Saturday 9 February 2013

Darussa 12 daga rayuwar Sayyid Zakzaky (H)


Kasantuwar wannan wata da muke ciki, wato Sha’aban, a cikinsa ne aka haifi Malaminmu, kuma Jagoranmu a wannan gwagwarmaya ta tabbatar da addini, wato Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), a wannan munasabar ta cika shekaru 61 a duniya.

A shekarar da ta gabata, a munasabar cikar Sayyid shekaru 60, an gabatar da rubutu me maudu’in ALHAMDULLILLAH! SHEKARU 60 MASU AL-BARKA JARABAWOWI DA KUMA NASARORIN DAKE CIKI, wanda a cikin rubutun an ]an yi bayani daidai gwagwardon iko dangane da jarabawowin da Sayyid ya fuskanta, ta fuskoki guda uku. 1. Jarabawowin da ya fuskanta ta fuskacin Hukuma. 2. Jarabawowin da ya fuskanta ta fuskacin mutanen gari. 3. Jarabawowin da ya fuskanta ta fuskacin ’yan uwa. Aka kammala rubutun da kawo wasu daga cikin nasarorin da Sayyid ya samu a cikin wa]annan shekaru masu albarka.
To a wannan shekarar insha Allah daidai gwagwardon iko, za a kawo wasu daga cikin ~angarorin rayuwar Sayyid (H) da nufin su kasance darussa gare mu da za mu darastu da su. Shi ya sa maudu’in ya kasance DARUSSA 12 DAGA RAYUWAR SAYYID ZAKZAKY (H).
Wa]annan darussa kuwa sune. 1. Fikirarsa. 2. Ibadarsa. 3. Nizaminsa. 4. Iliminsa. 5. Shaja’arsa. 6. Akla} ]insa. 7. Zuhudunsa. 8. Gwagwarmayarsa. 9. Mujahadarsa. 10. Ala}arsa da Allah (T). 11. Ala}arsa da Manzon Allah (S) da kuma Ahlul-Baiti (AS). 12. Yun}urinsa wajen ha]a kan al’ummar Musulmi.
Amma kafin shiga cikin wa]annan bayanai danagane da wa]annan darussa aka shimfi]a ko gabatarwa a ta}aice. Da farko dai rubutu ko bayani dangane da Sayyid Zakzaky (H) wani fage ne mai fa]in gaske, wanda mutum ba zai iya kewayawa da shi ba. Domin Sayyid (H) wata baiwa ce da kuma kyauta ta musamman da Allah (T) ya bai wa wannan nahiya da muke ciki. Da a ce mutum zai yi tunani kuma ya duba da kyau, zai ga cewa a duka baiwowin da Allah (T) ya yi wa wannan nahiya da muke ciki, a wannan zamanin, to suna komawa bayan wannan baiwa ta Sayyid Zakzaky (H) ne. Ta yiyu wani ya ja da hakan, amma iyakar maganar ke nan.
Misali kamar a ce lokacin Shehu Usman [an Fodiyo ne, akwai baiwar da Allah (T) ya yi wa al’ummar lokacin, wadda ta kai kyauta da ya bayar ta Shehu Usman [an Fodiyo? Mutum ya tambayi tarihin wannan nahiya, ya ba shi amsa. Cewa tun bayan zuwan ’yan mulkin-mallaka a wannan nahiya tamu, da abubuwan da suka yi na na]e shimfi]ar da Shehu Usman ya shimfi]a, wato nizaminsu, an samu wani Malami da ya yi da’awa, kuma ya dake a kan da’awar tsawon  shekaru, a kan cewa a koma kan nizamin da Shehu Usman ya shimfi]a, a kan haka ya fuskanci jarabawowi daban-daban, shi da wa]anda suka amsa masa da’awar?
Kai ba ma wannan }asar da muke ciki ba, }asashen nan ma}wabta da suke }ar}ashin Daular Usmaniyya gabanin ’yan mulkin-mallaka su yayyanka }asashen. To mutum ya dubi da aka yayyanka ]in, akwai wani Malami a cikin wa]annan }asashen wanda yake da’awa ta gwagwarmayar tabbatar da addini shigen ta Shehu Usman [an Fodiyo, kamar yadda Sayyid Zakaky (H) yake yi a nan?
Haka nan mu ]auki fahimta ta Ahlul Bait (AS), wato tamassuki da wilayar Ahlul Bait (AS) wacce }asa ce daga cikin }asashen Ahlus Sunnah da mutum ya sani a yau, wadda a cikinta aka samu wani Malami, wanda albarkacinsa, kuma sakamakonsa aka samu fahimta, kuma cikin ’yan shekaru ka]an adadi mai yawan gaske na mutane na maza da mata, yara da manya suka yi istibsari (wato fahimtar Ahlul Bait (AS) da kuma ri}o da su) kamar wannan }asar da muke ciki. Lallai in akwai zan so in san }asar. To ire-iren wa]annan misalsalai suna da yawa, wa]anda ke nuna lallai Sayyid Zakzaky (H) baiwa ce ta musamman da Allah (T) ya yi wa wannan nahiya da muke ciki.
Kuma in da mutum ya yi tunani kuma ya dubi wannan al’amari na Sayyid Zakzaky (H) tun daga lokacin da ya soma da’awa zuwa yanzu da irin matsalolin da jarabawowi da ya fuskanta daban-daban, musamman ma ta fuskacin masu tafi da iko na gwamnatoci daban-daban da nufin mur}ushe da’awar da kuma }ashe shi, in dai mutum bai ce Allah ba, to ba abin da zai ce. Wannan yin Allah (T) ne. Domin shi tabbatar da addini, wani abu ne wanda yake hannun Allah (T), amma ya saba yana amfani da mutane ne wajen tabbatar da addini ko jaddada shi. Kuma za~in wanda zai yi amfani da shi domin tabbatar da addini, da za~in inda addinin zai tabbata, da kuma za~in lokacin da zai tabbatar da addinin, duka a hannunsa suke.
