Saturday 9 February 2013

Bankwana da watan Ramadan (1) 1432 A.H


Inna-lillah-wa-inna-  ilaihi- rajiun, na tafiya da kuma rabuwa da wannan babban ba}o mai girma da kuma daraja da ya ba}uncemu, wato watan ramadan. Domin idan mutum ya bincika zai ga cewa a duk watanni 12 da ake da su a musulinci, babu wani wata da aka samu ruwayoyi daga Manzon Allah (S)da kuma A’imma na ahlul-baiti (AS) na bankwana  da shi da kuma umarni da yin haka  face watan ramadan, wanda wannan ka ]ai ya isa ya nuna falala da darajan wannan watan.
Misali shine ruwaya na addu’an bankwana da watan da aka samo daga Manzon Allah (S). An samo daga Jabir ]an Abdullah al-ansariy (RA), yace: “Na shiga wajen Manzon Allah (S) a juma’ar  }arshe ta watan ramadan, lokacin da Manzon Allah (S) ya ganni sai ya ce min,ya Jabir` wannan itace juma’an }arshe  ta watan ramada. kayi bankwana da shi, Ka ce; YA UBANGIJI! KADA KA SA YA ZAMA AZUMIN {ARSHE A RAWUWATA. IN KASA HAKA, TO, KA SANI CIKIN RAHAMAR KA, KADA KA SAN YANI CIKIN WA[ANDA AKA HARAMTA WA RAHAMA”. Manzon Allah (S) ya ce duk wanda ya fa]i haka, zai rabauta da ]aya daga cikin kyawawa  guda biyu: ko dai  Allah (T) ya raya shi zuwa watan Ramadan  na  gaba ko kuma Allah ya gafarta masa  ya yi masa rahama.
Haka nan akwai ruwayoyi daban-daban guda biyu na bankwana da aka samo daga Imam Zainul Abidin (AS) wanda idan mutum ya karanta su, musamman ma a ce lokacin da yake karantawa zuciyarshi na halarce, tabbas  zai  samu tasirin haka a ruhinsa. Domin zai ga yadda Imam Zainul Abidin yake magana da sallama da bankwana da watan ramadan da kuma jin zafin rabuwa da shi, kamar ka ce mutum ne yake gabansa yake  bankwana da shi da kuma nuna damuwa na rabuwa da shi. Ga misali wasu daga cikin kalmomi na bankwana da ya yi ga watan ramadan da suke a cikin addu’o’i  da  aka ruwaito daga wajen sa (AS). Yana cewa;”Innalillahi wa inna ilaihi rajiun saboda rabuwa da watan  azumi, watan tsayuwa kuma wata na al}ur’ani.  Ya kai wannan wata namu! Muna bankwana da kai ba domin mun }osa da azumi a cikin ka ba, ba domin muna son rabuwa da kai ba. Da a ce za a iya cewa wata, Allah ya sakamaka da alheri da an ce, Allah ya saka maka da alheri ya watan ramadan”. Awani wajen yana cewa muna bankwana da kai bankwana na ba}in ciki da kuma jin zafin rabuwa da kai”.
Akwai kuma wani sashe da ya jero sallama ga wannan wata mai albarka. Misali yana cewa;”sallama gareka ya kai wannan watan idin walliyyan Allah.Sallama gareka ya mafificin wanda ake abota dashi daga lokuta.Sallama gareka na ma}wabci,wanda  zukata suka lausasa a cikinsa,kuma zunubai suka }aranta  a cikinsa.Sallama  gareka na mataimaki daga mataimaka  akan she]an.Sallama gareka wanda kazo mana da albarkoki,ka kuma wanke mu daga dattin zunubai.Sallama  gareka  wanda  ake bege da nema  gabanin zuwansa,ake kuma ba}in ciki  gabanin rabuwa dashi.Sallama gareka da kuma lailatul }adari,wadda take mafi alheri daga wata dubu.Sallama gareka a bisa falalarka,wadda aka haramta mana da kuma albarkokinka wadanda suka shu]e,wanda  yanzu mun rasa su”.                                                                                               A ta}aice dai idan mutum ya biya wannan addu’a,  ta Imam Zainul Abidin [AS] ta bankwana da watan ramadan zai ga yayi wa wannan wata mai albarka sallama biye da juna, ]ai ]ai har guda 20.Haka nan Imam Sadi} [AS] an samo irin wannan addu’a  ta bankwana  da watan ramadan daga wajensa, kuma idan mutum ya duba dukkan wa]annan addu’oi  da aka samo daga Aimma [AS] zai ga Ahlulbayt [AS] in an  kwatanta da madrasah ]in Ahlus Sunna.Mu ]auki misali  addu’oin da ake yi na watan Ramadan ,wanda  shaikh Abbas Al-}ummy  ya kawo a cikin littafin sa na mafatihul jinan,ya duba zai ga irinsu a madrasah ]in Ahlus Sunna ?  