Thursday 9 May 2013

TAMBIHI


Wannan shafi na tambihi na maraba da ziyartarsa.
                                                          GABATARWA.
Da sunan Allah mai Rahma mai jin }ai, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah{T} ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta kuma cikamakon Annabawa,Annabi Muhammad da kuma alayensa tsarkaka.                                                                                                                                                                Bayan haka wannan shafi na Tambihi, rubuce rubuce ne da suka gabata a filin tambihi na jaridar Almizan.Filine da ake gabatar da Darussa  na wasu fannoni na ilimin Addinin Musulunci,kamar ilimin Akla},Fi}hu,Tarihi da kuma rayuwar Manzon Allah[SAAW] da Ahlul-Bayt[AS] da dai sauran Maudu’oi dabam-dabam. Saboda bu}ata da wasu sashen ‘yan uwa suka yi, na cewa rubutuk-tukan da ake gabatarwa da kuma wa]anda suka gabata a tattara su a bu]e masu shafi a Internet, domin tunatarwa da kuma fa’idantarwa da amfanuwa ga sauran mutane.                                                                                     Akan asasin haka aka bu]e wannan shafi .Kuma a halin yanzu yana da ~angarori guda hu]u sune:
Bangare na farko:DARUSSA DAGA RAYUWAR MANZON ALLAH {S.A.A.W} DA KUMA AHLUL-BAYT {AS}.Sune:
1.       Darussa daga rayuwar Manzon Allah [S.A.A.W].
2.       Darussa daga rayuwar Ummul-A’imma Fa]ima [AS].
3.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali [AS].
4.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan [AS].
5.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Husain [AS].
6.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali zainul Abidin [AS].
7.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Muhammad Al-Ba}ir [AS].
8.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Ja’afarus-Sadi} [AS].
9.       Darussa 12 daga rayuwar Imam Musa-Al-kazim [AS].
10.   Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali Arridha [AS].
11.   Darussa 12 daga rayuwar Imam MuhammadAl- Jawad [AS].
12.   Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali Al-Hadi [AS].
13.   Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan Al-askari [AS].
14.   Darussa 12 daga rayuwar ImamAl- Mahdi [AS].
Bangare na biyu:DARUSSAN  AKHLA{.Sune:
1.       Darasi na 1 Bayani kan fannin ilimin Akhla}.
2.       Darasi na 2 Bayani kan muhimmancin ilimin Akhla}.
3.       Darasi na 3 Bayani kan hanyoyin samun kyawawan Akla}.
4.       Darasi na 4 Bayani kan Ruhin mutum.
5.       Darasi na 5 Bayani kan Tazkiyatun-nafs.
Bangare na ukku:DARUSSAN FI{HU.Sune:
1.       Darasi na 1 Bayani kan fannin ilimin fi}hu.
2.       Darasi na 2 Bayani kan Ala}ar limaman mazhabobin Ahlus Sunna da Imaman Ahlulbayt [AS].
3.       Darasi na 3 Bayani kan Azumi [1].
4.       Darasi na 4 Bayani kan Azumi [2].
5.       Darasi na 5 Bayani kan Ijtihad da Ta}lid.
Bangare na hu]u :DARUSSA DAGA MAUDU’OI, DABAM-DABAM.Sune :
1.       Alamomin bayyanar Imam Mahdi [AF].
2.       Rubuce-rubucen shehu [an Fodio akan Imam Mahdi [AF].
3.       Tarihi da kuma Darussa daga rayuwar sayyida Zainab [AS].
4.       Tarihi da rayuwar sayyid Abul-fadhal Abbas [AS].
5.       Ranar ghadir a mahangar shi’a da sunna.
6.       Ashura a mahangar shi’a da sunna.
7.       Imama a mahangar  shi’a da sunna.
8.       Gudunmawar mata a wa}i’ar  karbala.
9.       Arba’in ]in Imam Husain [AS].
10.   Darussa 12 daga rayuwar Imam Khumain [KS].
11.   Tarihi da rayuwar shahid Ayatullah sayyid Muhammad Ba}ir  sadr.
12.   Shekaru 60 masu albarka na Sayyid Zakzaky [H].             
13.   Darussa 12 daga rayuwar Sayyid Zakzaky [H].
14.   Ruhin Azumi da kuma Ayyukan watan Ramadan.
15.   Ban kwana da watan Ramadan 1432 A.H.
16.   Ban kwana da watan Ramadan 1433 A.H.
17.   Hanyoyin samun Ta}wa.                                                                                                                                        Kuma Insha Allah za’a dunga samun }ari a wa]annan ~angarori guda hu]u,lokaci bayan lokaci.Da fatan abubuwan da zamu karanta, Allah {T} ya amfanar damu,ya kuma bamu ikon aiki dasu. Allah {T} yasa su kasance haske gare mu duniya da lahira. Allah {T} ya kiyayemu kada su kasance duhu da nauyi akan mu gobe }iyamah.                                                                                                                   Daga }arshe duk wanda yake da wata shawara, ko neman }arin bayani, ko kuma tambaya  kan abubuwan da ya karanta a wannan shafi na tambihi.To  yana iya rubutowa ta wannan adreshi na emel  TAMBIHI@GMAIL.COM.
MUHAMMAD SULAIMAN KADUNA.                                                                                                       WAS-SALATU WAS-SALAMU  ALA  MUHAMMADIN  WA  ALIHI[  [AYYIBINA[  [AHIRIN.                                                                                           

