Saturday 9 February 2013

ALHAMDU LILLAH SHEKARU 60 MASU ALBARKA NA SAYYID ZAKZAKY [H].


Alhamdulillah,kamar yadda muka sani,wannan wata da muke ciki,wato na sha’aban 15 gare shi.Sayyid Ibrahim Zakzaky [H] ya cika shekaru 60 cur-cur a duniya.Saboda haka naga zai yi kyau da kuma muhimmanci,akawo wasu darussa na jarabawowi da nasarori dake cikin wa]annan shekaru masu albarka,da nufin su kasance DARASI a gare mu
.Akan asasin haka ne na bu}atu da sake jin wasu daga cikin jawaban malam daya gabatar shekarun baya da suka wuce,misali shekaru 20,25 da makamantansu,musamman ma kasantuwar yadda nake so a wannan rubutu ya kasance abubuwan da za’a kawo na sashen wa]annan jarabawowi da nasarori su kasance nassin [ainihin] maganar malam ]in. Da farko wasu daga cikin jarabawowin da Malam ya fuskanta.Idan mutum ya bibiyi tarihin Malam zai ga cewa tun lokacin daya soma wannan da’awa,kimanin  shekaru 35 zuwa yau zai ga cewa ya fuskanci jarabawowi daban-daban,ta kuma fuskoki iri-iri.Amma a dun}ule wa]annan jarabawowi za’a iya kasa su gida uku.                                                                                                                                                                                             1.Jarabawowin  daya fuskanta ta fuskacin Hukuma.                                                                                                      2.Jarabawowin  daya fuskanta ta fuskacin mutanen gari.                                                                                            3.Jarabawowin  daya fuskanta ta fuskacin yan’ uwa.                                                                                                    Akan wannan tar-tibi za’a bada misalai na kowanne daga cikin ukun,insha Allah.                                                                              JARABAWOWIN DA YA FUSKANTA TA FUSKACIN HUKUMA.
Malam ya fuskanci jarabawowi masu yawan gaske daga ~angaren hukuma,wanda  saboda  yawan su da kuma gudun tsawaitawa, ba za’a iya kawo su gaba ]aya ba,amma  ga  guda uku:                                                                   A-Kamu da kuma ]aurewa a kurkuku:Idan mutum ya dubi shekaru 60 na Malam zai ga cewa sama da shekaru 10 daga ciki, yayi sune a kurkuku daban daban na }asar nan.Domin tun da ya soma wannan da’awa yana  ]alibi a jami’ar Ahmadu Bello dake  zaria aka soma  kama shi.Hatta a shekarar sa ta }arshe a jami’ar,a jarabawa ta fita bai samu yin wasu ‘papers’ ]in ba,sai daga baya.Saboda a lokacin yana  tsare.Bayan haka,duk yaci wa]annan  jarabawowin daya rubuta,amma hukumar jami’ar  ta hana shi takardar shaidar kammalawa,wanda  shima wani nau’in  jarabawa ne.      Kuma wa]annan kame-kamen da ]aure-]auren da Malam ya fuskanta,ba wai kawai sun ta}aita a haka bane,a’a cike suke da matsaloli da wahal-halu daya fuskanta a ciki.                                                                            Ga misalai na irin wa]annan matsaloli da wahalhalu da mMalam ya  fuskanta a tsare-tsare dabam- dabam da aka yi masa.Akwai lokacin da aka kama shi aka kulle a police station na zariya,kwana ukku ba abashi abinci ba,sai aka fito dashi da nufin ya amsa wasu tambayoyi.A haka dai sai da Malam ya rubuta masu shafi tara na amsoshin abinda suka tambaye shi.Har su jami’an tsaron su kayi mamaki.suna cewa dubi rubutun shi da kyau,kamar wanda bai sha yunwa ba.sai suka mai da shi cikin sel.Haka nan a wata tsarewa da aka yi masa a sakkwato,an ha]a shi zama sel guda da mahaukaci.Da rashin samun yin wanka da wanki na makwanni,kamar yadda Malam ya fa]i a wani jawabi na }arshen ijtima a masallacin ABU zariya.guda da  mahaukaci,an bu}atar damu da rashin wanka na makwanni,wankanka  shine  ka  ]auko hannu ka mulmula dau]a ka fitar.kuma mu kayi makwanni a haka,ba wanka ballantana fa wanki.Riga bata sawuwa sai dai na dole.”                                                                                             