wanda in mutum yayi bincike zai ga babban littafi da ake dashi a madrsah ]in Ahlus Sunna,da  ya tattaro addu’oi  da  kuma Azkar da aka samo daga Manzon Allah [S] shine  littafin Azkar na Nawawi,idan mutum na da shi ya ]auko ya duba babin da yazo na Azkar da kuma addu’oi na watan Azumi da kuma na daren lailatul }adr, zai ga ]aya bisa uku bai kai ba  akan yadda  suka zo a mafatihul jinan,kuma wannan  bai ta}aita  ga Azumi ba,a’a  haka abin yake ga dukkan janibobi na ibadat, kamar sallah da makamantansu,wanda  ko wanne  daga cikin salloli wajibai guda biyar,mutum zai ga bayanansu,suna  da  ta’a}ibat na amma,da kuma ta’a}ibat na kassa.Da sujudu shukur,wanda  shima wannan mutum ya  duba cikin wannan littafin Azkar na Nawawi, ya ga ko zai ga irin haka.Wanda wannan  kawai ya isa ya sa mutum ya yawaita  godiya ga Allah [T] a bisa ni’imar tamassuki da wilaya ]in Ahlulbayt [AS],wanda  dama sune Manzon Allah [S] ya bar wa wannan al’ummar wasiyyar yin  tamassuki  dasu.A ta}aice dai bayin Allah [T] kamar  yadda  suke shau}i da farin cikin zuwan watan Ramadan, saboda falaloli da darajoji  da  zau}iyyat da halawat  da kuma ma’anawiyyat  na  ibadodi da ake samu a cikin watan,wanda  babu  irin haka a sauran watanni,don me  haka bazai  zama ba  alhali  Allah [T]ne ya kirayi  bayinsa  zuwa ga liyafa, kamar yadda yazo a hadisi.Kamar yadda aka sani a liyafa,akan gabatar da abinci da abin sha daban daban,to ita wannan liyafa  abincinta  da abubuwan  shanta na ruhi, sune salloli,da karatun Alkur’ani,Azkar,Addu’oi da  sauran ayyuka na ]a’a  da  bayi suka tsayu da su a cikin watan,wanda halartar da zuciya lokacin yin wa]annan ayyuka na ibadat da aka ambata, shike haifar da samun wannan ma’anawiyyat da zau}i da halawa da aka ambata a sama.Saboda haka ya na da gayar muhimmanci duk wanda Allah Ta’ala ya raya shi ya nuna masa watan Ramadan tun daga  farkonsa har  }arshensa,to,ya gode wa Allah [T] ta hanyar salatu shukur,ko kuma sujudu shukur bayan watan Ramadan ]in,domin in mutum yayi tunani,zai ga da yawa akwai wa]anda basu samu wannan ni’imar ba.Wato Allah[T] bai raya su ya nuna masu watan ba,ko kuma Allah ya nuna masu watan amma basu ga }arshensa ba.                                                                                                                                                                                                       
Baya ga wa]annan Addu’oi da aka ruwaito daga ma’asumai [AS] na bankwana da watan Ramadan,malaman Irfan sun }ara da wasu ladubba da ake son mutum ya aikata }arshen  watan  Ramadan ]in,ko kuma  bayansa.Ga wasu daga ciki:Idan mutum ya duba  littafin  mai suna Mura}abat na Ayyatullah Mirza Jawad  Attabrizy;ya na ]aya daga cikin manya manyan malaman Irfan,kuma ya fitar da malamai da yawa a wannan fage, ya ma zo akan cewa Imam khumain [KS] ya yi karatun Irfan a wajensa.Idan mutum ya duba a wannan littafin na sa da aka ambata zai ga ya kawo wasu ladubba a fasali na tara a }arshensa.Ga guda uku daga ciki.                                                                                           1.Muhasaba:Wato mutum ya zauna yayi wa kansa hisabi,ta hanyar yin tafakkuri [tunani] ya binciki kansa,shin ya samu ci gaba a addinance in an kwatanta da gabanin  kamawar watan Azumi da kuma yanzu da ya kare.Misali alakarsa da Allah [T],alakarsa da manzon Allah [S] da kuma Ahlulbayt [AS] da damfaruwa da gidan lahira,iltizaminsa da addini,sun cigaba ne,ko suna nan yadda suke gabanin watan Azumi,ko kuma wa’iyazubillah ya samu ci baya?                                                                                                                   