A darasin da ya gabata,wato darasi na biyar,an kammala
shinfi]a da kuma
gabatarwa,aka yi bayanin cewa a darasi na gaba in sha Allah, za a shiga babin
farko wato babin tsarki.To kasantuwar babobin fi}hu suna da yawa,wa]ansu fu}aha
sun tafi a kan babobi hamsin ne,wato tun daga babin tsarki zuwa babin
diyyat.
Sunday 10 February 2013
Bayani kan Ijtihadi da Taklid.
Kamar yadda aka yi bayani a darasi na 3, cewa kasantuwar
zuwan watan Ramadan gabatarwa da kuma shimafi]a da ake yi na wannan darasi na
Fi}ihu za a dakatar a shiga babin Azumi, in ya so bayan watan Ramadan sai a
kammala gabatarwar da kuma shimfi]a, bayan haka kuma sai a shiga babin farko,
wato babin tsarki, bayan shi kuma babin Salla, da dai sauran babobi, insha
Allahu daidai gwargwadon iko.
Bayani kan fannin ilimin Fikhu.
Isha Allah saboda muhimmanci da kuma bu}ata daga wasu
’yan uwa na gabatar da darasi kan Fi}hu, shigen yadda ake gabatar da darussa 12
daga rayuwar A’imma (AS), ko kuma darasi kan A}lak ta ~angare na, na yi tunani
amsa wannan bu}ata domin gabatar da shi
wannan darasin na Fi}hu gwargwadon iko.
Bayani kan Azumi 2.
Kamar yadda ya gabata a darasin baya a wannan babi na
Azumi, wasu fasaloli guda hu]u. Yanzu za a tashi a fasali na biyar. Bayani
dangane da wanda ya yi abin da yake karya Azumi. a darasin da ya gabata a
fasali na hu]u, in za a duba, an kawo abubuwa guda 10, wanda ya wajaba mai
Azumi ya kame daga gare su. To shi wannan fasali na biyar, yana bayani dangane
da hukuncin mai Azumin da ya aikata ]aya daga cikin wa]annan ababe guda 10, ko
kuma wasu daga cikinsu.
Bayani kan Azumi 1.
Kamar
yadda aka ce a darasin da ya gabata, cewa insha Allah (T) a wannan darasi za a
kammala shimfi]a da kuma gabatarwa, da ma shiga cikin babobin Fi}hu. To
kasantuwar mun shiga cikin watan Ramadan ,ya zamanto zai yi kyau da kuma
muhimmanci mu shiga cikin babobin fi}hun, wato babin Azumi, in ya so bayan
kammala babin Azumin sai a kammala ita waccan shimfi]a da kuma gabatarwa da
shiga babin farko, wato babin tsarki. Saboda haka wannan darasi zai gudana ne a
babin Azumi. Kuma saboda ya yi sau}i wajen gabatar da shi, an yi masa fasali 12
ne. Ga yadda suke.
Bayani kan alakar limaman mazhabobin Ahlus-Sunnah da A’imma [AS].
Kamar yadda aka ambata a darasin da ya gabata cewa,
wannan darasi na Fi}hu insha Allah, za a dinga gabatar da shi a bisa Usulubi na
Fi}hul-Mu}arana ne, wato mu}arana tsakanin wa]annan Mazhabobi guda hu]u na
Ahlus-sunnah; Hannafiyya, Malikiyyah, Shafi'iyya, Hanbaliyya. A ]aya gefen kuma
da Ja'afariyya, amma za a }arfafa a Fi}hun Ja'afariyya ne.
Saturday 9 February 2013
Tarihi da rayuwar Shahid Ayyatullahi Sayyid Muhammad Ba}ir Sadr
Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Jimadal Ula, 23
gare shi ne a shekara ta 1400 Hijiriyyah, a miladiyyah kuma 9/4/1980 shahadar
Ayatullahi Sayyid Muhammad Ba}ir Sadr, ta kasance, a daidai wannan lokaci akan
yi tarurruka, musamman a Ira}i da kuma Iran, domin tunawa da shi da kuma
shahadarsa, wanda a irin wa]annan tarurruka akan tunatar da juna dangane da
tarihinsa, da kuma wasu ~angarori na rayuwarsa, da nufin su kasance darussa ga
mahalarta da kuma wa]anda za su ji ko su gani daga baya.
