Saturday 9 February 2013

Imama a mahangar Ahlul Baiti (AS) da Ahlus Sunna.


Alhamdulillah, kasantuwar wannan wata da muke ciki, wato na Zulhijjah cikinsa ne 18 gare shi wato Ranar Ghadir Manzon Allah (S) ya bayyana wa wannan al’umma wa]anda za su kasance Imamai, wato Khalifofi a bayansa, bayyanawa wadda za a siffata ta a matsayin bayyanawa RASMIYYAN, wato OFFICIALY. Saboda haka mabiya Ahlul Baiti (AS) a sassan duniya daban-daban suke gabatar da tarurruka da kuma rubuce-rubuce domin tunatar da juna dangane da wannan rana ta Ghadir.
Ko kuma abubuwan da suka faru kafin ranar Ghadir da kuma ranar da abin da ya biyo bayan ranar. Ko kuma tunatar da juna dangane da ayyukan da ake aikatawa a ranar Ghadir ]in da dai sauran mas’aloli da suke da ala}a da wannan ranar ta Ghadir, kamar al’amarin Imamanci.
A kan wannan asasin ne rubutun zai gudana insha Allah, wato Imama a mahangar Madrasa ]in Ahlul Bait (AS) da kuma Madrasa ]in Ahlus Sunna. Domin Mas’ala na Imamanci ko Khalifanci shi ne asasul-asas na sa~ani tsakanin Shi’a da Sunnah. Wato duk wani sa~ani da kuma rarraba da ya auku a wannan al’umma ta Manzon Allah (S) ya gangaro ne daga wannan asalin.
Haka nan kuma duk wani musgunawa da cutarwa da aka yi wa Ahlul Baiti (AS) da kuma mabiyansu na kisa na ]auri, kora daga }asa zubar da jininsu, ~arnatar da dukiyoyinsu, wannan shi ne sabab.
Hatta cutarwa ta farko da aka soma yi wa Ahlul Baiti (AS) da kuma mabiyansu bayan wafatin Manzon Allah (S) kan dai wannan al’amari ne. Mutum ya karanci tarihi na wa]annan makarantu guda biyu zai ga haka na abubuwan da suka faru a Sa}ifa da kuma abin da ya biyo bayan nan na kai hujumi gidan Sayyida Fatima(AS) da nufin cewa Imam Ali (AS) da wa]anda suke tare da shi a gidan dole su fito su yi bai’a. Abubuwan da suka faru a gidan mutum ya tambayi tarihi, me ya faru a gidan ya gani.
Bayan haka Imaman nan ]aya bayan ]aya baki ]ayansu, babu wanda ba a cutar da shi ba kan wannan al’amari. Mu duba inda aka haife su da kuma inda suka rasu. Idan mutum ya bibiyi tarihin A’imma (AS) 12 zai ga in ka ]ebe Imam Ali (AS) da aka haifa a Makka da kuma Imam Mahdi(AF) da aka haifa a Samarra da ke }asar Ira}i, to sauran iImamai 10 duka a Madina aka haife su, ko kuma kusa da Madina kamar Imam Kazim (AS) da aka haifa a wani waje mai suna Abwa kusa da Madina. Amma mu duba mu gani mafi yawan wa]annan Imaman }aburburansu na Madina ne, ko kuma nesa da Madina? Wannan ka]ai ya isa ya nuna wa mutum cewa lallai wasu al’amura sun faru da ya kai ga faruwar haka.
Kuma mu duba inda aka haifi Imam Mahdi (AS) a waje ne nesa da Makka da kuma Madina. Dalilin haka kuwa kamar yadda ya zo a tarihi shi ne; masu tafi da iko a lokacin suna da masaniyar cewa Imam Hasan Al-Askari shi ne Imami na 11, kuma shi zai haifi Imami na 12, wanda zai kau da zalunci da kuma azzalumai, ya shimfi]a adalci a bayan }asa baki ]aya. A kan asasin haka ne aka ]auko shi daga Madina zuwa Ira}i aka aje shi a Samarra a wani sansani na maya}a (barikin soja). Daga nan ne wannan la}abi nasa ya samo asali.