RUHI DA KUMA ASRAR NA SALLAH.


Sallah tana da ~angarori guda biyu,~angaren ruhinta,wanda shine ba]ininta da kuma ~angaren jikinta,wanda shine zahirinta.Malaman Irfan ko Tasawwuf sun yi rubuce-rubuce da kuma bayanai dangane  da Ruhin sallah da kuma Asrar ]inta.Kamar yadda Malaman Fi}hu suka yi rubuce-rubuce da kuma bayanai dangane da zahirinta.

ASRAR DA IBADODI NA WATANNIN RAJAB,SHA’ABAN,RAMADAN.


Watannin Rajab,Sha’aban da kuma Ramadan,watanni ne masu gayar falaloli da kuma Asrar,domin a dukkan watanni 12 na musulunci babu watannin da suke da ayyuka na Ibadodi kamar su.Shi yasa bayin Allah[T] suke farin ciki da shau}in zuwansu.Haka nan kuma suke ba}in ciki da ma kuka idan sun zo }arshe.wato saboda yankewar da zasu samu na falaloli da darajoji da zau}iyyat da halawat da kuma ma’anawiyyat na Ibadodin da ake samu a cikin watannin,wanda babu irin haka a sauran watannin.

ASALIN SHI’A DA ABUBUWAN DA AKA JINGINA MATA.


                Asalin kafuwar shi’a da abubuwan da aka jingina mata yana ]aya daga cikin ababen da Malamai dabam-dabam na shi’a,suka yi rubuce-rubuce da bayanai dabam-dabam akai,saboda haka akwai littafai masu yawa a wannan fagen.

Darasin fikhu {7}.


A darasin daya gabata bayani ya gudana akan shakka a rakao’in sallah da kuma raka’ar ihtiya]i.An yi bayani akan cewa shakka a sallah ta kasu kashi ukku.1-shakka a rakao’in sallar.2-shakka a asalin yin sallar.3-shakka a ayyukan sallar.Na farko bayanin sa ya gabata,yanzu sai bayanin na biyu dana ukku.Bayan haka kuma sai bayani kan sujudi sahawi da kuma mas’aloli da suke da ala}a dasu.

Darasin Akhlak {7}.


                A darasin daya gabata wato darasi na 6 bayani ya gudana akan {AL’B wato zuciya,an kawo abubuwa guda 9 da suke da ala}a da ita,amma an tsaya ana shidda,sauran aka ce sai darasi na gaba insha- Allah.Sabada haka a yanzu za a tashi ana 7-Magance bushewar zuciya:Malaman irfan ko tasawwuf sunyi bayani dangane hanyoyin maganin bushewar zuciya

Tuesday 7 May 2013

Tarihi Da Kuma Darussa Daga Rayuwar Marubucin Mafatihul Jinan.


