko kuma wasu ababe da suke da ala}a dashi.Akwai ma wani bature bama musulmi ba, dana ta~a gani yazo daga cikin wa]annan }asashe na yamma a birnin }um,wai yazo bincike dangane da WILAYATUL-FA{IH,abin ya ban mamaki sosai,da yake al-amarin wilayatul fa}ihi ya ]aure kai ga mafi yawan shugabbannin }asashen yamma,misali a jamhuriyar musulinci ta Iran suga cewa ga shugaban }asa,amma bashi yake da matsaya ta }arshe ba ga wasu ababe da suka shafi }asa ba,wato yana hannun waliyyil-amru ne,to da yawansu suna bincike su fahimci miyasa haka.Shaikh Abbas al-}ummiy da ya tafi Najaf acan ma yayi karatuttuka wajen malamai masu yawa,bayan nan ya dawo Iran ya zauna a mash-had shekaru 12,bayan haka ya sake komawa birnin Najaf,acan ya cigaba da zama har ya zuwa }arshen rasuwarsa.Ya rasu ranar Talata 22 ga watan zul-hijja shekara ta 1359 bayan hijira.Saboda haka }abarinsa yana a Najaf ne, a haramin Imam Ali [AS]Kuma ya rasu yana da shekaru 65 a duniya,ya rasu ya bar ‘ya’ya hu]u maza biyu mata biyu.Bayan wannan tarihi nasa a ta}aice,sai kuma wasu darussa daga cikin rayuwarsa mai albarka
1-      Girmamawarsa ga zuriyyar Manzon Allah[S] Shaikh Abbas Al-}ummiy ya kasance mai gayar girmama jikokin Manzon Allah[S]yazo a tarihinsa cewa duk inda yaga sayyid ya kan girmama shi,misali abin da aka kawo a sama na wani sayyid da suka ha]u dashi,da abun da ya gudana tsakaninsu dangane da mafatihul jinan,daga }arshe saboda garmamawa har shaikh Abbas al}ummiy ya sun banci hannunsa.Haka nan a ranar da zai rasu an kawo masa abin sha na tuffah,to a lokacin akwai wata ‘yar }aramar yarinya sayyida a gidan,sai yace a soma bata,in tasha ta rage sai a mi}o masa sauran,haka ko aka yi sai da tasha saannan yasha,wato dai saboda girmamawarsa ga jikokin Manzon Allah[S] akwai misalai da dama irin haka a ryuwarsa.
2-      Tawali’unsa :Shaikh Abbas al-}ummiy ya kasance mai gayar tawali’u.Akwai wani littafi da ya rubuta mai suna « Manazilul-Akhira »to mahaifinsa masallacin da yake sallah limamin masallacin ya kan karantar  da littafin a masallacin,to wata rana mahaifin nasa ya dawo daga masallaci,sai yake cema ]an nasa wato shaikh Abbas,kai ma da ace ka dun ga karantar da littafin,Amma saboda tawali’unsa maimakon yace ma mahaifinsa aini na rubuta littafin,amma sai yace masa ya baba na kayi mani addu’a, Allah ya bani muwafa}ar yin haka.
3-      Tahajjud ]insa :Shaikh Abbas Al-}ummiy ya kasance mai gayar tsayuwa da sallar tahajjud tsawon rayuwarsa.Babban ]ansa yana cewa bai ta~a ganinsa ba yana barci yayin ketowar alfijir,Haka nan wani daga cikin ‘ya’yansa yace a lokacin suna Najaf,a wani dare na jumma’a babana yana karatun Al}ur’ani  na suratu yasin,lokacin da yazo ga wannan aya « Hazihi jahannamul lati kuntum tuadun »haka ya dunga maimaita ayar bai wuce taba har ketowar alfijir.duk lokacin da ya biya ayar sai yace Auzu billahi minar nar.
4-      Haninsa ga Munkar :Shaikh Abbas Al-}ummiy ya kasance mai gayar hani ga munkar wato abubuwan }i,yazo a tarihinsa cewa duk inda yaga munkar ko yaji munkar to zai tsawatar akai.yazo akan cewa ba a giba a gabansa,mu duba mu gani bawai shi yayi giba ba a’a,a gabansa ba ayi.ance ya kasance mai gayar }yamar giba da kuma }arya ne.Akwa ma wani abun da ya ta~a faruwa a sa’udiyya lokacin yaje aikin hajji tsakaninsa da wani malami ba wahabiye,yai masa wata tambaya amma sai ya bashi amsa akan asasin ta}iyya,sai ya kasance gab da zai rasu a rashin lafiyar }arshe da yayi a rayuwarsa,wani Malami yazo gai da shi sai ya gan shi cikin damuwa da ba}in ciki,sai malamin ya tambaye shi dalilin haka ?sai ya fa]a masa abin da ya ta~a ha]a shi da wani malami a sa’udiyya,to yanzu ina tunanin waccan rana da kuma tunanin tsayuwata gaba ga Allah akan haka.To mu duba mu gani ta}iyya yayi, ba wai }arya ba, amma yana jin tsoron ha]uwarsa da Allah akan haka.
