Sallah tana da ~angarori
guda biyu,~angaren ruhinta,wanda shine ba]ininta da kuma ~angaren jikinta,wanda
shine zahirinta.Malaman Irfan ko Tasawwuf sun yi rubuce-rubuce da kuma bayanai
dangane da Ruhin sallah da kuma Asrar ]inta.Kamar
yadda Malaman Fi}hu suka yi rubuce-rubuce da kuma bayanai dangane da
zahirinta.
Wannan janibi na ruhin sallah,janibi wanda yake da gayar muhimmanci
wajen saninsa da kuma kiyaye shi,domin yin haka shi zai ba mutum kamalar
sallarsa da kuma samun amsuwar ta a wajen Allah[T]
Dama samun abinda yake shine manufa na wajabta mana sallah,wato kai wa ga matsayi na mushahada da mura}aba na Allah
ma]aukaki.Kuma wannan kiyaye ruhi bai ta}aita ga sallah kawai ba,a’a dukkan
ayyuka na ibadodi da kuma ayyukan ]a’a,kai hatta ma ayyuka na mubahat,kamar cin
abinci da yin barci,duk ana bu}atar mutum ya kiyaye ruhinsu wajen aikata
su.Kamar mutum ya ci abinci ko yayi barci da niyyar ya samu }arfin bauta ga
Allah ma]aukaki.
Malamai da yawa na madrasah ]in
Imamiyya sun rubuta littafai masu yawa dangane da Asrar na sallah,misali
littafin Asrarus-sallat na Imam Khumaini.Adabus-salatil- ma’anawiyya shima na
Imam Khumaini.Asrarus-sallat na Ayatullahi Jawad Amuliy.Asrarus-sallat na
Ayatullahi Jawad Attab-riziy.Asrarus-sallat na shahidus-sani.Da dai sauran
littafai makamantan wa]annan da Malaman Imamiyya suka rubuta dangane da Ruhi da
Asrar na sallah.Saboda haka a nan bayani zai gudana a kan wa]annan ababe da za
a ambata dai dai gwargodon iko kuma a ta}aice.
1-
Ladubba na ba]inin sallah.
2-
Muhimmancin Halartar da zuciya a cikin sallah.
3-
Hadisai
da suka zo dangane da Halartar da zuciya a cikin sallah.
4-
Abubuwan da suke hana halartar da zuciya a
cikin sallah.
5-
Abubuwan da suke taimaka ma mutum ya Halartar da zuciyarsa acikin sallah.
6-
Asrar na ~angarorin zahirin sallah.
7-
Sallah ta Ma’asumin da kuma wasu bayin Allah.
8-
Abubuwan da ke ~ata ba]inin sallah.
9-
Neman gafarar Allah[T]
ga sallolinmu.
1-
Ladubba na ba]inin sallah:Kamar yadda aka
ambata a baya sallah tana da ~angarori guda biyu,~angaren jikinta wato
zahirinta wa]anda sune,Tsayuwa,Ruku’u, Sujuda,Zama da abubuwan da ake karantawa
da aikatawa a cikin su.Sai kuma ~angaren ba]ininta wato Ruhinta,su guda goma
ne.1-Niyya.2-Iklasi.3-Khushu’i.4-Hudhurul-}alb.5-Tafahhum.6-Ta’azim.7-Khauf.8-Raja’a.9-Haya’u.10-Tawadi’u.Wa]annan
sune ladubba na ba]inin sallah,kuma da tsayuwa da sune sallah take samun
ruhinta da kamalarta,da kuma rashin tsayuwa da sune sallah take zama tamkar
gangan jiki ba ruhi.Littafan da aka ambata a sama,an kawo bayanai na wa]annan ababe
guda goma sanka-sanka
1-
Niyya:Ita niyya ruhi ce ga ko wane aiki,wato
ba wai ga ayyukan ibada ba kawai,shi yasa bayin Allah duk aikin da zasu yi sai
sun halartar da niyya kafin su yishi.wani lokaci ma aiki guda ]aya su kan yi
niyyoyi masu yawa a cikinsa,domin neman yawaitar lada.2-Iklasi:Wato ya kasance
duk aikin da mutum zai yi yayi shi akan asasin saboda Allah[T] da kuma neman yardarsa,wato ba domin
neman zukatan mutane ba.3-Kushu’i:Wato mutum ya kasance ya na sallah cikin
Khushu’i,kuma ya kasu kashi biyu khushu’i na zuciya da kuma khushu’i na ga~o~i, wato shine mutum ya
natsar da ga~o~insa na zahiri da ba]ini
a cikin sallah.4-Hudhurul- }alb,wato ya kasance mutum ya halartar da zuciyarsa
a cikin sallah,ba ya kasance mutum na sallah amma zuciyarsa na wani waje ba.5-Tafahhum,wato
shine ya kasance lokacin da mutum yake karatu acikin sallah,yana tare da
ma’anonin abin da yake biyawa,ba wai mujarradin lafazin ba.6-Ta’azim wato ya
kasance lokacin da mutum yake sallah,ya dunga shu’urin ]aukaka da kuma girman Allah
Ta’ala.7-Kauf wato ya kasance idan mutum na sallah ya dun ga shu’urin tsoron
Allah Ta’ala.8-Raja’a wato ya kasance idan mutum na sallah ya dun ga shu’urin fatar rahamar
Allah Ta’ala.9-Haya’u wato ya kasance idan mutum na sallah ya dun ga shu’urin
kunyar Allah Ta’ala.10-Tawadi’u:wato ya kasance idan mutum na sallah ya dun ga
shu’urin }as}antar da kai gaban Allah Ta’ala.