Bayani ko rubutu kan tarihi da kuma rayuwar Marubucin littafin Mafatihul-Jinan,wato shaikh Abbas Al-}ummiy wani fage ne mai fa]in gaske.Kuma sanin tarihinsa da kuma rayuwarsa yana da muhimmancin gaske,saboda zai yi wahala ka samu wani mabiyin Ahlul-bayt wanda bai da wannan littafi nasa na Mafatihul jinan,wani gidan ma kana iya samun mutum shi da iyalinsa kusan kowa nada nashi mafatihun

Sunday 10 February 2013

Bayani kan shakka na Sallah.


A darasin da ya gabata,wato darasi na biyar,an kammala shinfi]a da kuma gabatarwa,aka yi bayanin cewa a darasi na gaba in sha Allah, za a shiga babin farko wato babin tsarki.To kasantuwar babobin fi}hu suna da yawa,wa]ansu fu}aha sun tafi a kan babobi hamsin ne,wato tun daga babin tsarki zuwa babin diyyat.

Bayani kan Ijtihadi da Taklid.


Kamar yadda aka yi bayani a darasi na 3, cewa kasantuwar zuwan watan Ramadan gabatarwa da kuma shimafi]a da ake yi na wannan darasi na Fi}ihu za a dakatar a shiga babin Azumi, in ya so bayan watan Ramadan sai a kammala gabatarwar da kuma shimfi]a, bayan haka kuma sai a shiga babin farko, wato babin tsarki, bayan shi kuma babin Salla, da dai sauran babobi, insha Allahu daidai gwargwadon iko.

Bayani kan fannin ilimin Fikhu.


Isha Allah saboda muhimmanci da kuma bu}ata daga wasu ’yan uwa na gabatar da darasi kan Fi}hu, shigen yadda ake gabatar da darussa 12 daga rayuwar A’imma (AS), ko kuma darasi kan A}lak ta ~angare na, na yi tunani amsa wannan bu}ata domin  gabatar da shi wannan darasin na Fi}hu gwargwadon iko.

Bayani kan Azumi 2.


Kamar yadda ya gabata a darasin baya a wannan babi na Azumi, wasu fasaloli guda hu]u. Yanzu za a tashi a fasali na biyar. Bayani dangane da wanda ya yi abin da yake karya Azumi. a darasin da ya gabata a fasali na hu]u, in za a duba, an kawo abubuwa guda 10, wanda ya wajaba mai Azumi ya kame daga gare su. To shi wannan fasali na biyar, yana bayani dangane da hukuncin mai Azumin da ya aikata ]aya daga cikin wa]annan ababe guda 10, ko kuma wasu daga cikinsu.

Bayani kan Azumi 1.


Kamar yadda aka ce a darasin da ya gabata, cewa insha Allah (T) a wannan darasi za a kammala shimfi]a da kuma gabatarwa, da ma shiga cikin babobin Fi}hu. To kasantuwar mun shiga cikin watan Ramadan ,ya zamanto zai yi kyau da kuma muhimmanci mu shiga cikin babobin fi}hun, wato babin Azumi, in ya so bayan kammala babin Azumin sai a kammala ita waccan shimfi]a da kuma gabatarwa da shiga babin farko, wato babin tsarki. Saboda haka wannan darasi zai gudana ne a babin Azumi. Kuma saboda ya yi sau}i wajen gabatar da shi, an yi masa fasali 12 ne. Ga yadda suke.

Bayani kan alakar limaman mazhabobin Ahlus-Sunnah da A’imma [AS].


Kamar yadda aka ambata a darasin da ya gabata cewa, wannan darasi na Fi}hu insha Allah, za a dinga gabatar da shi a bisa Usulubi na Fi}hul-Mu}arana ne, wato mu}arana tsakanin wa]annan Mazhabobi guda hu]u na Ahlus-sunnah; Hannafiyya, Malikiyyah, Shafi'iyya, Hanbaliyya. A ]aya gefen kuma da Ja'afariyya, amma za a }arfafa a Fi}hun Ja'afariyya ne.

