A darasin da ya gabata,wato darasi na biyar,an kammala
shinfi]a da kuma
gabatarwa,aka yi bayanin cewa a darasi na gaba in sha Allah, za a shiga babin
farko wato babin tsarki.To kasantuwar babobin fi}hu suna da yawa,wa]ansu fu}aha
sun tafi a kan babobi hamsin ne,wato tun daga babin tsarki zuwa babin
diyyat.
wa]annan babobi dukkan su suna da muhimman ci,amma muhimman cin wa]ansu
babobin yafi wasu.wasu mas’alolin wajibine ma sanin su,kamar yadda Imam
Khumaini yayi bayani a cikin littafin Tahrirul wasila a gabatarwa a mas’ala ta
23,yana cewa wajibi ne sanin mas’alolin shakka da sahawu da dai makaman tansu
na abin da yake galibi mahallil ibtila’a.wato ake fuskantar jarrabawar sa
yau da kullum.To akan asasin haka nai
tunanin farawa da irin wa]annan babobi muhimmai na mahallil ibtila’a.
Saboda
haka wannan darasi zai guda ne akan
mas’alolin shakka da sujudi sahwu da Raka’atul-ihtiyat ko
salatu-ihtiyat,salatu-ihtiyat, raka’a ce ko raka’oi da ake yi domin gyara wasu
shakkoki da suka auku acikin sallah,bayanin haka zai kasance nan gaba.wani
tambihi anan shine Raka’atul ihtiyat ko salatu-ihtiyat,a fi}hun Imamiyya kawai
yake,wato babu shi a fi}hun Ahlus-sunna,kamar yadda har wala yau ba sujudar
}abliyya a fi}hun imamiyya sai sujudar ba’adiyya.Da yake tun farkon wannan
darasi na fi}hu an yi bayani za a dunga mu}arana tsakanin mazhabobin
Ahlus-sunna da na imamiyya,amma za a }arfafa a fi}hun imamiyya ne a
darussan.Saboda haka a wannan mas’ala ta sujudar }abliyya da baadiyya,mazhabar
malikiyya dashafi’iyya da hanbaliyya sune ka]ai suka tafi akan yin sujudar
}abliyya,amma mazhabar hanafiyya da imamiyya sun tafi akan rashin yinta,wato
sai sujudar baadiyya kawai. Saboda
haka bayani a nan zai kasance a matakai guda biyu1-Bayani kan shakka a sallah.2-Bayani
kan raka’ar ihtiyat. 1-Bayani
kan shakka a sallah-Shakka a sallah ya kasu kashi ukku,na farko shakka a raka’oin ita sallar,misali mutum ne
yana sallah sai yana shakka raka’a 2 yayi ko 3.ko kuma raka’a 3 yayi ko 4 da
dai sauran su,to ya zai yi.Na biyu ko shakka a ayyukan sallar,misali mutum ne
yana sallah,bayan daya soma karatun fatiha ko kafin ya soma karatun fatiha sai
yana shakka yayi takbiratul-ihram ko bai yiba.ko kuma wani misali yana
sallah,yana cikin karatun sura sai shakka tazo masa na ya karanta fatiha ko bai
karanta ba da dai sauran su,to ya zai yi.Na ukku ko shakka a asalin yin
sallar,misali yana sallar asar sai shakka tazo masa yayi sallar azahar ko bai
yi ba,da dai sauran su,to ya zai yi.Bayani dangane da wa]annan shakkoki guda ukku a ta}aice.