A wani waje a jawabin yana cewa, “An ba}utar dani  tare da wasu yan’ uwa da muke tsare da }war-}wata a jiki tare da ku]in cizo,ko’ina ka shafa a jikin ka ku]in cizo ne da }war-}wata,hatta  ma lokacin da aka kai ni kurkukun Inugu  sai da aka yi min aski  }wal-kwabo,domin duk }war-}wata  ta  cinye  kan.”Haka nan an bu}atar da ni zama da ‘fa]e’ [takalmi irin na danko] ina ta yi masa faci har shekara uku.Kuma an bu}atar da ni a kurkukun inugu in yi wanka ba sabulu har na tsawon wata shida.Ba kuma man shafawa har jini na ketowa”.                                                                                                                                                               Mu duba irin wannan wahala, da Malam ya sha tun farkon soma wannan da’awa,domin wannan tsarewa  ta  sakkwato ta kasance a 1981 ne,kuma Malam ya zauna a kurkukun inugu har shekara uku.Bayan fitowarsa daga kurkukun inugu,aka sake kama shi aka kai shi kiri-kiri,in da ya kasance a kiri-kiri na watanni.                                                                                                                                                          Shi kiri-kiri kamar yadda Malam ya ta~a  bayyanawa, waje ne da ake kai mutanen da ake so a musguna masu,ko azabtar dasu.Domin akwai kari-kitai na azabtar wa, daban daban duk aciki.Malam yake cewa,ko sauro mutum ya kashe sai an masa bulala,za’a ce masa  wai ya damu yaran gwamnati.                       Kuma yake cewa hatta tufafi riga da wando, ba’a yarda mutum ya shiga dasu ba,sai dai a shigar da mutum daga shi sai ‘pant’.Lokacin da  aka  kai Malam suka ce ya tu~e tufafi yace ba zai yiwu ba,yace musu dole da tufafin shi zai shiga,shine har na ciki suna ta mamaki.Malam yake cewa yana ganin shine farkon wanda ya soma shiga da tufafi.Haka Malam ya zauna a kiri-kiri ]in na tsawon wata uku.                                        Bayan haka kuma akwai lokacin da aka kama Malam aka sake tsare shi a kirikiri ]in,amma wannan na tsawon mako ]aya ne.Wannan kamar yadda wa]anda suke da masaniya suka ce,ya kasance lokacin Malam zai tafi ingila ne,to a filin jirgin sama na Malam Aminu kano aka kama shi.Daga nan aka kai shi Legas,washegari aka wuce dashi kirikiri,wanda acikin kirikirin Malam yayi addu’a yana cewa, “Ya Allah kasan nayi kurkuku shekaru uku a inugu,kuma nayi zaman kirikiri,kasan cewa ko daida da rana ]aya,ban ta~a  bu]e baki nace ka fisshe ni ba,sai dai da kanka ka fitar dani.Kuma nayi zama a kurkukun fatakwal.Abinda na ro}a wajenka kawai yayin da abubuwa suka yimin tsanani,shine ka raba ni zama da kafirai,don zama da arne bai da da]i.To,wannan karon Ya Rabbi! Ina son in fita”.Ikon Allah! Lokacin da Malam yayi wannan addu’ar bai jima ba kuwa Allah Ta’ala ya fitar dashi.Shi yasa mako ]aya yayi a wajen,domin lokacin da suka tsare shi sun nuna mishi zai jima anan.Shi ne yake ce masu ni kuma ina ro}on  Allah ya fitar dani daga }umbabinku.Lokacin da Malam yayi addu’ar yake cewa yana da ya}inin cewa Allah Ta’ala zai fitar dashi bada jimawa ba.Shine bayan nan yake cewa,sai ya yawaita fa]in “Ya Allah ka gaskata zatona gare ka.”                                                                                                                                             