Watannin Rajab,Sha’aban da kuma Ramadan,watanni ne masu
gayar falaloli da kuma Asrar,domin a dukkan watanni 12 na musulunci babu
watannin da suke da ayyuka na Ibadodi kamar su.Shi yasa bayin Allah[T] suke
farin ciki da shau}in
zuwansu.Haka nan kuma suke ba}in ciki da ma kuka idan sun zo }arshe.wato saboda
yankewar da zasu samu na falaloli da darajoji da zau}iyyat da halawat da kuma
ma’anawiyyat na Ibadodin da ake samu a cikin watannin,wanda babu irin haka a
sauran watannin.
Saboda ma muhimman cin wa]annan watannin zamu ga wasu daga
cikin Malaman Madrasah ]in Ahlul Bayt,sun yi littafai khususan a kan su,misali
littafin Fadha’ilul Ash-huris-salasa na
Shaikh Sadu}.Saboda haka a nan in sha Allah,rubutun zai gudana ne akan wa]annan
ababe sune.
1-
Asrar na wa]annan watanni.
2-
Falalolin wa]annan watanni.
3-
Ibadodin wa]annan watanni.
4-
Munasabobin wa]annan watanni.
5-
Tsokaci kan kiyaye muhimman lokuta.
1-Asrar
na wa]annan watanni:Idan mutum yayi binciken ruwayoyi na hadisai dabam dabam da
suka zo dangane da falaloli da darajoji
na watannin Rajab,Sha’aban da kuma Ramadan,da kuma shaidar da zasu yiwa mutumin
da ya girmama su a wannan gida na duniya.wannan kawai ya isa ya nuna ma mutum
cewa lalle wa]annan watannin suna da wani Asrar gaibiyya a wajen Allah Ta’ala.Misali
wannan Hadisi wanda aka samo daga Manzon Allah[S]
yace, “Duk wanda ya san daraja da matsayin watannin Rajab,Sha’aban da kuma
watan Ramadan,to wa]annan
watanni zasu yi masa shaida ranar }iyama,cewa ya darajta su da kuma girmama
su.Sai mai kira yayi kira,ya Rajab,ya Sha’aban,ya watan Ramadan,yaya wannan
bawa yayi aiki a cikin ku, ya kuma ]a’ar sa take ga ubangiji? Sai Rajab,
Sha’aban da kuma watan Ramadan,suce ya ubangijinmu a cikin mu bai yi wani abu
ba face neman yi maka ]a’a da kuma neman falalar ka, kuma yayi iya }o}arin sa
wajen neman yardarka da kuma neman sonka..Sai Allah Ta’ala yace ma Mala’ikun da
ya wakilta ga wa]annan watanni:mi za kuce dangane da wannan shaida da suka yi
ga wannan bawa? Sai suce ya Ubangijinmu Rajab da Sha’aban da watan Ramadan sun
yi gaskiya,wannan bawa ya kasance a wa]annan watanni yana mai yin }o}ari wajen
neman yardar ka da kuma yi maka ]a’a.kuma ya kasance ya na mai farinciki da
murna ga wa]annan watannin,ya na fatar rahamar ka da kuma }aunar afuwarka da gafararka……” Hadisin na da
tsawo ga mai bu}atar ganin Hadisin ya na iya duba Biharul Anwar juz’i na 94 ko
littafin Zadul ma’ad dukka littafan biyu
da aka ambata na Allama Maj-lisi ne.Dawowa ga cikon wancan hadisin, daga }arshe mala’ikun zasu ce Madalla da wannan
bawa,A lokacin sai Allah Ta’ala ya ba da umarni akai wannan bawa Aljanna.wato
saboda girmamawar sa ga wa]annan watanni da kuma tsayuwa da Ibadodi da kuma
ayyukan ]a’a da yayi a cikin su.Saboda haka wannan shaida da wa]annan watanni
zasu yi wa bawa,koma bayan sauran watanni ya nuna lalle suna da wani Asrar na
musamman a wajen Allah[T].Haka kuma daga cikin
abubuwan da suke nuna Asrar na wa]annan watanni,misali ruwayoyin addu’oi na bankwana da watan Ramadan.Domin
idan mutum ya bincika zai ga cewa a duk watanni 12 na Musulunci,babu wani wata
da aka samu ruwayoyi daga Manzon Allah[S] da kuma
Aimma[AS] na bankwana dashi da kuma umarnin yin haka face watan Ramadan.Idan
mutum ya biya addu’oi na bankwanar misali wadda aka ruwaito daga Imam Zainul
Abidin[AS] kuma lokacin da yake biyawa ace zuciyarsa na halarce,tabbas zai samu
tasirin haka a ruhinsa.Domin zai ga yadda Imam Zainul Abidin[AS] yake Magana da
sallama da bankwana da watan Ramadan da kuma jin zafin rabuwa dashi,kamar kace
mutum ne yake gabansa yake bankwana dashi da kuma nuna damuwa na rabuwa dashi.
