Saturday 9 February 2013

TARIHI DA KUMA RAYUWAR ABUL- FADHAL ABBAS {AS}.


Sayyid  Abul-Fadhal Abbas[AS] an haife shi a Madina,ranar 4 ga watan sha’aban,shekara ta 26 bayan hijira,Sayyid Abbas  a cikin ‘ya’yan Imam Ali[as] maza baya ga Imam Hassan da Imam Husain[AS] ba wanda ya kai shi daraja.
.Sayyid Abul-Fadhal Abbas[as] tanadi na musammam wanda Imam Ali[as] yayi ma Imam Husain [AS] domin waki’ar karbala,domin yazo a tarihi cewa lokacin da Imam Ali[as] yayi nufin yin auren  ya bukaci dan’uwan sa Akil dan Abi dalib,[da yake shi masanin nasabar larabawa ne] daya sama masa mata wadda ta fito daga gidan jarumai,domin ya aure  ta,da fatan ta Haifa masa ]a jarumi,wanda zai taimaka ma Imam Husain[as] a karbala,sai A}il yace masa ga Fatima ‘yar Hizam.Yazo a tarihi cewa gidan su gidan jaruntaka ne,Imam Ali[AS] ya amshi wannan Magana tasa,saboda haka sai ya sa shi a madadin sa,domin neman auren ta a wajen mahaifin ta. A}il ya tafi wajen baban ta,ya gabatar da wannan Magana gareshi,jin haka nan take mahaifin ta ya amsar maganar kuma yayi farin ciki mai yawa.Yazo atarihi cewa lokacin da A}il da mahaifinta suke wannan Magana,ita Fatima ‘yar Hizam tana labarta ma mahaifiyar ta wani mafarki da tayi cewa tana zaune a gida sai taga wata ya fa]o a gidan su,bayan haka kuma sai taurari hu]u suka biyo bayan sa.Ta gama fa]a ma mahaifiyar ta kenan wannan mafarki,sai ga baban ta ya shigo cikin gada da wannan albishir,na cewa A}il yazo da maganar neman auren Fa]ima ga Imam Ali[AS] jin haka sai mahaifiyar tace masa ai ga mafarkin da ta bani labara dashi yanzu,lokacin da baban ta yaji bayanin mafarkin da tayi,ya da]a farin ciki,har yake cema ‘yar tasa “Lallai Allah ya tabbatar da wannan mafarki naki,ina taya ki murnar samun sa’adar duniya da lahira”Bayan da akayi auren,ta tare gidan ImamAli[AS] lokacin da akayi auren yazo a tarihi cewa tana da kusan shekaru 20 ne,kuma yazo a tarihin ta cewa a daren farko data shiga gidan Imam Ali[AS] tace masa tana da wata bu}ata, ImamAli[as] yace miye bu}atarki? Tace masa ina so in zaka kira sunana,kada ka kirani da sunana Fa]ima,saboda jin sunan zai dunga sa,su Hassan da Husain da Zainab,su dunga tuna mahaifiyar su,wanda hakan zai dunga sosa masu rai.To sai Imam Ali[AS] tun daga lokacin,yak an ce mata ummul-banin,saboda haka wannan kinaya shi yasa mata shi,wato tun kafin ta haifi ‘ya’yan ta maza guda 4.sune Abbas,Abdullahi,Ja’afar da  kuma Usman.Imam Ali [as]yace nasa masa suna usman,saboda tunawa da sunan usman ]an maz’un,Usman ]an Maz’un  sahabi na Manzon Allah[S] ne,kuma ya rasu tun manzon Allah[S] yana raye,saboda haka sunan ba yana komawa bane ga sunan usman ]an Affan bane kamar yadda wasu zasu yi tsammanin haka.