5-      Ala}arsa da Lokaci :Shaikh Abbas Al-}ummiy ya kasance mai gayar kiyaye lokaci,wato bai wasa da lokacinsa komai }an}antarsa,yazo a tarihinsa cewa a kowace yana aikin awa 18 ne. wato tsakanin karatu da karantarwa,rubuce-rubuce na littafai da dai sauransu.Kuma wannan kiyaye lokaci bawai a halin zaman gida ba,a’a hatta a halin tafiya ya kan kula da lokacinsa gaya,misali yazo a tarihinsa cewa a tafiya idan an yada zango domin cin abinci da kuma hutawa,ana gama cin abinci da an shiga hira wato kafin a gama hutawa a wuce,sai ya ]auki littafinsa ko littafai ya koma gefe yana mu]ala’a ko rubutu,har akan ce masa, ka ]an zauna mana,mu tattauna,amsar da yakan bayar itace dukkan mu zamu tafi mu bar wa]annan abubuwan.wato rubuce-rubuce na littafai.Tabbas ko haka ne gashi yau bai duniya amma ga littafan da ya rubuta ana amfana dasu.wannan shima wani darasi ne babba garemu,wato muhimmancin aiki da lokaci
6-      Zuhudinsa :Shaikh Abbas Al-}ummiy ya kasance mai gayar gudun duniya,shima wannan akwai misalai da yawa ta kuma fuskoki dabam dabam a tarihin rayuwarsa.Ga mai bu}atar ganin wa]annan fuskoki na zuhudunsa misali ta fuskacin dukiya, matsayi da dai sauransu to yana iya duba littafinsa mai suna Muntahal Amal juz’i na ]aya wato a wajen gabatarwa na tarihin rayuwarsa.zai ga abubuwa na ban mamaki ta fuskacin zuhudinsa.
7-      Kukansa :Shaikh Abbas Al-}ummiy ya kasance mai yawan kuka saboda tsoron Allah[T] da kuma kuka dangane da abubuwan da suka samu Ahlul-bayt[AS] idan mutum ya bibiyi tarihin rayuwarsa zai ga haka.wato idan yana sallah yana kuka,idan yana karatun Al}ur’ani yana kuka,idan yana biya addu’oi yana kuka da dai sauransu na ibadodi.wannan shima darasi ne garemu wato kuka a ayyuka na ibadodinmu,domin rashin kuka yana alamta bushewar zuciya,bushewar zuciya yana alamta yawan zunubi.
8-      Ala}arsa da ilimin Hadisi :Shaikh Abbas Al-}ummiy ya kasance a dukkan fannonin ilimi na addinin musulunci ba fannin da yafi so kamar fannin ilimin Hadisi,Saboda haka yazo a tarihinsa cewa yana girmama malaman Hadisi da kuma littaffan hadisi,kai wuce nan ma yazo akan cewa bai ]aukar littafin Hadisi face sai yana da alwala,haka nan idan zai biya littafin hadisi ya kan zauna cikin ladabi kuma yana fuskantar al-}ibla,bayan haka sai ya soma karanta shi.Akwai ma wani abun da ya ta~a faruwa ko ace ma karama,wani lokaci idanuwansa suna ciwo wanda takai hatta nazarin littafi bai iyayi.]ansa yake bada wannan labari,yace ya barshi a gida a wannan hali ya tafi ]aukar karatu,amma da ya dawo sai ya same shi yana karatu da rubutu,abin ya bashi mamaki ya tambayi mahaifin nasa ya idanuwansa ?sai yace masa ai yanzu ciwon ya wuce baki ]aya.sai ]ansa yace ya akayi ya magantu ?sai yace masa abin da nayi shine nayi alwala,na zauna na fuskanci al}ibla,na aza littafin Hadisi na  Kafi gaban idanuwa na,ikon Allah sai ciwon idanuwana suka gushe.Ance kuma tun daga lokacin bai sake yin ciwon idoba har ya bar duniya.Shima wannan darasi ne babba garemu wato na ala}antuwa da ilimin hadisi,domin idan mutum yana son yasan rayuwar Manzon Allah[S] da kuma Aimma na Ahlul-bayt[AS]sanka-sanka,watu zantukansu,ayyukansu,halayensu,to sai a hadisai.shi yasa maanar hadisi a is]ilahi bawai a luggace ba,shine fa]ar Ma’asum ko aikinsa ko tabbatarwarsa.
