Alamomin bayyanar Imam Al-mahdi [AF] za’a iya
kasa su kashi uku.Na farko akwai alamomin da zasu gudana kafin bayyanarsa,Na
biyu akwai abubuwan da zasu gudana gaf
da bayyanarsa,misali shekarar da zai bayyana.Na ukku akwai alamomin da zasu
gudana lokacin da ya bayyana.Kuma duk bayanan wa]annan alamomin sun gangaro ne daga Manzon Allah [S] da kuma A’imma na
Ahlul-bayt [AS].
Saboda haka da mutum zai bibiyi littafan Hadisai na wa]annan makarantu guda biyu,wato na madrasah ]in
shi’a,da kuma madrasah ]in sunna,zai ci karo da
Hadisan da suke bayani dangane da alamomin bayyanar Imam Al-mahdi [AF]. Har ila yau kuma da mutum zai bibiyi littafan tarihi,musamman littafan da malaman imamiyyah
suka rubuta,zai ga cewa a tarihin Imam Mahdi [AF] galibi sukan kawo alamomin
bayyanarsa.kyakkyawan misali anan shine littafan tarihi na Muntahal A’mal na
shaikh Abbas Al-}ummiy. Littafin A’immatuna da kuma littafin Siratu Rasul wa Ahlulbayt
[AS];dukkan wa]annan littafan guda uku,a juzu’insu na biyu,malaman da suka rubuta su, sun
fitar da fasali ko babi da ke bayanin alamomin bayyanar Imam Mahdi [AS]. Baya
ga haka ma akwai malamai na wa]annan makarantu guda biyu da suka rubuta littafai khususan kan alamomin
bayyanar, Imam Mahdi [AS] Misali anan shine wanda shaikh Usman [an Fodio ya rubuta mai suna “ Alamatu Khurujul Mahdi”.Akwai kuma wanda ]ansa shaikh Ahmad Rufai ya rubuta mai wannan taken.Saboda haka anan insha
Allah za’a kawo bayanin wa]annan alamomin a ta}aice akan tar-tibin da aka ambata a sama,wato guda uku. Na
farko,alamomin da zasu gudana kafin bayyanarsa,Akwai alamomi da dama,amma anan
za’a kawo guda 10 domin gudun tsawaitawa.
1.Yawaitar zalunci da kuma danniya a duniya,kamar
yadda yazo daga Imam Ba}ir [AS] yace, “Imam Mahdi [AS] ba zai bayyana ba har sai zalunci ya kai
tsororowarsa”. A kuma wani hadisi wanda aka samo daga Manzon Allah [S] yace,
“ko da duniya ta kasance saura yini ]aya ne,to Allah [T] zai
tsawaita yinin domin Mahdi, ya cika ta da adalci kamar yadda aka ci kata da
zalunci da kuma danniya”.Wanda wannan bayyane yake a wannan zamanin,wato yadda
zalunci da kuma danniya suka cika duniya.
2.Yawai tuwar
kashe-kashe da mutuwa da kuma musibobi a bayan }asa.An
samo daga Imam Aliy[AS] yace, “Mahdi ba zai bayyana ba har sai an kashe ]aya bisa uku na mutanen duniya”.wannan magana ta Imam Aliy [AS] tazo
acikin littafin nan mai suna Al-burhan fi Alamati Mahdi Akhiraz-zaman,wanda malami ne na Ahlus Sunna
ya rubuta,Wannan shima a bayyane yake a wannan zamanin.Mu duba yadda kashe-kashe
ya yawaita a bayan }asa da mace-mace na fuj’a da musibobi na ambaliya,girgizar }asa,da dai sauransu.
3.Yawaitar fasadi da kuma sa~o a bayan }asa.Mu duba yadda ~arna da sa~on Allah[T] suka yawaita a duniya,wa]ansu ma sun mai da
fasadi da Zunubi a matsayin ado da kuma sana’a.