Mahaifiyar Sayyid Abul fadhal Abbas ta kasance mai kulawa da kuma girmamawa  ga Imam Hassan da Imam Husain[AS] akwai ma lokacin da take cema ‘ya’yan ta kada ta kuskura taji wanin su yana kiran Hassan ko Husain da sunan sa,sai dai suce ya shugaba na.kuma yazo a tarihin ta cewa ta kasance yadda take nuna so da kulawa da kuma }auna ga ‘ya’yan sayyida Fa]ima[AS] ko ‘ya’yan ta bata yima haka,kuma zamu ga haka a aika ce a rayuwar ta,bayan shahadar su Imam Husain[AS] lokacin da labari yazo madina na cewa an kashe su,wanda yazo da labarin da yake yi mata ta’aziyyar ‘ya’yan ta,]aya bayan ]aya,abinda take tambayar sa miya samu Husain?yana fa]in an kashe Husain,sai ta fashe da kuka.Akwai ma wani malami da yake cewa a tarihi ba a samu wata kishiya ba,da take fifita ‘ya’yan kishiyar ta akan ‘ya’yanta kamar ummul banin,wannan dai ya nuna irin gayar biyayya da kuma wula’a da ummul banin take dashi ga Ahlul-bait[AS]Kuma yazo cewa lokacin dasu Sayyida Zainab[as] suka dawo madina,ta kaima ummul banin ziyara ta musammam domin yi mata ta’aziyyar shahadar ‘ya’yanta,wato sayyid Abbas da kuma }annan sa ukku,Ga shekarun ko wannan su lokacin da yayi shahada,Sayyid Abul fadhal Abbas 34,Abdullahi 25,Usman 21,Ja’afar 19.
Kinayar sa-Anai masa kinaya da Abul-Fadhal,saboda yana da ]a wanda ake cema Fadhal har wala yau anai mai kinaya da Abul-}asim,shima saboda ]ansa mai suna }asim,yazo a kan cewa shima }asim ]in yayi shahada  a karbala.mu duba mu gani wannan wa}i’a ta karbala,kusan ko wane gida ta shafi iyaye  da ‘ya’yayen su.La}ubban sa-sayyid Abbas yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi shahara sune,A-}amaru bani Hashim,wannan kuma saboda gayar kyawan halitta da Allah[T] yayi masa.B-babul-hawa-ij,wato saboda yadda mutane suke samun biyan bu}ata idan suka yi tawassili da shi ga matsalolin su,kuma tabbas haka ne duk wanda yake da wata bu}ata,yayi tawassili da shi da iklasi,to Allah[T] zai biya masa bu}ata.C-Hamilu-liwa’a,a nai masa la}abi da wannan,wato ma]aukin tuta,da yake a wa}i’ar karbala a ranar Ashura shine Imam Husain[as] yaba tuta,kuma tuta ko ri}e ta musamman a lokacin ya}i wani abune wanda yake da asali da kuma tarihi a wannan addini na musulunci,Alal misali a duk ya}o}in da Manzon Allah[S] yayi akwai mari}in tuta a ya}in,misali a ya}in farko da Manzon Allah[S] yayi wato ya}in Badar mari}in tutar shine sayyiduna Hamza,a sauran ya}o}in da Manzon Allah[S]yayi mari}in tutar shine Imam Ali[AS]saboda haka Abul fadhal a ranar Ashura,shi yake ]auke da tuta.kuma sai da takai yana ri}e da tutar da hannun dama,aka sare hannun,ya ri}e ta da hannun hagu,aka sare hannun hagun,ya ri}e da }irjin sa,kuma lokacin da wannan abu ya faru ba kowa daga shi sai Imam Husain[AS] da yake duk sauran mazajen an kashe su.Kuma tutar da take }ubba ]in haramin Imam Husain[AS] tana alamta tutar da Imam Husain[as] ya ba sayyid Abul-fadhal Abbas[as] ne,kuma a kan canza ta duk shekara ne,a watan muharram,idan aka canza a kan yi kyauta da wadda aka cire ne.To al-hamdu-lillah wadda aka cire bana an baiwa Malamin mu kuma Jagoran mu a wannan gwagwarmaya ta tabbatar da addini,Sayyid Ibrahim Zakzaky[H] Kuma wannan tuta da take haramin Imam Husain[AS] itace wadda Imam Mahdi [AS]Zai yi amfani da ita,idan ya bayyana,domin ]aukar fansa akan wa}i’ar karbala da kuma tabbatar da addini a bayan }asa baki ]aya.Ta yiyu wani yayi tunanin ]aukar fansa akan suwa, tun da wa]anda suka aukar da wa}i’ar basu duniya,amsa anan itace ai ko wane zamani akwai yazidawa da kuma Husainawa,wato akwai magadan yazidawa  koda basu gade su ajini ba,a aiki sun gade su.kuma baya ga haka daga cikin a}ida na mabiya Ahlul bait,akwai RAJ’A,baya ninsa na muhallin sa.Saboda haka]aukar fansa ga wannan wa}i’a ta karbala wani abune wadda yake tabbatacce lokaci ne kawai,in mutum yace yaushe?Amsa daure dai,daure dai Ashura na zuwa.