Haka nan ta janibin akla} ]insa ya da ]a samun tsal-kakuwa  daga  akla} marasa kyau da kuma siffantuwa da kyawawan akla}? Da dai sauran abubuwa na muhasaba  da shi mai littafin ya kawo.Shine daga }arshe  yake cewa duk wanda watan Ramadan ya kama ya }are bai samu tasirantuwa da hasken watan Ramadan ba,to ya sani duhun zunubansa  sun wuce  hasken  wannan wata mai haske mai haskakawa.yace in ba haka ba yaya za’ayi ace ba zai tasirantu da hasken watan Ramadan ba da kuma na dararen lailatul }adar? Yace irin wannan mai zaluntar kansa yaji tsoron fa]awa cikin addu’ar   Manzon Allah [S] da yake cewa; “duk wanda watan Ramadan ya wuce ba’a gafarta masa ba,ka da Allah ya gafarta masa”.yace wannan kuwa itace mafi tsananin musiba.                                                                                           Dama  musiba kamar yadda aka sani takan samu bawa, imma  a fagen duniya,ko kuma a fagen addini.Musiba a fagen duniya itace;misali rashin lafiya,}uncin rayuwa,rashin aminci,cutarwa  sakamakon  kama tafarkin Allah [T],ko  kuma sakamakon  ri}o da Ahlul bayt [AS],duk  wa]annan alheri ne ga bawa.Domin  ta  hanyar haka zai samu lada da kuma daraja a wajen Allah[T].Sa~anin musiba a addini,wanda shine mutum ya dinga aikata sa~o,ko kuma zai iya aikata wani aikin ]a’a,  ya zamanto bai aikatawa,ko kuma yayi abinda zai janyo masa fushin Allah [T],ko kuma ya janyo Manzon Allah [S] da Ahlul bayt [AS] ba su son shi.Shi  ya sa yazo a wata addu’a daga Manzon Allah [S] cewa, ‘Ya Allah kada ka sanya musibarmu a addininmu’.                                                                                                                                                              A ta}aice dai musiba ce babba ga mutum watan Ramadan ya }are, bai samu sauyi da kuma tasirin watan ba.A cikin wani littafi na Imam khumain [KS] mai suna jihadul- Akbar  yana cewa, ‘Idan watan Ramadan ya wuce mutum bai samu wani canji a ‘suluk’[]abi’unsa  da ayyukansa] ]insa ba,to ya sani bai tsayu da Azumi yadda ake so ya tsayu dashi.Yace a wannan wata an kiraye ku liyafa ne,idan saninku  ga Allah bai }aru ba,to ku sani baku amsa wannan kira [na liyafar] yadda ya kamata ba.Wannan kenan a ta}aice kan muhasaba.Kuma ita muhasaba in son samu ne,mutum ya kasance ko wace rana ya na yinta,ko da safe ko da yamma,ko in zai kwanta da daddare, ko kuma in ya tashi tahajjud to ya bainciki kansa kyawawa da munanan ayyukan da ya aikata a ranar,daga }arshe kyawawa ya  gode wa Allah [T] da yayi masa muwafa}ar aikatawa,munana  ya nemi  Allah [T] ya gafarta masa,an samo daga Imam kazim [AS] yana cewa, ‘Ba ya daga cikin mu wanda bai yi wa kansa hisabi ko wace rana’.                                    
2.Afuwa:A nan shima littafin mu}araba,ya kawo wata }issa mai tsawo wadda Imam  Zainul Abidin [AS] ya kasance yana aikatawa tsakaninsa da bayinsa idan watan Ramadan ya }are.Kulasar }issa ]in shine Imam Zainul Abidin [AS] ya kasance idan watan Ramadan ya kama,bayinsa baki ]aya  duk  wanda yayi laifi bai ce masa komi,bai yi masa komai sai dai ya rubuta wane yayi laifi kaza,rana  kaza,sai daren }arshe na watan Ramadan ya tara wa]annan bayinsa baki ]aya ya ]auko wannan littafi yace; “Wane kai ka aikata abu kaza rana kaza  banyi maka komai ba,ka tuna? Yace, “lallai na tuna ya ]an Manzon Allah [S]”.Haka  zai dinga kiransu  ]aya bayan ]aya wa]anda su kayi laifi ]in,sannan sai  ya mi}e tsaye a tsakaninsu, yace masu ku ]aga  sautinku  kuce, “Ya Ali Bn Husain! Lallai ubangijinka ya kiyaye duk abinda ka aikata,kamar yadda ka kiyaye duk abinda  muka aikata,saboda haka kai mana afuwa kamar yadda kake fatan ubangiji yayi maka afuwa”.Sannan sai Imam Zainul Abidin [AS] yace, “Ya ubangijinmu,ka umurce mu mu yi afuwa ga wanda ya zalunce mu,ha}i}a mun zalunci kawukanmu, mun yi afuwa ga wanda ya zalunce mu kamar