Saturday 9 February 2013

Hanyoyin samun ta}awa a Ramadan


Kasantuwar wannan wata mai albarka, wato watan Ramadan, wanda Allah (T) ya azurta mu da azumtar sa. Daga cikin hikima da kuma manufa na wajabta mana Azumi a cikinsa, shi ne domin mu samu Ta}awa, kamar yadda Allah (T) yake fa]i a cikin Al}ur’ani mai girma, a suratul Ba}ara aya ta 183. “Ya ku wa]anda suka yi imani, an wajabta maku azumi, kamar yadda aka wajabta shi ga wa]anda suke gabaninku, domin ku samu ta}awa”.
Daga wannan aya mutum zai iya fahimtar manufa da kuma Hikimar wajabta mana azumi shi ne domin mu samu ta}awa.
Saboda  haka ke nan azumi yana ]aya daga cikin hanyoyin samun ta}awa.  Fatarmu a nan ita ce, Allah (T) ya saka mu cikin wa]anda za su fito cikin wata na Ramadan da satifiket na ta}awa. Tambayoyi a nan su ne 1- mece ce ma’anar ta}wa? 2- Mene ne matsayin ta}awa a addini? 3- Mene ne siffofin masu ta}awa? 4-Wa]anne hanyoyi ne na samun ta}awa? 5- Wa]anne abubuwa ne suke hana samun Ta}awa? 6- Wa]anne matakai ko maratib ne na ta}awa? 7- Mene ne fa’idoji ko Natijoji na samun Ta}awa?
Insha Allah a kan wa]annan tambayoyi da suke da ala}a da ta}awa, wannan Rubutun zai gudana. Tambaya ta farko, Mece ce ta}wa? Wato ma’anarta. Malaman Tafsiri da kuma Malaman Irfan, sun fassara ta, ta fuskoki daban-daban. Idan mutum ya duba littafin Minhajul-Abidin na gazaliy Juz’i na ]aya, zai ga ya kawo fassarori daban-daban na Malaman Tasawwuf ko Irfan. Akwai wasu daga cikin Fassarori na ma’anar ta}wa a Is]ilahance, ba a luggance ba, da Malaman tafsir da irfan suka bayar, su ne:- 1-Akwai wa]anda suka fassara ta da cewa, Ta}wa ana nufin tsoron Allah (T). 2- Wasu kuma sun fassara ta da cewa, tana nufin biyayya ga Allah (T), wato ]a’a gare shi, a bayyane da kuma ~oye. 3-Wasu kuma sun fassara ta da cewa tana nufin nisantar zunubi na zahiri da ba]ini, har ma wa]anda suka tafi a kan wannan fassara, suna kafa hujja da wannan ayar, wadda ta ce “Duk wanda ya yi ]a’a ga Allah da Manzonsa, kuma ya ji tsoron Allah, ya yi ta}wa gare shi, to wa]annan su ne masu samun babban Rabo”. Suka yi bayanin cewa, a cikin ayar ga shi an ambaci ]a’a ga Allah (T) da kuma tsoron shi, sannan kuma aka ambaci ta}wa. Suka ce lalle ke nan ta}wa tana da wata ma’ana banda ]a’a da kuma tsoro ga Allah (T). 4- Akwai kuma wa]anda suke fassara ta}wa, tana nufin mara}aba, wato mutum ya dinga Shu’urin (Jin) cewa Allah (T) yana ganin sa, yana jin sa, ya kuma san abin da yake cikin zuciyarsa. 5-Akwai kuma wa]anda suka fassara ta}wa da cewa tana nufin misaltuwa da umarnin Allah (T) da kuma hanuwa da haninsa. Mafi yawan Malamai a kan wannan fassara suka tafi. Kuma wannan fassara ta yi kama da wadda ta zo daga Imam Sadi} (A.S), lokacin da aka tambaye shi dangane da tafsirin ta}wa. Shi ne Imam Sadi} (AS) ya ce, ta}wa tana nufin kada Allah (T) ya rasa ka a inda ya umarce ka, kada kuma ya ganka a inda ya hana ka”. Saboda haka a nan idan mutum na son ya zama mai ta}wa, sai ya ]abba}a ko ya aikata duk wa]annan fassarori da aka ambata, wato ya kasance mai tsoron Allah (T) mai mura}aba gare shi, sannan kuma ya misaltu da umurnin Allah (T) ya kuma nisanci haninsa. Wannan ke nan dangane da ma’anar ta}awa. Sai tambaya ta biyu.