Sayyid Abul fadhal Abbas –ya Tashi gaban mahaifin sa Imam Ali[AS] ya kuma rayu tare dashi  kusan shekaru 14,Akwai lokacin da Imam Ali[as] ya zaunar dashi akan }afafuwan sa, wato lokacin yana }arami,sai ya sun banci hannuwan sa yana kuka,sai ummul banin tace wannan kukan fa? Yace ina duban wa]annan hannaye nasu da kuma abinda zai same su,tace mi zai same su? Imam Ali[as] ya bata amsa cikin juyayi da ba}in ciki,yace za a sare sune,tace mi yasa za a sare su? Yace mata za a sare sune wajen taimaka ma ]an uwan sa Husain,jin haka sai ummul banin ta fashe da kuka.Haka nan yazo akan cewa gab da Imam Ali[as] zai rasu ya tara ‘ya’yan sa dukkan su ,domin yi masu wasiyya, kuma yayi masu wasiyya mai tsawon gaske.Saannan ya sanya dukkan ‘ya’yan sa ,}ar}ashin kulawar Imam Hassan[as] in banda sayyid Abbas[as] Ganin haka sai Sayyid Abbas ya fashe da kuka,sai ImamAli[as] ya jawo shi,yasa Imam Husain[as] ya mi}o hannun sa,sai ya ]ora hannun Sayyid Abbas akan na Imam Husain,yana mai cewa, “Ya Husain na sanya Abbas ya zauna }ar}ashin ka,shine wanda zai wakilce ni,a ranar da zaka yi mafi girman sadaukar da kai,domin addinin Allah[T].Zai yi duk abinda ya kamata in yi wajen baka kariya inda ina raye.” Saannan ya juya wajen Abbas yace:”Ya ]ana Abbas nasan akwai matu}ar so da }auna tsakanin ka da Husain,idan lokaci yazo,ka tabbatar da cewa babu wata rai wadda take da }ima wajen sadaukar da ita ga Husain da iyalan sa.”Sayyid Abul fadhal Abbas[as] ya aiwatar da wannan wasiyya ta mahaifin sa,idan mutum ya bibiyi tarihin rayuwar sa a karbala zai ga haka,wato yadda ya sadaukar da kansa da komi nasa domin bada kariya ga Imam Husain[as] da kuma iyalin sa,alal misali yazo a tarihin sa cewa tsawon kwanakin da aka yi a karbala,to ko wane dare , shi yake kula da kuma gadin hemar Imam Husain[AS] da kuma sauran hemomi na iyalan sa, ga kuma sauran hidimomi da yai ta gabatar wa, a hanyar zuwa karbala da kuma a karbala ]in, misali nemo abinci da ruwan sha da dai sauran su.Domin sayyid Abbas[as] tun taso warsa,yana da ala}a ta musamman da Imam Husain[as] wato baya rabuwa da Imam Husain[as] ko tafiya zai yi,yakan kasan ce tare dashi ne.Bayan shahadar Imam Ali[AS] ya rayu tare da Imam Hassan[as] kusan shekaru 24. Ya kuma rayu tare da Imam Husain[as] shekaru 34.Lokacin da Imam Husain[as] ya baro madina zuwa karbala suna tare ne.Saboda haka dukkan abubuwan da suka faru a hanya gaban idon sane.