yadda kayi umurni, kai mana afuwa”.Sannan sai ya juya ga wa]annan bayin na sa,yace musu na yi maku afuwa,ni ma kun yi mani afuwa? Sai suce, “mun yi maka afuwa ya shugabanmu!” sai ya sake ce masu kuce; “Ya ubangiji kayi afuwa ga Ali Bn Husain kamar yadda yayi mana afuwa”.Sai Imam Zainul Abidin yace, “Allahumma Amin Ya Rabbil Alamin”.Wannan  }issar duk  da  kulasar  ta  aka kawo, akwai  darussa masu yawa aciki  amma ba za’a iya fitar dasu ba saboda gudun tsawaitawa,mu duba Imam Ma’asumi a ii-ti}adinmu,kuma khalifan Manzon Allah [S] ya na aikata irin haka, domin neman afuwa a wajen Allah [T],to,ina ga mu.Shine mai wannan littafi daga }arshe yake cewa,idan mutum zai yi koyi da Imaminsa a wannan aiki ya na da kyau, ya ba da misalin mutum zai iya yin haka cikin iyalinsa da ‘ya’yansa, a ta}aice dai abinda ake so,kamar yadda ko wanne yake fata yake kuma kyautata zato ga Allah [T] cewa,Allah [T] ya gafarta masa, ya yafe masa }arshen watan Ramadan, shima  ya yafe wa wa]anda suka zalunce shi,ko suka munana masa musamman ‘yan uwansa  mabiya Ahlul bayt [AS] domin kamar yadda wani malami yake cewa zai ji kunyar Manzon Allah [S] gobe }iyama,  a ce gashi ya tsaya da wani masoyin gidan Manzon Allah [S] domin wani ha}}insa.Saboda haka wannan malamin ya kasance ko wace rana yakan ce; “Ya Allah! Duk wani mabiyan Ahlul bayt [AS] da aka rubuta masa laifi saboda ni yau na yafe masa”.Saboda kamar yadda mutum yake fata ya fita watan Ramadan yana yafaffe,to shima ya yafe wa mutane.Wannan kenan a ta}aice.                                                                               
3.Tuba:kamar yadda mai littafin mura}abat ]in ya kawo,shine mutum ya tuba da kuma neman gafara wajen Allah [T] dangane da ta}aituwarsa wajen tsayuwa da ayyukan ibadodi a watan da kuma rashin kyautatawarsa  ga ayyukan ibadodi da ya aikata,wato wajen tsayuwa da ruhin ibadodi yadda ya kamata.Da ma  Malaman Irfan sun kasa  tuba kashi uku.                                                                                                                       1.Tuba ta awwam, ita ce tuba daga zunubi.                                                                                                                        2.Tuba ta kusus,[za~a~~un  bayin Allah],ita ce tuba daga gafala.wato daga tunanin Allah[T] ko kuma tunanin gidan lahira.3-Tuba ta kususul-kusus[za~a~~un- za~a~~un bayin Allah[T] ita  ce tuba daga ta}aitawa da kuma rashin  kyautatawa ga ayyukan bauta,watau duk da yawaituwar ayyukan su na bauta da kuma kyutatawa a cikinsu watau wajen ruhinsu.Suna ganin sun ta}aita kuma basu kyautata ba a ciki,shi yasa  wasu daga cikin malaman irfan suka  tafi akan cewa kalmomi na tuba,gafara, neman afuwa da suka zo daga Addu,oin  ma’asumai [AS]  wannan  nau’in  tuba na ukku ne.Domin su Ma’asumai basa aikata zunubi,haka nan basu kasancewa cikin gafala.saboda haka neman tubar su,a wajen Allah[T] na yadda suke shu’urin ta}aitawar su ga bautar AllahT]. kamar yadda yazo a hadisi,akwai mala’ikan da tun da aka halicce shi yake sujuda,wani yana ruku’u,wani yana tsaye da dai sauransu,amma ranar gobe }iyama zasu ce, ya Allah ba mu bauta maka ba ha}i}anin bauta”.Bayan haka ana son mutum ya samu isti}ama da sabati ga wa]annan ayyuka na ibadodi dai dai gwargwadon iyawar  sa, ya tsayu akai har ya zuwa wani watan Ramadan  insha Allah.Daga  }arshe babu abin cewa face mu na godiya ga Allah [T] daya nuna mana farkon wannan wata,kuma ya nuna mana }arshen sa.Ayyuka na ibadodi da Allah [T] ya bamu ikon aikatawa,Allah[T]ya kar~a mana,Addu’oin da muka ro}a,Allah[T] ya bamu  fiye da abinda muka ro}a.Abubuwan da muka nemi tsari na sharrori,Allah ya tsare mu fiye da abinda muka nemi tsari a kai,Amin.

No comments:

Post a Comment