Meye matsayin Ta}wa a addini na Musulunci? Idan mutum ya karanta Al-}ur’ani mai girma tun daga farko har }arshe, zai ga cewa babu wata siffa kyakkyawa, wadda ambatonta ya zo a wurare da yawa kuma ya maimaitu, kamar ta}wa wannan ka]ai ya isa ya nuna matsayin ta}wa a addinin Musulunci. Kuma duk al’ummun da Allah (T) ya ba su Littafi gabanin wannan al’umma ta Manzon Allah (S) da ma wannan al’umma ta Manzon Allah (S). Baki ]ayansu, Allah (S) ya yi masu wata wasiyya guda ]aya, wannan wasiyya ita ce, wasiyya ta ta}wa. Kamar yadda Allah (T) ya fa]i, a cikin Suratul-Nis’i, aya ta 131. “Ha}i}a lalle mun yi wasiyya ga wa]anda aka ba Littafi gabaninku, da ma ku kanku da ku yi ta}wa ga Allah (T)”. Haka nan dukkan Manzannin da Allah (T) ya aiko, tun daga Manzon farko har ya zuwa Manzon }arshe, To babu wani Manzo daga cikin wa]annan Manzanni, sai da ya ce ma mutanensa da su yi ta}wa. Ga misalan haka, a cikin Suratu Shu’ara aya ta 105, Allah (T) yana cewa, “Mutanen Nuhu sun }aryata Manzanni, lokacin da ]an’uwansu Hud ya ce masu, shin ba za ku yi ta}wa ba.” Haka nan kuma a surar, aya ta 160 Allah (T) yana cewa, “Mutanen Lu] sun }aryata Manzanni. A lokacin ]an uwansu Lu] ya ce masu, shin ba za ku yi ta}wa ba”. Har walayau dai a cikin surar a aya ta 176, Allah (T) yana cewa “Mutanen Aikati (wato mutanen Annabi Shu’aibu sun }aryata Manzanni, A lokacin da Shu’aibu ya ce musu, shin ba za ku yi ta}wa ba.” A kuma cikin Suratu Saffat aya ta 123. Allah yana cewa. “Lalle Ilyas yana daga cikin Manzanni, a lokacin da ya ce ma mutanensa, shin ba za ku yi ta}wa ba.”
A ta}aice kamar yadda aka ambata, babu wani Manzo daga cikin Manzanni, face sai da ya ce ma mutanensa su yi ta}wa. Bayan haka kuma mafificin guzuri da mutum zai yi a wannan gida na duniya, shi ne guzuri na ta}wa, kamar yadda Allah (T) yake cewa a Suratul-Ba}ara aya ta 197. Ku yi guzuri, amma mafi alhairin guzuri shi ne ta}wa”. Kuma ta}wa ita ce mafi alherin tufa na ba]ini, kamar yadda Allah (T) yake cewa a Suratul A’araf aya ta 26 “Tufafin ta}wa shi ya fi alheri”.
Kuma Allah (T) ya sanya Waliyyansa, su ne masu ta}wa, kamar yadda yake cewa a suratu Yunus “Ku saurara, lalle Waliyyan Allah babu tsoro gare su, ba kuma ba}in ciki, su ne wa]anda suka yi imani kuma suka kasance masu ta}wa”. A Suratul Anfal kuma aya ta 34, yana cewa “Lalle Waliyyansa su ne masu ta}wa”.