TARIHI DA KUMA RAYUWAR ABUL- FADHAL ABBAS {AS}.
Sayyid Abul-Fadhal Abbas[AS] an haife shi a
Madina,ranar 4 ga watan sha’aban,shekara ta 26 bayan hijira,Sayyid Abbas a cikin ‘ya’yan Imam Ali[as] maza baya ga Imam
Hassan da Imam Husain[AS] ba wanda ya kai shi daraja.
TARIHI DA KUMA DARUSSA DAGA RAYUWAR SAYYIDA ZAINAB [AS].
Rubutu ko bayani dangane da
sayyida Zainab[AS] fage ne mai fa]in
gaske.Kuma Malamai da dama sun rubuta littafai,game da tarihinta da kuma
rayuwar ta,misalin wasu daga cikin littafan sune,Zainabul-Kubra na shaikh
Ja’afar Najdiy.kasa-isus-zainabiyya na sayyid Nurud-din.
ALHAMDU LILLAH SHEKARU 60 MASU ALBARKA NA SAYYID ZAKZAKY [H].
Alhamdulillah,kamar
yadda muka sani,wannan wata da muke ciki,wato na sha’aban 15 gare shi.Sayyid Ibrahim
Zakzaky [H] ya cika shekaru 60 cur-cur a duniya.Saboda haka naga zai yi kyau da
kuma muhimmanci,akawo wasu darussa na jarabawowi da nasarori dake cikin wa]annan
shekaru masu albarka,da nufin su kasance DARASI a gare mu
Ruhin Azumi da kuma ayyukan watan Ramadan
Azumi kamar sauran
ibadodi yana da ~angarori guda biyu,~angaren
ruhi,wanda shine ba]ininsa,da kuma ~angaren
jiki,wanda shine zahirinsa.Malaman irfani ko
tasawwuf sunyi rubuce-rubuce da kuma bayanai dangane da ruhin azumi kamar yadda
malaman fi}hu sukayi rubuce-rubuce da bayanai
dangane da zahirinsa.Misali,sharu]]an
azumi,abubuwan dake inganta shi,ko kuma abubuwan dake ~ata
shi,da dai sauransu.
Rubuce-rubucen Shehu [an Fodio a kan Imam Mahdi AF
Watan sha’aban da muka fita,kamar yadda aka sani,a cikinsa
ne aka haifi Imam Mahdi [AF],saboda haka ne mabiya Ahlulbayt [AS] a sassan
duniya daban daban ke gabatar da tarurruka,domin tunatar da juna dangane da ~angarori daban
daban da suke da ala}a
da Imam Mahdi [AF].misali,wiladarsa,gaiba ]insa,shaksiyya
]insa,alamomin
bayyanarsa,bayanai da rubuce rubuce na malaman madrasah ]in Ahlus sunna dangane dashi,da dai
sauransu
RANAR GHADIR A MAHANGAR AHLULBAIT [AS] DA AHLUS SUNNA.
Al-hamdu-lillah,kasantuwar wannan wata da muke
ciki,wato na zul hijja,a cikin sa ne,kamar yadda aka sani,18 gare shi,shekara
ta goma bayan hijira,wannan munasaba ta ghadir ta kasance.Kuma tun daga wancan
lokaci har ya zuwa yau dinmu wato yau shekara sama da dubu da dari hudu,mabiya
Ahlulbaiti [AS] a duk shekara a kuma sassan duniya dabam dabam suke raya wannan
rana ta ghadir ta fuskoki daban daban.
Imama a mahangar Ahlul Baiti (AS) da Ahlus Sunna.
Alhamdulillah, kasantuwar wannan wata da muke ciki, wato
na Zulhijjah cikinsa ne 18 gare shi wato Ranar Ghadir Manzon Allah (S) ya
bayyana wa wannan al’umma wa]anda za su kasance Imamai, wato Khalifofi a
bayansa, bayyanawa wadda za a siffata ta a matsayin bayyanawa RASMIYYAN, wato
OFFICIALY. Saboda haka mabiya Ahlul Baiti (AS) a sassan duniya daban-daban suke
gabatar da tarurruka da kuma rubuce-rubuce domin tunatar da juna dangane da
wannan rana ta Ghadir.
