Sunday 3 February 2013

Bayani kan tazkiyatu-Nafs.


A darasin da ya gabata, an tsaya ne a bayani dangane da muhimmancin Tazkiyatu Nafs (tsarkake rai). Amma gabanin nan an yi bayanai a kan ma’anar Akhla}, cewa shi ne, “sura ba ]iniyya ta mutum”. Wato siffa ta ba]ini (~oye) ta mutum. Domin shi mutum yana da ~angarorin guda biyu a halittarsa.
Akwai ~angaren zahirinsa wato jikinsa akwai kuma ~angaren ba]ininsa, wato ruhinsa. Kuma shi ruhin mutum yakan kasance ne a ]ayan siffofi guda biyu. Ko dai siffa kyakkyawa, ko kuma siffa mummuna.
To shi ilimin Akhla} yana bayani ne dangane da wa]annan siffofi na ruhi guda biyu. Amma a wajen bayani ko gabatarwa galibi Malaman Akhla}, sukan gabatar da bayani a kan munanan siffofi na ruhi da kuma yadda za a tsarkaka daga gare su. Sa’annan bayan haka bayani dangane da kyawawan siffofi na ruhi da kuma yadda za a ]abi’antu da su. A kan asasin haka ne, aka soma gabatar da ~angaren Tazkiyatu-Nafs, wato tsarkakuwa daga munanan siffofin ruhi, kafin siffatuwa da kyawawansa.
Saboda haka a nan bayani zai gudana ne a kan:
1- Bu}atuwa ga Tazkiyar Nafs.
2- Illolin rashin Tazkiyar Nafs.
3- Hanyoyin Tazkiyar Nafs.
4- Matakai na Tazkiyar Nafs.
5- Natija ko sakamakon na Tazkiyar Nafs.
6- Ha]afi ko manufa na Tazakiyar Nafs.
7- {issar wasu bayin Allah (T) da suka yi Tazkiyar Nafs ]in su. Insha Allah ga bayani a ta}aice dai dai gwargwado a kansu.
1- Bu}atuwa ga Tazkiyar Nafs:- Shi ]an’adam  mabu}aci ne ga Tazkiyar Nafs, wato tsarkake ransa. Saboda shi  asalin halittarsa tsarkakakke ne. Wato yakan zo wannan gida na duniya da ruhinsa a tsarkake ne. Daga baya ne sakamakon zunubi, ko munanan ayyuka da mutum yake aikatawa, sai ruhin ya munana kuma ya }azance. Wato sai ya fita daga siffarsa ta asali ta tsarkaka ya koma ga siffa ta rashin. Tsarkaka. Wanda kuma a cikin mutane wa]anda suke ruhinsu, a tsarkake yake tun daga farko har }arshe su ne Ma’asumai (AS). Wa]anda wannan ka]ai ya isa ya nuna bu}atuwa na Tazkiyyar Nafs. Tun da mutum ya san shi ba Ma’asumi ba ne, ashe ke nan ruhinsa zai iya kasancewa, wani lokaci daga cikin lokuta na rayuwarsa ta duniya, ya samu matsala ta tsarkaka, ko ma rashin tsarkakar baki ]aya. Saboda haka shi mutum mabu}aci ne ya dinga Tazkiyyar Nafs ]insa, har ya zuwa saukar ajalinsa. Domin ala}antuwa da Allah (T) ko ]amfaruwarsa. Haka nan kuma ala}antuwa da Manzon Allah (S) da kuma Ahlu Baiti (AS) a ba]inance.
Asasinsa shi ne tsarkakuwar ruhi. Domin su tsarkakakku  ne, saboda haka wanda zai ala}antu da su ya ]amfaru da su a ba]inance, dole shi ma ya zama mai tsarki. In ba haka ba, zai zamanto ala}antuwar da rauni, ko kuma ta dunga zuwa tana gushewa. Misali wani lokaci shu’urinsa ga Allah (T) ya zamanto yana da }arfi, wani lokaci kuma da rauni. Wani lokacin akwai shi, wani lokaci kuma babu shi. To duka abin da yake haifar da wa]annan yanayoyi, shi ne idan ruhi ya samu tsarkaka ko kuma rashin tsarkaka. Ko kuma wani lokaci mutum zai kasance yana son ya yi mafarkin Manzon Allah (S), ko kuma wani Imam daga cikin A’imma na Ahlul Baiti (AS), amma haka bai samu ba, }ila ma har ya biya wasu addu’o’i ko azkar da suka zo a ruwayoyi cewa, in mutum ya biya su, zai yi mafarki da Manzon Allah (S), ko kuma Ahlul Baiti (AS), ya karanta ]in, amma kuma bai ga haka ]in ba.