Haka nan kuma kar~ar aiki, Allah (T) yana yi ne kawai ga masu ta}wa. Kamar yadda yake cewa a Suratu Ma’ida aya ta 27 “Lalle yana kar~a ne kawai daga masu ta}wa”. Kuma siffatuwa da ta}wa hanya ce ta samun son Allah (T), kamar yadda ya zo a wurare da yawa cikin Al}ur’ani, cewa “Lalle Allah yana son masu ta}wa,” haka nan kyakkyawar a}iba ta masu ta}wa ce, kamar yadda Allah (T) yake fa]in haka a wurare daban-daban a cikin Al}ur’ani “Lalle A}iba ga masu ta}wa”. Haka nan kuma ma’iyya ta Allah (T), wato ya kasance Allah (T) yana tare da mutum ga dukkan al’amuransa, kamar yadda  Allah (T) yake cewa a Suratu Taubat, aya ta 36 “ Ku sani lalle Allah yana tare da masu ta}wa”.
Haka nan ma’auni na matsayi a wajen Allah (T) ko rashin matsayi, shi ne ta}wa, kamar yadda a suratul hujurat aya ta 13 “Lalle mafi matsayi a wajen Allah, shi ne wanda ya fi ku ta}wa”. Wato ke nan daidai ta}war mutum, daidai matsayinsa a wajen Allah (T). Wa]annan abubuwan da aka ambata na matsayin ta}wa, ga abubuwan da suka shafi rayuwar mutum a duniya ke nan. Idan kuma aka juya ga abubuwan da suka shafi rayuwar mutum ta lahira, za mu ga cewa Aljanna da abin da ke cikinta na ni’imomin Allah (T) ya yi tanadinsu ne ga masu ta}wa, kamar yadda ya fa]i haka a wurare da yawa a cikin Al}ur’ani mai girma. Ga misali na wasu daga ciki. A Suratu Dukhan aya ta 51-57. “Lalle ne masu ta}wa suna cikin matsayi amintacce a cikin gidajen aljanna da maremari, suna masu tufatuwa da tufafin alhariri mai kauri da kuma marar kauri. Suna masu fuskantar juna a aljanna, sannan muka aurar masu da mata na Hurul’in. Kuma suna masu kira a cikin gidan aljanna ga dukkan ’ya’yan itacen marmari, kuma suna amintattu, wato daga dukkan abin tsoro, ba su ]an]anar mutuwa a cikinta, face mutuwar farko, kuma Allah ya tsare su daga azabar Jahim. Saboda falala daga ubangijinka, wancan shi ne babban rabo, mai girma.
A cikin suratu }amar aya ta 54 “lalle masu ta}wa suna cikin gidajen aljanna da kuma }oramu”. A kuma cikin suratu Naba’i aya ta 31-36 “Lalle ne masu ta}wa suna da babban rabo, lambuna da kuma inabobi, da ’yan mata tsararrakin juna, da kofuna cikakku. Ba su jin lagwu a cikinta, kuma ba su jin }aryatawa wannan sakamako daga ubangijinka, kuma kyauta mai yawa”. Kuma a cikin suratu mursalat aya ta 41-44. “Lalle ne masu ta}wa suna a cikin inuwowi da kuma maremari. Da ’ya’yan itace irin wa]anda suke marmari, Ana ce masu ku ci, ku sha cikin ni’ma, saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa. Lalle ne mu haka muke saka wa masu kyautatawa”. Da dai sauran ayoyi makamantan ta}wa ne.
Idan kuma aka koma zuwa ga Hadisai da aka samo daga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul-bait (AS) da suke nuna matsayin ta}wa, su ma za mu ga suna da yawa, amma ga ka]an daga ciki. An samo daga Imam Ali (A.S) yana cewa “Ta}wa ita ce Shugabar Akhla}. Manzon Allah (S) ya ce “Mafi yawan abin da zai shigar da ‘yan al’ummata aljanna, su ne ta}wa  da kuma kyawawan ]abi’u”. Imam Ali (A.S) ya ce, “mafificiyar taska, ita ce ta}wa”. Har wala yau daga Imam Ali (A.S) ya ce  “Ta}wa ita ce mabu]in karama”. A wani hadisi kuma Imam Ali (AS) yana cewa “Duk wanda ya shuka itacen ta}wa, to ha}i}a zai girbi ’ya’yan itace na shiriya.” Da dai wasu hadisai da aka samo daga ma’asumai (AS) da suke nuni ga matsayin ta}wa. Wannan ke nan a ta}aice dangane da matsayin ta}wa a addinin Musulunci.