4.Ci gaban ilimin kimiyya da kuma
fasaha.Wannan shima a bayyane yake a wannan zamanin,mu duba yadda ilimin
kimiyya da fasaha ya kai matsayi mai girma,kuma kullum ci gaba ake samu a
wannan fagen,wanda in mutum ya duba wasu zantuka na Aimma na Ahlulbayt [AS] da suka
fa]a wa mabiyansu dangane da ilimin kimiyya da fasaha a wancan lokacin,da
yawansu zai yi masu wahalan fahimta,amma mutumin wannan zamanin zai ga abin a
bayyane.ga misali guda biyu, acikin littafin hadisi na Al-kafi akwai hadisi da
aka samu daga Imam sadi} [AS],wanda abinda hadisin ya }unsa shine cewa idan Imam
Mahdi [AS] ya bayyana zai kasance yana magana a waje ]aya
ne,amma sauran mutane na sassan duniya daban-daban zai kasance suna jinsa kuma
suna ganinsa,alhali kuma yana waje ]aya ne,[misali a ce yana
Makka yana jawabi,amma mutanen dake Iran,yaman,misra,madina da dai sauran
sassan duniya, a lokaci guda suna kallonsa,kuma suna jinsa],fahimtar haka a
wancan lokacin tana da wahala,amma ga mutumin wannan zamanin mai sau}i ne,mutum yana magana a talabijin a waje ]aya
na duniya,amma sauran mutane na sassan duniya daban-daban suna kallonsa,kuma
suna jinsa. Har ila yau kuma
a wani hadisi da aka samo daga Imam sadi} [AS] yana cewa, “Mumini
a zamanin }a’im[wato Imam Mahdi [AF] yana gabashin duniya,zai kasance yana ganin ]an uwansa da yake yammacin duniya.Haka kuma wanda yake yammacin duniya
zai kasance yana ganin wanda yake gabashin duniya;.Wanda wannan dai yana nuni
ne da irin ci gaban da ilimin kimiyya da fasaha zai kai.
5.Ta~ar~arewar tattalin
arziki na duniya da kuma tsadar kayayyaki.shima wannan yana daga cikin alamomin
bayyanar Imam Mahdi [AF],kamar yadda yazo a littafai.Wanda shima wannan bayyane
yake a wannan zamanin.Mu dubi yadda tattalin arzikin duniya, yake ta ta~ar~arewa da kuma yadda tsadar kayayyaki suke a yanzu a kasuwannin duniya.Wanda
wannan kawai ya isa ya nuna mana matsayin da A’imma na Ahlulbayt [AS] suke
dashi,wanda kuma dama sune wa]anda Manzon Allah [S] ya bar ma wannan al’ummar da su yi ri}o dasu a bayansa.Zantukan da suka fa]i a zamaninsu, sama da
shekaru dubu da wani abu da suka wuce,amma yau gashi suna gudana a aikace a
wannan zamanin namu.
6.Nisantar koyarwar addinin musulunci da kuma }e}ashewar zukata,shima wannan bayyane yake a wannan zamanin.Mu dubi yadda addini
ya zama ba}o,haka nan ma wanda ya siffanta dashi.har ma suka }e}ashe,idanuwa suka
bushe.
7.Yawaitar rarraba da kuma sa~ani tsakanin musulmi da kuma samuwar sa~ani
da rarraba tsakanin mabiya Ahlul Baiti [AS].shima wannan yana daga cikin
alamomin bayyanarsa.Kamar yadda yazo a wasu hadisai daga Ma’asumai [AS].Mai bu}atar ganin wa]annan hadisai yana iya duba littafi mai suna “Imam Al-mahdi- fil Ahadis-
mush-taraka –Bainas- Sunna was-shi’a”.ko kuma littafin muntahal Amal,juzu’I na
biyu na shaikh Abbas Al-}ummy,wato mawallafin littafin mafatihul jinan.
8.Yawaitar bayyanar ayoyi daban-daban a
halittun Allah[T].shima wannan a bayyane yake a wannan zamanin,musamman ma a
‘yan shekarunnan,sai ka ga an samu wani ganye ko itaciya ko wuri ko kuma wani
abu dai da sunan Allah [T] a jiki,ko sunan Manzon Allah [S],ko wata aya ta Al-}ur’ani mai girma,ko kuma abinda yayi kama da haka,duk wa]annan suna daga cikin alamomin bayyanarsa [AF].
9.Samun yun}urin neman sauyi da
kuma gwagwarmaya a sassan duniya daban-daban.Shima wannan a bayyane yake
awannan zamanin,mutum ya duba musamman a }asashen musulmi,zai ga
cewa akwai yun}uri da kuma gwagwarmaya ta neman sauyi,wanda ire-iren wa]annan yun}uri da kuma gwagwarmayar kamar shinfi]a ce ga zuwan Imam
Mahdi [AS] kamar yadda bayanai suka zo a littafai.Akwai ma wa]anda har ha}arsu ta neman sauyi da gwagwarmaya ta cimma ruwa.Misali,kafuwar jamhuriyar
musulunci ta iran.