Saturday 9 February 2013

Tarihi da rayuwar Shahid Ayyatullahi Sayyid Muhammad Ba}ir Sadr


Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Jimadal Ula, 23 gare shi ne a shekara ta 1400 Hijiriyyah, a miladiyyah kuma 9/4/1980 shahadar Ayatullahi Sayyid Muhammad Ba}ir Sadr, ta kasance, a daidai wannan lokaci akan yi tarurruka, musamman a Ira}i da kuma Iran, domin tunawa da shi da kuma shahadarsa, wanda a irin wa]annan tarurruka akan tunatar da juna dangane da tarihinsa, da kuma wasu ~angarori na rayuwarsa, da nufin su kasance darussa ga mahalarta da kuma wa]anda za su ji ko su gani daga baya.

TARIHI DA KUMA RAYUWAR ABUL- FADHAL ABBAS {AS}.


Sayyid  Abul-Fadhal Abbas[AS] an haife shi a Madina,ranar 4 ga watan sha’aban,shekara ta 26 bayan hijira,Sayyid Abbas  a cikin ‘ya’yan Imam Ali[as] maza baya ga Imam Hassan da Imam Husain[AS] ba wanda ya kai shi daraja.

TARIHI DA KUMA DARUSSA DAGA RAYUWAR SAYYIDA ZAINAB [AS].


Rubutu ko bayani dangane da sayyida Zainab[AS] fage ne mai fa]in gaske.Kuma Malamai da dama sun rubuta littafai,game da tarihinta da kuma rayuwar ta,misalin wasu daga cikin littafan sune,Zainabul-Kubra na shaikh Ja’afar Najdiy.kasa-isus-zainabiyya na sayyid Nurud-din.

ALHAMDU LILLAH SHEKARU 60 MASU ALBARKA NA SAYYID ZAKZAKY [H].


Alhamdulillah,kamar yadda muka sani,wannan wata da muke ciki,wato na sha’aban 15 gare shi.Sayyid Ibrahim Zakzaky [H] ya cika shekaru 60 cur-cur a duniya.Saboda haka naga zai yi kyau da kuma muhimmanci,akawo wasu darussa na jarabawowi da nasarori dake cikin wa]annan shekaru masu albarka,da nufin su kasance DARASI a gare mu

Ruhin Azumi da kuma ayyukan watan Ramadan


Azumi kamar sauran ibadodi yana da ~angarori guda biyu,~angaren ruhi,wanda shine ba]ininsa,da kuma ~angaren jiki,wanda shine zahirinsa.Malaman irfani ko tasawwuf sunyi rubuce-rubuce da kuma bayanai dangane da ruhin azumi kamar yadda malaman fi}hu sukayi rubuce-rubuce da bayanai dangane da zahirinsa.Misali,sharu]]an azumi,abubuwan dake inganta shi,ko kuma abubuwan dake ~ata shi,da dai sauransu.

Rubuce-rubucen Shehu [an Fodio a kan Imam Mahdi AF


Watan sha’aban da muka fita,kamar yadda aka sani,a cikinsa ne aka haifi Imam Mahdi [AF],saboda haka ne mabiya Ahlulbayt [AS] a sassan duniya daban daban ke gabatar da tarurruka,domin tunatar da juna dangane da ~angarori daban daban da suke da ala}a da Imam Mahdi [AF].misali,wiladarsa,gaiba ]insa,shaksiyya ]insa,alamomin bayyanarsa,bayanai da rubuce rubuce na malaman madrasah ]in Ahlus sunna dangane dashi,da dai sauransu

RANAR GHADIR A MAHANGAR AHLULBAIT [AS] DA AHLUS SUNNA.


Al-hamdu-lillah,kasantuwar wannan wata da muke ciki,wato na zul hijja,a cikin sa ne,kamar yadda aka sani,18 gare shi,shekara ta goma bayan hijira,wannan munasaba ta ghadir ta kasance.Kuma tun daga wancan lokaci har ya zuwa yau dinmu wato yau shekara sama da dubu da dari hudu,mabiya Ahlulbaiti [AS] a duk shekara a kuma sassan duniya dabam dabam suke raya wannan rana ta ghadir ta fuskoki daban daban.

Imama a mahangar Ahlul Baiti (AS) da Ahlus Sunna.