Haka nan ya zauna a kurkukun portharcourt har sau biyu shima,banda wasu kurkuku daya zauna daban daban na }asar nan, kamar na kaduna da dai makamantansu.Wannan kenan a ta}aice.          Haka nan idan muka juya ta fuskacin cutarwa da musgunawa lokacin kamu,shima akwai misalai da yawa.Daga cikin ababe na cutarwa da musgunawa da akayi masa harma da iyalinsa,banda kuma sace-sace da ]auke-]auke da akeyi masa a wasu lokutan da akazo kama shi,da kuma kame-kame na bazata.Wanda sai da takai Malam a wani lokaci,ya aje wata jaka,a cikin ta yasa sabulun wanka dana wanki,man shafawa,turare da tufafi na canzawa da dai makamantansu,yake cewa jakar bai ta~a ta,tana aje ne,da anzo kama shi sai dai ya ]auke ta yace,muje zuwa!                                                                                                             Akwai kuma cutarwa ta aka mashi bada an shaida masa ina za’a kai shi ba.Sai dai a ]auke shi daga wannan waje zuwa wancan.misali,abinda  akayi masa a kamun da akayi masa a kano,wanda aka ambata a baya.A lokacin da suka ]auko shi daga filin jirgin sama basu shaida masa ina zasu da shi ba,sun dai zo da mota suka ce ya shiga,suka kaishi wani gida a cikin kano ]in,washegari da safe suka zo da mota cewa ya shiga zasu tafi.To,shine a lokacin Malam yake fa]a wa jami’an tsaron cewa, “ku me yasa ba zaku yi ]abi’a kamar ku mutane ba? Domin wannan ]abi’a taku, tama sa~a  da ]abi’a irin ta mutunci,domin ni mutum ne kuka ]auko ni,ba akuya ba.Kaga idan zaka saka akuya a cikin mota ka kai ta legas,baka bu}atar kayi mata bayani,kace ke akuya zan kai ki legas.Haka nan kuma idan zaka ]auki buhun shinkafa,baka bu}atar  kace masa zan kai ka wuri kaza,sai dai ka kai shi.Amma ni mutum ne,me nene ya hanaku kuce min a jiya, cewa an umurce ku,ku hana ni tafiya,kuma yau da safe kuce an umurce mu da mukaika legas,shi kenan.”                                                                                                                                                  Bayan kamu kuma akwai lokacin tsarewa,wanda a tsarewar zaka ga an kai Malam kotu kusan sau goma ko sama da haka,wato ana ]aga shari’ar.Wanda shima wani nau’i ne na cutarwa.A nan babban darasin da za’a fitar,shine duk da irin wannan kame-kame da cutarwa da akayi ma Malam,to Malam bai ta~a nuna damuwa ko ba}in ciki akan haka ba.A kasin haka ma yayi,wato nuna farin cikinsa da kuma jin da]in sa.Ga misalai daga haka,lokacin da aka kai shi kirikiri zuwa na farko ya rubuto ma yan uwa,a ciki yake cewa, “lokacin da ake tu}a ni zuwa kirikiri,naji wani da]i da farin ciki wanda ban ta~a jin irinsa ba.” Haka nan lokacin da ya fito daga kurkukun inugu,cikin abinda yake cema yan uwa shine, “wani abune wanda yake shu’uri,wato ji a jika,wanda sai kaima kaji[wato zaka iya fahimta].Abinda na gani a zamana na a kurkukun inugu tunda ba’a yarda ,da mutum yaje ya }wan}wasa  kurkuku,yace abu]e masa ya shiga.Duk randa akazo aka kamani zuwa can zan yi farin ciki.”Haka nan mu duba abinda Malam ya fa]a ma al}alin da ya yanke masa hukunci na zuwa kurkukun porthacourt na ]aya.Lokacin da za a yanke hukuncin,sai shi Al}alin mai suna karibi-white yace,ko yana da magana,Abinda Malam yace shine,ka yi wanda yafi muni.Idan kana da za~i tsakanin harbi ,a firing-squard da ]aurin rai da rai, bani harbi da firin-squard,’’Shine al}alin ya tsaya yana mamaki.Wannan kenan baki ]aya ta ~angaren kame-kame da kuma tsare-tsare.                                                                                                                                                                                    