10.Ya]uwar ilimin Ahlulbayt
[AS] a bayan }asa.shima wannan bayyane yake a wannan zamanin,mutum ya dubi yadda
wilaya da ilimin Ahlulbayt [AS] suke ta ya]uwa a sassan duniya
daban-daban,in ma mutum bai san wani waje ba,to ya duba nan in da yake,wannan
ma yana daga cikin alamomin bayyanarsa kamar yadda yazo,da dai sauran alamomin wa]anda ba za’a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa. Sai kuma kashi na biyu wato
alamomin da zasu guda na gaf da bayyanarsa.Saboda gudun tsawaitawa za’a kawo
guda biyar: 1.Bayyanar Dajjal:Yazo
akan cewa dajjal zai kasance gaf da bayyanarsa.Bayannan shi dajjal ]in da irin
~arna da kuma ta’asar da zai yi mutum sai ya koma a littafai,musamman na hadisai
domin samun bayanai akai.in mutum ya bincika zai ga akwai adduo’in da aka samo daga
Manzon Allah da kuma Ahlulbayt daban-daban na neman tsari daga sharrin shi
Dajjalda kuma fitinarsa. 2.khusufin
rana a tsakiyan watan ramadan da kuma }arshen watan ramadan ]in,wato sa~anin yadda ya saba gudana na cewa khusufin wata,ya kan kasance a tsakiyar
wata, na rana kuma }arshen wata.Akan wannan ma akwai hadisi da yazo daga Imam Ba}ir [AS] yace, “Ayoyi guda biyu zasu kasance gabanin tsayawar }a’im,wa]anda basu ta~a kasancewa a doron }asa ba.sune khusufin rana a tsakiyar watan ramadan,da kuma khusufin
wata }arshensa. 3.Kashe
Nafsuz-zakiyyah:yana daga cikin jikokin Manzon Allah [S],za’a kashe shi a makka
ne tsakanin ruknu da ma}amu Ibrahim [AS],sunansa shine muhammad ibn Hassan,ya mazo a hadisi cewa
tsakanin kashe shi da kuma bayyanar Imam Mahdi [AF] kwana 15 ne. 4.Jin
kira daga sama,hadisai da dama sunzo da bayani akan haka,cewa gaf da Imam Mahdi
[AF] zai bayyana,a daren 23 a watan ramadan, za’ayi kira da sauti daga
sama,wanda yazo akan cewa duk wanda yake doron }asa
ko’ina yake zai ji wannan kira,abinda kiran yake cewa shine; “yaku taron
halitta!Ga Mahdi na Ahlulbaitin Muhammad, kuyi masa bai’a,ku shirya,kada ku sa~a wa al’amarinsa ku ~ace!”. 5.Bayyanar
tafin hannu a sama,A wata ruwaya fuska da }irji
da kuma tafin hannu zasu bayyana a tsakiyar }wallon
rana.wannan kenan a ta}aice. Sai
kuma alamominsa da zasu kasance a lokacin daya bayyana; shima saboda gudun
tsawaitawa za a kawo guda uku:
1.Yazo akan cewa zai bayyana a makka,ranar
Ashura wato ranar shahadar Imam Husain [AS],duk da akwai ruwayoyi dabam dabam
kan wannan al’amari.Haka nan yazo akan cewa zai bayyana ranar jumma’ce,a wani
zan ce kuma ranar Asabar.Haka nan kuma
shekarar da zai bayyana zata kasance
akan witri,wato ko dai shekarar ta kasance da1,Ko da3,ko da5,ko da7,ko da
9.wannan shima yazo a hadisi,gamai bu}atar ganin wa]annan hadisai da suka zo da wannan,yana iya duba littafi mai suna,Mun
takhabul- asri fil- Imamis-sani- Ashra’’ na Ayyatullahi Golfeganiy.
Sai dai tambihi a nan kada mutum ya samu ish-kal
a nan cewa hadisai ba sun ayyana lokaci ba ne, wato ba su yi karo da hadisan da suka zo na ayyana
lokacin bayyanar Imam Mahadi (AF) ba, domin wace Ashura ce ba a ayyana ba, wace
juma’a ce ko asabar, ba a ayyana ba. Haka nan wace ta 1, 3, 5, 7, 9, ba a bayyana
ba. A ita ruwayar da ta zo cewa zai bayyana a makkah, yazo akan idan ya bayyana
]in, farkon abun da zai fara furuci da shi, shi ne wannan ayar ‘Ba}iyyatullahi khairun-lakum in kuntum muminin`.