Alhamdulillah, kasantuwar wannan wata da muke ciki, wato na Zulhijjah cikinsa ne 18 gare shi wato Ranar Ghadir Manzon Allah (S) ya bayyana wa wannan al’umma wa]anda za su kasance Imamai, wato Khalifofi a bayansa, bayyanawa wadda za a siffata ta a matsayin bayyanawa RASMIYYAN, wato OFFICIALY. Saboda haka mabiya Ahlul Baiti (AS) a sassan duniya daban-daban suke gabatar da tarurruka da kuma rubuce-rubuce domin tunatar da juna dangane da wannan rana ta Ghadir.

Hanyoyin samun ta}awa a Ramadan


Kasantuwar wannan wata mai albarka, wato watan Ramadan, wanda Allah (T) ya azurta mu da azumtar sa. Daga cikin hikima da kuma manufa na wajabta mana Azumi a cikinsa, shi ne domin mu samu Ta}awa, kamar yadda Allah (T) yake fa]i a cikin Al}ur’ani mai girma, a suratul Ba}ara aya ta 183. “Ya ku wa]anda suka yi imani, an wajabta maku azumi, kamar yadda aka wajabta shi ga wa]anda suke gabaninku, domin ku samu ta}awa”.

Gudummawar mata a wa}i’ar Karbala.


Kasantuwar wannan wata da muke ciki wato Muharram,wata ne na zaman makoki wanda akan tunatar da juna dangane wannan wa}i’a ta karbala,misali abubuwan da suka auku gabanin Ashura da abubuwan da suka auku ranar Ashura,da kuma abubuwan da suka biyo bayan Ashura da kuma darussan da zamu koya daga wannan wa}i’ar ta Ashura dadai sauran ~angarori dake da ala}a da wannan al’amarin na Ashura,

Darussa 12 daga rayuwar Sayyid Zakzaky (H)


Kasantuwar wannan wata da muke ciki, wato Sha’aban, a cikinsa ne aka haifi Malaminmu, kuma Jagoranmu a wannan gwagwarmaya ta tabbatar da addini, wato Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), a wannan munasabar ta cika shekaru 61 a duniya.

Darussa 12 daga rayuwar Imam Khumaini [KS]


Watan jiya,wato watan jimada sani shine wata wanda aka haifi Imam khumaini a cikinsa,domin an haife shine ran 20 ga watan jimada sani hijira na da shekara 1321,kuma ranar haihuwarsa tayi muwafa}a da ranar  haihuwar shugaban mataye baki ]aya,wato ‘yar Manzon Allah [S],sayyidah fa]ima [SA].

Bankwana da watan Ramadan


Inna Lillahi Wa Inna Ilahi Raji’un! Na rabuwa da kuma tafiyar wannan babban ba}o mai girma da kuma daraja da ya ba}unce mu, wato watan Ramadan. Wannan wata na Ramadan, wata ne wanda gabanin zuwan sa bayin Allah (T) ke shau}insa (begensa) da kuma murna da farin ciki.

Bankwana da watan Ramadan (1) 1432 A.H


Inna-lillah-wa-inna-  ilaihi- rajiun, na tafiya da kuma rabuwa da wannan babban ba}o mai girma da kuma daraja da ya ba}uncemu, wato watan ramadan. Domin idan mutum ya bincika zai ga cewa a duk watanni 12 da ake da su a musulinci, babu wani wata da aka samu ruwayoyi daga Manzon Allah (S)da kuma A’imma na ahlul-baiti (AS) na bankwana  da shi da kuma umarni da yin haka  face watan ramadan, wanda wannan ka ]ai ya isa ya nuna falala da darajan wannan watan.

ASHURA A MAHANGAR AHLUL-BAIT [AS] DA AHLUS- SUNNAH.


Da farko dai   watan  muharram, da waki’ar Ashura ta auku,wata ne na juyayi da ba}in ciki dama kuka,a mahanga ta Ahlul bait,tun daga farkon watan har }arshen sa.kuma ko da a munasabobi na wiladar Aimma in mutum ya bincika zai ga babu wani imami daga cikin Aimma wanda wiladar sa tazo a cikin watan muharram,wato akasin kamar yadda a shi kuma watan shaaban babu wani Imami daga cikin Aimma wanda wafatin sa yazo aciki.sai dai wiladar su.