Hanyoyin samun ta}awa a Ramadan
Kasantuwar
wannan wata mai albarka, wato watan Ramadan, wanda Allah (T) ya azurta mu da
azumtar sa. Daga cikin hikima da kuma manufa na wajabta mana Azumi a cikinsa,
shi ne domin mu samu Ta}awa, kamar yadda Allah (T) yake fa]i a cikin Al}ur’ani
mai girma, a suratul Ba}ara aya ta 183. “Ya ku wa]anda suka yi imani, an
wajabta maku azumi, kamar yadda aka wajabta shi ga wa]anda suke gabaninku,
domin ku samu ta}awa”.
Gudummawar mata a wa}i’ar Karbala.
Kasantuwar
wannan wata da muke ciki wato Muharram,wata ne na zaman makoki wanda akan tunatar
da juna dangane wannan wa}i’a ta karbala,misali abubuwan da suka auku gabanin
Ashura da abubuwan da suka auku ranar Ashura,da kuma abubuwan da suka biyo
bayan Ashura da kuma darussan da zamu koya daga wannan wa}i’ar ta Ashura dadai
sauran ~angarori dake da ala}a da wannan al’amarin na Ashura,
Darussa 12 daga rayuwar Sayyid Zakzaky (H)
Kasantuwar
wannan wata da muke ciki, wato Sha’aban, a cikinsa ne aka haifi Malaminmu, kuma
Jagoranmu a wannan gwagwarmaya ta tabbatar da addini, wato Sayyid Ibraheem
Yaqoub Zakzaky (H), a wannan munasabar ta cika shekaru 61 a duniya.
Darussa 12 daga rayuwar Imam Khumaini [KS]
Watan jiya,wato
watan jimada sani shine wata wanda aka haifi Imam khumaini a cikinsa,domin an
haife shine ran 20 ga watan jimada sani hijira na da shekara 1321,kuma ranar
haihuwarsa tayi muwafa}a da ranar haihuwar shugaban mataye
baki ]aya,wato
‘yar Manzon Allah [S],sayyidah fa]ima
[SA].
Bankwana da watan Ramadan
Inna Lillahi Wa Inna Ilahi Raji’un! Na rabuwa da kuma
tafiyar wannan babban ba}o mai girma da kuma daraja da ya ba}unce mu, wato
watan Ramadan. Wannan wata na Ramadan, wata ne wanda gabanin zuwan sa bayin
Allah (T) ke shau}insa (begensa) da kuma murna da farin ciki.
Bankwana da watan Ramadan (1) 1432 A.H
Inna-lillah-wa-inna- ilaihi- rajiun, na tafiya da kuma rabuwa da
wannan babban ba}o mai girma da kuma daraja da ya ba}uncemu,
wato watan ramadan. Domin idan mutum ya bincika zai ga cewa a duk watanni 12 da
ake da su a musulinci, babu wani wata da aka samu ruwayoyi daga Manzon Allah
(S)da kuma A’imma na ahlul-baiti (AS) na bankwana da shi da kuma umarni da yin haka face watan ramadan, wanda wannan ka
]ai ya isa ya nuna falala da darajan wannan watan.
ASHURA A MAHANGAR AHLUL-BAIT [AS] DA AHLUS- SUNNAH.
Da farko dai watan muharram, da waki’ar Ashura ta auku,wata ne na
juyayi da ba}in ciki
dama kuka,a mahanga ta Ahlul bait,tun daga farkon watan har }arshen sa.kuma ko da
a munasabobi na wiladar Aimma in mutum ya bincika zai ga babu wani imami daga
cikin Aimma wanda wiladar sa tazo a cikin watan muharram,wato akasin kamar
yadda a shi kuma watan shaaban babu wani Imami daga cikin Aimma wanda wafatin
sa yazo aciki.sai dai wiladar su.