2. Ha]uwar mataimakansa su
313 a lokaci guda, wato za su ha]u, za su kuma kasance ne daga sassan duniya daban-daban, amma kuma bisa
ikon Allah (T) yana bayyana wa]annan matamaika nasa 313, za su ha]u tare da shi. Kamar
yadda Allah (T) ya ke fa]i a cikin al-kur’ani mai girma “Duk inda kuke Allah zai zo da ku baki ]aya, kuma Allah mai iko ne akan komai.
3. Saukar Annabi Isah (AS). Shi ma wannan zai kasance idan ya bayyana. Kuma hadisai na
shi’a da sunna sun zo da bayani akan haka. Wannan ke nan baki daya a ta}aice dangane da alamomin bayyanar Imam Mahdi (AF).
Sai kuma abin da ya shafi ladubban gaiba, wato
fakuwarsa. Da yake zamuna a wannan al’umman sun kasu kashi hu]u, wato wa]anda suke da ala}a da Ma’asumin (AS) na farko akwai asrun-nubbuwa, wato zamanin da Manzon
Allah (S) yake a raye. Na biyu akwai asrul-Imama, wato zamanin da Imaman Ahlul
bait 12
suke raye. Na uku, asrul-gaiba, wato zamanin da Imam Mahadi (AF) ya ke ba a
bayyane ba. Shine wannan zamanin da muke a ciki, na hu]u.
Akwai asruz-zuhur, wato zamanin da Imam Mahdi (AF) ya ke a bayyane.
To wannan zamani da muke ciki, wato zamanin
gaiba, akwai wasu ladubba da ake son ko wane mutum mace da namiji musamman ma
mabiya ahlul baiti (AS) da su lizimta, wato ta hanyar aikata wa]annan ladubban da siffantuwa da su. A kan haka ne malamai da dama a
madarasah ]in ahlul baiti (AS) sun yi
wallafe wallafe na littafai da suke bayanin wa]annan ladubban, da ake son lizimtar su a zamanin gaiba. Alal misali akwai littafi mai suna “adabu asril gaiba”, na sheikh Hussain
khoraniy da kuma littafi mai suna “wazifatul –anami- fi-
zamani- gaibatil- Imam (AS), na Ayatullahi Mirza Muhammad At-ta}iy al-musawiy, wanda wa]annan littafai guda biyu babu komai a cikin su, face bayanan wa]annan ladubba. Amma saboda gudun tsawaitawa za a kawo 17 daga cikin su.
1.
SANINSA: Wato mutum ya san Imam Mahadi (AF) sani a dun}ule ko a war-ware. Wato ya san shi
ta fuskoki daban-daban. Misali sani ta fuskacin matsayin sa,nasabar sa, shaksiyyar
sa, wiladar sa, gaiba ]in sa,
zuhur ]in sa,
da dai sauran su. Akwai ma hadisai da suka zo suna nuni ga muhinmancin kowane
musulmi ya san Imamin zamanin sa. Alal misali akwai hadisin da ya zo a cikin
littafi mai suna « kamaluddin wa tamamun ni’ima » na shaikh sadu}, yana cewa “Duk wanda
ya mutu amma bai san Imam ]in
zamaninsa ba, to yayi mutuwar jahiliyya”. Har ila yau wani hadisi wanda shaikh [usi ya ruwaito a
littafin sa mai suna ‘gaiba` hadisin yana cewa « wanda ya san Imamin sa,
sannan ya mutu gabanin bayyanarsa, to yana da lada kamar wanda ya kasance tare
da shi lokacin bayyanar sa ».
2.
ADDU’A:
Na farko wadda ake yiwa Imam Mahadi (AF), akwai wadda aka ruwaito daga Imam Ridah
(AS) ya yi umarni da a karanta wa Imam Mahdi (AF). Ga mai bu}ata yana iya duba mafatihul jinan, tana kusa
da dua’un nudba. Akwai kuma wata addu’an da ake son, adun ga karantawa bayan
kowace sallah. Addu’ar tana farawa ne da
“Allahumma- Kun-liwaliyyika - hujjatu bin Hassan………”. Da kuma yawaita addu’ar ,
Allah ya gaggauta bayyanarsa. Domin ya zo akan cewa bayin Allah da dama da suka
sadu da shi, cikin abun da yake ce masu shine,Su yawaita addu’ar Allah ya gaggauta bayyanarsa. Na biyu :daga
cikin addu’ar da ake son mutum ya yawaita biyata. Akwai addu’a wadda aka samo daga Imam
Sadi} (AS)
ana son ya biyata, da lizimtar ta a zamanin gaiba itace, “YA ALLAH YA RAHMAN YA RAHEEM YA MU{ALLIBUL {ULUB SABBIT {ALBIY ALA DINIK” Ana
cema wannan addu’ar du’a’ul gari}. Akwai
kuma wata addu’a wadda itama ana son lizamtar tana soma wa da “Allahumma arrifni naf.