9-      Tasirin zantukansa da kuma rubutunsa :Shaikh Abbas Al-}ummiy ya kasance zantukansa suna da tasiri a zukatan mutane da kuma }wa}walensu.Lokacin da yake zaune a mash-had wa]ansu suka same shi,da bu}atar ya dunga gabatar masu da darasin Akla} a daren Alhamis da kuma jumma’a.sai ya amsa wannan bu}atar.shi wanda yake bada wannan labari kuma ]aya daga cikin mahalarta darasin yace,mu kanji tasirin darasin nasa tsawon mako.Haka nan a jawaban da ya kanyi a zaman makoki kamar na Imam Husain[AS] da kuma sayyida zahra [AS]da dai sauransu,su kan kasance masu tasirin gaske a zukatan mutane,har ma akwai wa]anda suka tafi akan cewa,a lokacinsa acikin khu]aba na Imam Husain[AS]to ba wanda ya kaishi tasiri a zukatan mutane wajen gabatar dasu,kuma mutane ne masu yawan gaske suke halartar wa]annan majalis nasa cikin har da manyan malamai da kuma mujtahidai,kai dama manyan maraji’ai,misali Ayatullahi shaikh Hairi,Ayatullahi Bujardi,da dai sauransu.kuma kamar yadda Allah ya azurta shi da tasiri a magana haka kuma ya azurta shi da tasiri a rubutu.mutum in ya karanci littafansa zai fahimci haka.kuma wa]annan abubuwa guda biyu wato tasiri a magana ko a rubutu baiwa ce ta Allah,amma mabu]insu shine iklasi,aiki da abunda mutum ya fa]a ko ya rubuta,sai kuma tawali’u wato mutum ta kasance mai }as}antar da kai ga Allah da kuma bayinsa.
10-   Ala}arsa da Aimma na Ahlul-bayt[AS] Shaikh Abbas Alkummiy ya kasance yana da gayar ala}a da Ahlul bayt[as],wato ala}a ta zahiri da ba]ini.A zahirance wajen koyi da ]abio’insu,ayyukansu da kuma zantukansu.A kuma ba]inance wajen sonsu shau}in saduwa dasu,girmama su,yawan tunaninsu dadai sauransu.Akwai ma wani babban malami a lokacin yana cewa duk wanda yake son ya haskaka da zantukan Ahlul-bayt to ya halarci majalisin karantarwa na Shaikh Abbas Al}ummiy.wanda wannan yana alamta saninsa da ahlul bayt da kuma asrar na hadisansu.
11-  Ala}arsa da littafai :Shaikh Abbas Al}ummiy ya kasance yana da ala}a da littafai,ta fuskoki dabam misali ta wajen nazarinsu ko rubuta su ko girmama su.ta yadda yazo a tarihinsa cewa babu ranar da bai muamala da littafi,wato ko dai ya ]auke shi ya karanta ko ya karantar dashi ko ya rubuta wani abu dashi,yazo akan cewa yatsun hannunsa saboda rubutu har kanta sukayi.
12-  Ala}arsa da littafin mafatihul-jinan :Shaikh Abbas Al}ummiy ya kasance mai aiki ga duk abubuwan da suka zo a mafatihu,wato duka salloli azkar da adduo’i da ziyarori da suka zo ya kasance yana yinsu.wato ba wai kawai ya rubuta littafin mafatihun bane,a’a ya tsayu da aikata abunda ya rubuta.Kuma in mutum ya dubi littafin mafatihu ba wai kawai jagorane ga mutum ga ayyuka na ibadodi da kuma munasabobi ba,A’a har ma jagorane ga mutum na sanin littafan Addu’oi,wato yadda yake kawo sunayen wasu littafai da ya ciranto wasu addu’oi aciki.Daga }arshe muna ro}on Allah ma]aukaki ya gafarta masa,ya }ara haskaka }abarinsa,ya }ara ]aukaka darajojonsa,ya kuma }ara kusanta shi da Manzon Allah[S] da kuma Ahlul-bayt[AS].
           
              

No comments:

Post a Comment