Kasantuwar
3 ga watan Rajab ne wafatin Imam Aliy Alhadi (AS), kamar yadda aka saba a irin
wa]annan munasabobi na wafati da kuma shahadar Ma’asumai (AS), akan gabatar da
Darussa a ta}aice daidai gwargwado, na tarihinsu da kuma wasu ~angarori na
rayuwarsu daban-daban, da nufin su kasance madubi da za mu dubi kawukanmu da
kuma rayuwarmu da su, da kuma yin mujahada daidai ikonmu.
Domin mu ga cewa mun
aikata abubuwan da muka karanta, domin aikata abin da mutum ya sani, yana bu]e
wa mutum }ofar ilimin da bai sani ba.
Kamar yadda ya zo a Hadisi cewa,
“duk wanda ya aikata abin da ya sani, Allah (T) zai gadar masa ilimin da bai
sani.” Wannan tabbas haka ne. Mutum ya jarraba haka a rayuwarsa, ya gani.
Misali duk lokacin da mutum ya ji ko ya karanta wani Hadisi ko kuma ruwaya ta
Manzon Allah (S) da kuma Ahlul-Bait (AS) ya kuma aikata daidai ikonsa, sai
mutum ya ga ba da jimawa ba Allah (T) ya sake ni’imta shi da sanin wa]ansu
domin ya aikata. Haka nan abin yake a ayoyi na Al}ur’anin da muke karantawa. In
har mutum na karanta Al}ur’ani mai girma tare da aikatawa daidai gwargwadon
ikonsa, to, zai ga Allah bisa falalarsa yana sanar da shi wasu daga cikin asrar
na ayoyin da yake karantawa, watau ba]ini na ayoyin. Kamar dai fa]in Allah (T)
da ya ce, “ku yi ta}awa ga Allah, Allah ya sanar da ku.” Kamar yadda aka sani
]aya daga cikin fassarori na ta}awa shi ne misaltuwa da umurnin Allah (T) da
kuma hanuwa da haninsa. Kuma rashin aikata abin da mutum ya sani zai kasance ne
musiba ga mutum gobe }iyama, kamar yadda haka ya zo a Hadis. Domin zai kasance
ke nan hujja a kan mutum. Kuma shi aikata Addini ko kuma aikata abin da mutum
ya sani zai yi shi ne da ‘Ikhlasi’. Wato saboda Allah(T) da kuma neman
yardarsa, ba domin a yaba masa ko samun matsayi ko kuma wani abu na duniya ba. Domin kamar yadda rashin aikata abin
da mutum ya sani zai kasance musiba ga mutum gobe }iyama, to, haka ma idan ya
sani kuma ya aikata, amma ba tare da ‘Ikhlasi’ ba, shi ma zai kasance musiba ga
mutum gobe }iyama.
Ya zo a wani Hadis, mai ban tsaro da
kuma ta da hankali cewa za a zo da wasu mutane gobe }iyama wa]anda suka rayu a
fagage daban-daban na ba da gudummuwa ga Addini, amma daga }arshe Allah (T) zai
ce a kai su wuta, saboda rashin ‘Ikhlas’ a cikin ayyukansu. Wannan ko ba
}aramar hasara ba ce. A ce aiki ba mummuna ba watau na sa~o, kyakkyawa na ]a’a,
amma sakamakon rashin ‘Ikhlasi’ a ciki, ya yi sanadiyyar zuwan mutum wuta. Shi
ya sa in mutum ya duba kuma ya bibiya zai ga cewa Malam, watau Sayyid Zakzaky
(H) a mu’utamarori daban-daban da aka gabatar, ake kuma gabatarwa, lokaci bayan
lokaci a garuruwa daban-daban, yana yawan magana da kuma }arfafawa a kan ilimi,
aiki da ikhlasi. Zai yi wahala ka ga a kullewar Mu’utamar, Sayyid Zakzaky bai
yi magana a kansu ba, ko wani daga ciki, watau saboda gayar muhimmancinsu.