Na
farko shakka a raka’oin sallah,Idan irin wannan shakka ta auku,A- akwai wadda
take ~ata sallah.B-akwai wadda za a iya gyarawa.C-akwai wadda ba a la akari da
ita.Shakka a raka’oin da suke ~ata sallah sune.sallolin farilla mai raka’a
2,raka’a 3,da kuma raka’oi 2 na farko a sallolin farilla masu raka,a 4.Saboda
haka idan mutum na sallar asuba ko magariba sai shakka ta same shi, na raka’a
nawa yayi,misali yana shakkar raka’a ]aya yayi ko biyu.To anan sallah ta ~aci,
sai dai ya soma sabuwa,Haka nan ma a raka’a oi biyu na farko na sallar
azahar,la’asar da kuma isha’a,idan shakka ta samu mutum a wa]annan raka’oi biyu
na farkon su, wato yana shakkar raka’a 1 yayi ko 2,to anan ma sallah ta
~aci.Haka nan a sallah ta }asaru,ita ma idan mutun na yinta sai shakka ta same
shi,yana tunanin raka’a 1 yayi ko 2,to shima sallah ta ~aci,sai dai ya sake
sabuwar sallah.Wa]annan da aka kawo sune
shakkar da in ta auku,a raka’oin su,suke ~ata sallah.Sai kuma shakkar da
inta auku,za a iya gyarawa, wato sallah bata ~aci ba.Su guda takwas
ne,sune1-Shakka tsakanin raka’a 2 da 3 amma fa da shara]in bayan ya kamala
sujuda guda biyu,to a nan sai yayi gini a kan raka’a ukku,sai yazo da raka’a ta
4.ya cika sallarsa,bayan ya sallame sallar,zai yi raka’ar ihtiya]i,a nan yana
da za~i wato na raka’ar ihtiya] ]in,ko dai yayi raka’a ]aya a tsaye ko kuma
raka’a biyu a zaune.In-sha Allah nan gaba ka]an bayani zai zo na yadda ake yin
wannan sallah ta ihtiya]i da kuma wasu mas’alolin ta.2-Shakka tsakanin raka’a 3
da 4,to haka in ta faru sai mutum yayi gini a kan hu]u yayi,hukuncin gyaran sa
kamar na baya ne.wato bayan ya kamala sallar sa,zai yi raka’a ]aya ta ihtiya]i
a tsaye ko kuma raka’a biyu na ihtiya]i a zaune.3-Shakka tsakanin raka’a 2 da 4
amma da shara]in bayan ya kamala sujuda
guda biyu wato na raka’a biyun farkon,to a nan in haka ya faru,abin da
zai yi shine sai yayi gini a kan raka’a hu]u yayi,bayan ya sallame sallar sai
yayi raka’ar ihtiya]i guda biyu a tsaye.4-Shakka tsakanin raka’a 2 ko 3 ko 4,to
anan idan mutun na sallah haka ta same shi,yadda zai yi shine,zai yi gini a kan
hu]u yayi,bayan ya sallame sallar sa,zai yi raka’ar ihtiya]i biyu a tsaye da
kuma biyu a zaune.sai dai anan na tsayen zai soma gabatarwa wato kafin raka’oin
zaunan.5-Shakka tsakanin raka’a 4 da 5,wato mutum na sallah sai shakka ta zo
mashi,raka’a 4 yayi ko 5,to a nan akwai fuskoki guda biyu,na farko ko haka ya
faru ne a lokacin daya ]ago kai a sujuda ta }arshe,to anan zai yi gini akan
hu]u yayi,saboda haka sai yayi tashahhud wato tahiya yayi sallama.bayan haka
sai yayi sujudu sahwu, wato baadiyya,fuska ta biyu ko haka ya faru ne yana
tsaye, to a nan hukuncin sa irin na wanda yayi shakka ne,tsakanin 3 da 4,sai
yayi gini akan 4,kuma wajibi ne ya rusa tsayuwar sa,wato zai zauna ne,yayi
tahiya yayi sallama,bayan haka kuma sai yayi raka’ar ihtiya] guda biyu a zaune,
ko kuma guda ]aya a tsaye. 6-Shakka tsakanin raka’a 3 da 5,lokacin da mutum
yake tsaye,shima wannan hukuncin sa ko abinda zai yin a irin wanda yayi shakka
ne tsakanin 2 da 4,wato zai yi gini a kan hu]u yayi,bayan ya sallame sai yayi
raka’ar ihtiya]i guda biyu a tsaye. 7-Shakka tsakanin raka’a 3 da 4 da 5
lokacin da mutum yake tsaye,shima abinda
zai yi na shigen wanda yayi shakka ne tsakanin 2 da 3 da 4 wato zai ]auka hu]u
yayi,bayan yayi sallamar sallarsa sai yayi raka’ar ihtiya]i biyu a tsaye da
kuma biyu a zaune. 8-Shakka tsakanin 5 da 6,yana tsaye,to shima hukuncin
sa,irin na wanda yayi shakka ne tsakanin 4 da 5,saboda haka zai rusa tsayuwar
sa ta biyar wato ya zauna,bayan yayi tashahhud ko tahiya yayi sallama,sai yayi
sujudu sahawu kawai,sai dai abin lura a nan kamar yadda yazo a hukunci sujudar
sahawun zai yi sau biyu ne,Wa]annan sune shakkoki guda takwas,wa]anda in sun
auku za a iya gyara akai.Amma Imamu khumaini yayi bayani cewa,shakka ta nombar
5,6,7,8.bayan mutum yayi gyaran su,to ihtiya]i is-tihibabi.wato taka tsan-tsan
shine mutum ya sake sallar.