Ba su tsaya nan ba, Khalifan Abbasawa na lokacin ya sa aka samu mata wa]anda suka }ware wajen sanin cikin ’ya mace ya sa su lokaci bayan lokaci su dinga bibiyar iyalin Imam Askari (AS) su ga wacce ce take da ciki a shaida masa. Amma ta Allah ba tasu ba, a irin wannan yanayi ne aka haifi Imam Mahdi (AS). Allah (T) ya kare shi har ya shekara biyar kafin rasuwar Mahaifinsa da dai sauran abubuwa masu yawa da suka faru marasa kyau ga Ahlul Baiti (AS) da kuma mabiyansu, saboda al’amarin Imama ko Khalifanci. Wannan kenan dai a ta}aice.
Dangane da Imama a mahangar Ahlul Baiti (S) da kuma Ahlul Sunnah, a dun}ule wannan mahanga ]in guda biyar ne, kamr yadda suka zo a littafin A}a’id sune:
1. Imama, Usulul-Deen ce ko Furu’ud-deen?
2. Imama, Nassi ce ko shura?
3. Dawamul-Imama
4. Mas’uliyyar Imam.
5. Shuru] na Imam.
Ga mahangar kowanne ga wa]annan abubuwan guda biyar da aka ambata.
Na ]aya Imama Usul ce ko Furu’u? Shi’a sun tafi a kan cewa Imama tana cikin Usuld-din ne, shi ya sa in mutum ya duba littafi na A}ida na Madrasa ]in Ahlul Baiti (AS) zai ga bayan bayani kan Nubuwa, abin da yake biyowa baya mubasharatan shi ne bayani dangane da Imama.
Su kuma Ahlus Sunna suka tafi a kan cewa Imama tana cikin Furu’ud-din ne, wato Fi}hu. Ga zantukan wasu daga cikin Malaman Ahlus sunna a kai. Gazzali ya ce “Mas’alar Imama ba ya cikin A}a’id, yana cikin Fi}hu ne”. Wani Malami mai suna Amudi ya ce; “Ka sani bayani dangane da Imama ba ya cikin Usulud-din”. Haka nan wani Malami ya ce; “Bahasin Imama a wurinmu yana cikin Furu’ud-din ne”. Ibn Kaldun ya ce; “Al’amarin Imama mas’ala ce ijtima’iyya bai cancanci ya zama cikin babin A}ida ba”. Wani kuma Malami mai suna Taf-tazani ya ce; “Babu jayayya a kan cewa mas’alar Imama ya fi dacewa da ilimin Furu’ud-din”. Da dai sauran zantuka na Malaman Ahlus Sunnah dangane da haka.
Na biyu: Imama nassice ko Shura, wato ayyanawa ne daga wajen Allah (T), ko ko an bar wa mutane su tattauna tsakaninsu su za~a? Shi’a suka tafi a kan cewa al’amarin Imama Nassice  daga wajen Allah (T), wato kamar yadda Allah (T) shi ya za~i Annabawa, to, haka nan Imamai shi ya za~e su. Kamar yadda babu wani Annabi daga cikin Annabawa da mutanen zamaninsa suka tattaru suka za~e shi, sannan suka ce sun mai da shi Annabi. To haka nan al’amarin Imama yake a Madrasa ]in Ahlul Bait(AS). Ba mutane ne suke ha]uwa su za~i Imam ba, (amma nan a lura, Imam nan ana nufin da ma’anarsa ta Is]ilahi ba ta lugga ba. Wato ana nufin Khalifa na Manzon Allah (S)). Saboda haka Shi’a suka tafi a kan cewa, Manzon Allah (S) kafin ya bar duniya ya bayyana wa]anda za su kasance Khalifofi a bayansa. Ya bayyana a dadinsu, wato su 12 ne, ya kuma bayyana sunayensu, na farkon su shi ne Imam Ali (AS), na }arshensu shi ne Imam Mahdi (AS). Ya bayyana haka RASMIYYAN a ranar Ghadir da kuma wasu munasabobi a tarihin rayuwarsa, ta hanyar ishara, ko kuma kai tsaye, kamar yadda ya auku tun farkon da’awarsa wato a Makka a muhadarar da aka fi sani da Yaumud Dar.