Saboda haka in Allah (T) ya za~i wanda zai yi amfani da shi domin tabbatar da addini ko jaddada shi. An so, ko ba a so ba, an yarda, ko ba a yarda ba, da shi ]in zai yi amfani, kuma duk wani }ulle-}ulle ko makirce-makirce, ko zagon }asa, ba su isa su hana abin da Allah (T) ya yi nufi ba. Kuma irin wa]annan bayi da Allah (T) kan za~a yana ba su kariya ta musamman daga wajensa. Mu duba yun}urin }isan da Sayyid Zakzaky (H) ya fuskanta a lokuta daban-daban tun lokacin yana ]alibi a Jami’a, har ya zuwa yau. Saboda haka al’amarin Sayyid (H) al’amari ne na Allah.
Ko da ba abubuwa na ba]inance, akwai abubuwa a zahirance da suke nuna cewa lallai Sayyid (H) da kuma da’awar da yake yi al’amari ne na Allah (T). Ga wasu daga ciki.
1. Ayoyi daban-daban, ta kuma fuskoki daban-daban, a lokuta daban-daban da suka faru a cikin da’awar. Misali wasu ayoyi da aka gani a wasu lokuta ga Shuhada’u na wannan gwagwarmaya. 2. Ishara daga wasu Malamai da kuma bayin Allah (T) dangane da Sayyid (H) da kuma da’awarsa. 3. Alamomi na kan hanya, wato na abubuwa da suka same shi da kuma mabiyansa, wato alamomi wanda suka nuna lallai mutum na kan hanyar Annabawa da kuma masu tajdidin addini. 4. Mafarkai na Ma’asumin (AS), wanda ’yan uwa da ma wa]anda ba ’yan uwa ba suka yi a lokuta daban-daban dangane da Sayyid da kuma da’awarsa. Misali ka ga wani ya yi mafarki da Manzon Allah (S) ko ]aya daga cikin A’imma (AS) ya ce masa tafarkin da Sayyid yake kai, tafarki ne na daidai, saboda haka ya bi shi, ya kuma kasance tare da shi, ko kuma Ma’asum (AS) ya nuna masa cewa lallai abin da Sayyid yake a kai, shi ne shiriya da dai makamantarsu.
Ta yiwu wani ya ce ai mafarki ba hujja ba ne, amma ai bushara ne ko? 5. Yun}urin kau da shi da kuma da’awar, amma haka ya gagara. Da kuma }arshen wa]anda suka cutar da shi da kuma mabiyansu. Mutum ya waiwoyi baya ya gani, ya ga }arshen wa]anda suka cutar da shi, ta fuskacin masu tafi da iko da mutanen gari da dai sauransu ya ga ya Allah (T) ya yi da su tun a nan duniyar. Wanda wannan dai baki ]aya na wa]annan abubuwa da aka kawo na ba]inance da kuma zahirance yana nuna cewa lallai alamomin Sayyid (H), in dai ba ka ce wannan yin Allah ba ne, to ba abin da mutum zai ce. Wannan ke nan dai a ta}aice dangane da wannan shimfi]a da kuma gabatarwa, sai kuma darussa daga ~angarori na rayuwarsa mai albarka.
1. FIKIRARSA: Duk wanda yake tare da Sayyid, ko ya san Sayyid, zai tabbatar da cewa, babban asasi ko ginshi}i da ya bambanta shi da sauran Malamai a wannan nahiya da muke ciki, ita ce fikirarsa, domin da yawa za ka iya samun mutum da ilimi ko kuma ma Malami, amma a wannan janibi na fikira, sai ka ga akwai matsala. Wato abubuwa da yawa suna shige masu duhu, ko ma su ru]ar da shi, sai daga baya ya gane ko al’amarin ya bayyana masa. Mutane da yawa za su iya al}alanci a kan haka. Abubuwa da dama sun sha faruwa, tun a shekarun baya har ya zuwa yanzu, Sayyid (H) ya ]auki matsaya a kai, sauran Malamai da jama’ar gari su ]auki su ma matsaya a kai. Sai daga baya ta bayyana matsayar Sayyid (H) ita ce daidai, sai ta bayyana matsayar da su suka ]auka ba daidai ba ne, wasun su ma har sukan yi i’itirafi da hakan. Mutum ya waiwaya baya ya gani, zai ga haka. Kuma ya dubi na baya-bayan nan, wato na al’amarin za~e.
Shi ya sa in muka duba a jawabi na rufe Mu’utamar, Sayyid (H) na yawan }arfafawa kan wannan janibi na fikira. Kuma yana yawan fa]in cewa wannan janibi na fikira shi ne ya bambanta wannan da’awa da sauran da’awowi ko }ungiyoyi na addini da suke wannan nahiya tamu. Domin duk wanda ka gani, to zantukansa da ayyukansa da kuma ]abi’unsa, sakamakon fikirarsa ne, wato tunaninsa. Ashe ke nan fikira salihiya, kuma salimiya, wadda ta yi daidai da koyarwar addinin Musulunci tana da gayar muhimmanci ga mutum. Tun da zantukansa da ayyukansa sakamakon ta ne.
Shi ya sa in mutum ya duba zai ga sakamakon irin wannan fikira ta Sayyid (H) tun da ya soma wannan da’awa har ya zuwa yanzu, a kan basira da ya}ini yake a kai. Akwai ma wani lokaci da na ji yana cewa, a wani zama da aka yi na Amirori sakamakon wasu matsaloli da suka taso, a lokacin yake cewa, bisa baiwa ta Allah (T) gare shi, tun da yake bai ta~a samun matsalar fikira ba, wato yau ya ce kaza, gobe ya dawo ya ce kaza. A wani jawabi nasa yana cewa; “Wannan fikira ba wai wani }o}ari ba ne, ko ilimi, ko jarumtaka, ko kuma dabara. A’a baiwa ce daga wajen Allah (T) wanda ya yi mana.”