Monday 4 February 2013
Arba’in ]in Imam Husain [AS]
Ranar arba’in ]in
Imam Husain [AS] rana ce wadda take da muhimmanci,musamman ma ga mabiya Ahlul bayt [AS],kuma kiyaye ranar
yana daga cikin alamomin mumini,kamar yadda haka yazo daga Imam Hassan Al-askari
[AS],in da yace, “Alamomin mumini [wato ]an shi’a] guda
biyar ne.
Alamomin Bayyanan Imam Mahdi[AF] da kuma Ladubban Zamanin Gaiba.
Alamomin bayyanar Imam Al-mahdi [AF] za’a iya
kasa su kashi uku.Na farko akwai alamomin da zasu gudana kafin bayyanarsa,Na
biyu akwai abubuwan da zasu gudana gaf
da bayyanarsa,misali shekarar da zai bayyana.Na ukku akwai alamomin da zasu
gudana lokacin da ya bayyana.Kuma duk bayanan wa]annan alamomin sun gangaro ne daga Manzon Allah [S] da kuma A’imma na
Ahlul-bayt [AS].
Sunday 3 February 2013
Hanyoyin samun kyawawan ]abi’u da kuma tsarkaka daga munanan ]abi’u.
Kamar yadda ya gabata a darasi na Akhla} na biyu, da yake an samu lokaci mai tsawo ba’a gabatar
da wannan darasi na Akhla}
ba,dalili ko
shine,kamar yadda aka ce a baya,lokaci bayan lokaci za’a ri}a
samun yankewar darasin,
Bayani kan tazkiyatu-Nafs.
A darasin da ya gabata, an tsaya ne a bayani dangane da
muhimmancin Tazkiyatu Nafs (tsarkake rai). Amma gabanin nan an yi bayanai a kan
ma’anar Akhla}, cewa shi ne, “sura ba ]iniyya ta mutum”. Wato siffa ta ba]ini
(~oye) ta mutum. Domin
shi mutum yana da ~angarorin guda biyu a halittarsa.
Bayani kan Ruhin mutum.
Darussa
guda uku da suka gabata na Akhla}, dukkansu suna matsayin shimfi]a da kuma
gabatarwa, a wannan darasi na Akhla}. A wannan darasi ne za a shiga ainihin
Akhla} ]in. Da farko dai mene ne Akhla}, a fannin Ilimi na Irfan? Ma’anar
Akhla},
Bayani kan muhimmancin Akhla}.
A darasin daya gabata,an ]anyi
bayani a ta}aice, kuma a dun}ule dangane da ilimin irfani da kuma cewa Akhla}, ~angare ne na shi wannan ilimin irfani,da kuma muhimmancin Akhla} da yadda kyakkyawan Akhla},
yake iya canza ma}iyi ya zama masoyi,kamar yadda aka bada misalai daga Manzon Allah [S] da
kuma Aimma na Ahlul Bait [AS]
Bayani kan Kalb {zuciya}.
A darasin daya gabata bayani ya gudana dangane da Tazkiyatus
Nafs wato tsarkake rai.A wannan darasi bayani zai kasance ne,dangane da ~angarori biyu na
tazkiyatus nafs.~angaren ba]ini wato zuciya da kuma ~angaren zahiri wato
ga~u~~a,Da farko ~angaren ba]ini wanda shine tazkiyya na zuciya wato tsarkake
zuciya,wanda in ya samu ]aya ~angaren zai iya samuwa wato ~angaren tazkiyya na
ga~u~~a.
Bayani kan fannin ilimin Akhla{.
Akhla}
~angare
ne na ilimin irfani,wato misali kamar yadda
ilimin fi}hu,yake
da manyan ~angarori guda biyu,wato Ibadat da Mu’amalat,
ilimin A}a’id
kuma yake da manyan ~angarori
guda biyar,Tauhid,Adl,Nubuwwa,Imama da kuma Ma’ad,to shima ilimin irfani yana da manyan ~angarori
guda biyu,sune AKHLA{,wanda wani lokaci
ake cewa IRFANIL-AMALIY,da kuma MA’ARIFA,wanda ake cewa IRFANIN-NAZARIY.