3.
3. YIN ZIYARA GARE SHI:Shaikh
kaf’ami yace a cikin littafinsa mai suna
baladul Amin,mustahabbi ne ziyartar Imam
Mahdi[AF] a kowane waje a kuma kowane lokaci.kuma ziyarar tasa tazo da sigogi
dabam dabam.A}alla Akwai ziyara da ake yi gare shi ta ranar juma’a, yana da kyau mutum ya
lizimce ta.Ga mai bu}atar ganin wa]annan ziyarori yana iya duba littafin mafatihu,babi na ]aya,fasali
na biyar,da kuma babi na ukku,fasali na goma.
4.GIRMAMASHI: Tashi
tsaye domin girmamawa gare shi,lokacin da mutum yaji an an baci la}abinsa na Al}a’im. kuma wannan abu ya samo asali
ne daga A’imma na Ahlul baiti [AS], misali yazo akan cewa Imam Sadi} [AS] ya kasance a wani majalisi sai aka ambaci wannan lakabin, sai aka gan shi ya mi}e
tsaye, kuma an samo makamancin hakan
daga Imam Ridah [AS] yana zaune da aka ambaci
wannan la}abin sai aka ga ya Tashi tsaye ya ]an sun kuyar da kansa mai albarka ya kuma ]ora
hannun daman sa a kansa yace, “Allah ka gaggauta bayyanarsa”.
5.YIN BAI’A GARE
SHI:Mustahabbi ne kamar yadda yazo yin bai’a ga Imam Mahdi [AS] ko wace rana,ko
mako musamman ran juma’a, ko wata,ko shekara.Sigar bai’a ]in
itace kamar yadda yazo a addu’a wadda ake cewa, Du’a’ul Ahad ta nan cikin
Mafatihu gaban Du’a’ul Nudba.In son samu
ne duk bayan sallar asuba mutum ya dun ga biya ta.
6.JIRANSA: Wato
intizar,jira anan ba yana nufin mutum ya kame hannunsa bai yin komai a fagen
addini ba.A’a zai zamanto da farko shi }ashin kansa ya siffanta
da addini.Na biyu kuma ya zamanto yana bada gudummuwa a fagen addinin da irin
bai war da Allah [T] yayi masa.Na uku ya zamo mutum yana da ruhi na jihadi da kuma mujahada.Akwai
hadisai masu yawa da suka zo da bayanan falalar intizar.Ga guda biyu daga
ciki.An samo daga Imam Sadik [AS] yace, “Duk wanda ya rasu yana intizarin
wannan al’amarin zai kasance kamar wanda yake a zamanin bayyanarsa.” An samo daga Manzon Allah [S] yana cewa,
“Mafificin ayyukan al’ummata shine intizarin far’j” wato bayyanar Imam Mahdi [AF].
7.SHAU{I
GARE SHI:Wato mutum ya zamanto mai yawan begen Imam Mahdi [AS],mutum ya gina
kansa a haka har ya kai matsayin da zai dunga kuka, saboda shau}insa
gare shi.Lizimtar Du’a’ul Nudba
zata taimaka wa mutum akan haka.Domin akwai fa}arori a cikin Addu’ar da suke gina mutum ga shau}insa.
8.NUNA DAMUWA GARE SHI:Damuwa da ba}in
ciki na rashin ganinsa da kuma saduwa dashi.Shima wannan mutum ya gina kansa
akan haka har ya kai matsayin da zai zubar da hawaye saboda haka.Wannan kuwa
zai kasance ne idan mutum yana yawan tunanin Imam Mahdi [AS].