Baya ga wa]annan matakai uku watau
Ilimi, aiki da ikhlasi, sai kuma’ Khauf’, watau mutum ya zauna cikin tsoro
tsakanin sa da Allah (T), ya dinga yawan tunanin cewa shi }ashin kansa da kuma
’yan ayyukan da yake aikatawa kar~a~~u ne a wajen Allah (T) ko ba kar~a~~u ba
ne? Yaya a}ibarsa ko }arshensa zai kasance a Addinance a wannan gida na duniya?
Kuma ya al’amarinsa zai kasance gobe }iyama? Ana son mutum ya zauna cikin
tsoron wa]annan abubuwa da aka ambata da ma wa]anda ba a ambata ba; musamman ma
tunanin tsoron a}iba. Domin da za a tambaya a ce, me ya fi komai muhimmanci a
rayuwar ]an Adam? Amsa ita ce yadda }arshensa ya kasance a Addinance a zamansa
a wannan gida na duniya. Domin a kan abin da mutum ya mutu a kai, a kansa za a
tashe shi.
Maganin mummunar a}iba a Addini, kamar
yadda Malaman ‘Irfani’ suka yi bayani yana samuwa ta hanyoyi uku: 1. Yawaita
Addu’ar neman kyakkyawar A}iba daga wajen Allah (T) 2. Nisantar Zunubi, watau
mutum ya yi iyakar iyawarsa wajen ganin cewa ya nisanci zunubi, watau Sa~o.
Domin yadda ya zo a Hadisi cewa, duk lokacin da mutum ya yi zunubi, idan bai
tuba ba, akan sa ba}in ]igo a zuciyarsa, in ya sake, a sake sa ba}i. Kama-kama
in ya ci gaba a haka, har zuciyar ta zama ba}i-}irin. Domin shi zunubi
illolinsa da kuma gubarsa suna da yawan gaske. Misali yana iya dabaibaye mutum
daga ayyukan ]a’a. Watau ya kasance mutum ya saba yin wasu ayyuka na ibada,
amma sakamakon wani zunubi da ya yi, ya samu kansa bai iya aikata komai, ko
kuma ya shamakance mutum daga addu’o’insa da dai makamantansu na illolin
zunubi. Shi ya sa in mutum ya duba zai ga bayin Allah (T) da ya za~a, su
kasance Hujjoji ga bayinsa, dukkansu suna da wannan siffa ta ‘isma,’ wadda ]aya
daga cikin ma’anoninta shi ne rashin aikata sa~o.
3. Hanya ta uku ta maganin mummunar A}iba ita ce kyautata wa Allah (T)
zato. Kamar yadda ya zo a Hadisi cewa, Allah (T) yana nan inda bawansa yake
zaton sa, watau mutum ya dinga tunanin cewa, insha Allah, Allah (T) zai yi masa
kyakkyawan }arshe a Addini, ba mummunan }arshe ba. Khulasar da aka ambata shi
ne Ilimi, aiki ‘ikhlas da ‘khauf’, watau
tsoro na ababen da aka ambata. Kuma wa]annan abubuwan guda hu]u da aka ambata,
ba za su samu ba, sai tare da yin mujahada da ‘Nafs’ ]insa (ransa) da kuma
Shai]ani da kuma duniya da kuma mutane. Haka mutum zai ta fama da wa]annan
~angarori na mujahada matu}ar yana raye, hutunsa sai ran da ajalinsa ya sauka.
Kamar yadda ya zo a Hadis cewa, mutuwa hutu ce ga mumini, watau daga irin
wannan dama da kuma mujahada da ransa da shai]ani da dai sauransu.