Sai kuma tambaya ta uku, wato siffofin masu ta}awa. Allah (T) a cikin Al}ur’ani mai girma, a wasu ayoyi ya bayyana Siffofi na masu ta}awa. Alal misali a cikin Suratul Ba}ra akwai wuri biyu. A cikin suratu Ali-imran, shi ma akwai waje biyu. A cikin suratu Anbiya akwai waje ]aya. A cikin suratu Zariyat, shi ma waje ]aya. Ga siffofin kamar yadda suka zo a cikin wa]annan surori da aka ambata. A suratul-Ba}ara waje na farko shi ne farkon Ba}ara ]in. Wato A.L.M, wancan littafin babu kokwanto a cikinsa, kuma shiriya ne ga masu ta}wa (sai ya kawo siffofinsu) su ne 1- Wa]anda suke imani da gaibi. 2- Suke tsaida sallah. 3-Suna ciyar da abin da Allah ya azurta su. 4-Suna masu imani da abin da aka saukar wa Manzon Allah (S) da kuma abin da aka saukar gabaninsa. 5- Kuma su masu ya}ini ne game da lahira.
Waje na biyu na siffofin masu ta}wa a Suratul-Ba}ara shi ne aya ta 177. “Bai zama ]a’a ba don kun juyar da fuskokinku, wajen Gabas da Yamma, amma ]a’a shi ne ga wanda ya yi (sai aka jero siffofin da aka saukar da Annabawa. 2- Kuma ya ba da dukiya a kan yana sonta ga ma’abota zumunta da marayu da matalauta da ]an hanya da masu tamabaya da kuma fansar wuya, 3- Kuma ya tsayar da sallah, 4- Kuma ya ba da zakka, 5- Da kuma cika al-}awari, idan an yi al}awarin, 6- Da kuma yin dauriya a lokacin tsanani (talauci) da cuta (rashin lafiya) da kuma lokacin ya}i. To wa]annan da suke siffata da wa]annan siffofi su ne masu gaskiya, wato suka gasgatawa. Kuma wa]annan su ne masu ta}wa.
Sai kuma siffofin masu ta}wa da suka zo a suratu Ali-Imran. Waje na farko shi ne aya ta 15-17. “Ka ce shin in gaya maku mafi’alhairi daga wannan? Ga wa]anda suka yi ta}wa suna ]a’a wajen Ubangijinsu, gidajen aljanna, wanda }oramu ke gudana }ar}ashinsu. Suna masu dawwama a ciki da kuma mataye tsarkaka da yarda daga Allah. Kuma Allah mai gain ne ga bayinsa. (sai aka jero siffofin masu ta}awar) 1- Wa]anda suke cewa ya ubangijinmu, lalle mu, mun yi imani, ka gafarta mana zunubbanmu, kuma ka tsare mu daga azabar wuta. 2- Masu dauriya. 3- Masu kuma Istigfari a lokacin As-har (As-har, lokaci kafin ketowar al-fijir). Sai kuma waje na biyu a suratu Al-Imran na Siffofin masu ta}awa. Aya ta 133-136. “Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku, da Aljanna wadda fa]inta sammai da }assai, An yi tattalinta domin masu ta}wa (sai aka jero siffofinsu. 1-Wa]anda suke ciyarwa, a cikin sau}i da tsanani. 2- Kuma masu ha]iye fushi. 3- Kuma masu afuwa ga mutane. Kuma Allah yana son masu kyautatawa. 4- Kuma wa]anda suke, idan suka aikata alfasha, ko suka zalunci kansu, sai su tuna Allah, sai su nemi gafarar zunubbansu. Kuma wane ne yake gafarar zunubbai face Allah? Kuma ba su dogewa a kan abin da suka aikata, alhali suna sane. Wa]anda sakamakonsu gafara ce daga Ubangijinsu da kuma gidajen aljanna, wa]anda }oramu ke gudana }ar}ashinsu. Kuma suna masu dawwama a cikinta,  kuma madalla da sakamakon masu aiki.