Su kuma Ahlus Sunni suka tafi a kan cewa a’a, Manzon Allah (S) ya bar duniya ne ba tare da ya bayyana Khalifa ba. Alal misali, mutum na iya duba littafin Tarikhul Khulafah na Suyu]i, ya duba fasali na farko a littafin , zai ga yana bayani ne a kan cewa; “Manzon Allah (S) bai khalifantar da wani ba, da kuma sirrin hakan”.
To amma da mutum zai ]ebe ta’asubanci da kuma tunanin abin da ya gada, wato abin da ya taso a kai, kuma ya bu]i ido a kai, ya yi bincike kan hujjojin wa]annan ~angarori na Musulmi guda biyu (watau Shi’a da Sunna), bayan ya gama binciken sai ya zo ya yi mu}arana, wato ya kwatanta hujjojin ya gani, na wa ya fi }arfi, kuma abin rinjayarwa? Sai ya yanke wa kansa hukunci.
A bisa gaskiya in da mutum zai yi wannan bincike, daga }arshe zai ga cewa hujjojin da Shi’a suka kawo kan wannan al’amarin hujjojin ne masu }arfi wa]anda kuma za su iya tabbatar da wa]annan hujjoji ba wai a littafansu kawai ba, a’a, hatta ma a littafan Ahlus Sunnah.
Misali guda ]aya a nan shi ne abin da su Shi’a suka tafi a kai na cewa Khalifofin Manzon Allah su 12 ne, wannan yana nan a littafan Hadisai na Ahlus Sunna, wato Bukhari, Muslim Nisa’i, Tirmizi da kuma Musnad na Ahmad, wato Shugaban Mazhaban Hanbaliyya. Duka sun fitar da wannan Hadisin, wato wanda yake bayani da kuma nuni ga Khalifofi 12. Nassin Hadisin shi ne; Manzon Allah (S) ya ce: “Alkhulafa’u min ba’adi isna Ashr”. Wato Khalifofi a bayana 12 ne. Abin tambaya a nan su waye wa]annan sha biyun? Zai yi kyau mutum ya samu littafin da aka ambata a baya wato Tarikhul Khulafah na Suyu]i ya ga yadda ya kawo zantukan fitattun Malaman Ahlus Sunnah dangane da shi wannan Hadisin. A duba fasali na uku a littafin.
Daga }arshe in mutum ya duba zai ga cewa, babu matsaya ]aya ko fahimta ]aya na Malaman Ahlus Sunnah kan wannan Hadisin, kamar yadda Suyu]i ]in ya kawo a littafin. Ga bayanan da ya kawo na wasu daga cikin fitattun Malamai na Ahlus Sunnah yadda su suka fahimci Hadisin ga abin da yake cewa; “{hadi Iyad (watau wanda ya yi littafin Asshifa) ya ce }ila abun da ake nufi da 12 a wa]annan hadisan da wa]anda suka yi kama da su, shi ne wa]annan Khalifofi za su kasance a zamanin izzar Khalifanci da }arfin Musulunci da kuma ijma’i  akan wanda ya tsayu da khalifanci. Ibn Hajar a sharhin Sahihul Bukhari ya }arfafa wannan magana ta Khadi Iyad, inda yake cewa maganar Khadi Iyad, ita ce mafi kyawun abin da aka fa]i a wannan Hadisi, kuma abin rinjayarwa”.
Ya ci gaba da cewa; “Abin da ake nufi da ijma’i shi ne wanda mutane suka ha]u a bai’arsa. A ta}aice idan an fahimci bayanin Khadi Iyad da kuma Ibn Hajar kan wannan Hadisin na Khaliffofi 12 cewa ana nufin wa]anda mutane suka ha]u a bisa yarda da khalifancinsu ba wa]anda ba a ha]u a kan khalifancinsu ba. Shi ne Ibn Hajar ya zano sunayensu kamar haka. 1. Abubakar. 2. Umar. 3. Usman. 4. Ali. 5. Mu’awiyyah. 6. Yazid. 7. Abdulmalik. 8. Walid. 9. Sulaiman. 10. Yazid (watau [an Abdulmalik). 11. Hisham. 12. Walid [an yazid”.