Dawowa
ga wannan munasaba ta Imam Ali Alhadi (AS), Imam Aliy Alhadi kamar yadda aka
sani shi ne, Imam na goma a jerin }idaya na Imamai 12. An haife
shi a wani gari kusa da Madina, ana ce masa Sarya, a ran 15 ga watan Zul Hijja,
shekara ta 212 bayan Hijira. Mahaifinsa kamar yadda aka sani shi ne Imam Jawad
(AS). Sunan Mahaifiyarsa Sumanatu, amma an fi sanin ta da Sayyida, kuma ana yi
mata kinaya da Ummi Fadhal. Kamar yadda
ya zo a tarihi, ta kasance mai yawan
ibada, musamman ma ta ~angaren Azumi. Kuma ta kasance mai ta}awa da kuma zuhud,
watau gudun duniya. Imam Aliy Alhadi (AS) ya kasance yana da la}ubba da yawa,
amma wa]annan biyun su suka fi fice, Alhadi da kuma Anna}iy. Imam Aliy Alhadi
(AS) ana yi masa kinaya da Abul Hasanis-Salis,Abul Hasanis- Sani, shi ne Imam
Ridha( AS), domin a wasu littafan tarihi ko Hadisi, kinayar kawai sukan fa]i na
wa]annan Imamai, ko kuwa wani lokaci a littafai mutum ya ci karo da wannan
kinayar Abu Jafarul Awwal. Ana nufin Imam Ba}ir (AS) ko kuma Abu
Jafarus-Sani, ana nufin Imam Jawwad (AS).
Imam Aliy Alhadi ya rayu tare da
Mahaifinsa Imam Jawwad (AS) shekaru 8, bayan wafatinsa, Imamanci ya dawo gare
shi. Muddar Imamancinsa shekara 33, a wata ruwaya kuma 34. Imam Alhadi (AS) ya
kasance yana da yara 5 - maza 4, mace 1. Sune: Imam Hasan Al’askari (AS),
Husain, Muhammad, Jafar da kuma Aliyya. Imam Aliy Alhadi (AS) ya zauana a
Madina, kusan Shekaru 22 yana Madina. Khalifan Abbasawa mai suna Mutawakkil, ya
sa a zo a ]auke shi daga Madina zuwa Ira}i. Ya aiko runduna na maya}a zuwa
Madina domin su tafi da Imam Hadi (AS) a cikin dare. Da suka shiga gidan, sai
suka same shi zaune yana karatun Al}ur’ani mai girma, suka bincike gidan baki
]ayansa. Bayan haka suka kama hanya da shi zuwa Ira}.
A wannan tafiya Imam Aliy Alhadi
(AS) da zai fita, ya fita tare da ]ansa Imam Hasan Al’askari (AS), lokacin yana
shekara hu]u da watanni. Da suka isa Ira} an kai Imam Hadi (AS) wajen
Mutawakkil, a inda abubuwa marasa da]in ji da kuma karantawa suka gudana,
wa]anda shi Mutawakkil ya yi ga Imam Hadi (AS). Da yake lokacin da suka isa
wajen Mutawakkil ]in yana shan giya ne, watau a buge yake. Ga mai bu}atar sanin
abubuwan da suka gudana, yana iya duba littafi mai suna A’immatuna Juzu’i na
biyu. Haka Imam Aliy Alhadi (AS) ya zauna a Ira}i, a garin Samarra, a wata
unguwa da ake kira da Askar tare da ]ansa, Imam Hasan Askari (AS). Shi ya sa
daga cikin la}ubban Imam Hadi (AS) akwai Askari, saboda haka a nan ya }are
sauran rayuwarsa, watau a Ira}. Ya zauna a cikinta shekaru 20. Imam Aliy Alhadi
(AS) ya rayu a duniya shekaru 42. {abarinsa yanzu haka yana Samarra ne tare da }abarin
]ansa Imam Askari (AS).