2-
Muhimmancin Halartar da zuciya a cikin sallah:Halartara
da zuciya a cikin sallah,kamar yadda aka ]an yi bayani a baya wato mutum ya zamanto tunaninsa ya na cikin sallah ba
wajen sallah ba,Saboda daga cikin dasisosin da shai]an yakan yi ga mutum shine
da zarar mutum ya soma sallah zai dunga yawo da tunaninsa, ya tunano wannan ya
tunano wannan,ta yadda daga }arshe zai kasance yayi sallar cikin gafala,kuma
wannan dama shine manufar shai]an wato yaga cewa mutum yayi sallar cikin
gafala.Shi yasa ya nada gayar muhimmanci mutum yayi ma kansa tarbiyya na iya
ri}e tunaninsa cikin sallah,ka da ya bar shi ya na yawo,kuma wannan mai
yiyuwane.domin yin haka yana da falala mai yawa,misali yazo a wani Hadisi daga
Manzon Allah[S] yace. “Duk wanda yayi sallah
raka’a biyu,a cikin sallar bai yi tunanin wani abu na duniya ba,to za a gafarta
masa zunuban da ya gabatar.”A wani Hadisi kuma daga Manzon Allah[S] yace,
“Allah baya duban sallar da mutum bai halartar da zuciya ba a cikinta.”Saboda
haka halartar da zuciya a cikin sallah yana da fa’idodi masu yawan gaske,domin
zai ba sallar mutum kamala,zai kuma sa mutum ya samu zau}i da halawa na sallah,wato
da]inta,kuma irin wannan sallah mai ruhi wato wadda aka halartar da zuciya a
cikinta, irin ta ke hana mutum ya aikata Munkar,ba sallah wadda aka yi ta cikin
gafala ba,domin ita sallah kamar yadda yazo a Al}ur’ani tana hana al-fasha da
munkar,yazo a wani Hadisi da aka samo daga Imam Sadi}[AS] yace, “Duk wanda yake so ya san an kar~i sallarsa ko ba a kar~a
ba,to ya duba ya gani sallarsa ta hana shi alfasha da munkar,domin dai dai
gwargwadon yadda ta hana shi dai dai yadda aka kar~i sallar tasa kenan.”Har
wala-yau irin wannan sallah mai ruhi wadda aka halartar da zuciya aciki,itace
take tsarkake mutum domin sallah asasi ce babba ta Tazkiyyar naf’s ]in mutum,
kamar yadda malaman Irfan ko Tasawwuf suka yi bayani.Misali wani Hadisi da yazo
daga Imam Ba}ir[AS] daga Manzon Allah[S] yace,
“Da ace akwai kogi a }ofar
gidan ]ayan ku,kuma ko wane yini yana wanka so biyar a ciki,wani datti zai
kasance a jikinsa?sai sahabbai suka ce a’a,sai Manzon Allah yace misalin sallah
kamar kogi ne mai gudana,duk lokacin da mutum yayi sallah sai ta kankare
zunuban da mutum ya aikata tsakani.”Saboda haka sallah tana wanke ruhin mutum
daga zunuban daya aikata,amma alura ba ko wace irin sallah ba,sai wadda ta
kasance an yita cikin ya}’za }albiyya wato zuciya tana falke ba cikin gafala
ba.Wannan kenan a ta}aice dangane da muhimmancin Halartar da zuciya a cikin
sallah.