9.{ASKANTAR
DA KAI GARE SHI:Wato mutum ya zamanto mai yawan girmama wa ga Imam Mahdi [AS]
ya kuma kasance mai yawan {askantar
da kai gare shi.Misalin da aka bayar abaya
na cewa Imam Sadi} [AS] da
kuma Imam Ridah [AS] da aka ambaci la}abin
na Al’}aim sai da suka mi}e tsaye saboda girmama shi.Akwai ma fa]in Imam Sadik [AS] yana cewa, “Da ya riski Imam Mahdi [AS],to da
yayi masa hidima tsawon rayuwar sa…..”.
10.YI MASA TA’AZIYYA GARE SHI:Yi masa ta’aziyya da kuma taya shi murna
duk lokacin wafatin [rasuwar] ko wiladar [haihuwar] wani daga cikin Ma’asumai
ta zaga yo,wato Manzon Allah [S] da kuma Ahlulbaiti [AS].Misali ace yau ranar
wafatin Imam Ali ce,to sai kayi masa ta’aziyya a wannan ranar,ko kuma ace yau
ranar wiladar Imam Ali ce to sai ka taya shi murna a ranar,ta hanyar yi masa
sallama sai ka mika ta’aziyyar ka ko murnan ka.
11.RASHIN AMBATON SUNANSA:An yi hani ga ambaton sunansa, sai dai ambaton
sa da la}ubbansa
kamar Mahdi,Sahibuz zaman,Muntazar da dai makamantansu.Kuma kamar yadda muka
sani sunan sa,yayi muwafa}a
da na Manzon Allah [S] ne.
12.SANIN ALAMOMIN BAYYANARSA:Muhimmancin haka kamar yadda Malamai suka
yi bayani shine: i.Tsare kai daga fa]awa tarkon masu i}i-rarin Mahadawiyya.Domin in mutum ya bibiyi tarihin
wannan al’umma,zai ga an samu wa]anda
sukayi iki-rarin cewa sune Mahdi.Misali,wanda aka yi a Sudan shekaru 50 bayan
rasuwar Sheikh [an
Fodio. ii.Shiga
cikin rundunar sa.Ga wanda Allah yayi wa muwafa]a,yana
raye ya bayyana.Wato kasantuwar ya san alamomin bayyanarsa cikin sau}i zai iya gane shine ko bashi bane.
13.TAWASSULI DA KUMA ISTIGASA DA SHI:Mutum ya dunga yin tawassuli dashi ga dukkan al’amuransa na duniya da na addini da kuma na lahira .Yana da
kyau mutum ya saba wa kansa da haka.Domin yin haka zai taimaka wajen samun ala}a }albiyyah
[wato damfaruwa da shi a zuciya]
14.HADDIYA GARE SHI:Wato mutum yayi wani aiki na ibada ko ]a’a da nufin Allah [T] ya kai ladar ga Imam
Mahdi [AF] shima wannan ya nada kyau mutum ya saba da shi.
15.TSAYAWA DA BADA HU{U{-MALIYYA:Ga wanda ya kai matsayin ya bayar,misali khumusi da makamantansu,domin
kamar yadda aka sani a cikin khumusi, akwai abinda ake cewa Sahmul-Imam [AS] da
kuma Sahmus Sadat,wannan bayaninsu sai a koma Risala Amaliyyah.
16.TA{ALIDI DA
[AYA DAGA CIKIN NUWWAB [INSA NA AMMA:A FAGEH FI{IHU. wannan wajibi ne ba ma mustahabbi ba.Kamar
yadda yazo akan cewa idan mutum shi ba mujtahidi bane ko muhta]i ba,to, dole
ne ya samu wani daga cikin mujtahidai, domin yayi Ta}lid da shi ga ayyukansa na ibadat da kuma
mu’amalat.Wannan shi ma sai a koma ga Risala Amaliyyah domin }arin bayani.
17.RAYA AL’AMURUNSA TSAKANIN MUTANE:Wannan shi ma ta fuskoki daban daban,misali
kiyaye ranar haihuwarsa ,yin tarurruka domin }ara wa juna ilimi dangane da shi,yin
rubuce-rubuce dangane da shi da dai sauransu.Ya ma zo daga Imam Sadi} [AS]
yace Allah Ta’ala yayi rahama ga wanda ya rayar da al’amarinmu.A wani hadisi
kuma yace, “Allah Ta’ala yayi rahama ga bawan da ya sanya sonmu a zukatan mutane”. Wannan
kenan baki ]aya a ta}aice da fatan Allah [T] ya amfanar da mu abubuwan
da muka karanta ya kuma bamu ikon aiki da su.
No comments:
Post a Comment