Sai kuma siffofin masu ta}wa da suka zo a suratul-Anbiya, aya ta 48-49. “Ha}i}a mun baiwa Musa da Harun rarrabewa da Haske da kuma ambato ga masu ta}wa. 1- Wa]anda suke tsoron Ubangijinsu a ~oye. 2- Kuma su dangane da sa’a (tashi }iyama), masu jin tsoro ne. Sai kuma siffofin masu ta}wa da suka zo a cikin Suratu-Zariyat aya ta 15-19. “Lalle ne masu ta}awa suna cikin gidajen al-janna da kuma maremari, suna masu kar~ar abin da Ubangijinsu ya ba su. Lalle su sun kasance gabanin haka (wato a duniya) sai aka jero siffofin 1- Sun kasance masu kyautatawa ne. 2- Kuma sun kasance ka]an ne cikin dare suke barci. 3- A lokacin As-har kuma suna Istigfari. 4- Kuma a cikin dukiyarsa, akwai ha}}i ga mai ro}o da wanda aka hana ma ro}o. (wato suna bayarwa ga wanda ya ro}e su, da ma wanda bai ro}e su ba). Wa]annan su ne siffofi na masu ta}wa da suka zo a cikin wa]annan surori.
Kuma saboda gudun tsawaitawa ne ya sa ba zan yi sharhi a kan kowace siffa ba. Amma abin da yake da muhimmanci a nan shi ne, mutum ya dubi wa]annan siffofi da aka kawo ]aya bayan ]aya, ya kuma binciki kansa, ya siffantu da su. In ya siffanta da su mutum sai ya gode wa Allah (T) ya kuma da]a }aimi wajen da]a siffantuwa da su. In ko aksin haka ne, to sai mutum ya yi mujahada wajen ganin cewa ya siffatu da su. Domin ya kasance da taimakon Allah (T) ya samu ya shiga wannan aji na masu ta}wa.
Bayan haka, idan mutum ya duba littafin Nahjul-Balagha, zai ga akwai wata khu]uba wadda a cikinta Imam Ali (AS) ya kawo siffofin masu ta}wa. Wanda asalin wannan khu]uba shi ne, wani daga cikin mabiyansa, sunansa Hammam, an ce mutum ne mai yawan ibada, ya bu}aci Imam Ali (A.S) da ya siffata masa masu ta}awa kamar yana ganinsu. Imam Ali (AS) ya yi jinkiri wajen ba shi amsa, saboda abin da yake gani zai faru in ya ba shi amsa. Daga baya sai ya ce masa “Ya Hammam ka kasance mai ta}wa, mai kuma kyautatawa, domin Allah (T) yana tare da masu ta}wa da kuma wa]anda suke masu kyautatawa.” Duk da haka dai Hammam ya sake bu}atar Imam Ali (AS) da ya yi masa bayanin Siffofin masu ta}awa, To Shi ne Imam Ali (AS) ya yi wannan khu]uba, bayan ya yi godiya da yabo ga Allah (T),kuma ya yi salati ga Manzon Allah (S), bayan haka shi ne ya yi bayanin siffofin masu ta}wa. Imam Ali (AS) yana cikin kawo siffofi da alamomi na masu ta}wa. Hamman ya suma, nan take kuma ya rasu, sai Imam Ali (AS) ya ce, Wallahi dama abin da na guda ke nan.” Khu]ubar tana da tsawo, amma ga mai bu}ata yana iya duba Nahjul-Balagha. Wannan ke nan a ta}aice dangane da siffofin masu ta}wa.
Sai tambaya ta hu]u, wato hanyoyin samun ta}awa. Idan mutum ya duba littafin Jundullahi na Sa’id Hawa, zai ga a cikinsa, ya kawo hanyoyi na samun ta}wa, ya kawo hanyoyi guda hu]u wanda ko wanne ]aya daga ciki, ya yi dogon bayani a kai. Insha Allah bayanin wa]annan hanyoyi na samun ta}wa. Da kuma sauran tambayoyi, wato 5-Abubuwan da suke hana samun ta}wa. 6-Matakai na ta}wa. 7- Da kuma fa’idoji da Natijoji na samun ta}awar. Wani lokaci za a ]ora a kai.



No comments:

Post a Comment