A nan zai yi kayau mutum ya nemi wannan littafi na Tarikhul Khulafa na Suyu]i ya karanci tarihi da kuma rayuwar wa]annan da Ibn Hajar ya kawo a matsayin Khalifofi, ya samo daga Khalifa na shidda wato Yazid [an Mu’awiyya zuwa na 12 wato Walid [an Yazid. In ba zai iya karantawa duka ba, to a}alla ya karanta na shida da na 12. Bayan ya karanta ya auna da hankalinsa. Anya kamar Yazid ko Walid su ne Khalifofin Manzon Allah (S)? Wal’iyazubillah.
Ga wanda }ila ba zai iya samun littafin domin ya karanta ba, ko kuma ba zai iya karantawa ba. To ga ka]an daga cikin abubuwan da Suyu]i ya kawo a cikin littafin kan abin da ya shafi Yazid [an Mu’awiyya. Ya soma banayanan nasa ne dangane da yadda aka yi ya zamo Khalifah da abin da ya soma yi bayan da aka na]a shi, sannan ya kawo }issar wa}i’ar Karbala da kuma kashe Imam Husain (AS), har yake cewa kisansa }isa ce mai tsawo, wanda zuciya ba ta iya jurewa da ambaton }issar.
A nan sai ya kawo Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Ya kuma kawo bayani dangane da canje-canjen da aka gani a sama da kuma }asa da duwatsu da dai sauran halittu bayan kashe Imam Husain (AS). Wannan ya faru ne a shekarar farko ta hawan Yazid.
A shekararsa ta biyu ya sa aka kai hari Madina. An kashe mutane da dama. Daga ciki akwai ma Sahabban Manzon Allah (S), aka kuma yi wa mata da yawan fya]e! Aka }wace dukiyoyi da kuma kayayyakin mutane. A nan ma Suyu]i ya sake kawo Inna Lillahi Wa Inna Ilahi Raji’un. Har ma ya kawo wani Hadisi wanda Musulim ya ruwaito cewa Manzon Allah (S) ya ce; “Duk wanda ya tsoratar da mutanen Madina, Allah zai tsoratar da shi, kuma la’antar Allah da Mala’ikunsa da kuma mutane baki ]aya ta tabbata a gare shi”. A takaice wa]annan sojojin nasa sai da suka }wace Madina na tsawon kwanaku uku suna wannan ta’asa.
A kuma shekararsa ta uku ya aika da maya}a zuwa Makka domin ya}ar Abdullah [an Zubair, wanda haka ya yi sanadiyyar }onewar Ka’aba da kuma muhimman abubuwan da ke kusa da ita. To fa wannan shi ne Yazid [an Mu’awiyya a ta}aice kamar yadda Suyu]i ya kawo.
Akwai ma inda Suyu]in ya kawo cewa; “Akwai wani da aka ce wa Naufal [an Abu Furat, ya ce na kasance wajen Umar [an Abdul’aziz, sai wani mutum ya ambaci Yazid ya ce Amirul Muminin Yazid [an Mu’awiya, ya ce sai Umar [an Abdul’aziz ya ce ka ce Amirul Muminin? Ya ba da umurni a yi masa bulala 20”. Mutum ya duba cikin wannan littafin na Suyu]i shafi na 114. Amma abin mamaki a ’yan wa]annan shekaru sai ga gwamnatin Saudiyya ta buga wani littafi wanda a ciki aka yi }o}arin wanke Yazid ga duk abubuwan da ya yi, alhali suna nan a rubuce a littafan tarihi na Ahlus Sunna. Abin ma da aka rubuuta a bangon littafin shi ne Amirul Muminin, Yazid Ibn Mu’awiyyah. Wannan ke nan a ta}aice kann shi Yazid.
Sai kuma wai Khalifah na 12, wato Walid, shi ma ka]an daga cikin rayuwarsa kamar yadda Suyu]i ya kawo a wannan littafi nasa na Tarikhul Khulafa cewa ya yi; Walid Khalifah ne fasi}i, ya kasance fasi}i, mashayin giya mai keta hurumin Allah (T). Ya ci gaba da cewa akwai lokacin da ya yi niyyar zuwa Hajji domin ya sha giya a saman Ka’abah.