3-
Hadisai da suka zo dangane da Halartar da
zuciya a cikin sallah:Akwai Hadisai masu yawa da suka zo akan haka.Ga wasu daga
ciki,A-Manzon Allah[S] yace,
“Idan mutum ya tsaya a cikin sallarsa,ya kasance kuma cikin tunanin Allah,zai
fita sallar kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.”wato zai dawo bai da
zunubi.B-Wani hadisi da aka samo daga
Manzon Allah[S] yake cema Abu Zarr,ya Aba Zarr Raka’a biyu matsakaita wanda aka
yisu cikin Tafakkur tafi tsayuwar dare baki ]aya al-hali zuciya tana cikin gafala.C-An
ta~a kawo ma Manzon Allah kyautar ra}uma guda biyu manya-manya,sai yace ma
sahabbansa duk wanda yayi sallah raka’a biyu, amma bai yi tunanin wani abu na
duniya ba,to zai bashi kyautar ]aya,ko ya kasa sai Imam Ali[AS] shine Manzon Allah[S] ya bashi guda
biyun duka.Domin Imam Ali[AS]ya kasance saboda gayar Fana’insa acikin sallah
idan yana yin ta,bai jin duk wani abinda ya samu jikinsa,alal misali akwai wani
ya}i da mashi
ya shiga }afarsa,ba a iya ]ebe shiba sai Sayyida Fa]ima[AS] tace,a wata ruwar Manzon Allah[S] yace a
barshi sai ya soma sallah sai a cire mashin,haka ko akayi yana sallah aka cire
kuma bai jiba.D-An samo daga Manzon Allah[S] yace, “Lalle mutum biyu, a
al-ummata zasu iya tsayuwa a sallah,ruku’unsu da sujudarsu ]aya amma ya kasance
tsakanin sallarsu kamar nisan sama da }asa.”wato sun banbanta wajen tsayuwa da
ruhin sallar da kuma ma’anawiyya ]in ta.E-An samo daga Imam Sadi}[AS] yace, “Idan zaka yi sallah ka fuskantar
da zuciyarka zuwa ga Allah[T]domin babu wani bawa wanda zai fuskantar da
zuciyarsa a cikin sallarsa da kuma Addu’arsa ga Allah[T] face Allah ya
fuskantar da zukatan muminai gareshi.F-An samo daga Imam Bakir[AS] yace, “Lalle
bawa za a
]aukaka sallarsa amma wani za a amshi rabinta,wani sulusinta,wani rubu’inta,wani
khumusinta.Abin da za a amsa ya danganta ga yadda mutum ya fuskantar da zuciyarsa
a cikin sallah,an umarta da yin nafila domin kammala na}asun da aka samu a
sallah ta Farilla.” Wato wannan hadisin ya nuna dai dai gwargodon yadda mutum
ya tsayu da ruhin sallah,dai dai yadda za a amsa daga ita sallar.Wannan kenan a
ta}aice dangane da Hadisai da suka zo na Halartar da zuciya a cikin sallah.
4-
Abubuwan da suke hana Halartar da zuciya a
cikin sallah:Sun kasu kashi biyu,wato ko dai ya kasance abin da ya hana
halartuwar zuciyar a cikin sallah abune daga waje ko daga ciki,abin da ake nufi
daga waje ga~o~insa na zahiri misali kunnensa ko idonsa,wato ace mutum yana sallah
sai kunnensa yaji wani abu ko idonsa yaga wani abu,sai hakan yaje ma zuciya na
abun da yaji ko ya gani,ita kuma ta dun ga tunani akai,to wannan sai ya zama
sanadiyyar shamakance zuciya daga tunani a cikin sallah,ko kuma ya kasance daga
cikin zuciya ne rashin halartar da zuciyar yake tasowa misali ta’alla}uwa da
duniya da kuma tarkacenta,wanda mafi yawa wannan shi yake hana mutane halartar
da zuciya a cikin sallah.Wani kuma abun da yake hana mutane halartar da zuciya
a cikin sallah shine,zuciya bisa ]abi’arta mai yawan jujjuyawa ce a tunani,shi
yasa ma ake ce mata }alb.