                Sayyid Abul Fadhal Abbas[AS] a karbala, shine mutum na biyu baya ga Imam Husain[as] Idan mutum ya bibiyi tarihin abubuwan da suka auku a karbala zai ga haka,baya ga yadda ya tsayu da hidimomi dabam-dabam,wa]anda aka ambata a baya.To abubuwan duk da suka taso, a tsawon kwanakin da suka yi a karbala,Imam Husain[AS]shi yake wakiltawa don gudanar da abun,misali a ranar tasu’a, wato tara ga wata da yamma,Imam Husain[as] yana zaune a gabar hemarsa,sai ya sun kuyar da kai barci ya ]an ]auke shi,sai yai mafarki da Manzon Allah[S] yana ce masa, “Ka kusan zuwa wajen mu.” Yana cikin wannan yana yi sai ga Sayyida Zainab[AS]  kasan tuwar taji sukonawar dawakai da kuma hayaniyar mutanen  dake kai, tace ma Imam Husain[as] tana ganin ma}iya sun kusanto garesu,sai Imam Husain[AS] yace ma Sayyid Abbas hau doki ka same su,kaji mi yake tafe dasu,mi kuma suke nufi,Sayyid Abbas[as] ya hau doki ya same su,ya tambaye su dalilin zuwan su? Suka ce sun zone akan ko dai suyi bai’a ga Yaziduko kuma ya}i.ya dawo ya fa]a ma Imam Husain[AS] manufar zuwan su,sai Imam Husain[as] yace masa ya koma ya same su,ya shawo kansu,su jinkirta zuwa gobe, saboda muyi salloli a wannan daren,da adduo’i da kuma istigfari,yace Allah[T] yasan ina son sallah gare shi da karatun Al}ur’ani da yawan Adduo’i da kuma istigfari.Sayyid Abbas sai ya koma wajen su,ya nemi su jirkin ta zuwa gobe.Domin su sun so su aiwatar da aika-aikar da suka yi  a ranar Ashura tun a ranar Tasu’a ne da yamma.Bayan haka kuma a daren Ashura,Imam Husain[as] ya tara wa]anda suke tare dashi baki ]ayan su,yai masu jawabi daga cikin abinda yace masu a jawabin,yai yabo da godiya gare su,ya kuma ce Allah ya saka masu da al-hairi,bayan haka yace masu ya basu damar ko wannan su,yayi amfani da wannan duhun daren ya tafi,ya koma garin su, yace masu tunda wa]annan ma}iyan ni suke nema,jin haka sai sayyid Abbas ya mi}e yace;mi yasa za muyi haka saboda mu rayu a bayan ka?kada Allah ya nuna mana haka har abada.Bayan shi aka samu wa]ansu daga cikin sahabban Imam Husain[as] suma su kayi jawabi makaman cin haka na cewa ba inda zasu tafi,ga misalai na guda 3 daga cikin su.1-Muslim ]an Ausaja[RA] yace ,mu tafi mu barka me za muce ma Allah[T] gobe  }iyama wajen tsayuwa da ha}}in ka,yace wallahi har sai nayi ma wa]annan ma}iya ruwan kibau na kuma sassare su da takobi na matu}ar yana hannuna,kai ko banda takobin da zan ya}e su das hi zan jejjefe su da duwatsu.2-Zubairu ]an }ain[RA] ya Tashi yace,wallahi zan so a kasheni a ta dani,saannan a kasheni a ta dani haka-haka har sau dubu,saboda kariya gareka da kuma Ahlul bait ]inka.3- Muhammad ]an Bashir al-hadrami,yace zakoki su cinya ni a raye in na barka.To haka dai sahabbansa su kayi jawabi mai kama da juna,na cewa suna nan tare dashi.Bayan wannan haka su Sayyid Abbas [as] suka kwana suna ibada a daren Ashura.                                                                                                                                                               