Ya ce Shams-Suddin Azzahabi, ya siffanta shi da cewa Walid ya shahara wajen shan giya da kuma luwa]i. Kai akwai ma lokacin da ya kekketa Al}ur’ani ya ce in ya je wajen Allah ya ce Walid ne ya kekketa shi. Wannan ke nan a ta}aice.
Mu duba mu gani wannan littafin ba wai Malamin Shi’a ya rubuta shi ba, ballantana mutum ya sa shakku, ko kuma ta’asubanci a kai, wanda ya rubuta shi wato Suyu]i yana ]aya daga cikin manya-manyan Malaman Ahlus Sunnah, wanda kuma ya yi rubuce-rubuce a fannoni daban-daban, wanda ya san tarihinsa zai fahimci haka.
Dawowa ga wannan Hadisi da yake bayani dangane da Khalifofi 12. Suyu]i ya ci gaba da cewa wa]ansu Malamai sun ce abin da ake nufi shi ne samuwar Khalifofi 12 tsawon muddan Musulunci har zuwa tashin }iyama, wa]anda suke aiki da gaskiya ko da ba su kasance suna biye da juna ba. A kan wannan ra’ayi da fahimta Suyu]i ya tafi ya kuma }arfafa a kan haka, inda yake cewa (wato a }arshen fasalin); “Na ce a kan wannan (wato fassara) an samu daga cikin wa]annnan Khalifofi 12, Abubakar, Umar, Usamn, Ali, sai Hasan ]an Ali dai Mu’awiyya, sai Ibn Zubair, sai Umar [an Abdul’aziz”. In ka yi lissafi za ka ga su ne ya ci gaba da cewa za a iya ha]uwa da Muhta]i na Abbasawa. Shi ne ya }ar}are da cewa sauran ana jira su. [ayan su Mahdi ne, domin yana daga cikin Ahllul Bait (AS). Wannan ita ce nassin maganar Suyu]i.
To a nan mutum zai ga yadda Suyu]i ya fahimci Hadisin, wato a kan cewa wa]annan Khalifofi 12 ana nufin Khalifofin da suka kasance mutanen }warai suka kuma tsaya kan gaskiya da kuma aikata adalci ko da ba a biye suke da juna ba. Wato za su kasance jefi-jefi a cikin tarihi, kamar yadda ya kawo sunayen 10 ya ce saura biyu.
Sai kuma tafsiri na uku da Malaman Ahlus Sunna suka kawo dangane da wannan Hadisin shi ne wanda Ibnul Arabi ya ce a sharhin Sunan na Tirmizi, inda ya ce; “Idan muka lissafa bayan Manzon Allah (S) Khalifofi 12 muka same su kamar haka, Abubakar, Umar, Usman, Ali, Hasan, Mu’awiyya, Yazid, Mu’awiyat [an Yazid, Marwan, Abdulmalik [an Marwan, Walid Sulaiman, Umar ]an AbdulAziz…”. Haka dai ya dinga zana su har zuwa zamaninsa. Shi ne sai ya ce; “Idan muka lissafa 12 daga cikinsu, za mu ga adadi 12 ya tu}e ne ga Sulaiman”. Shi ne daga }arshe ya ce; “Ni dai ban san ma’anar wannan Hadisi ba”.
Akwai zantuka na Malaman Ahlus Sunna kan yadda suka fahimci wannan Hadisin saboda gudun tsawaitawa ba za a iya kawo su ba sai dai ga mai bu}atar ganin zantukan yana iya samun littafi mai suna Ma’alimul Madrasatain, mujalladi na 1, wato na Sayyid Murtadha Al-Askari domin ya duba.