5-
Abubuwan
da suke taimaka ma mutum Halartar da zuciyarsa cikin salla:Suna da yawa amma ga
wasu daga ciki,1-Mujahada wajen ri}e
tunani da kuma tattara tunanin a cikin sallah,wato mutum yayi iyaka iyawarsa
wajen hana tunaninsa yawo.da tunaninsa ya fita cikin sallah wato yana tunanin
wani abu wanda bai da ala}a da sallah,sai yayi }o}ari ya dawo da tunanin nasa
cikin sallar,farkon farawa idan mutum bai saba ba yana da wahala,kamar yadda
Imam Khumaini yace a cikin littafinsa na Asrarus-salat,amma yace idan mutum
yayi mujahada akan haka abune mai yi wuwa,har ya ba da misali mutum ya ]auki
lokaci yana ri}e tunaninsa acikin sallah a ]aya bisa goma,yazo biyu bisa
goma,ukku bisa goma kama-kama dai har ya kai matsayin da yake iya ri}e
tunaninsa baki ]aya acikin sallah.2-Zuhudu wato guje ma duniya, kamar yadda aka
sha yin bayani cewa,zuhudu ba shine kada ka mallaki abin duniya ba,abinda ake
nufi dashi shine kada ka ta’alla}u dashi,ko da ka malleke shi,wato ya zamanto
duniya da tarkacenta basu da tasiri a zuciyarka,to idan mutum ya samu haka
ha}i}a ya samu hanya babba na samun halartar zuciyarsa a cikin sallah,saboda
mafi yawan abinda yake hana tattaruwar tunani acikin sallah duniya ce.to idan
mutum ya zamanto duniyar ba tada tasiri gareshi,shi kenan ya huta da wannan
makamin da shai]an yake amfani dashi na son duniya domin hana zuciya halartuwa
a cikin sallah.3-Mura}aba,wato mutum ya dunga shu’urin cewa Allah Ta’ala yana
ganinsa kuma yana jinsa kuma yasan tunanin da yake yawo a zuciyarsa,wannan
shu’uri na mura}aba shima hanya ce babba na halartuwar zuciya a cikin sallah.4-Mutum
ya ]auka itace sallarsa ta }arshe a duniya,wato daga cikin abubuwan da suke
taimaka ma mutum halartar da zuciya a cikin sallah akwai wannan.Domin da mutum
yasan idan yana sallah,sallar itace ta }arshe, bayanta mala’ikan mutuwa zai
kar~i ransa,zai yi iyaka iyawarsa yaga cewa ya kyautata sallar zahirinta da
ba]ininta.yazo a hadisi cewa idan mutum zai yi sallah to yayi sallar mai
bankwana.
6-
Asrar na ~angarorin sallah:ko wane ~angare na
sallah yana da asrar ]insa,kai tun ma kafin shiga cikin sallah misali tsarki,al-wala,azan.i}ama,duk
suna da asrar ]insu,shiga cikin sallar
tun daga kan Takbiratul-ihram har zuwa sallamewa,ayyukan da akeyi
tsakaninsu sanka-sanka duk suna da asrar ]insu,saboda haka bayani ne mai
tsawo,amma ga mai bu}atar ganin wa]annan Asrar na ayyukan gabanin sallah da
cikin sallah da kuma bayan sallah,yana iya duba ]aya daga cikin littafan da aka
ambata sama na Asrarus-salat.
7-
Sallah ta Ma’asumin da kuma wasu bayin Allah
Ta’ala.Idan mutum ya bibiyi rayuwar Manzon Allah[S]
da kuma Ahlul bayt[AS] da kuma wasu bayin Allah[T] ta ~angaren sallolinsu,idan
lokacin sallah yayi yadda akan ga canji a jikinsu da launinsu da kuma
mu’amalarsu.Ga misalai:1-[aya daga cikin matayen Manzon Allah[S] tace,Annabi[S] ya kasance yana hira damu
muna hira dashi amma idan lokacin sallah yayi,yakan kasance kamar bai sammu
ba,bamu san shi ba.2-Imam Ali[AS] in ya soma al-wala fuskarsa ta kan canza
saboda tsoron Allah.Haka nan kuma idan lokacin sallah yayi,akan ga launinsa ya
canza,har akan ce masa miya same ka ya Amirul muminin? Ya kan amsa da
cewa,lokacin Amana wadda Allah ya bijirar da ita ga sammai da kasa da
duwatsu,amma basu ]auka
ba,sai mutum ya ]auka,to ban sani ba zan iya kyautata abin da na ]auka ko a’a.3-Sayyida
Fa]ima[AS] ta kasance tana yawan kuka
idan tana sallah saboda tsoron Allah[T].Imam Hassan[AS] ya kasance idan ya gama
alwala zai yi sallah launin jikinsa kan canza,sai aka tambaye shi dalilin haka?