Kuma ma in mutum ya bibiyi tarihin bayin Allah (T) da ya yi amfani da su wajen tajdidin addini zai ga babban abin da ya bambanta su da Malaman zamanin ko nayiharsu shi ne wannan janibi na fikira. Misali mutum ya dubi Shehu Usman [an Fodiyo da kuma Imam Khumaini.
2. IBADAR SA: Sayyid (H) ya kasance mai yawan ibada ne. Duk wanda ya kasance tare da Sayyid (H), ko zama ya ha]a su da Sayyid (H), misali a kurkuku, ko a aikin Hajji, zai tabbatar maka da hakan. Ga misalan wasu daga cikin ibadodinsa. A. Tahajjud ]insa: Wato Sallar dare. Sayyid Zakzaky (H) ya kwashe shekaru masu yawa, yana tashi }arfe 2:00 na dare domin ya yi Tahajjud. Wasu dararen ma yana raya sune da ibadodi ba tare da yin barci ba a cikinsu. Haka nan ya kasance mai yawan yin Salloli na nafilfili, musamman ma wa]anda suka zo a ruwayoyi.
B. Karatun Al}ur’ani: Sayyid (H) ya kasance mai yawan karatun Al}ur’ani, akwai ma lokacin da yake cewa, lokacin yana zaune a kurkuku, yakan so ya sauke Al}ur’ani }asa da kwana uku, amma tun da Sunna shi ne }arancin sauka kwana uku, to yakan tsaya a kan hakan.
C. Azkar ]insa: Sayyid (H) ya kasance mai yawan Azkar ta fuskoki daban-daban, wato na sigogi. Shi Azkar ]in wanda ya zauna da shi zai tabbatar maka da hakan.
D. Addu’o’insa: Sayyid ya kasance mai yawan addu’o’i, musamman ma addu’o’in da aka samo daga Ma’asumai (AS) duk wanda yake tare da shi ko ya zauna da shi zai tabbatar maka da haka.
E. Azuminsa: Sayyid (H) ya kasance mai yawan Azumi, shi ma wannan duk wanda suke tare da shi, ko suka zauna da shi, za su yi shaida a kan haka. Saboda ma yawan Azuminsa, wa]annan watanni uku masu albarka, wato Rajab, Sha’aban, Ramadan yakan yi Azumin su ba}i ]aya ne. Kuma ya ]auki shekaru a kan haka.
A ta}aice dai Sayyid Zakzaky (H) ya kasance mai yawan ibada ne ta fuskoki daban-daban, wanda ko da a ce mutum bai san Sayyid ba, kuma bai ta~a ganin sa ba, in zama ya ha]a shi da shi, to zai yi wahalar gaske ya zamanto bai tasirantu da ibadodin Sayyid (H) ba.
3. NIZAMINSA: Sayyid (H) ya kasance komai nasa a cikin nizami yake, wato lokutansa da dukkan al’amuransa duka a tsare suke, wato babu wani abu nasa wanda ba a cikin nizami yake ba. Kuma in muka duba za mu ga albarkacin wannan nizami nasa ga al’amura abin ya yi naso ga ’yan uwa dukkan al’amuransu cikin nizami ne. Wanda hakan yakan ba mutum sha’awa.
4. ILIMINSA: Duk wanda yake tare da Sayyid (H) zai tabbatar maka da cewa, lallai Sayyid (H) masanin Allah ne, masanin addininsa, kuma masanin zamaninsa, kuma mutum ko ba tare da Sayyid yake ba, in dai yana zaune a wannan nahiyar, kuma zai yi ma kansa adalci, zai ga abubuwa sukan taso yau da kullum, ya ga matsayar Sayyid, a ]aya ~angaren kuma ga matsayar wasu Malamai, daga }arshe sai ka ga ta bayyana matsayar Sayyid ita ce daidai. To mutum ya kwatanta haka da wani Hadisi da aka samo daga Manzon Allah (S) yana tambayar wani Sahabinsa cewa, shi kasan a cikin mutane wanene ya fi sani? Sai Manzon Allah (S) ya ce masa mafi sanin mutane, shi ne wanda ya fi su gane gaskiya idan sun sassa~a. Kuma duk wanda yake tare da Sayyid, ko ya san shi, zai tabbatar maka da cewa lallai Sayyid (H) yana da haza}a ta musamman da Allah (T) ya yi masa baiwa da ita. Kuma wannan tun tasowarsa haka abin yake. ’Yan uwansa na jini da abokansa da suka taso tare, duk sun tabbatar da haka. Alal misali }aninsa, Malam Badamasi, akwai lokacin da da yake cewa a duk ’ya’yan Mahaifinsu ba hazi}i kamar Sayyid (H). Ya ce akwai yayyin Sayyid, wato Abdul}adir da kuma Malam Sani, idan Mahaifinsu ya karantar da su, duk da cewa Sayyid bai kai inda suke ba, amma idan sun manta, Sayyid suke tambaya domin ya tuna masu. Haka nan Yayar Sayyid mai suna Hajiya Fatima ita ma ta tabbatar da haka, ta ce Sayyid (H) yana da }o}ari da haza}a. Ta ce a bisa gaskiya, a lokacin ya fi sauran yayyinsa gane karatun da ake karantar da su. Ta ce, kuma a lokacin ma akwai wani yayansa da ya kai }ararsa cewa shi kullum Sayyid (H) in ya samu ku]i bai sayen komai sai littafai, kuma ma yakan sayi littattafan da suka fi }arfinsa. Har ma take cewa Mahaifinsu na yawan cewa Sayyid ya fi su }o}arin karatu. Akwai kuma wani abokin Sayyid (H) da suka taso tare, ana tambayarsa dangane da yarintar Sayyid yake cewa; “A cikinsu ya bambanta a tsakaninsu”. Ya ce ya taso da neman ilimi da kuma neman sanin tarihin kowane abu”
A ta}aice dai Sayyid ya taso tun yana }arami da son karatu da kuma neman ilimi, kuma har ya zuwa yau ]inmu da ya kawo shekara sama da 60 bai daina zuwa neman ilimi ba. Wanda wannan darasi ne babba gare mu. Mu karanta shekarunmu da kuma shugul ]inmu da na shi, amma duk da haka yana zuwa karatu. Shi ya sa duk wanda yake tare da Sayyid, ko ya bibiyi tarihinsa, zai ga cewa baki ]ayan rayuwarsa, tun daga tasowarsa zuwa yanzu, tana gudana ne a kan ginshi}ai guda uku: 1. Neman ilimi da kuma ilimantarwa. 2. Ibada domin kusanci ga Allah (T). 3. Gwagwarmaya domin tabbatar da addini, wato Hukuma Islamiyya. Kuma duk wanda yake wannan Harka ta gwagwarmaya zai tabbatar da cewa Sayyid ya kasance yana yawan }arfafa ’yan uwa da kuma shajja’a su kan neman ilimi. Ba zan manta ba Ijtimar da aka yi a 1986, a ciki Sayyid yake cewa, akwai bu}atar a samu wasu ’yan uwa wa]anda za su ba da rayuwarsu baki ]aya su zamo ba su da wani aiki face neman ilimi da kuma }urbani ga Allah (T), wato neman kusanci gare shi.