Imam Hadi (AS) ya rasu ranar Litinin
3 ga watan Rajab shekara ta 254 bayan hijira. Ya rasu ne sakamakon guba, wadda
Khalifan Abbasawa mai suna Mu’utazaz ya sa masa. Imam Aliy Hadi (AS) ya yi
zamani da Khalifofin Abbasawa guda shida. Su ne Mu’utassim, Wasik, Mutawakkil,
Muntasir, Musta’in, Mu’utazaz. To, a cikin wa]annan guda shidan, wanda ya fi
gallazawa da cutarwa ga Imam Hadi (AS) shi ne Mutawakkil (LA). Kuma cikin su
shida ]in shi ya fi su tsawon shekaru a mulki, don shekararsa 14 a karagar
mulki. Kuma a cikin wa]annan shekaru ya yi munanan abubuwa masu yawan gaske. Ga
goma daga ciki:
1. [auko Imam Hadi (AS) da kuma raba
shi da Madina, birnin Manzon Allah (S). 2. Sa Imam Hadi (AS) da kuma mabiya
]aruruwan Ahlul-Bait (AS) a kurkuku, wanda sai bayan mutuwarsa aka saki mafi
yawan su. 3. Ya sha yun}urin kashe Imam Hadi (AS) Allah (T) ya tsare. 4. Nuna
}iyayya da gaba ga Imam Aliy (AS) da kuma Sayyida Fa]ima (AS). Ya zo a
tarihinsa cewa saboda gayar }iyayya da gaba har zagin su yana yi. Zagin nasa ma
bai ta}aita ga Imam Aliy (AS) ba, a’a har ga Sayyida Fatima (AS),
wa’iyazubillah. Wannan mummunan aiki nasa na zagin wa]annan bayin Allah (T) shi
ya zama sanadiyyar ajalinsa.
Abin da ya faru shi ne, wata rana
]ansa mai suna Muntasir ya ji shi yana zagin Sayyida Fatima (AS). Abin ya ~ata
masa rai matu}a, shi ne ya je ya samu wani Malami ya tambaye shi, ga munanan
abin da mahaifinsa yake yi, zai iya kashe
shi? Sai Malamin ya ce masa eh. Shi ne
ya shirya, shi da wasu abokansa suka samu la’ananne a cikin gida, inda
yake shaye-shayensa na giya, suka auka masa, suka kashe shi. Shi wannan ]an
nasa shi ya zama Khalifan Abbasawa a bayansa.
5. Ya sa aka rushe }abarin Imam
Husain (AS) da kuma gidajen da ke kewaye. Duk wannan bai ishi Mutawakkil ba, ya
sa a yi gona a wajen, wai saboda }abarin da alamominsa su ~uya ga mabiyaAhlul
bait. To, ta Allah ba ta shi ba, }abarin bai ~oyu ba. 6. Kafin ba da wannan
umurni nasa na a rusa }abarin Imam Husain (AS), sai da ya sa a rin}a kamawa da
kuma azabtar da masu ziyarar Imam Husain (AS). Akwai ma lokacin da ya ba da
umurnin cewa duk wanda aka kama yana ziyartar Imam Husain (AS) a yanke masa
hannu tun daga kafa]a har ya zuwa yatsun hannu. A ta}aice dai hannun baki ]aya.
In ya sake kawo ziyarar, ]aya hannun ma ai masa haka. In ya sake a zo ga }afa,
ita ma baki ]aya. To, akwai wani da aka yi masa haka, saboda ziyarar Imam
Husaini (AS) aka yanke masa hannaye biyu. Ya zamanto yana zuwa ziyarar a kan
dabba. Aka yanke masa }afa. Ya zamanto saura }afa ]aya. Da ya sake zuwa aka
]auke shi aka kai shi har wajen Mutawakkil, shi ne yake tambayar sa, kai me ya
kai ka kake wannan abu haka? Ya ba da amsa da cewa, saboda so da kuma shau}insa
ga Imam Husain (AS). Ya ce kuma ko da za a yayyanka naman jikinsa, matu}ar zai
iya zuwa ziyarar, sai ya je.