Sai
kuma wasu mas’aloli da suke da ala}a da
shakka na raka’oi.Mas’ala-1-Idan irin wannan shakka ta auku ga mutum,sai daga
baya ta gushe,to shi kenan ba komi akan sa,misali mutum yana sallah sai shakka
tazo masa akan raka’a ta 3 yake ko ta 4,yana cikin wannan tunanin sai ya}ini
yazo masa akan raka’a ta 3 yake,to anan shike nan ba komi akan sa,in da
wa]ancan hukunce-hukunce na gyara yake hawa kan mutum sai idan shakkar bata
gushe ba,amma idan ta gushe,shika nan ba komi kan mutum.Mas’ala ta-2-Dukkan
shakkok na raka’oii wa]anda basu cikin wa]annan guda takwas da aka ambata,suna
wajab tar da ~acin sallah,kuma idan aka lura dukkak wa]annan shakkoki guda
takwas da aka ambata,a sallah mai raka’a hu]u ne suke,wato sallar
azahar,la’asar da kuma isha’i.kuma abun lura na biyu shine dukkan su su kan
kasan ce ne bayan raka’a biyu na farkon su,domin shakka a raka’a biyun farkon
su,yana ~ata sallah ne.wato in ya auku baza a,iya gyarawa ba,sai dai a sake
sabuwar sallah.Mas’ala ta-3-Wanda bai iya Tashi tsaye yayi sallah,sai irin
wannan shakka da ake raka’atul-ihtiyat a tsaye ta bijiro masa,to zai yita a
zaune ne.Mas’ala ta-4-Bai halatta ga mutum idan irin wa]annan shakkoki da ake iya gyarawa sun bijiro masa yace ya
yenke sallah ya fari sabuwa,abin day a wajaba akan sa shine,yayi aiki, irin na
wannan shakkar.Mas’ala ta-5-Idan ]ayan wa]annan shakkoki guda takwas ya bijiro
ma mutum,alhali yana cikin sallah,kuma bai san yadda zai yi ba,to anan ya
danganta ]ayan biyu,in akwai yelwar lokaci na sallar,kuma zai iya zuwa ya
bincika,misali ta hanyar ya tambaya ko ya bincika a littafi,to anan Imam
khumain yace mutum na iya yenke sallar,ya bincika ]in.amma yace mutum zai iya
kamala sallar da abin da mutum yake tsammani haka ne zai yi,bayan sallar sai ya
bincika.in yayi muwafa}a yace ya wadatar, in kuma bai yi ba to sai ya sake
sallah.Wannan hukunci in akwai yelwar lokaci kenan kuma mutum zai iya
bincikawa.To idan ba yelwar lokaci,ko kuma mutum ba zai iya bincikawa ba,to
anan Imam yace abin da ya ayyana akan sa, shine aiki da abinda yafi rinjaye
azuciyar sa,misali yana tunanin kaza ne zai yi wani kuma tunanin nace masa kaza
ne,wato sai yayi aiki da abin da yafi rinjaye a tunanin sa,in kuma ba wanda ya
rinjaya to sai yayi aiki da kowanne,ya kammala sallar haka,bayan nan sai ya
sake sabuwar sallah a matsayin ihtiya]i.Mas’ala ta-6-Zato a adadin raka’oi yana
matsayin ya}ini ne,misali mutum na sallah sai yana zaton a raka’a ta 2 yake,to
anan zai tafi akan raka’a ta biyun yake,haka nan yana zaton a ta 3 yake to zai
tafi a kan ta ukkun,da yake shi zato yafi shakka }arfi,domin akwai shakka,akwai
zato,akwai kuma ya}ini,to a wannan mas’ala ta zato a adadin raka’oi sai shari’a
taba zato matsayi na ya}ini.kuma wani tambihi anan shine idan zato ya bijiro ma
mutum koda a sallah mai raka’a biyu ne misali kamar sallar asuba,ko ta magriba
ko kuma biyun farko na sallah mai raka’a hu]u,to anan zai yi aiki da zaton kuma
sallah bata ~aci ba,sa~anin ko inda shakka ne ta auku,a misalan da aka bayar to
anan sallah ta ~aci.