5. SHAJA’ARSA: Shi ma wannan fage na shaja’a, wato jarumtaka. Duk wanda yake tare da Sayyid (H) da ma wanda bai tare da shi, lallai zai yi masa shaida cewa shi jarumi ne. Wato bai tsoron kowa in ba Allah (T) ba. Akwai ma lokacin da yake cewa idan akuya za ta ba shi tsoro, to arne ko azzalumi zai ba shi tsoro. Wato tunda akuya ba za ta ba shi tsoro ba, to, babu wani abu da ya isa ya ba shi tsoro. Akwai misalai da yawan gaske na rashin tsoron Sayyid (H), amma ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.
Kuma Sayyid (H) ba wai kawai bai da tsoro ne ba. A'a ya tarbiyyantar da da ’yan uwa a kan haka, kuma mutane shaida ne a kan haka. Sai ka ga abin da zai ba su tsoro, ga ’yan uwa sai ka ga abin ba haka yake ba. Wanda wannan in muka yi tunani za mu ga ni’ima ce babba gare mu, musamman ma a halin da muke ciki a wannan nahiyar da muke zaune, wato na haifar da wani yanayi na rayuwar da ake so mutane su zauna a ciki, wato yanayin zaman tsoro da kuma zullumi. Amma duk da haka sai ka ga mabiya Sayyid (H) suna cikin natsuwa da kwanciyar hankali da kuma rashin jin tsoron kowa da komai in ba Allah (T) ba, da kuma abin da yake so a ji tsoro, wato azabarsa. Saboda haka in muka yi tunani wannan ba }aramar ni'ima ba ce.
6. AKLA{ [INSA: Sayyid Zakzaky (H) ya kasance mai kyawawan ]abi'u ta kowace fuska. Ga misalan wasu daga cikin aklak ]insa.
A. Tawali'unsa: Duk wanda ya zauna da Sayyid (H) ko ya yi mu'amala da shi, zai tabbatar da haka. Saboda gayar tawali’unsa ya kasance yakan yi ma kansa hidima. Kuma ayyukan yau da kullum na gida ya kasance yakan yi. Kai hatta ma wani lokaci yakan yi hidima ga al’amajiransa. Duk wa]anda Allah (T) ya azurta su da jimawa da Sayyid (H) za su iya ba da shaida a kan haka. Domin akwai misalsalai masu yawa a kan haka.
B. Ha}urinsa: Sayyid (H) ya kasance mai yawan ha}uri, an cutar da shi ta fuskoki daban-daban a kuma lokuta daban-daban a rayuwarsa, amma matakin da ya ]auka shi ne na ha}uri, musamman ma cutarwar da ya samu ta ~angaren ’yan uwa a lokutun fitintunu. Misali fitinar Tawawiyya. Mu duba abubuwan da suka yi a lokacin da gangan da kuma manufa , wai na ~ata shaksiyyar Sayyid. Mu duba abubuwa marasa da]in ji da suka jingina wa Sayyid. Haka Sayyid  ya yi ha}uri har ya zuwa lokacin da Allah (T) ya yi hukunci tsakani.
C. Afuwarsa: Sayyid ya kasance mai yawan afuwa ga wa]anda suka yi masa abin da ba daidai ba. Ba zan mantawa ba a lokacin fitina ta ’yan Zuhudu. Akwai wa]anda suka yi maganganu  ga Sayyid (H), wasu kuma suka rubuta. To daga baya wasu sun farga. Saboda haka sai suka zo wajen Sayyid domin ya yi masu afuwa, Sayyid ya yafe su. Shi ne ma lokacin da ya zo jawabin kulle Ijtima, ya yi magana, a cikin bayanin nasa, yake cewa, duk wanda ya san ya ce wani abu gare shi, ba sai ma ya a zo ya ce ya yafe masa ba. Shi ya yafe masa. Da dai sauraan misalai irin wannan na afuwarsa, wanda yana da gayar muhimmanci mu ’yan uwa ya zamanto mun ]abi’antu da irin wa]annan ]abi'o'i na Sayyid na ha}urinsa, afuwarsa, tawali’unsa da dai sauransu.
D. Tausayinsa: Sayyid (H) ya kasance mai yawan tausayi. Akwai lokacin da na ji yana cewa, lokacin yana zaune a kurkukun Kaduna, yana sauraron BBC sashen Hausa, sai ya ji ana tattaunawa da wasu ’yan mata Musulmi, wa]anda suka mai da fasi}anci a matsayin sana’a, suka ce kuma da abin da suke samu ne suke ]aukar ]awainiyar kansu da ma ta iyayensu. Shi ne Sayyid ya ce da ya ji hirar, saboda tausayinsu sai da ya zubar da hawaye.