To duka ire-iren wa]annan abubuwa, natijarsu tana da ala}a ne da tsarkin ruhin mutum. Haka nan kuma samun zau}i da asrar na ibadodi, misali Salla, karatun Al}ur’ani, Azkar, Addu’o’in Ma’asumin (AS), duka yana da ala}a ne da Tazkiyyar Nafs ]in mutum. Ashe ke nan idan mutum yana son ya samu wa]annan zau}iyyat ]in da kuma asrar na ibadodi. To dole ne Asasul-Asas ya tsarkake Nafs ]insa. Wanda wannan shi ma yana nuna bu}atuwa ga Tazkiyyar Nafs. Domin inda za a yi tambaya a ce, a duniyar mene ne ya fi komai da]i? Amsa in aka ce Salla. Wani zai ce Salla! Alhali ko a wajen bayin Allah (T) wa]anda suka ]an]ani da]i da kuma za}in Salla, sun tabbatar da cewa, a duniyar nan ita tafi komi da]i, shi ya sa irin wa]annan bayin Allah (T) da suka ]an]ani za}i da halawa na Salla suka yi rubuce-rubuce khususan kan asrar na Salla. Alal misali littafin Asraru-ssalat na Imam Khumain ({S). Littafin Asraru-ssalat na Ayatullah Jawad Amuliy, wanda shi yana Raye, yana zaune a birnin {um ne, babban Malamin Fal-safa ne da kuma Irfan. Da dai sauran littattafai na Asraru-ssalat da Malamai na madrasah ]in Imamiyya suka rubuta. Saboda haka mabu]i na asrar ]in Salla, shi ne Tazkiyyatu Nafs.
Haka nan kuma Taziyyar Nafs, yakan sa mutum ya samu ilmummuka na ba]ini na Al}ur’ani mai girma, wanda irin wannan ilimi, shi ake ce wa ilimin LADUNNI, wato ilimi ne wanda Allah (T) kan ilhamantar da shi ga bayinsa, kuma  mabu]in samun wannan ilimi shi ne ta}awa, wanda kuma ]aya daga cikin ~angarorin ta}awa, shi ne  Tazkiyyatu Nafs. Wato dai fa]in Allah (T) ku yi ta}awa, Allah (T) ya sanar da ku. A ta}aice dai akwai ababe da dama  wa]anda suke nuna bu}atuwa ga ]an’adam na ya tsarkake Nafs ]insa.
2- Illolin rashin Tazkiyyar Nafs. Akwai illoli masu yawan gaske da mutum yakan kasance ciki, saboda rashin Tazkiyyar nafs ]in, ga wasu daga ciki:-
i- Yakan sa ala}ar mutum da Allah (T) ko kuma ala}arsa da Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) ta zamanto mai Rauni.
ii- Yakan hana mutum samun abubuwa na ba]ini  na ibadodi, kamar asrar ]insu, ko kuma samun zau}insu da kuma halawa ]in su lokacin aikata su.
iii- Yakan hana wa mutum samun ilmummuka na ba]ini daga wajen Allah (T), musamman ma ilmummuka da asarar da ke cikin bu]un na ayoyin Al}ur’ani mai girma, wanda in akwai Tazkiyyar Nafs, to ko da Allah (T) zai raya mutum shekara 100, a duniya. Kuma a ce kullum yake saukewa. To duk lokacin da ya sauke ya dawo, sai ya samu ilhama na ilimi da asrar na wasu ayoyi. Amma fa da shara]in in akwai Tazkiyyar Nafs.
iv- Daga cikin illolin rashin Takiyyar Nafs yakan dabaibaye mutum daga ayyukan ]a’a da ya saba aikatawa. Kamar }issar wani cikin magabata da aka ta~a kawowa. Cewa ya saba yana tashi Sallar Tahajjud. Amma sakamakon ya munana wa wani zato. Sai da ya ]auki lokaci mai tsawo bai tashi. Kuma kullum yakan kwanta da nufin tashi. Saboda haka duk lokacin da mutum ya saba aikata wasu ayyuka na ibadodi daga baya ya samu kansa bai aikatasu, ko kuma ya yi rauni wajen aikata su, to ya binciki kansa. Tabbas wani abu ya faru a ba]ininsa wato a ruhinsa. Domin shi ]abi’ar ruhi matu}ar ana tsarkake shi to zai dinga ci gaba ne wajen haskaka da kuma tsarkakuwa.