2-Falalolin wa]annan watannin:Idan
mutum ya ]auki wa]annan watanni ]aya bayan ]aya zai ga ko wane ]aya daga ciki,
akwai falaloli da suka zo dangane dashi.A-Watan Rajab ya na ]aya daga cikin
watanni guda hu]u masu al-farma,kuma Allah Ta’ala ya hana zaluntar kai a
cikinsu,yazo akan cewa hatta lokacin jahiliyya sun kasance suna girmama
watan,kuma wata ne na Allah Ta’ala,Sha’ban kuma wata na Manzon Allah[S]watan Ramadan kuma wata na Al’ummarsa.Ga
wasu Hadisai daga cikin falalar watan Rajab.An samo daga Imam Kazim[AS] yace,
“Rajab wani kogi ne Acikin aljanna,farinsa yafi nono,za}insa kuma yafi zuma;duk
wanda ya azumci rana guda daga cikinsa,To Allah Ta’ala zai shayar dashi daga
wannan kogi”.Haka nan a wani Hadisi da aka samo daga Manzon Allah[S] yace, “Duk wanda ya azumci rana guda
acikin watan Rajab,to zai samu yardar Allah[T] da kuma nisanta daga
fushinsa,kuma za’a rufe masa }ofa
daga cikin }ofofin wuta”.Wani hadisi har wala yau daga Imam Kazim[AS]
yace, “Wanda ya azumci rana guda a cikin watan Rajab,to za’a nisanta shi daga
wuta kimanin tafiyar shekara guda,wanda ko ya azumce shi kwana 3,to za a sanya shi a aljanna”.Wata rana
wani tsoho yazo wajen Manzon Allah[S]yace masa:Ya
Manzon Allah,lalle bani da }arfin
azumtar dukkannin kwanukan Rajab,sai Manzon Allah yace masa;ka azumci farkon
watan,tsakiyarsa da kuma }arshensa,to za a baka lada kamar wanda ya azumci
dukkan watan.Haka nan a wani Hadisi da aka samo daga Imam Sadi}[AS] yace:Ranar Al }iyama mai kira zai yi kira
a }ar}ashin Al-arshi,ina Rajabawa?sai wa]ansu mutane su tashi fuskokinsu suna
haske da kuma haskakawa,a kawukansu akwai kambi na mulki wanda aka yi masa ado
da lu’ulu’u da ya}uti,kuma ko wane daga cikin wa]annan Rajabawa akwai mala’ika
dubu a gefensa na dama da kuma dubu a gefensa na hagu.Mala’ikun suna ce
masa,farin ciki ya tabbata gare ka ya kai wannan bawan Allah,sai kira yazo daga
wajen Allah yace:Bayina na rantse da buya ta zan girmama makomarku kuma zan nunnuka
sakamakonku,kunyi azumi saboda ni a cikin watan da na girmama darajarsa,sai
Allah yace Mala’ikuna ku shigar da bayina Aljanna.Da dai sauran hadisai masu
yawa da suka zo dangane da falalar watan Rajab.B-Falalar watan Sha’aban:Manzon
Allah[S] ya kasance ya na cewa
Sha’aban wata na ne,duk wanda ya azumci yini daga cikin watan to aljanna ta
wajaba gareshi.An ruwaito daga Imam Sadik[AS]yace Imam Sajjad[AS]ya kasance idan
watan sha’aban ya kama yakan tara sahabbansa yace: “Ya sahabbai na ko kun san
wannan watan sha’aban ne?Manzon Allah ya kasance yana cewa sha’aban wata na
ne,saboda haka ku azumci wannan watan saboda so ga Annabinku da kuma kusanci ga
ubangijinku.Ina rantsuwa da wanda raina yake hannunshi,ha}i}a naji baba na Husain
yana cewa,yaji daga babansaAmirul muminin yana cewa,duk wanda ya azumci
sha’aban saboda so ga Manzon Allah da kuma neman kusanci zuwa ga Allah
ma]aukaki,to Allah zai so shi kuma zai kusantar dashi zuwa ga darajojinsa.