Kuma Sayyid saboda tausayinsa ga ’yan uwa, wasu abubuwa yakan bar su, ko ya nisance su, saboda yana ganin mustawar tunaninsu ko fahimtarsu ba ta kai haka ba, wato ta ’yan uwa. Misali guda a nan shi ne, a 1980 lokacin da yake aikata wasu abubuwa na Mazhabar Ja’afariyya, sai ya ga ana yi masa tambayoyi cewa an ga ya aikata kaza a alwala. An ga ya aikata kaza a Salla. Sayyid ya ce saboda gudun fitinarwa ya nisanci haka. Kuma tsayuwarsa a wannan da’awa duk ko da irin jarabawowin da ya fuskanta, kuma yake fuskanta, har da tausayinsa ga jama’a da makomarsu, wato yana duban in da za su je, da kuma abin da za su tarar.
E. Kyautarsa: Sayyid ya kasance mai yawan kyauta da kuma share wa mutane hawaye a kan matsalolinsu. Kuma ya kasance mai yawan biyan bu}atar masu bu}ata, idan sun kawo masa, duk wanda yake tare da Sayyid ko ya zauna da shi zai yi shaida a kan haka. Wato duk bu}atar da aka kawo wa Sayyid, indai zai iya biyan bu}atar, ko kuma yana da hanyar da za a iya samun biyan bu}ata, to Sayyid (H) ko zai yi. A nan zan ba da misali ]aya da ya shafe ni kai tsaye. Akwai lokacin da nake son zuwa karatu Iran a birnin {um, wato na Hauza. Wannan a 1994 ne ya auku. Sai na yanke tunani akan in samu Sayyid (H) in shaida masa. Ikon Allah, yana gab da zai yi wata tafiya zuwa Iran ne. Na same shi na shaida masa cewa ina son zuwa birnin  {um, domin yin karatun Hauza, amma ban san yadda suke ]aukar ]aliban ba. Shi ne Sayyid (H) ya yi min bayani a kan yadda suke ]auka. Amma ya ce in ya je zai binciko min.
Bayan da Sayyid ya tafi ya dawo, sai ga shi ya samar mana zuwa karatu a birinin {um, ba ma ni ka]ai ba, a’a har da wasu ’yan uwa mu 12. ’Yan uwan sune; Malam Adamu Tsoho, Malam Ibrahim A}il, Malam Abdurahman Yola, Malam Abubakar Maina, Malam Hamza Lawal, Malam Sa’ad Macci]o, Malam Abdullahi Zango, wanda Alhamdulilah shi har yanzu yana karatu a {um ]in, Marigayi Malam Hasan Khalifa, Marigayi Malam Abubakar Malumfashi, Malama Fatima matar Malam Hamza da kuma Malama Maryam, matar Malam Abdullahi Zango. Akwai misalsalai na irin wannan da yawa daga wajen Malam, wato na biyan bu}atun masu bu}ata idan suka kai masa.
7-ZUHUDUNSA:- Duk wanda yake tare da Sayyid Zakzaky (H), ko ya zauna da shi, ko kuma ya bibiyi tarihin rayuwarsa, zai ga cewa lalle duniya da abin duniya ba su da tasiri a zuciyarsa. Akwai lokacin da yake cewa a wani jawabinsa; “Duk wanda ya fuskantar da zuciyarsa ga Allah (T) zai ga komai wula}antacce ne, zai ga sutura wula}antatta ce, zai ga komai a wula}ance. Kai duniya baki ]aya ba za ta kai darajar fuffuken }uda ba a wajensa.”
A wani waje kuma yana cewa; “Mutum idan akwai Allah a zuciyarsa in ya kalli Allah, komai sai ya zamo masa duhu, ba abin kallo ba”. Saboda haka duk wanda yake tare da Sayyid Zakzaky (H), zai tabbatar da cewa lalle Sayyid Zakzaky (H) ba mai neman jama’a ba ne, ballantana a ce saboda jama’a yake yi. Sayyid ba mai neman matsayi ba ne, ballantana a ce saboda matsayi yake yi. Haka nan ba mai neman dukiya ba ne. Ballantana a ce saboda samun dukiya yake yi. Sayyid Zakzaky yana yin abubuwansa ne saboda Allah (T) da kuma lahira. Alhali inda za mu dubi Malaman wasu }ungiyoyi na addini, za mu ga cewa da yawansu ’yan kasuwar addini ne, inda riba a yi, in ba riba a kama wani abin. Kuma ai an yi hukumomi daban-daban a }asar nan, wa]anda wasunsu suka gwada ~ullowa ta dama ga Sayyid Zakzaky (H), wato ta hanyar ba da tarkacen duniya, amma ai ba su samu nasara ba. Kamar yadda wa]anda suka ~ullo ta hagu su ma ba su sami nasara ba, shi ya sa a lokacin ’yan Tawayiyya da suke ganin wai su suka kawo jama’a, Sayyid  Zakzaky (H) ya ce su kwashe jama’arsu su tafi.
Akwai misali da dama a rayuwar Sayyid Zakzaky (H) da ke nuna duniya da tarkacenta, ba su da tasiri a zuciyarsa. Wani abin da ya faru mai ban dariya, lokacin da Sayyid (H) yana kurkuku a ku]ancin }asar nan. A cikin kurkukun wani ya kawo masa tsegumi cewa, abincin da ake kawo masa, akwai wanda yake ]e~e masa kifin da aka sa masa. Sai Sayyid Zakzaky (H) ya ce masa; “Ka bar shi ya yi ta ]e~ewa yana ci, ka ga ya zama giwa ne?” Sai mutumin da ya kawo wannan tsegumin, ya tsaya yana mamaki. Shi ne har yake ce wa Sayyid Zakzaky (H); “Oga kai ba ka damu ba?”
Wani misali kuma shi ne, bayan rikicin za~e da aka yi. Akwai daga cikin Kiristoci da suka zo gidan Sayyid Zakzaky (H) domin godiya gare shi, saboda kariya da almajiransa suka ba su daga kai masu hari. To cikin wa]anda suka zo ]in akwai sashen Kirisatoci mata. To cikin abin da suka ce baya ga godiya, shi ne, suna fatan Allah ya sa ya zama Shugaban }asa. Shi ne Sayyid Zakzaky (H) ya ce; “Kayya-kayya, in dai wannan ne, ban so.”