Ranar Ashura itace ranar }arshe ta Sayyid Abul fadhal Abbas[AS] a rayuwarsa t a duniya,kuma abubuwa da yawa sun faru gare shi a ranar,wanda dama shi ta nadi na musammam ne domin ranar. Amma anan kasantuwar tarihi ne,na sayyid Abbas[as] abubuwan da za a kawo nan na ranar ashura zai kasance ne wan]anda suke da ala}a da shine kai tsaye.Ma}iya a ranar ashura sun yi wani yun}uri na wauta da tsukewar tunani wai na raba Sayyid Abbas da Imam Husain,kasantuwar suna ganin wa]anda suke tare da Imam Husain[AS] shi yaba tuta kuma  babu jarumi kamar sa. Saboda haka sai suka bi ta hanyar wa]anda suke da ala}a dashi ta jini ko wata ‘yan uwantaka ta kakanni,a cikin ma}iya,ta hanyar rubuta masa aminci,ga misalan guda biyu daga ciki.Ibn Ziyad[LA] ya rubuta takarda ta aminci,aka bada ita ta hannun wani ]an uwan ummul banin mai suna Abdullahi ]an Hizam,akan yaba sayyid Abbas,da aka kai mashi takardar,yace bai da bu}atar wannan aminc,amincin Allah shi yafi alhairi gareshi akan na ibn Ziyad.Da suka ga wannan wautar tasu bata yiba,sai suka sake bin wata hanya wato ta hanyar shimru[LA] da yake shi kuma akwai ala}a ta yan’uwan taka tsakanin kakan sa da kuma kakan ummul banin,shi wannan ba takarda ne suka rubuto ba,A’a shi Shimru ne da kansa ya tafi inda Imam Husain suke da yaje sai ya tsaya,ya kira Abbas da yan’uwan sa,basu kula shi ba,sai Imam Husain [as]yace masu Sayyid Abbas ku amsa masa duk da cewa dai fasi}i ne,sai suka amsa masa suka ce minene? Sai yace masu yaku ‘ya’yan ‘yar uwata, ku amintattu ne kada ku kashe kawukan ku tare da Husain,ku shiga cikin ]a’ar Amiril muminin Yazid,jin haka nan take sai Sayyid Abbas yace masa, Allah ya tsine maka ya tsine ma amanar ka,yanzu zaka amintar damu al-hali ]an Manzon Allah bai cikin aminci,kuma kana umarnin mu da mu shiga cikin ]a ar la’anan nu ‘ya’yan la’anan nu.jin wannan amsa ta sayyid Abbas ga Shimru,sai wani dattijo daga cikin sahabban Imam Husain[as] mai suna Zuhairu ]an }ain abin ya bashi sha’awa,yace  ma sayyid Abbas in baka wani labari dana kiyaye shi? Yace na’am:yace babanka lokacin da yayi nufin yin aure, ya bu}ata daga ]an’uwan sa A}il domin shi yasan nasabar larabawa,day a za~a masa wadda zata Haifa masa ]a jarumi wanda zai taimaka ma Husain ,taimaka ma ]an uwanka da kuma kariya gare shi.To shine Sayyid Abbas yace ma Zuhair kana shajja’ani a irin wannan rana,Wallahi zan nuna maka abin daba ka ta~a gani ba wato na jarun taka.Haka dai ma}iya suka koma da rashin nasara na wannan wauta tasu.domin shi ba ahalin yin haka bane.Saboda haka da suka ga wannan yun}uri nasu bai yi nasara sai suka fara kai hari,suka kashe sahabban Imam Husain[AS] baki ]aya da kuma mazaje baki ]aya na Ahlul bait,sai ya zamanto ba wa]anda suka rage daga shi sai sayyid Abbas[as] sai kuma Imam Zainul Abidin[as] shima dun baida lafiya ne.                                                                        