Ranar al}iyama kuma zai wajabtar da aljanna gareshi.” Haka nan an ruwaito daga
Safwan Jammal yace Imam Sadi} yace man: “Ku kwa]aitar da wanda suke kusa daku
dangane da azumin Sha’aban.”Sai nace masa in zamo fansa gareka,Akwai wani abune
akan haka?sai Imam Sadi}[AS] yace:Lalle Manzon Allah ya
kasance idan yaga watan sha’aban,yakan sa mai kira yayi kira a cikin madina
yace:yaku mutanen madina ni ]an sa}on Manzon Allah ne zuwa gareku,yace sha’aban
wata na ne,Alla yayi rahama ga wanda ya taimakeni a wata na.sai Imam Sadi} ya
ci gaba da ce masa;Lalle Amirul muminin ya kasance yana cewa:Azumin Sha’aban
bai ta~a ku~uce min ba tun lokacin da
naji mai kiran Manzon Allah yana kira a watan sha’aban.kuma in Allah ya yarda
azumin sha’aban ba zai ta~a ku~uce min ba matu}ar ina da rai.”wannan kenan a
ta}aice dangane da falalar watan sha’aban.C-Watan Ramadan:wata ne wanda yake da
falaloli da darajoji fiye da sauran watanni,kamar yadda yazo a ruwayoyi na
Hadisai,wata ne wanda a cikinsa Allah Ta’ala yake ‘yanta bayinsa daga wuta,fiye
da yadda yake ‘yantawa a sauran watanni.Wata ne wanda Allah Ta’ala kan nunnuka
ayyukan bayinsa a ciki.Wata wanda acikin sa ake bu]e }ofofin rahama,}ofofin
Aljanna,ake kuma kulle }ofofin wuta.Wata ne wanda a cikinsa ake ]aure
Shai]anu.Wata ne wanda acikinsa Allah Ta’ala ke gafarta ma bayinsa zunubansu
baki ]aya.Wata ne wanda a cikinsa yake ]aukaka darajojin bayinsa.Wata ne wanda
a cikinsa akwai wani dare wanda ibada acikinsa,tafi ibadar wata dubu,wato dare
lailatul }adri.Wata ne wanda a cikinsa Allah Ta’ala yake tsarkake bayinsa ya
kusanta su gareshi.Wata ne na samun Ta}wa fiye da sauran watanni.A ta}aice dai
wata ne wanda yake cike da tarin alkhairai da kuma albarkoki wa]anda ba za iya lissafa su ba.kuma watan Ramadan shine shugaban watanni.
3-Ibadodin wadannan
watanni:Kamar yadda aka ambata a baya wa]annan watanni
ukku,suna da ayyuka na ibadodi masu yawa fiye da sauran watanni.Ayyukan ibadodi
da ake aikatwa cikin watannin sun kasu kashi biyu.Akwai ayyukan ibadodi na Amma
da kuma khassa,ibododi na amma cikin watannin sune wa]anda mutum zai kwashe watanni ukku
yana aikatawa misali sallolin nafila na ko wane dare,idan mutum ya duba
littafin Dhiya’us-salihin ko Baladul Amin ko littafin I}bal sun kawo wa]annan salloli,wanda mutum zai soma
tun daga daren farko na watan Rajab har
ya zuwa daren }arshe
na watan Ramadan,yana da muhimmanci mutum yayi iyaka iyawarsa yaga cewa wa]annan salloli
na watannin ukku bai rasa ko ]aya daga ciki ba.Daga
cikin Ayyukan da ake aikatawa a wa]annan
watannin baki ]aya,akwai
wasu surori na Al}ur’ani
da Azkar da ake son biyawa ko wace rana,mai son ganin waannan surori da Azkar
yana iya duba littafin mafatihul Jinan Babi na biyu,a ayyuka na 20 na }ismil Awwal na
ayyukan wata Rajab.Haka nan akwai wasu salloli da ake son yi a dararen 13,14,15
na wa]annan
watanni guda ukku,mutum na iya duba }ismus sani na ayyukan watan Rajab,a ayyukan daren 13,za
a ga yadda sallar take da kuma abin da ake biyawa.Sai kuma ayyukan ibadodi na
khassa,sune ibadodin da ake son yi a muhimmam kwanuka acikin wa]annan watanni
ukku.Misali daren farko da ranar farko na watan Rajab,ko 13,14,15,27 ]in shi.ko
kuma misali a watan Sha’aban shima daren farko da ranar farko,ko daren 15
]insa.Misali kuma na watan Ramadan daren farkonsa da kuma ranar farkon sa,ko
13,14,15,ko kuma daren 19,21 da 23.Wa]annan sune misalan wasu daga cikin
ayyukan ibadodi khassa na watanni ukkun.kuma ana son mutum ya tsayu da wa]annan
ibadodi na amma da kuma khassa,wato wa]anda ake yi kullum a cikin watannin da
kuma wa]anda ake yi a muhimman kwanuka na watannin.