Wani misali kuma shi ne, abubuwa sun sha faruwa a samu mutanen gari su bi abin ]uu, amma Sayyid (H) ya tsaya }yam a kan abin da yake ganin shi ne daidai. Misali a nan, Rikicin Kafancan, al’amarin Saddam a lokacin ya}in Tekun Fasha, al’amarin Shari’a da dai sauransu. Ga wa]anda suke da masaniya lokacin da wa]anan ababuwan suka faru, sun san akwai Malaman da suka yi amfani da wannan damar, su suna ganin ga wata dama ta samun jama’a. Saboda haka su ma suka goyi bayan jama’ar gari suka bi su ]uu. Sai daga baya abubuwa suka kwaranye masu.
A ta}aice dai duniya da tarkacenta ba su da tasiri a zuciyar Sayyid Zakzaky (H), kuma wannan shi ne ha}i}anin ma’anar Zuhudu, kamar yadda Malaman Irfan suka yi bayani.
 Wato Zuhudu ba shi ne kada ka mallaki abin duniya ba, a’a shi ne ya zamanto kada abin duniya ya mallake ka. Wato ma’ana ko da a zahirance kana mu’amala da duniya da kuma tarkacenta, to a ba]inance ya zamanto ba su da tasiri gare ka. Wato ba su shagaltar da mutum ba daga tunanin Allah (T) da kuma gidan lahira. Ma’ana ya zamanto duniya da tarkacenta, ba su da tasiri a zuciya, shi ne ya kasance babu TA’ALLU{-{ALBIYYA gare su.
8- GWAGWARMAYARSA:- Masoyansa da ma ma}iyansa, duk za su iya yi masa shaida a wannan fage na gwagwarmaya da zalunci da kuma azzalumai. Shi ya sa ko da mutum bai tare da Sayyid Zakzaky (H), in ya ji sunansa, abin da zai soma fa]owa a ransa, shi ne gwagwarmaya da Hukuma. Wanda saboda wannan gwagwarmaya Sayyid (H) ya fuskanci cutarwa da makirce-makirce da }ulle-}ulle da zagon }asa, iri-iri ta fuskoki daban-daban. Misali ~angaren Hukuma da kuma wasu daga mutanen garin, musamman ma wasu daga cikin Malamai. Amma duk da haka Sayyid Zakzaky (H) yana nan }yam, sai ma abin da ya yi gaba. Sakamakon wannan gwagwarmaya ya yi zama a gidajen kurkuku daban-daban na Kudancin }asar nan da kuma Arewacinta. An yi yun}urin kashe shi a lokuta da dama, tun yana ]alibi a Jami’ar ABU, har ya zuwa yau. Akwai ma lokacin da yake cewa, an sha kukin ]in bindiga da nufin a harbe shi. Ya ce wannan ya kai tashi uku. Amma duk wa]annan yun}uri na kisa na wa]anda suka bayyana da ma wa]anda ba su bayyana ba, Allah (T) ya kare shi.
Haka nan zaman kurkukun da ya yi. Akwai wajen da aka ha]a shi ]aki ]aya da mahaukaci. Mahaukaci kuma tuburan ba mai }aramar hauka ba. A ta}aice dai saboda wannan gwagwarmaya Sayyid Zakzaky (H) ya fuskanci jarabawowi masu yawan gaske ta kuma fuskoki daban-daban, a kuma lokuta daban-daban. Amma duk da haka ya dake ya tsaya }yam a gwagwarmayar, tun yana shi ka]ai, aka kai gomomi, aka kai ]aruruwa, aka kai dubbai, yau ga shi ana maganar miliyoyi. Wannan abu in mutum bai ce yin Allah (T) ba, to me zai ce? Kuma wannan Aya ce babba ga masu tunani.
9-MUJAHADARSA:- Duk wanda yake tare da Sayyid Zakzaky (H) zai iya ba da shaidar cewa, mai yawan mujahada ne. Mujahada ita ce mutum ya yi fa]a da nafs ]insa da kuma Shai]an, har ya kai mustawar da zai samu sul]ani (iko) a kansu. Wato ya zamanto shi yake juya (nafs ]in da Shai]an), ba su suke juya shi ba. Kuma wannan mai yiyuwa ne. Akwai bayin Allah (T) da yawa, wa]anda suka kai wannan matsayin da nafs ]insu da Shai]an ba su da tasiri a zuciyarsu. Kamar yadda duniya da mutane ba su da tasiri a zuciyarsu, kuma wa]annan abubuwa guda hu]u wato nafs, Shai]an, mutane da kuma duniya, a ilimin Irfan su ake ce wa AWA’I{. Wato ababen da suke hana mutum isa gun Allah (T). Ko kuma su zama wa mutum hijabi tsakaninsa da Allah (T). Saboda haka mutum za yi ta mujahada ne da wa]annan ~angarori guda hu]u, har ya kai matsayin da ba su da tasiri a zuciyarsa. Saboda haka a sashen mujahada, mutane sun kasu kashi  uku ne. 1-Akwai wa]anda suke sun samu sul]a (iko) a kan nafs ]insu da kuma Shai]an. 2- Akwai wa]anda suke nafs ]insu da Shai]an, su suke da sul]a a kansu. 3-Akwai kuma wa]anda suke wani lokaci su samu sul]a a kan nafs ]insu da Shai]an, wani lokaci kuma nafs ]insu da Shai]an su samu sul]a a kansu. Wato dai kamar kokawa, wani lokaci su yi kaye, wani lokaci a kada su. Saboda haka mujahada wani abu ne da mutum zai ta yi har ya zuwa saukar ajalinsa. Kuma duk wanda ya san Sayyid Zakzaky (H) ya san cewa mutum ne mai yawan mujahada. Kuma wa]annan abubuwa guda hu]u da aka ambata, ya kai matsayin da dukkansu ba su da tasiri a zuciyarsa. Wato son ransa, son ran mutane, Shai]an da kuma duniya. Shi ma wannan akwai misali da dama, amma ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa. Akwai ma inda a cikin wani jawabinsa yake cewa; yana mai tsoro a ce ga abin da Allah (T) yake so, shi kuma ga abin da ransa yake so. Ya bar na Allah, ya bi son ransa. Ya ce yana mai tsoron haka. A wani jawabinsa kuma yana cewa dangane da mujahada. “[abba}a kyawawan ]abi’u yana wahala. Amma fa]a za ka yi da zuciyarka da kuma babban abokin gaba Shai]an. Wanda kullum yake sawwala wa ranka sha’awa, yake kasalantar da kai lokacin da ka zabura, za ka yi abin kirki. Ko mi}a wani abu, sai ya ri}a ce maka, ‘don Allah kai ba kana so ba? Ya za ka ba shi?’ Sai ka danne wannan tunanin ka mi}a har mi}awar ta zamo siffarka.”