Amma idan mutum zai juya ya duba a littafin Shi’a zai ga sun kawo sunayen wa]anann Khalifofin kamar haka: 1. Imam Ali (AS), 2. Imam Hasan (AS), 3. Imam Husain (AS), 4. Imam Ali-Zainul-Abidin (AS), 5. Imam Muhammad Ba}ir (AS), 6. Imam Jafar Sadi} (AS), 7. Imam Musa Kazim (AS), 8. Imam Ali Arridah (AS), 9. Imam Muhammar Jawad (AS), 10. Imam Ali Alhadi (AS), 11 Imam Hasan Askari (AS), 12 Imam Mahdi (AS). A nan babu abin cewa face Alhamdulillahil lazi hadana li haza, wama kunna linahtadiya laula an hadanallah.  Mutum ya je ya binciki tarihin wa]annan bayin Allah (T) dukkaninsu jinin Manzon Allah ne, dukkansu daga {uraish ne, kuma cikin Bani Hashim. Mutum ya karanci tarihinsu ]aya bayan ]aya ya ga irin shaida da Malaman Ahlus Sunnah suka yi masu na zamanin kowanne ]aya daga cikinsu.
Ba don gudun tsawaitawa ba, da an kawo shaida da Malamai na zamaninsu suka yi masu. Da mutum zai bincika zai ga cewa dukkansu 12 babu wanda ba a yi wa shaida cewa a zamaninsa ya fi kowa ilimi, ya fi kowa ibada, ya fi kowa akla} da duka janibobun addini ba. Ga misali na ilimin guda ]aya daga A’imma 12, shi ne Imam Jafar Sadik (AS), wanda Limaman Mazahib guda biyu na Ahlus Sunna suka yi zamani da shi, wanda ba wai kawai sun yi zamanin da shi ba ne, a’a, sun yi ma karatu a wajensa su ne; Abu Hanifa, wato Shugaban Mazhabar Hannafiya, ga shaidar da ya bayar ga Imam Sadi} (AS). Abu Hanifa ya ce; “Ban ta~a ganin wanda ya kai ilimin Imam Jafar Sadi}(AS) ba”. Wani waje kuma yana cewa; “Ba domin shekaru biyu ba da Nu’uman ya halaka”. Wato yana nufin shekaru biyun da ya yi wajen Imam Sadi} yana karatu.
Sai kuma abin da Malik [an Hasan, wato Shugaban Mazhabar Malikiyya yake cewa, wato na shaida ga Imam Sadi}(AS); “Ban ta~a ganin wani ba ko jin wani ba a zamanina wanda ya fi Jafar [an Muhammad ilimi ko ibada ko kuma tsantsani ba”. Ya ci gaba da cewa; “Na yi kai-komo wajen Jafar [an Muhammad lokuta daban-daban, duk lokacin da na je sai in same shi ko yana Salla ko Azumi ko kuma kararun Al}ur’ani”.
Haka nan Ahmad Ibn Hambal, Shugaban Mazhabar Hambaliyya ya yi karatu gun Imam Musa Kazim (AS). Akwai wani abin mamaki da ya ta~a gani wajen Imam Kazim (AS) shi ne ya yi masa bayani.
Akwai kuma wani tambihi a nan shi ne; Ahmad Ibn Hambal shi ya riskar da Imam Ali (AS) a cikin Khalifofi guda hu]u wa]anda Ahlus Sunna suka tafi a kai, domin tsawon mulkin Banu Ummayya Khalifofi uku ne suke lissafawa. Kuma wannan ko a hankali mutum ya auna ya gani, wanda ake zagi a masallatai, ya za a saka shi cikin Khalifofi? Saboda haka a lokacin Abbasawa ne Ahmad Ibn Hambal ya riskar da shi, shi ya sa ba wani Hadisi da muutum zai iya kawowa ko da ko dha’ifi ne, wanda ya ce Manzon Allah (S) ya ce Khalifofi a bayan guda hu]u ne.
Saboda haka a nan yana da gayar muhimmanci musamman ga ’yan uwanmu Musulmi na Madrasa ]in Ahlus Sunna da su rin}a yin bincike a kan abubuwan da aka samu sa~ani a kai, tsakanin Shi’a da Sunna, domin mutum ya ga hujjojin kowa, sannan ya kwatanta, domin yin haka insha Allah zai taimaka wajen rage gaba da kuma }iyayya da take gudana tsakanin juna. Wanda wannan ba ana nufin mutum ya bar na shi ya zo na wani ba ne, a’a, a}alla ana son ka fahimci hujjojin da shi ma ]an uwanka Musulmi yake a kai.
Insha Allah sauran mahanga guda uku wani lokaci za a ]ora a kai.


No comments:

Post a Comment