7. Shi ya sa aka cire dabinnai
wa]anda Manzon Allah (S) ya shuka a Fadak da hannayensa masu albarka, watau
Fadak da Manzon Allah ya bai wa Sayyida Fatima (AS). Shi wanda aka sa ya yi
wannan aika-aikar ta cire dabinan, daga baya jikinsa ya shanye. 8. Kamawa da
kuma }wace dukiyar duk wanda ya taimaka wa Sadat, watau jikokin Manzon Allah
(S). Wannan abu da ban mamaki, idan mutum ya duba littafi mai suna
TATIMMATUL-MUNTAHA FI TARIKHIL KHULAFAI na Shaikh Abbas {ummy, watau marubucin
Littafin Mafatihul Jinan, zai ga ya kawo abubuwa daban-daban na matsalolin da
aka jefa Sadat a ciki. Ba don komai ba, saboda }iyayyarsa ga Imam Aliy (AS) da
kuma Sayyida Fatima (AS).
[aya daga cikin matsalolin da aka jefa su da gangan ita ce ta talauci. Ya
zo a kan cewa saboda rashi, ta kai ga wasu daga cikin Sadat mata, ba su da
tufafin da zai rufe jiki baki ]aya a lokacin Sallah sai guda ]aya, saboda haka
yadda suke yi shi ne in ]aya ta yi Sallah, in ta gama sai ta ba ]ayar. Haka
Sadat suka kasance a cikin wannan yanayi har sai bayan da ya mutu, ]ansa
Muntasir, ya kyautata ma Sadat. Ya kuma saki ]aruruwan mabiyan Ahlul-Bait (AS)
da aka ]aure a kurkuku. 9. Daga munanan ayyukan da Mutawakkil ya sa aka yi shi
ne, kashe Malamin ’ya’yansa, kisa mummuna, watau na Musla. Abin da ya faru shi
ne. Wata rana Mutawakkil ya tambayi wannan Malami ’ya’yana wane da wane watau
Mu’utazaz da kuma Mu’ayyid su suka fi maka ko ko Hasan da Husain? Sai Malamin
ya ba da amsa da cewa, “Mai yi wa Imam Aliy (AS) hidima (watau Bawan sa) ya fi
ka, ya fi ’ya’yanka”. Shi ne Mutawakkil ya fusata ya sa a yanke harshensa, a
farka masa ciki; haka dai daga }arshe aka yi masa gunduwa-gunduwa. Mu duba irin
wannan bushewar zuciya tasa.
10. Daga
cikin munanan ayyukan Mutawakkil akwai azabtar da mutanae da wuta, watau ya sa
a }ona wasu ~angarori na jikin mutum ko kuma ya sa a jefa shi a wuta baki ]aya.
A ta}aice dai rayuwar Mutawakkil baki ]ayanta rayuwa ce ta fasadi da zalunci da
kuma fasi}anci, shi ya sa da wa]annan munanan ayyukan nasa suka tsananta, Imam
Aliy Alhadi ya yi addu’a,akan sa. Mutawakkil ko bai kwana uku ba ya mutu. Aka
huta da shi. Allahu Akbar. Saboda munanan ayyuka na Mutawakkil, shi ya sa wasu
Malaman Tarihi suke kwatanta shi da Yazid (LA), a cikin Khalifofin Banu
Umayya.
Watau shi
Mutawakkil shi ne Yazid ]in Khalifofin Abbasawa. Al’amarinsa in mutum ya
bincika tarihi zai ga sun yi kama da na Yazid ta fuskoki daban-daban. Alal
misali, kamar yadda ]an Yazid mai suna Mu’awiyyah bai bi halinsa ba, haka shi
ma ]an Mutawakkil mai suna Muntasir bai bi halinsa ba. Domin bayansa, shi ya
kyautata wa AhlulBait (AS) da kuma mabiyansu. Duk Sadat da babansa ya jefa
cikin talauci, haka ya dinga bi yana aika masu da ku]a]e da kuma kayayyaki.
Wannan ke nan dai a ta}aice, sai kuma wasu ~angarori na rayuwar Imam Hadi (AS)
1.