v- Daga cikin illoli na rashin Tazkiyyar Nafs, shi ne yakan sa ayyukan mutum na ]a’a da kuma addu’o’insa, su sami shamaki daga kar~uwa. Wato ya zamanto ba su sami kar~uwa ba daga wajen Allah (T).
vi- Daga cikin illoli na rashin Tazkiyyar Nafs, yakan iya janyo wa mutum ayyukan da ya aikata ko yake aikatawa na ]a’a da kuma ibadodi su lalace. Misali aikin da mutum ya aikata amma gabanin aikin ko lokacin aikin ko bayan aikin riya ta shiga ciki ko ujub da dai makamantansu na cututtukan zuciya, kamar hassada wadda take cin kyawawan ayyukan mutum.
vii- Daga cikin illolin rashin Tazkiyyar Nafs, yakan kasantar da mutum, MUFLIS gobe }iyama, wato shi ne wanda zai zo gobe }iyama da ayyuka na }warai masu yawa. Amma a gidan duniya, ya yi giba da wannan ya zalunci wannan ya munana wa wannan zato, ya zagi wannan da dai sauransu. To haka za a dinga ]aukar ladarsa, ana bai wa wa]anda ya yi wa wa]annan munanan abubuwa.
Daga }arshe sai ya tashi a tutar babu. Amma da a ce mutum ya samu wannan Tazkiyyar Nafs. To ba zai aikata wa]annan abubuwa ba. Ballantana, su kai shi ga wannan mummunan hali gobe }iyama. Wannan ke nan a ta}aice dangane da illolin rashin Tazkiyyar Nafs.
3- Hanyoyin Tazkiyyar Nafs:- Malaman Akhla}, sun yi bayanin hanyoyi daban-daban da mutum zai bi domin Tazkiyar Nafs ]insa, amma a nan ga wasu daga ciki:
i- Mutum shi }ashin kansa ya zauna ya yi tunani, ya binciki kansa, wato ya yi wa kansa muhasaba ya ga wane mummunan Akhla} yake da shi ko wane aibi na Nafs yake da shi. Misali ya soma da zuciyarsa, shin yana da cuttuttuka na zuciya, kamar hassada, riya, ujub ko ananiyya da dai sauran cuttuttuka na zuciya. Bayan haka kuma sai ya dawo ga ga~o~insa na zahiri, kamar harshensa ya binciki kansa yana giba fa]in }arya ko annamimanci ko kuma suka da aibanta juna da shi. Haka nan kunnensa yana jin wani abu, wanda a shari’a haramun ko makruhi ne jin sa.
Haka nan idanuwansa yana ganin abubuwan da suke haramun ko makruhi ne ya gani. Haka zai bi ga~u~~ansa na zahiri guda bakwai ]aya bayan ]aya yana bincikawa. To idan ta bayyana masa cewa yana da wasu ko ]aya daga cikin wa]annan aibobi da aka ambata, to abin da ya hau kansa shi ne sai ya yi mujahada, wajen tsarkaka daga mummunar siffar ko munanan siffofi.
ii- Hanya ta biyu wajen samun Tazkiyya Nafs. Ita ce ta hanyar mutane. Wato duk mummunar Akhla} da ka gani ga wani ko wasu ko ka ji ga wani ko wasu sai ka tambayi kanka  kana da wannan munanan ]abi’un ko ba ka da shi? In ya kasance mutum na da su. To sai ya yi mujahada wajen ganin cewa ya tsarkaka daga wa]annan munanan Akhla}.
iii- Daga cikin hanyoyin samun Tazkiyyar Nafs shi ne ta hanyar masoyi ko ma}iyi, domin shi ]abi’ar ma}iyi shi ne kullum yana neman aibin mutum domin ya aibanta shi da shi, wato ya soke shi da shi. To mutum sai ya yi amfani da wannan damar ya ga cewa yana da aibin ko bai da shi, in yana da shi, sai ya yi }o}ari domin ya tsarkaka daga aibin. ko kuma sanin aibin ta hanyar masoyinsa, kamar mutum ya ke~ance ka ya fa]a maka wani abin da kake yi wanda bai dace ba, ko dai wani aibi naka. Wato dai da nufin nasiha. To a nan sai mutum ya amshi irin wannan nasiha da farin ciki da ma godiya ga wanda ya yi masa. Domin ya taimake ka ne. Misali kamar kana tafiya ne ba ka kula ba, akwai rami gabanka, sai wani ya ce maka, ga rami nan gabanka. Ai ka ga za ka yi farin ciki har ma da gode masa. Wani tambihi a nan shi ne, sau da yawa, haka zai iya samun mutum, misali yana da wani aibi da yake aikatawa ko wata mummunar ]abi’a ai masa nasiha a kai, maimakon ya ji da]in haka a zuciyarsa sai akasin haka ta kasance, sai ya zamo bai ji da]i ba, ko kuma ya dage a kan abin da bai dace ]in ba. Wato ya}i gyarawa. Alhali }in gyara aibin nafs, ya fi muni kan wancan misali da aka bayar na fa]awa rami. {ila shi in ka fa]a ya tsaya ga jin raunuka ko mutuwa. Sa~anin aibin nafs ko mummunan Akhla} in mutum ya mutu bai gyara ba, to illar haka za ta bi shi har lahira, ba wai za ta tsaya a gidan duniya ba. Saboda haka yana da gayar muhimmanci duk lokacin da aka yi wa mutum nasiha kan wani abu da yake aikatawa wanda bai dace ba, to sai ya yi }o}ari ya ga cewa ya tsarkaka daga wannan abin. Wannan ke nan a ta}aice kan hanyoyin samun Tazkiyyar Nafs.