A wani jawabinsa kuma yana cewa; “Shai]an ba }yale mu zai yi ba, Tunda bai }yale Annabawa ba. Shi kullum yana neman wa]anda ba su tare da shi ne, domin ya same su ya sa a aljihunsa, wa]anda suke cikin aljihunsa ya ga cewa ya tabbatar ba su fita ba”.  Da dai sauran iri-iren wa]annan kalmomi na Sayyid Zakzaky (H) da suke da ala}a da mujahada.
10- ALA{ARSA DA ALLAH (T):- Duk wanda yake tare da Sayyid Zakzaky (H), kuma Allah (T) ya azurta shi da sanin sa daidai gwargwado ya san cewa yana da gayar ala}antuwa da Allah (T) da kuma ]amfaruwa da shi. Abubuwa da yawa na jarabawoyi sun faru, a cikin wannan gwagwarmaya ]in wasu da, da ana tare da su a cikin Harkar suka bar ta. Misali ’yan Zuhu]u, ’yan Tawayiyya da dai sauransu, amma duk da haka Sayyid Zakzaky (H) ko gezau bai yi ba. Saboda me? Saboda gayar ala}antuwarsa da Allah (T). Saboda haka Sayyid Zakzaky (H) ya kasance mai gayar tawakkali da ya}ini ga Allah (T), mai gayar kyautata zato da si}}a da Allah (T), mai gayar ta’azimi da ikhlasi ga Allah (T), mai gayar so da kuma shau}i ga Allah (T), tsoro da kuma kwa]ayi ga Allah (T). A ta}aice dai ala}ar Sayyid Zakzaky (H) da Allah (T) wani abu ne wanda ba za a iya bayani a kai ba, sanka-sanka sai a dun}ule. Kuma Sayyid Zakzaky (H) ya kasance a jawabansa, musamman ma na kulle Mu’utamar yana yawan yin magana ne dangane da muhimmancin ala}antuwa da kuma ]amfaruwa da Allah (T). Har ma yakan ce, kada mutum ya zama ]an cika wuri. Ya ce ]an cika wuri shi ne, duk abubuwan da ake yi na ‘programs’, da shi ake yi, amma shi a }ashin kansa ala}arsa da Allah (T) tana da rauni. Kuma yakan ce, kowannenmu ]an uwa ne ko ’yar uwa ya binciki kansa ya ga ya ala}arsa take da Allah (T), mutum ya kyautata ala}arsa da Allah (T), da dai sauran ire-iren wa]annan kalmomi na Sayyid Zakzaky (H) da suke da ala}a da kyautata ala}a da Allah (T) da kuma ]amfaruwa da shi.
11- ALA{ARSA DA MANZON ALLAH (S) DA KUMA AHLUL BAIT (AS):- Ala}ar Sayyid Zakzaky (H) da Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Bait (AS), shi ma wannan wani fage ne wanda bayaninsa yana da wuya a warware, sai dai a dun}ule. Saboda haka a dun}ule Sayyid Zakzaky (H) yana da gayar ala}antuwa da Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS). A ba]inance da kuma a zahirance. Kuma duk wanda yake tare da shi zai tabbatar da haka, domin duk abin da zai yi, sai ya dace da koyarwar Manzo Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS). A ta}aice dai duk wani abu wanda yake Sunna ce ta Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) bai barin sa face ya aikata shi, shi ya sa ga wanda Allah (T) ya azurta da sanin Sunnoni na Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS). To in ya duba rayuwar Sayyid Zakzaky (H) zai dinga ganin sa a zantukansa, da ayyukansa da kuma a ]abi’o’insa, kuma kamar yadda yake koyi da kuma bi sau da }afa ga Manzon Allah (AS) da kuma Ahlul Baiti (AS), ga dukkan sunnoninsu, to haka yake so ’yan uwa su kasance. Wani misali da ya ta~a faruwa a ni kaina. A wata Ijtima da aka yi shekaru 27 da suka wuce. An zo za a ci abinci kamar yadda wasu suka sani, a lokacin in za a ci abinci akan aje shi ne a yi Da’ira a ci. To an zo za a ci abincin, sai ban cire takalmi ba, da yake ya zo a Hadisi cewa Sunna ce in mutum zai ci abinci ya cire takalmi. To a lokacin sai Sayyid Zakzaky (H) ya dube ni, bai ce komai ba, ganin haka sai na tu~e takalmin. Duk da wannan abu ya faru shekaru masu yawa, amma har yanzu akwai tasirinsa a cikin zuciyata, wato na cewa duk wata Sunna ta Manzon Allah (S) bai kamata mutum ya bar ta ba, matu}ar zai iya aikata ta. Kuma za mu ga abubuwa da dama wa]anda mafi yawan Musulmi galibi sukan gudanar da su ne a al’a]ance da kuma yayin zamani. Misali aure, zaman aure, tarbiyyar yara da dai sauransu, za mu ga Sayyid Zakzaky (H) na yawan }arfafa ’yan uwa a kan su gudanar da su a kan asasin koyarwar Manzon Allah (S). Kuma akwai Sunnoni da yawa na Manzon Allah (S). Shukran La Fakhran. Sayyid Zakzaky (H) shi ne asasin rayasu a wannan nahiya tamu da muke ciki, wanda ba ’yan uwa kawai ba, a’a hatta sauran jama’ar gari, da yawa sun kwaikwayi wa]annan Sunnoni, wasu ma sun ginun a kai. Haka nan kuma mu duba yadda Sayyid Zakzaky (H) yake kiyaye munasabobi na wilada da kuma wafatin Ma’asumai (AS), wato Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS), wanda irin wa]annan tarurruka na munasabobi, ko duniyar Shi’a mutum ya je iyakar abin da zai gani ke nan.