4-Munasabobin
wa]annan watannin:Wato
muhimmam ababen da suka auku na Tarihi a cikin watannin ko kuma Haihuwa ko
Rasuwa na ]aya daga cikin Aimma na Ahlul Bayt[AS]
da dai sauransu.1-Munasabobin watan Rajab:1 ga watan Rajab Haihuwar Imam Ba}ir[AS]. 3 ga watan Rajab Shahadar Imam Ali
al-Hadi[AS]. 10 ga watan Rajab Haihuwar Imam Jawad[AS]. 13 ga wtan Rajab
Haihuwar Imam Ali[AS]. 15 ga watan Rajab Wafatin Sayyida Zainab[AS].25 ga watan
Rajab Shahadar Imam Musa al-Kazim[AS]. 26 ga watan Rajab Wafatin Sayyiduna Abu
Talib[AS]. 27 ga watan Rajab Ranar Mab’as wato ranar da aka aiko ma Manzon
Allah[S] da sa}o.29
ga watan Rajab Wafatin Ummul muminin Khadija.Sai kuma munasabobin watan
Sha’aban:3 ga watan Sha’aban Haihuwar Imam Husain[AS].
4 ga watan Sha’aban Haihuwar Sayyid Abul-Fadhal Abbas[AS]. 5 ga watan Sh’aban
Haihuwar Imam Zainul Abidin[AS. 15 ga watan Sha’aban Haihuwar Imam Mahdi[AF].Sai
kuma Munasabobin watan Ramadan: 15 ga watan Ramadan Haihuwar Imam Hassan[AS].
17 ga watan Ramadan ya}in
Badar ya kasance. 21 ga watan Ramadan Shahadar
Imam Ali[AS].Wa]annan
sune wasu daga cikin muhimmman munasabobin wa]annan watanni,sai dai wani
Tambihi anan shine ana iya samun sa~ani na ruwayoyi,a irin wa]annan kwanuka na
wilada ko wafatin ]aya daga cikin Ma’asumin[AS].Wanda
aka kawo nan wa]anda
suka fi shahara ne a tsakanin Malaman Tarihi.
5-Tsokaci kan kiyaye muhimman
lokuta:Yana da gayar muhimmanci mutum ya kasance yana kiyaye muhimman
lokuttan wa]annan watanni 12 na
Musulunci.Saboda wa]ansu lokuta akwai ayyuka na ibadodi da ake son aikatawa a
cikin su,idan mutum ba yana kiyayewa ba sai irin wa]annan ayyuka su dunga
ku~uce ma mutum,ko kuma ya dunga abin da ake cema fargad daji,wato bayan ranar
ko daren da ake son aikata wani aiki na ibada
sai mutum yaji.alhali kuma ga lokacin ya wuce,sai mutum ya kasance yayi
hasarar ladar aikata ayyukan.Ko kuma wata munasaba ta gitto na wilada ko wafatin
]aya daga cikin Aimma na Ahlul Bayt[AS],in mutum bai kiyayewa sai
ta gitto ta wuce mutum bai sani ba,ga shi ko yazo daga Imam Sadi}[AS] yace, “Masoyanmu sune wa]anda suke murna da
murnanmu,suke kuma ba}in ciki da ba}in cikinmu.”Kuma kiyaye wa]annan munasabobi
yana daga cikin hanyoyin kyautata ala}ar mutum da Manzon Allah[S] da kuma Ahlul Bayt[AS].
No comments:
Post a Comment