Sai kuma na biyu yun}uri da kuma niyyar kashe shi.Shima wannan idan mutum ya duba,tun ]agowar wannan kira na Malam,zai ga cewa hukuma ta hanyoyi dabam-dabam da kuma uslubi dabam-dabam sun bi,domin suga sun kashe Malam.Ga misalai daga ciki,Malam tun yana ]alibi a jami’ar A.B.U Zariya aka so a kashe shi,kamar yadda yake cewa a wani jawabi da yayi na yun}urin kashe shi da akayi shekaru biyu da suka wuce a watan Ramadan.yana cewa, “shekaru kamar talatin da suka wuce an nemi a kashe ni,lokacin muna ]alibta.”                                                                                                                                                  Haka nan lokacin yana kurkukun kaduna a 1996,shima anyi wannan niyyar daga wajen hukuma ta hanyar yi masa allurar mutuwa.Kamar yadda ya fa]i haka a jawabi na yaumus Shuhada’u 2000 miladiyya.A lokacin wani ne ya shaida wa Malam cewa ga abinda aka shirya,saboda haka ko da yayi ciwo, kuma akwai bu}atuwar a yi masa allura,kada ya yarda.Ikon Allah Malam bai samu wata rashin lafiya ba,tsawon zamansu a kurkukun,sai wani lokaci da yayi ]an fama da ciwon ha}ori,aka turo a duba shi,shine aka ce akwai bu}atar ayi masa allura saboda ciwon ha}orin.Shine Malam yake cewa ai shi ba’a yi masa allura tun yana }arami,saboda wata matsala.Wannan shiri ya rushe.                                                                                Ga abinda ya auku a kano lokacin tawayiyya.Sau biyu ana yin wannan yun}urin.Da dai misalai da yawa na irin wannan yun}urin da niyyar kisa.Na baya bayan nan shine wanda akayi niyyar yi a shekaru biyu da suka wuce ta hanyar Bom.Ayi ‘Bombing’ ]in gidansa,wanda a wani jawabi da Malam yayi inda yake cewa, “Ni dai kam alhamdulillah,gaskiyar magana itace ni abin alfahari ne,ya zamo an kashe ni akan abinda nake yi;abin alfaharina ne.Yau shekara talatin kana ta da’awar abu ]aya,kuma a nata yun}urin a kashe ka,amma baka kasu ba har da’awa ta kafu daram,kuma ba yadda za’a iya da’ita.”A wani waje a jawabin yana cewa, “Ni in kuka kashe ni,ba wani abu bane,kuna iya kashewa.An kashe wa]anda  suka fini a wannan zamanin da na da.Saboda haka in ma an kashe ni sunna ce.”                                                                                          
Na uku wato jarrabawar daya samu ta fuskacin hukuma shine cutar da mabiyansa,ta fuska daban-daban shima.Domin idan mutum ya duba zai ga tun lokacin da wannan kira da Malam yake yi yayi }arfi,to ba’a samu lokaci cikin lokuta ba, da wani ko wasu daga cikin mabiyansa wanda bai hannun hukuma a tsare ko dai wata cutarwa.Kyakkyawan misali,yan’ uwa na sakkwato da aka karkashe a lokuta daban daban da wa]anda aka jima ciwo a wa}i’oi daban daban,da kuma ~arnatar da dukiyoyin yan uwa a lokuta daban daban.Misali anan abinda akayi a 1430 na }ona gidan Alhaji [anlami da abubuwan da akayi ma yan uwa na sakkwato na rushe gidajensu da kuma cibiyoyin kasuwancinsu dadai makamantansu na ire-iren wa]annan abubuwa da suka faru kuma suke faruwa,tsawon zamani a cikin harkar kamar na rushe zawiyya.Wa]annan abu da suka faru kuma suke faruwa ga yan uwa shima wata jarabawa ce da Malam ya fuskanta kuma yake ciga ba da fuskanta daga bangaren hukuma.Wannan kenan a takaice dangane da jarabawowin da malam ya fuskanta a wadannan }angarori guda uku daga hukumar }asa.Sai kuma sashe na biyu;jarabawowin da Malam ya fuskanta ta fuskacin mutanen gari.                                        JARABAWOWIN DAYA FUSKANTA TA FUSKACIN MUTANEN GARI.