Monday 4 February 2013

Arba’in ]in Imam Husain [AS]


Ranar arba’in ]in Imam Husain [AS] rana ce wadda take da muhimmanci,musamman ma  ga mabiya Ahlul bayt [AS],kuma kiyaye ranar yana daga cikin alamomin mumini,kamar yadda haka yazo daga Imam Hassan Al-askari [AS],in da yace, “Alamomin mumini [wato ]an shi’a] guda biyar ne.

Alamomin Bayyanan Imam Mahdi[AF] da kuma Ladubban Zamanin Gaiba.


Alamomin bayyanar Imam Al-mahdi [AF] za’a iya kasa su kashi uku.Na farko akwai alamomin da zasu gudana kafin bayyanarsa,Na biyu akwai abubuwan da zasu gudana  gaf da bayyanarsa,misali shekarar da zai bayyana.Na ukku akwai alamomin da zasu gudana lokacin da ya bayyana.Kuma duk bayanan wa]annan alamomin sun gangaro ne daga Manzon Allah [S] da kuma A’imma na Ahlul-bayt [AS].

Sunday 3 February 2013

Hanyoyin samun kyawawan ]abi’u da kuma tsarkaka daga munanan ]abi’u.


Kamar yadda ya gabata a darasi na Akhla}  na  biyu, da yake an samu lokaci mai tsawo ba’a gabatar da wannan darasi na Akhla}  ba,dalili ko shine,kamar yadda aka ce a baya,lokaci  bayan  lokaci za’a ri}a samun yankewar darasin,

Bayani kan tazkiyatu-Nafs.


A darasin da ya gabata, an tsaya ne a bayani dangane da muhimmancin Tazkiyatu Nafs (tsarkake rai). Amma gabanin nan an yi bayanai a kan ma’anar Akhla}, cewa shi ne, “sura ba ]iniyya ta mutum”. Wato siffa ta ba]ini (~oye) ta mutum. Domin shi mutum yana da ~angarorin guda biyu a halittarsa.

Bayani kan Ruhin mutum.


Darussa guda uku da suka gabata na Akhla}, dukkansu suna matsayin shimfi]a da kuma gabatarwa, a wannan darasi na Akhla}. A wannan darasi ne za a shiga ainihin Akhla} ]in. Da farko dai mene ne Akhla}, a fannin Ilimi na Irfan? Ma’anar Akhla},

Bayani kan muhimmancin Akhla}.


A darasin daya gabata,an ]anyi bayani a ta}aice, kuma a dun}ule dangane da ilimin irfani da kuma cewa Akhla}, ~angare ne na shi wannan ilimin irfani,da kuma muhimmancin Akhla} da yadda kyakkyawan Akhla},  yake iya canza ma}iyi ya zama masoyi,kamar yadda aka bada misalai daga Manzon Allah [S] da kuma Aimma na Ahlul Bait [AS]

Bayani kan Kalb {zuciya}.


A darasin daya gabata bayani ya gudana dangane da Tazkiyatus Nafs wato tsarkake rai.A wannan darasi bayani zai kasance ne,dangane da ~angarori biyu na tazkiyatus nafs.~angaren ba]ini wato zuciya da kuma ~angaren zahiri wato ga~u~~a,Da farko ~angaren ba]ini wanda shine tazkiyya na zuciya wato tsarkake zuciya,wanda in ya samu ]aya ~angaren zai iya samuwa wato ~angaren tazkiyya na ga~u~~a.

Bayani kan fannin ilimin Akhla{.


Akhla} ~angare ne na ilimin irfani,wato misali kamar  yadda ilimin fi}hu,yake da manyan ~angarori guda biyu,wato Ibadat da Mu’amalat, ilimin A}a’id  kuma yake da manyan ~angarori guda biyar,Tauhid,Adl,Nubuwwa,Imama da kuma Ma’ad,to shima ilimin  irfani yana da manyan ~angarori guda biyu,sune AKHLA{,wanda wani lokaci ake cewa IRFANIL-AMALIY,da kuma MA’ARIFA,wanda ake cewa IRFANIN-NAZARIY.