SHAHADAR SA:Sayyid Abul Fadal Abbas lokacin daya kasance ba kowa daga shi sai Imam Husain[as] yace ma Imam Husain[as] zuciya ta tayi }unci dangane da wa]annan munafukai,ina son in ]auki fansa na abubuwan da suka yi,Imam Husain[as] yace ya ]an’uwa na kai ne ma’abucin tuta ta,yace to kaje ka samo ma yara ruwa. Sayyid Abbas ya tafi zuwa gasu maya}an tun da sunyi dandazo a bakin kogin ruwan,akan su Imam Husain[as] baza suyi amfani da shi ba,saboda haka Sayyid Abbas[as] yayi masu wa’azi mai ratsa zuciya amma duk da haka basu yarda an ]ibi ruwan ba,ga wani sashe na abinda yace masu, “Ina ji maku tsoron fushin ubangiji ya sauka akan ku,ya bu]e baki da }arfi yace ya umar ]an Saad ga Husain ]an ‘yar Manzon Allah[S] kun kashe masa sahabbai, kun kashe masa Ahlu baitin sa,ga iyalin sa can da ‘ya’yan sa suna cikin tsananin }ishin ruwa.saboda haka ku basu ruwa su sha mana “.Duk da bushewar zukatan su maganar tayi tasiri ga wasu daga cikin maya}an,ganin haka nan take Shimru[LA] ya bu]e baki da }arfi yace,ya ]an Abu Turab,da ace }asa baki ]aya ruwane kuma yana }ar}ashin ikon mu,to ba zamu shayar daku koda ]igon ruwa ba sai kun yima Yazidu bai’a. Haka dai sayyid Abbas[as] ya dawo gun Imam Husain[AS] ba tare da ruwa ba.da ya dawo yai tajin kukan yara suna }ishi-}ashi,ya sake komawa,ya kutsa cikin maya}an da akasa su gadin ruwan ,ya kashe na kashewa,saura suka tarwatse,ya isa bakin ruwan  ya cika abinda ya tafi dashi,bayan haka ya kanfata zai sha,sai ya tuna }ishin Imam Husain[as] sai ya watsar da ruwan,ya kamo hanya zai dawo suka sake yo ca akan sa, a nan aka samu wani laananne daga cikn su,ya sare hannun sa na dama, ya ri}e tutar dake hannun sa na damar zuwa ga na hagu,shima hannun aka sare ya ri}e tutar da dulgummin hannayen sa da aka sare ya manne ta da }irjin sa,bayan haka ne mai aukuwa ta auku,aka samu wani ya sare shi aka,Inna lillahi wa-inna-ilaihi-rajiun, ya fa]o daga kan dokin sa,ya ]aga muryar sa da }arfi yace ka riskeni ya ]an uwane, a wata ruwaya yace sallama daga gareni zuwa gare ka ya Aba Abdullah,jin haka Imam Husain[as] yazo da sauri,ko da yazo ya same shi ba hannun dama bana hagu ga kuma kan sa an Rotsa,a hannun Imam Husain[AS] ya cika,Imam Husain[as] yayi kuka a lokacin kuka mai yawa,wani abin lura anan muhimmi,wanda yake nuna matsayi da daraja na Sayyid Abul Fadhal Abbas[as]wajen Imam Husain[AS] shine,a lokacin da yayi shahada Imam Husain[AS]yace, “}ashin bayana ya karye.”Haka Imam Husain[AS]ya koma hemar sa shi ka]ai yana kuka,Sayyida Zainab[as] tana ganin sa cikin damuwa da kuka,tace lafiya kake kuka ?yace ‘yar uwata tuta ta fa]i,an kashe Abbas,jin haka Sayyida Zainab ta yanke jiki ta fa]i,,tana cewa,wa akah, wa Abbasah.To a wannan lokacin  ne Imam Husain[AS]ya fa]is wasu kalmomi,wa]anda suka shahara sune,Hal-min-nasirin-yan suruna.Hal-min-mugisin-yugi-suna,ma’ana akwai wani mai taimako ya taimaka mana,akwai wani mai agaji ya agaza mana. Labbaika ya Husain,Labbaika ya Husain,Labbaika ya Husain.

No comments:

Post a Comment