Daruusa 12 daga rayuwar Imam Mahdi (AS)
Kasantuwar
wannam wata da muke ciki, wato na Sha’aban a cikinsa ne aka haifi Hujjar Allah
a doron }asa, kuma Shugababn wannan zamani, wato Imam Mahdi (AS), kamar yadda
aka sani shi ne Imam na 12 a jerin }idaya na Imamai 12, wato shi ne Khalifan
Manzon Allah (S) na }arshe.
Darussa12daga rayuwar Imam Husain [AS] 2
Har yanzu muna cikin wannan wata na juyayi,ba}in ciki dama
kuka,musamman ga mabiya Ahlulbayt [AS],saboda yadda ake keta mutuncinsu da kuma
alfarmar iyalan gidan Manzon Allah [S] a cikin watan,wato akasin yadda wasu
sashen ‘yan uwa musulmi na madrasah ]in
Ahlus-Sunnah suka ]auke
shi wata na farin ciki da kuma yalwata wa iyali
Darussa daga rayuwar Ummul A’imma Fatima (AS).
Kasantuwar watan Jimada Sani 3 gare shi ne wafati ko
shahadar Ummul A’imma, wato Sayyada Zahra (AS), amma wannan a ruwayar da ta fi
shahara, domin akwai ruwayoyi da suka zo akasin haka, rubutu ko bayani dangane
da tarihi ko rayuwar Sayyada Fatima (AS), wani fage ne mai fa]in gaske, wanda
ba za a iya cimma ma}urarsa ba,
Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) 3
Kasantuwar
ba mu jima da fita daga wata mai albarka ba, wato watan Maulidin Manzon Allah
(S), kuma a darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) da ya gabata, in za a iya
tunawa mun tsaya ne a bayani dangane da Akhlak ]in Manzon Allah (S), wanda muka
kakkawo bayani kan kyautarsa a ta}aice da bayani a kan ha}urinsa da kuma
afuwarsa, shi ma a ta}aice.
Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) 2
Kasantuwar
wannan wata da muke ciki, wato na Rabi’ul Awwal, wata ne na wiladar Manzon
Allah da kuma Imam Sadiq (AS). Kamar yadda ya zo a tarihi a ruwayar Iyalan
Gidan Manzon Allah (S), an haifi Manzon Allah (S) ne a lokacin fitowar Alfijir
ranar Juma’a 17 ga Rabi’ul Awwal a shekarar da ake wa la}abi da shekarar Giwa.
Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) (1)
Kasantuwar
watan da muka fita, wato Safar a cikinsa ne wafatin Manzon Allah (S), a 28 gare
shi. Wannan a kan abin da Malaman Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) suka tafi a
kai. Amma abin da Malaman Madrasah ]in Ahlus Sunna suka tafi a kai shi ne, 22
ga watan Rabi’ul Awwal.
Darussa 12 daga rayuwar Imam Aliy Alhadi (AS)
Kasantuwar
3 ga watan Rajab ne wafatin Imam Aliy Alhadi (AS), kamar yadda aka saba a irin
wa]annan munasabobi na wafati da kuma shahadar Ma’asumai (AS), akan gabatar da
Darussa a ta}aice daidai gwargwado, na tarihinsu da kuma wasu ~angarori na
rayuwarsu daban-daban, da nufin su kasance madubi da za mu dubi kawukanmu da
kuma rayuwarmu da su, da kuma yin mujahada daidai ikonmu.
Darussa 12 daga rayuwar Imam Sadik [AS].1
Imam Sadi}[AS],kamar
yadda aka sani shine imam na 6 a jerin I mamai
12.kuma wannnan munasaba ce ta wafatinsa,domin
ya koma ga Allah [T] ne ranar 25 ga wannnan wata da muke ciki na
shawwal,a shekara ta 148 bayan hijra.Ya rasu sakamakon guba da aka sa mishi a
inabi,kuma ya rasu ya nada shekara 65, a wata ruwaya shekara 68
Darussa 12 daga rayuwar Imam Sadi} (AS) 2
Kamar
yadda ya gabata a munasabar wafatin Imam Sadi} (AS) a shekarar da ta gabata, an
tsaya ne a darussa na hu]u daga cikin rayuwarsa (AS, kuma aka ce insha Allah a
wata munasabar wafatinsa za a ]ora a kai.
Darussa 12 daga rayuwar Imam Ridhah [AS].