Daruusa 12 daga rayuwar Imam Mahdi (AS)


Kasantuwar wannam wata da muke ciki, wato na Sha’aban a cikinsa ne aka haifi Hujjar Allah a doron }asa, kuma Shugababn wannan zamani, wato Imam Mahdi (AS), kamar yadda aka sani shi ne Imam na 12 a jerin }idaya na Imamai 12, wato shi ne Khalifan Manzon Allah (S) na }arshe.

Darussa12daga rayuwar Imam Husain [AS] 2


Har yanzu muna cikin wannan wata na juyayi,ba}in ciki dama kuka,musamman ga mabiya Ahlulbayt [AS],saboda yadda ake keta mutuncinsu da kuma alfarmar iyalan gidan Manzon Allah [S] a cikin watan,wato akasin yadda wasu sashen ‘yan uwa musulmi na madrasah ]in Ahlus-Sunnah suka ]auke shi wata na farin ciki da kuma yalwata wa iyali

Darussa daga rayuwar Ummul A’imma Fatima (AS).


Kasantuwar watan Jimada Sani 3 gare shi ne wafati ko shahadar Ummul A’imma, wato Sayyada Zahra (AS), amma wannan a ruwayar da ta fi shahara, domin akwai ruwayoyi da suka zo akasin haka, rubutu ko bayani dangane da tarihi ko rayuwar Sayyada Fatima (AS), wani fage ne mai fa]in gaske, wanda ba za a iya cimma ma}urarsa ba,

Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) 3


Kasantuwar ba mu jima da fita daga wata mai albarka ba, wato watan Maulidin Manzon Allah (S), kuma a darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) da ya gabata, in za a iya tunawa mun tsaya ne a bayani dangane da Akhlak ]in Manzon Allah (S), wanda muka kakkawo bayani kan kyautarsa a ta}aice da bayani a kan ha}urinsa da kuma afuwarsa, shi ma a ta}aice.

Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) 2


Kasantuwar wannan wata da muke ciki, wato na Rabi’ul Awwal, wata ne na wiladar Manzon Allah da kuma Imam Sadiq (AS). Kamar yadda ya zo a tarihi a ruwayar Iyalan Gidan Manzon Allah (S), an haifi Manzon Allah (S) ne a lokacin fitowar Alfijir ranar Juma’a 17 ga Rabi’ul Awwal a shekarar da ake wa la}abi da shekarar Giwa.

Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) (1)


Kasantuwar watan da muka fita, wato Safar a cikinsa ne wafatin Manzon Allah (S), a 28 gare shi. Wannan a kan abin da Malaman Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) suka tafi a kai. Amma abin da Malaman Madrasah ]in Ahlus Sunna suka tafi a kai shi ne, 22 ga watan Rabi’ul Awwal.

Darussa 12 daga rayuwar Imam Aliy Alhadi (AS)


Kasantuwar 3 ga watan Rajab ne wafatin Imam Aliy Alhadi (AS), kamar yadda aka saba a irin wa]annan munasabobi na wafati da kuma shahadar Ma’asumai (AS), akan gabatar da Darussa a ta}aice daidai gwargwado, na tarihinsu da kuma wasu ~angarori na rayuwarsu daban-daban, da nufin su kasance madubi da za mu dubi kawukanmu da kuma rayuwarmu da su, da kuma yin mujahada daidai ikonmu.

Darussa 12 daga rayuwar Imam Sadik [AS].1


Imam Sadi}[AS],kamar yadda aka sani shine imam na 6 a jerin I  mamai 12.kuma wannnan munasaba ce ta wafatinsa,domin  ya koma ga Allah [T] ne ranar 25 ga wannnan wata da muke ciki na shawwal,a shekara ta 148 bayan hijra.Ya rasu sakamakon guba da aka sa mishi a inabi,kuma ya rasu ya nada shekara 65, a wata ruwaya shekara 68

Darussa 12 daga rayuwar Imam Sadi} (AS) 2


Kamar yadda ya gabata a munasabar wafatin Imam Sadi} (AS) a shekarar da ta gabata, an tsaya ne a darussa na hu]u daga cikin rayuwarsa (AS, kuma aka ce insha Allah a wata munasabar wafatinsa za a ]ora a kai.