4- Matakai na Tazkiyyar Nafs:- Tazkiyyar Nafs yana da matakai kamar yadda Malaman Akhla} suka yi bayani, mataki na farko shi ne, tsarkake ga~u~~a guda bakwai na zahiri su ne:- i- Harshe, ii- Ido, iii- Kunne, iv- Hannu, v- {afa, vi- Ciki, vii- Gabansa (al-aurarsa). Wa]annan ga~o~i guda bakwai mutum ya tsarkake su, ta yadda cewa duk wani abin da Allah (T) ya haramta ko ya karhanta, bai aikatawa da su, face abin da Allah (T) ya halatta masa.
Mataki na biyu, shi ne Tazkiyyar zuciya, wato mutum ya tsarkake zuciyarsa daga dukkan cuttuttuka na zuciya kamar Hassada, Riya, Rowa, Fushi, Girman kai, Munana zato, Son duniya Son kai dadai sauransu na cuttuttukan zuciya.
Mataki na uku wanda wannan ya ke~anta ne ga Ma’asumai (AS) da kuma ]ai]aiku na wasu bayin Allah (T) wa]anda suka kai mustawa-aliya wajen ala}antuwa da Allah (T). Misali a nan kamar bautar Allah (T) ba domin wuta ba ko aljanna ba, kamar yadda aka ruwaito haka daga Imam Ali (AS) domin hujub, wato hijabai da ke shamakance mutum daga Allah (T), wa]anda Malaman Irfan ke bayani. Ya kasu kashi biyu: Akwai hijabai na duhu, akwai kuma hijabai na haske. Hijabai na duhu, misalinsa shi ne kamar ta’alla}uwa da duniya da kuma tarkacenta, wanda a wannan ta’alla}uwa ]in ya kai ga ya shamakance mutum daga tunanin Allah (T).
Hijabai na haske kuwa, misalinsa shi ne kamar tunanin mutuwa, wuta,  Aljanna da dai makamantansu. Wa]annan ababe da aka ambata, in muka duba, za mu ga tunaninsu, abu ne mai kyau kuma addini ya kwa]aitar da kuma }arfafawa wajen yin tunaninsu. Amma ga wasu bayin  Allah (T) kamar Ma’asumai (AS) tunanin wa]annan hijabi ne gare su, daga tunanin Allah  (T). Shi ya sa abin da ake so ga Tazkiyyar Nafs, mutum ya keta wa]annan hijabai guda biyu, wato hijabai na duhu da kuma hijabai na haske ya kai inda ake ce wa MA’ADINIL-AZMA. Kamar yadda ya zo a Du’a’us Sha’abaniyya. Wato ya kai ga tunanin Allah (T) kawai. Bai tunanin komai, bai ganin komai in ba Allah (T) ba. Kamar yadda aka tambayi Imam Sadi} (AS) dangane da wannan Ayar; “Ranar da dukiya da ’ya’ya ba su amfani, face wanda ya je wa Allah da zuciya salima.” Aka ce masa, mece ce wannan }albu-salim? Ya ce ita ce zuciyar da za ta je gobe }iyama, babu komi a cikinta face Allah (T). Saboda haka wannan mataki na uku na Tazkiyyatu Nafs, shi ne mutum ya tsarkake ba]inin zuciyarsa.
A lura a mataki na biyu tsarkake zuciya. Amma a mataki na uku tsarkake ba]inin zuciya. Wato ta tsarkaku daga tunanin komai in ba Allah (T) ba. Wannan mataki yana bu}atar mujahada mai tsawo kuma mai yawa fiye da mataki na ]aya da na biyu.