Kasantuwar wannan wata
da muke ciki na Zul –}ada
a cikinsa ne wilada da kuma wafatin Imam Ali ibn Musa Ar-Ridah[AS]suka
kasance,domin yazo a tarihi cewa an haife shi ranar Alhamis 11 ga watan zul }ada
a shekara ta 148 bayan hijira.Ya rasu 23 ga watan zul }ada
shekara ta 203 bayan hijira.Amma a wata ruwaya,yazo
a kan cewa rasuwarsa ta kasance a watan safar ne
Darussa 12 daga rayuwar Imam Musa Al-Kazim (AS)
Kasantuwar
wannan watan da muke ciki mai alfarma, wato watan Rajab 25 gare shi ne Shahadar
Imam Musa Alkazim (AS). Kamar yadda aka sani, shi ne Imam na bakwai a jerin kidaya
na Imamai 12 (AS) .
Imam Kazim (AS) an haife shi ne
ranar Lahadi 7 ga watan Safar shekara ta 128 bayan hijira, a wani gari da ake
ce wa Abwa, yana tsakanin Makka da Madina ne.
Darussa 12 daga rayuwar Imam Muhammad Al-Ba}ir [AS].
Wannan wata da muke ciki na zulhijja,bakwai gare shine
wafatin Imam Muhammad Ba}ir [AS] domin ya rasu ne ranar litinin 7 ga zulhijja shekara ta 114 bayan hijra.Ya
rasu ya na da shekaru 57 a duniya,muddan imamancinsa kuma shekara 19.Kabarinsa
yana madina ne,watau a Ba}i’a.Kuma
kamar yadda aka sani a jerin }idaya
na Imamai goma sha biyu,shine Imam na biyar.Kuma shi ]ane ga Imam Zainul Abidin [AS] ]an Imam Husain
[AS].
Darussa 12 daga rayuwar Imam Husain (AS) I
Kasantuwar
wannan watan da muke ciki, wato Muharram a cikinsa ne, 10 ga shi, shahadar Imam
Husain (AS). Shahadar tasa ta kasance ranar Juma’a, a wata ruwaya ranar Asabar shekara
ta 61 bayan hijira. Kuma shahadar tasa ta kasance kamar yadda aka sani a
Karbala. Tsakanin isar sa Karbala da shahadarsa, kwanaki takwas ne.
Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan (AS)
Kasantuwar
wata da muka fita na Safar, 28 gare shi, shi ne wafatin Imam Hasan (AS) a wata
ruwaya kuma 7 ga Safar, da ma wani lokaci akan samu wannan sa~anin na ruwayoyi
tsakanin Malaman tarihi na wilada ko wafatin Ma’asummin (AS), wato Manzon Allah
(S) da kuma A’imma na Ahlul Baiti (AS) wanda akan asasin wa]annan ruwayoyi
mutum zai ga mabiya Ahlul Baiti (AS) a wata nahiya sun tafi a kan ruwaya kaza
wata nahiyar kuma sun tafi a kan ruwaya kaza,
Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan Al-Askari (AS)
Kasantuwar
ran 8 ga watan jiya, wato Rabi’ul Awwal shi ne ya yi daidai da wafatin Imam
Hasan Al-Askar. Kamar yadda ya zo a tarihinsa, ya rasu ne ranar Juma’a 8 ga
Rabi’ul Awwal Hijira ta 260. Imam Hasan Al-askari (AS) an haife shi ne a
Madina, a watan Rabi’us-Sani, sai dai an samu sa~ani dangane da ranar da aka
haife shi, da kuma nawa ga wata aka haife shi.
Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali Zainul Abidin (AS)
Kasantuwar watan da muka fita wato na Muharram, 25 gare
shi ne wafatin Imam Ali Zainul Abidin (AS) a wata ruwaya 12 gare shi, saboda
haka kamar yadda aka saba a irin wa]annan munasabobin na wafatin A’imma na
Ahlul Baiti (AS) akan gabatar da darussa a ta}aice daga rayuwarsu da nufin su
kasance madubi da za mu dubi rayuwarmu da kuma yin sa’ayi na Mujahada
Subscribe to:
Posts (Atom)