Bayanin
yadda ake yin sallar ihtiya]i ko raka’ar ihtiya]i.Raka’ar ihtiya]i wajiba
ce,saboda haka in ta samu mutum dole ne yazo da ita,wato bai halatta mutum ya
bar ta yace ya sake sabuwar sallah ko kuma mutum yace yayi baadiyya a makwafin
ta.kuma mutum na sallame sallah,mubashara tan zai yi ta,wato ba tare da yayi
jinkiri ba,misali ace baadiyya mutum zai yi,ai yana sallamewa zai yita kai
tsaye,to ita ma haka ne.kaifiyya ]in yin ta,wato yadda ake yinta shine,bayan
mutum yayi sallama sai ya mi}e tsaye da niyyar yin raka’ar ihtiya]i,sai yayi
kabbarar harama,ya biya fatiha,amma ba a biya mata sura,fatiha kawai ake
karantaw,kuma karatun a ~oye ba abayyane ba,kuma ba a }unuti a cikin ta,bayan mutum
ya kammala fatihar sai yayi ruku’u da sujuda guda biyu,bayan haka sai ya zauna
yayi tashahhud wato tahiya,bayan haka sai yayi sallama,shike nan,ya gama.To
haka zai yi ko da yazo akan cewa raka’atul-ihtiya] ]in a zaune ne zai yi,da
yake wani lokaci ya kanzo a kan cewa a tsaye mutum zai yi wani lokaci kuma a
zaune,wani lokaci kuma a tsaye da zaune.to ko ta wace fuska tazo,wannan dai
shine yadda ake yin ta.Sai wasu mas’aloli da suke da ala}a da
raka’atul-ihtiyat.Mas’ala ta -1-Idan mutum wanda sallar ihtiya]I ta hau kan
sa,to bayan day a gama sallah,sai shakka tazo masa yayi sallar ihtiya]in ko bai
yiba,to in bayan fitar lokacin sallah ne shakkar tazo masa,to anan zai yi watsi
ne da ita,in ko a cikin lokaci ne,kuma bai shiga cikin wani aiki na dabam
ba,kuma bai zo da abinda yake ~ata sallah ba,kuma lokaci bai tsawaita ba,to sai
yayi gini akan bai zo da ita ba,wato ma’ana mutum sai yayi ta.misali ace dama
yana nan inda yayi sallar, kuma bai yi wa]annan ababen da aka ambata ba,nan
take sai yayi sallar ihtiya]in.Mas’ala ta -2-Da zai yi shakka a wani aiki daga
ayyukan salatul-ihtiya],to zai zo dashi idan yana a mahallin,in ko ya wuce
mahallin aikin sai yayi gini akan
yayi,to da zai yi shakka akan raka’ointa,a nan zai yi gini ne,akan abin da yafi
yawa,misali yana shakka raka’a 1 yayi ko 2.to sai ya ]auka biyu ne yayi,to amma
inda shakka yake biyu ne yayi ko ukku, to anan zai ]auka biyu ne yayi.Mas’la ta
-3-Da mutum wanda sallar ihtiya] ta hau kan sa,to da ya gama sallah sai ya
manta,ya shiga wata sallah ta nafila ce ko ta farilla,to a nan zai yank e
sallar ne,yazo da sallar ihtiya] ]in.In-sha Allah a darasi na gaba,za a yi
bayani kan shakka a ayyukan sallah da kuma shakka a asalin yin sallar da kuma
sujudi sahawu.
No comments:
Post a Comment