Saboda haka dai a ta}aice Sayyid Zakzaky (H) yana da gayar ala}a da Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) aba]inance, wajen son su, shau}in su, girmama su da dai sauransu. Da kuma a zahirance wajen yi masu biyayya a dukkan sunnoninsu na umurni da kuma hani.
12- YUN{URINSA WAJEN HA[A KAN AL’UMMAR MUSULMI:- Ha]a kan al’ummar Musulmi na wannan nahiya da muke ciki, da ma sauran duniya baki ]aya, yana ]aya daga cikin abubuwan da Sayyid Zakzaky (H) yake }arfafawa da kuma kwa]aitarwa a kai. Duk wanda yake cikin wannan da’awa zai tabbatar da haka. Duk wani abin da zai kawo rarraba tsakankanin Musulmi, Sayyid Zakzaky (H) yakan }yamaci abin, yakan kuma yi kashedi a kan haka. Abin da kuma zai }arfafa ha]in kan Musulmi, yakan tsayu da shi. Akwai misalai da dama na abubuwa da Sayyid Zakzaky (H) ya yi a aikace, ya kuma tarbiyantar da ’yan uwa a kai, na ganin cewa al’ummar Musulmi sun samu ha]in kai a tsakaninsu, ga wasu daga ciki: 1- Kai wa Malamai na wasu }ungiyoyi ziyara. 2- Rashin fitar da Musulmi cikin Musulunci, wato kafirta su. 3- Gina ’yan uwa a kan yin Salla a masallatai na Musulmi, ba tare da bambancewa ba. Wato na a ce sai ’yan masallacin kaza mutum zai yi Salla. 4- Gina ’yan uwa a kan yi wa Musulunci hidima ta fuskoki daban-daban ba tare da bambancewa ba. Wato na cewa suna tare da mu, ko ba su tare da mu. Misali wasu ayyuka na ’yan Medical Team, Aikin gayya da Hurras suke yi na gyaran ma}abarta da dai sauran ayyuka ga Musulmi baki ]aya. 5- Yin Makon Ha]in Kai, wato wanda ake yi a watan Maulidi wanda a kan gayyato Malamai, wa]anda suke a kan fahimta daban-daban domin gabatar da jawabai da nufin samun kusanci da juna da kuma fahimtar juna da dai sauran hanyoyi da Sayyid Zakzaky (H) ya gina ’yan uwa a kai, domin ha]in kan al’ummar Musulmi da ke wannan nahiyar.
Wannan baki ]aya a ta}aice, dangane da darussa 12 daga rayuwar Sayyid Zakzaky (H) sai dai kafin kullewa da godiya ga Allah (T) da kuma addu’a ga Sayyid Zakzaky (H). Wasu nasihohi guda biyar wa]anda Sayyid (H) yana yawan magana a kansu a jawabansa.
1- Isti}ama da kuma sabati a wannan tafiya ta gwagwarmaya, har ya zuwa saukar ajalin mutum. Wato ko mutum ya mutu yana kan tafarkin, ko kuma a kashe shi a kan tafarkin.
2- Dauriya a kan jarabawoyi da kuma fitinoni da suke gudana na cikin gida da na waje. Wato cikin gwagwarmayar da kuma wajenta. Domin wa]annan jarabawowi da fitinoni in mutum ya daure masu hanya ce ta samun lada gare shi. Kuma Aljanna sakamako ne na dauriya.
3- Iltizami da addini, wato mutum ya ga cewa ya siffatu da addini a zantukansa, ]abi’unsa da kuma ayyukansa. Wato dai ya kasance alami na addini. In an gan shi an ga addini, in an ji shi a ji addini, in an yi mu’amala da shi a ga addini. To idan mutum ya samu wannan, ko da Allah (T) bai raye shi ba ya ga tabbatar addini, to ya samu babbar nasara.
4- Ba da gudummawa a wannan Harka ta gwagwarmaya, wato kowannenmu ]an uwa ne ko ’yar uwa ya duba ya ga wace gudummawa zai bayar. Kuma ya tsayu da ba da wannan gudummawa har zuwa komawarsa ga Allah (T). Kuma Alhamdulillah a cikin wannan gwagwarmaya ga sashe na ayyuka nan daban-daban. To mutum ya duba ta wane sashe ne shi zai dinga ba da gudummawa. Domin kamar yadda aka sani daidai gudummawar da kowa ya bayar, daidai sakamakon da zai samu gobe }iyama.
5- Ikhlasi:- Wato ya kasance kowannenmu duk abubuwan da zai yi, ya yi su ne saboda Allah (T) da kuma neman yardarsa. Misali wannan iltizami da addini, da ba da gudummawarsa a  tafarkin, da kuma dakewa a tafarkin, duk su kasance a kan asasin ikhlasi ne, ba akasin iklasi ba. Domin shi ikhlasi shi ne ruhin ayyuka.
Daga }arshe muna godiya ga Allah (T) da wannan baiwa da kyauta a wannan nahiyar da muke ciki. Kuma muna }ara godiya ga Allah (T) da ya yi wannan baiwa da kyauta a zamaninmu. Kuma muna }ara godiya ga Allah (T) da ya azurta mu da amsar wannan baiwa da kyauta da baiwa da ya ba mu. Addu’armu ga Sayyid Zakzaky (H), Allah (T) ya saka masa da alheri, ya da]a kare shi, ya da]a ba shi lafiya, ya kuma da]a masa yawancin kwana, ya kuma da]a masa darajoji. Amin.

No comments:

Post a Comment