Shima wannan za’a iya dubansa ta fuskoki guda ukku,Fuska ta farko cutarwa ta zuciya misali }iyayya, hassada,munana zato da makamantansu,fuska ta biyu shine cutarwa da harshe,wanda ya ha]a da soke-soke,zage-zage,aibantawa,sa sunaye iri-iri gare shi da kuma yan uwa da dai makamantansu.Fuska ta uku cutarwa ta hannaye,wanda ya ha]a  da kafa }ungiyoyi domin fa]a da harka,wanda duk yawancinsu sun zama tarihi.Misali,kamar }ungiyar Sahihul jihad,wadda Malam yake cema Safihul jihad,da kuma }ungiyoyi irinsu yan banga,yan tauri,guguwar bala’i dadai sauransu wa]anda sun zama tarihi a yanzu.                                                                                                                                                              A ta}aice dai jarabawowin da Malam ya samu ta fuskacin mutanen gari,to mafi yawa ta kasance daga fuskacin malamai ne.Duk wanda ya kasance cikin harka ko ya bibiyi tarihinta zai tabbatar da haka.Sai kuma sashe na uku,wato jarabawowin da Malam ya fuskanta ta fuskacin yan uwa.                                                     JARABAWOWIN DAYA FUSKANTA TA FUSKACIN ‘YAN UWA.
Duk wanda ya kasance cikin wannan harka,musamman shekaru 20 zuwa sama yasan cewa an wuce marhaloli da kuma matsaloli daban daban na cikin gida.Domin wa]ancan  jarabawowin da aka ambace su a sama ta fuskacin hukuma da kuma mutanen gari,matsaloli ne da za’a iya siffata su,na waje .kuma ]acinsu da gubar su bata kai ]aci da gubar cikin gida ba.matsalolin suna da yawa,amma a tawa yar fahimta ]in za’a iya dun}ule su a kasa su gida uku,sune:1-Matsalar isti}ama. 2-Matsalar kamala. 3-Matsalar ikhtilafi.                                                                                                                                                                                           1.Matsalar isti}ama:Abinda nake nufi anan shine,idan mutum ya dubi tun lokacin da Malam ya soma wannan da’awa kimanin shekaru 35 zuwa yau,zai ga an yi yan’uwa maza da kuma mata da yawa,a lokuta daban daban a cikin wa]annan  shekarun,wa]ansu  da yawansu yau babu su,sakamakon wa]ansu  fitinoni da suka auku ko kuma sakamakon shi mutum karan kansa yabar harkar.Wanda in mutum ya bibiyi jawaban Malam na da,da kuma na yanzu,za iga yana yawan magana  dangane da abinda ya shafi isti}ama  da kuma tabbata a ita tafiya ]in.Yana yawan fa]in cewa “babban nasararmu itace dakewa a tafarkin har mutuwa ta riske mu,ko a kashe mu akai.” Zan iya tunawa a wata ijtima da akayi a kano,kimanin shekara 26 da suka wuce a watan shawwal na 1406.Malam ya ]auki lokaci mai tsawo yana magana akan ita wannan isti}ama,shine lokacin yake cewa a matsayin misali, “da ace idan mutum ya shigo wannan harkar zai yi al}awari na cewa zai dake a harkar har mutuwarsa,in ko ya barta Allah Ta’ala yayi masa kaza da kaza kuma yasa hannu,sa hannun nan ma mutum yasa da jininsa,”da dai misalai ire-iren wa]annan da Malam ya bayar a lokacin.                                                                                                                                