Dole ne duk wanda zai tsaya gaban Allah launin shi ya canza.4-Imam Sajjad[AS]
ya kasance idan yayi alwala launinsa kanyi fatsi-fatsi,sai iyalansa suka
tambaye shi kan haka?sai yace masu,kun san ko gaban wanda nike so in tsaya.Haka
nan wata rana yana sallah sai al-kyabbarsa ta fa]i daga kafa]arsa,amma bai gyara ta ba,har sai da ya gama sallah,aka
tambaye shi mi yasa bai gyara ta ba?sai yace ma wanda ya tambaye shi,kaitonka
kasan gaban ko wanda nike? Lalle bawa gwargwadon yadda ya halartar da zuciyarsa
acikin sallah,dai dai abin da za a amsa kenan na sallarsa.sai mutumin yace in
zamo fansa gareka lalle mu mun halaka,sai Imam Sajjad yace masa a’a.Allah yana
cika na}asu na sallar bawa da nafilfili.Haka kuma yazo akan cewa idan Imam
Sajjad yana sallah kamar kace itaciya ce tsaye,bata ka]awa face abinda iska ta
ka]a.wannan kenan a ta}aice na sallolin Ma’asumin.misali biyu kuma daga cikin
sallolin wasu bayin Allah Ta’ala shine Ayatullahi Bahajati,duk wanda Allah yasa
yai sallah a bayansa zai ba da shaidar cewa sallarsa baki ]aya yakan yi ta
cikin kuka ne,yana tsaye yana kuka,yana ruku’u yana kuka,yana sujuda yana
kuka,yana Tahiya a zaune yana kuka,so da yawa na lura in yana zaune domin
tahiya,to lokacin da yake cewa,Assalamu-Alaika ayyuhan Nabiyy,ya kan yawaita
kuka a wajen.Tabbas sallah a bayansa yana gusar da }aswa ]in zuciya wato
bushewar ta,shi yasa wasu malamai a nan }um lokacin yana raye suna }arfafa
]alibansu da yin sallah a bayansa.Sai kuma wani Malami da na biya }issar shi,ya
kasance idan yazo sallah,ya kan gina
tunaninsa akan cewa,a bayansa ga Mala’ikan mutuwa yana jiransa ya sallame
sallah ya ]auki ransa.A }asan }afafuwansa yana akan sira]i.A gefen damarsa ga
Aljanna.A gefen hagunsa ga wuta.A gabansa kuma ga Allah Ta’ala.To da wannan
tunanin yake kasancewa tun daga farkon sallarsa har }arshenta.
8-
Abubuwan dake ~ata ba]inin sallah:Kamar yadda
akwai abubuwan da suke ~ata zahirin sallah wato jikinta,wanda malamai na fi}hu
suka yi bayanansu,to haka ba]inin sallah wato Ruhinta malaman Irfan sunyi
bayanin abubuwan dake ~atata.Kuma irin wannan sallah wadda a ba]inance ta
lalace,amma a zahirance dai dai,sai ta kasance a zahirance ya sauke Taklif wato
na yin ta da yayi,Amma a ba]inance bata kar~u ba,wato wajen Allah Ta’ala.misalan
abubuwan da suke ~ata ba]inin sallah,akwai Riya da kuma ujubu
acikin sallar.In sha Allah a darasin Akla} bayani zai zo kansu.
9-
Nemam gafarar Allah ga Sallolinmu:Kamar yadda
muke sujudu shukur a bayan sallolin mu,wato na godiya ga Allah na muwafa}ar da
yayi mana na yin sallar da muka yi.To haka nan yake da muhimmanci duk sallolin
da mukayi na farilla mu nemi gafarar Allah Ta’ala kan na}asun dake cikin sallolin
mu a zahirancensu da kuma ba]inancensu.wato a jikin sallolinmu da kuma
ruhinsu.Domin in muka dubi mafi yawan sallolinmu gawawwaki ne,wato jikkuna ne
ba Rai.mai bu}atar }arin bayani kan wannan ya duba cikin littafin Al-arbauna
Hadis na Imam Khumaini,a hadisi na ukku,wato wanda yake Magana kan ujub,a
fasalin dake bayanin cewa Hubbun Naf’s Asasul ujub.Yana da kyau idan mutum na
da littafin ya duba wajen yaga yadda Imam khumaini yai bayanin irin sallolinmu
da kuma ha]arin da muke ciki dangane dasu.
No comments:
Post a Comment