ILIMIN SA: Imam Aliy Alhadi (AS) a wannan fagen babu wanda ya kai shi a
zamaninsa ballantana ma ya wuce shi. Hatta ma}iyansa sun tabbatar da haka. Ga
wata }issa da ta faru lokacin yana shekara takwas a duniya mai ban mamaki da
kuma ban dariya ga wa]anda suka shirya al’amarin. Abin da ya faru shi ne,
Khalifan Abbasawa, wanda ake ce wa Mu’utassim, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar
Mahaifinsa, watau Imam Jawad (AS) bayan wafatin Imam Jawad (AS), sai shi wannan
Khalifa Mu’uttasim ya yi tunanin cewa ]ansa Imam Hadi (AS) tun da shi ne Imam
na gaba, bayan Imam Jawad (AS) kuma shi
a lokacin shekarunsa takwas, to, bari ya samo wani Malami wanda ya san yana
gaba da kuma }iyayya ga Ahlul-Bait (AS), domin wai ya karantar da Imam Hadi
(AS), kuma wai ya cusa masa }iyyayya da Ahlul-Bait (AS) (abin dariya). Ilai ko,
sai sai ya aika Madina ga Gwamnansa, ga abin da yake bu}ata. Sai aka ce ai ga
Malam wane, kowa ya san gabarsa da kuma }iyayyarsa ga Ahlul Bait (AS). Sai aka
ha]a shi da Imam Alhadi (AS), wai ya dinga karantar da shi. Sai wannan Malami
ya soma karantarwar, amma sai ya ga abubuwan da suka ba shi mamaki. Sai ya ga
duk fannin da yake so ya karantar da Imam Hadi (AS), sai ya ga ya fi shi
fahimtar fannin.
Wata rana wani wanda yake da
masaniyar wannan shirin, da suka ha]u, sai yana tambayar Malamin, ya yaron da
kake karantarwa? Sai Malamin ya ce kai wannan ba yaro ba ne dattijo ne.
Duk abubuwan da nake karantar da shi ya fi ni sanin su. Ya ba shi misali da
karatun Al}ur’ani cewa wani lokaci sai ya ce ba zai tashi ba sai ya karanta
sura kaza, sai ya fa]i surar da bai kai ba, amma sai ya ji ya karanta. Sai ya
fahimci cewa Al}ur’anin baki ]aya ya haddace shi. Bayan kwana biyu da Malamin
ya sake ha]uwa da mutumin yake tambayar sa, ya ya ga wanda yake karantarwa? Sai
Malamin ya ce wa mutumin, “Wallahi a bayan }asa babu wanda ya kai shi ilimi da
kuma daraja.” Ikon Allah sai wannan Malami wa]annan karamomin da kuma ayoyi da
ya gani ga Imam Hadi (AS) ya zama sanadiyyar wanke }iyayya da gaba da ke
zuciyarsa ta Ahlul Bait (AS) zuwa ga soyayya da kuma }auna ga Ahlul Bait (AS). A ta}aice
dai tun daga lokacin ya zama ]an Shi’a, watau mabiyin Ahlul Bait (AS). Mu duba
mu gani daga }arshe shi aka gyara. Allahumma salli ala Muhammad wa Aaliy
Muhammad.
2.
JARABAWOWIN SA: Imam Hadi (AS) ya fuskanci jarabawowi masu yawa a rayuwarsa,
musamman ma ga masu tafiyar da iko. Ga misalan wasu daga ciki: Zama a kurkuku,
yana ]aya daga cikin Imaman da suka yi zaman kurkuku, da kai hari a gidansa da
sunan bincike, wai yana tara makamai. An kai masa irin wannan harin lokacin
yana Madina da kuma Ira}i; kuma haka ya auku ba ]aya ba, ba biyu ba. Kuma duk
lokacin da suka kai irin wannan harin sukan same shi yana ibada ne. Akwai
lokacin da suka je suka same shi yana sallah. A wani harin kuma suka samu yana
karatun {ur’ani a zaune a }asa mubasharatan, watau ba wai yana kan tabarma ba
ko buzu, wannan abu ya ba su mamaki, watau su jami’an tsaro ]in da aka aiko.
Wannan ke nan baki ]aya a ta}aice. Sai In Allah ya kai mu shekara mai zuwa a
munasabar wafatinsa insha Allah za a ]ora.
No comments:
Post a Comment