5-Natija ko sakamakon Tazkiyyatu Nafs. Akwai natijoji masu yawa da mutum zai samu, a addininsa, a duniyarsa da kuma lahirarsa. Sakamakon yin Tazkiyyar Naf’s. Misali a duniyarsa, zai yi rayuwa ]ayyiba. A addininsa zai dunga samun TARA{{IY, wato ci gaba a ba]inance wajen salukinsa zuwa ga Allah (T) a lahirance kuma ayyukansa za su samu kar~uwa da kuma samun darajoji, wato ba zai zama MUFLIS ba. Kamar yadda aka yi bayani a baya.
6- Hadafi ko manufa na Tazkiyatu Nafs: Manufar ita ce yadda mutum ya zo wannan gida na duniya a tsarkake, to ya bar ta yana tsarkake. Saboda haka yana da gayar muhimanci ga mutum kafin mutuwarsa ta zo, ya yi iyakar iyawarsa ya ga cewa ya tsarkake kansa. Musamman ma a matakai guda biyu, wato na farko da na biyu da aka ambata a baya. Wato ga~o~insa da kuma zuciyarsa. Domin su wa]annan ga~o~i amana ce ilahiyya wadda za a tambayi mutum a kai gobe }iyama, kamar dai yadda Imam Khumain ({S) ya yi bayani a littafin jihadul-Akbar.
7- {issar wasu bayin Allah (T) da suka yi Tazkiyyar-Nafs. In mutum ya bibiyi tarihi da kuma rayuwar wasu bayin Allah (T), zai ci karo da irin wa]annan. Amma saboda gudun tsawaitawa ga ]aya daga ciki. Akwai wani Malami da bai ga abin rubutunsa ba, wato al}alaminsa. Ya ]auka ya aje shi a wani waje ne. Sai ya tambayi iyalinsa ga shi ya aje al}alaminsa amma bai gani ba, ko sun canza masa waje ne? Suka ce a’a, su ba su ma gani ba. Aka ]auki kwanaki a haka, har ma yake ce wa almajiransa, ya a je abin rubutunsa iyalinsa sun canza masa inda ya aje kuma sun ce a’a ba su yi ba. To bayan da aka tashi karatu, sai ]aya daga cikin almajiransa ya tsaya bai tafi ba, sai da kowa ya wuce sai ya samu Malamin nasa ya ce, Malam ai abin rubutunka yana cikin aljihun rigarka ce daka aje, jin haka Malamin ya je ya duba aiko sai ya gani. Ganin haka sai Malamin tunani ya zo masa cewa, lalle wannan ]alibi nasa yana da ala}a da bayin Allah (T) }ila ma yana da ala}a da Imam Mahdi (AF). Saboda  haka wani lokaci ya ke~ance da ]alibin yana tambayarsa. Ko yana da ala}a da Imam Mahdi (A.F)? Sai ]alibin ya yi shiru bai ba shi amsa ba. Amma da ya matsa, sai ya ce masa na’am yana da ala}a da shi. To jin haka sai Malamin ya ce yana son ya ba shi sa}o zuwa gare shi, sa}on shi ne ya yi shekara da shekaru yana son ya gan shi, amma har yanzu. Sai ]alibin ya ce insha Allah zai isar da sa}on gare shi. Bayan kwanaki Malamin ya ji shiru. Har ta kai ga ya sake ke~ancewa da ]alibin ya ce, batun sa}o ne na ji shiru.
Sai ]alibin ya yi shiru, amma da Malamin ya matsa masa yana son ya ji amsar sa}onsa, sai ]alibin ya ce masa abin da ya ce in gaya maka shi ne; “Ka tsarkake kanka, zai zo da kan shi.” Wannan shi ne mahalli shahid na }issar.
Saboda haka daga wannan }issa za mu fahimci cewa bayin Allah (T) da yawa da suka samu muwafa}ar ganin Imam Mahdi (AS) jasadiyyan ba wai ruhinyyan ba, mabu]in haka shi ne Tazkiyyatu-Nafs kuma har yanzu }ofa a bu]e take. Bacin gudun fita daga abin da ake bayani a kai na Tazkiyatu-Nafs, da an kawo sunayen wasu Malamai da kuma wasu bayin Allah (T) a wannan zamani namu. Na madrasah ]in Imamiyya wa]anda suka samu muwafa}ar ganin Imam Mahdi (AS), kuma waccan }issa da aka kawo ta wancan Malami da almajirinsa, littafai da yawa na Tarihin Malaman Imamiyya sun kawo ta. Wannan ke nan baki ]aya a ta}aice, dangane da Tazkiyyar Naf’s.


No comments:

Post a Comment