Darussa 12 daga rayuwar Imam Ridhah [AS].


Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Zul }ada a cikinsa ne wilada da kuma wafatin Imam Ali ibn Musa Ar-Ridah[AS]suka kasance,domin yazo a tarihi cewa an haife shi ranar Alhamis 11 ga watan zul }ada a shekara ta 148 bayan hijira.Ya rasu 23 ga watan zul }ada shekara ta 203 bayan hijira.Amma a wata ruwaya,yazo a kan cewa rasuwarsa ta kasance a watan safar ne

Darussa 12 daga rayuwar Imam Musa Al-Kazim (AS)


Kasantuwar wannan watan da muke ciki mai alfarma, wato watan Rajab 25 gare shi ne Shahadar Imam Musa Alkazim (AS). Kamar yadda aka sani, shi ne Imam na bakwai a jerin kidaya na Imamai 12 (AS) .
Imam Kazim (AS) an haife shi ne ranar Lahadi 7 ga watan Safar shekara ta 128 bayan hijira, a wani gari da ake ce wa Abwa, yana tsakanin Makka da Madina ne.

Darussa 12 daga rayuwar Imam Muhammad Al-Ba}ir [AS].


Wannan wata da muke ciki na zulhijja,bakwai gare shine wafatin Imam Muhammad Ba}ir [AS] domin  ya rasu ne ranar litinin  7 ga zulhijja shekara ta 114 bayan hijra.Ya rasu ya na da shekaru 57 a duniya,muddan imamancinsa kuma shekara 19.Kabarinsa yana madina ne,watau a Ba}i’a.Kuma kamar yadda aka sani a jerin }idaya na Imamai goma sha biyu,shine Imam na biyar.Kuma shi ]ane ga Imam Zainul Abidin [AS] ]an Imam Husain [AS].

Darussa 12 daga rayuwar Imam Husain (AS) I


Kasantuwar wannan watan da muke ciki, wato Muharram a cikinsa ne, 10 ga shi, shahadar Imam Husain (AS). Shahadar tasa ta kasance ranar Juma’a, a wata ruwaya ranar Asabar shekara ta 61 bayan hijira. Kuma shahadar tasa ta kasance kamar yadda aka sani a Karbala. Tsakanin isar sa Karbala da shahadarsa, kwanaki takwas ne.

Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan (AS)


Kasantuwar wata da muka fita na Safar, 28 gare shi, shi ne wafatin Imam Hasan (AS) a wata ruwaya kuma 7 ga Safar, da ma wani lokaci akan samu wannan sa~anin na ruwayoyi tsakanin Malaman tarihi na wilada ko wafatin Ma’asummin (AS), wato Manzon Allah (S) da kuma A’imma na Ahlul Baiti (AS) wanda akan asasin wa]annan ruwayoyi mutum zai ga mabiya Ahlul Baiti (AS) a wata nahiya sun tafi a kan ruwaya kaza wata nahiyar kuma sun tafi a kan ruwaya kaza,

Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan Al-Askari (AS)


Kasantuwar ran 8 ga watan jiya, wato Rabi’ul Awwal shi ne ya yi daidai da wafatin Imam Hasan Al-Askar. Kamar yadda ya zo a tarihinsa, ya rasu ne ranar Juma’a 8 ga Rabi’ul Awwal Hijira ta 260. Imam Hasan Al-askari (AS) an haife shi ne a Madina, a watan Rabi’us-Sani, sai dai an samu sa~ani dangane da ranar da aka haife shi, da kuma nawa ga wata aka haife shi.

Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali Zainul Abidin (AS)


Kasantuwar watan da muka fita wato na Muharram, 25 gare shi ne wafatin Imam Ali Zainul Abidin (AS) a wata ruwaya 12 gare shi, saboda haka kamar yadda aka saba a irin wa]annan munasabobin na wafatin A’imma na Ahlul Baiti (AS) akan gabatar da darussa a ta}aice daga rayuwarsu da nufin su kasance madubi da za mu dubi rayuwarmu da kuma yin sa’ayi na Mujahada