2.Matsalar kamala:Abinda nake nufi anan shine za kaga ]an, uwa ko yar’ uwa,an jima ana tafiya dashi cikin harka,amma ala}antuwarsa  da addini a aikace tana da rauni.Wato wajen siffantuwarsa da addini a zantukansa da ayyukansa da ]abiunsa,haka nan da ]amfaruwarsa da Allah.Malam yana yawan cewa kada mutum ya zamo ]an cika wuri ko ]an rakiya,yace ]an cika wuri ko ]an rakiya shine,wanda duk programs da shi akeyi,amma ala}ar shi da Allah da kuma Addini tana da rauni.Saboda haka yana da gayar muhimmanci,kowannen mu yayi sa’ayi da mujahada wajen samun kamala.Dama ita kamala kamar yadda aka sani,mutum bai kaiwa ga iyakarta,sai dai mutum zai ta yi har saukar ajalinsa.Wanda shima wannan idan mutum ya bibiyi jawaban Malam,musamman na mu’utamarori zai ga yana yawan magana akan haka.Wani lokacin ma yakan nuna cewa, “Abinda yake bani takaici shine naga wasu ‘yan uwa suna ]abi’oi irin na ‘yan Najeriya”.                                                 3.Matsalar ikhtilafi:Wato sa~ani, wa]anda  sukan auku jefi-jefi tsakanin ‘yan uwa isu-isu,wanda Malam ya sha fuskanta da warware ire-iren wa]annan  matsaloli,wanda wani lokacin sukan kai ga yawo da tsegunguma ko munana ma mutum zato,sukar juna dadai makamantansu.                                                                                Wanda in muka dubi wadannan ababe da aka kawo guda uku a ta}aice, zamu ga jarabawowi ne wa]anda Malam ya fuskanta ta ~angaren ‘yan uwa.Da fatan ‘yan uwa zasu tausaya wa Malam,musamman wa]annan  shekaru da Allah Ta’ala ya kawo shi, ta hanyar sa’ayi wajen da]a samun kamala,da kuma da]a  son juna da }aunar juna da kuma samun isti}ama,da sabati a harka ]in.                    Sai kuma ~angare na biyu na wannan rubutun,wato nasarori cikin wa]annan  shekaru masu albarka.wa]annan  nasarori za’a iya siffanta su a matsayin “La tu’addu wala tuhsa.”wato saboda yawansu.Amma ga 12 daga ciki:
 1.Tsayawa da ita da’awar tsawon wa]annan  shekarun,duk da matsaloli daban-daban da aka fuskanta na cikin gida da waje.
2.Tasirin ita da’awar ga sauran musulmi dama tasirinta ga wa]anda  basu ta~a  zama cikinta ba.
3.Assasa cibiyoyi daban daban a cikin harkar,kamar Mu’assatus Shuhada’u,medical team,Mu’assasa ta buge buge na rubuce rubuce,misali,Almizan da pointer express,Mu’assasa ta  fodiyya,Hurras da dai makamantan wa]annan,suna da yawa wa]anda har takai sauran al’umma suna cin gajiyar irin wa]annan  cibiyoyi.misali,irin nasu medical team dadai sauransu.
 4.fito da matsayin mata,musamman a fagen addini,wa]anda in mutum ya duba shekarun baya zai ga ba}on abune ganin mata a fagen addini.Amma yanzu abun ba haka yake ba,zaka ga mata a harkoki na addini,dama isilamiyoyin su na karatu,wanda wannan albarkacin wannan da’awa ta Malam ne,ta yiyu wani yaji mamakin haka,amma ga wanda yake da masaniya yasan asasin su daga wajen Malam ne.
 5.sa’ayi wajen ha]a kan al’ummar musulmi da kuma ganinsu a matsayin musulmi.misali gudanar da makon ha]in kai,ziyarar malamai a lokutan jauloli da dai suransu na ababe da ke kawo ha]in kai da kuma kusantar juna.  
6.Raya masallatai ta hanyar yin wa’azozi a ciki,karantarwa a ciki,I’itikafi a ciki dadai makamantansu,wanda a shekarun baya galibi masallaci sai dai a shiga lokacin salla, ayi a watse.Amma kasantuwar yadda wa]annan  ababe suka zama jiki a yanzu, ana yin su a masallatai,mutum zai ]auka haka abin yake a shekarun baya.wanda Allah[T] yasa ya da]e a wannan harka zai tabbatar da haka,na  cewa wa]annan ababen da aka ambata,da yawansu Malam ne ya assasu,a masallacin ABU, lokacin yana ]alibi a jami’a,misali ]aya anan shine,wa’azin da akeyi ranar jumma’a a masallatai kafin liman ya shigo.
 7.Raya al’amarin Ahlulbayt [AS].wato abinda ya shafi wilaya da kuma ulum na Ahlulbayt [AS].gina cibiyoyi na Husainiyya.misali,Husainiyya ta Bakiyyatullah.wanda mutum yanzu zai iya dukan }irji yace,babu wata }asa daga cikin }as ashen Ahlus-sunna,wadda take da mabiya Ahlul-bait kamar wannan }asa.mutum yayi tunani ko ya bincika ya gani,zai ga haka.
 8.Fito da matsayi na sharifai [sadat] wato jikokin Annabi.Shima wannan ga wanda yake da masaniya akai zai tabbatar da haka,misali yadda almajiran Malam suke girmama su,da ziyartar su musammam a watan maulidi,dama yi masu hidimomi ta fuskoki dabam-dabam.
 9.Kai ‘yan uwa karatu zuwa waje,musamman Iran,wanda yanzu akwai ‘yan uwa maza da mata da yawa da suke karatu a sassa daban daban a cikin Iran,kamar Qum,Mashhad,Isfahan da kuma makamantansu,a kuma ~angarori daban daban na fannin ilimi.Wanda wannan yana nuna yadda Malam ke }arfafa al’amarin ilimi da kuma nemansa.
 10.Isar da wannan da’awa lungu-lungu,sa}o-sa}o,na }asar nan,musamman ma a  arewacin ta.Domin mutum zai iya cewa babu wata jiha a cikin arewacin }asar nan wadda Malam bai je ba,domin isar da wannan da’awa.Haka nan a jihohi na kudancin }asar nan da yawa yaje domin isar da wannan da’awa.
 11.Yin muzahara da ya shafi bayyanar da wani abu na addini ko kuma inkarin wani abu da akayi ma addinin musulunci da kuma musulmi,wanda a shekarun baya a wannan nahiyar ba’asan yin haka ba a fagen addini,sai dai a fagen neman wani abu na duniya.
 12.Gina jama’a kan fikira guda da kuma aikace aikace guda.Ta yadda sai kaga abu zai faru a cikin }asa,’yan uwa na birni da }auye,ba tare da an ce masu kuyi kaza ba,sai kaga an ]auki matsaya bai ]aya.Wanda ya bibiyi wannan harkar zai ga misalan haka da yawa.                                                                                 Wannan kenan baki ]aya a takaice,Da fatan Allah Ta’ala ya amfanar damu da abubuwan da aka rubuta.Daga }arshe babu abinda zamuce ma Malam face Allah [T] ya saka masa da alheri,ya da]a bashi lafiya,ya kuma da]a masa yawancin kwana.ya kuma da]a kare shi daga dukkan sharrori da makirce-makirce na ma}iya na cikin gida da waje.       

No comments:

Post a Comment