Kamar yadda ya gabata a darasi na Akhla} na biyu, da yake an samu lokaci mai tsawo ba’a gabatar
da wannan darasi na Akhla}
ba,dalili ko
shine,kamar yadda aka ce a baya,lokaci bayan lokaci za’a ri}a
samun yankewar darasin,
saboda rubutu na wafati ko shahadar Aimma na Ahlul Bayt
[AS] wanda akan kawo da unwanin Darussa
12.Alal misali,watan muharram da safar daya gabata,akwai shahadar Imam
Husain[AS],wafatin Imam zainul Abidin [AS],wafatin Imam Hasan [AS],da kuma wafatin
Manzon Allah [S],a ta}aice dai rubutu kan wa]annan ~angarori daya gabata, shine
dalilin da yasa aka samu kusufi na wani lokaci ba’a gabatar da wannan
darasi na Akhla} ba. Idan
ba’a manta ba,a darasin daya gabata an tsaya ne akan wasu tambayoyi guda uku
sune,1.yaya za’ayi mutum yasan aibobin Nafs ]insa?
Wato ya san ko yana da munanan Akhla} ko bai dasu.2.wa]anne hanyoyi ne mutum zai bi domin ya ku~uta?
Wato ya tsarkaka daga munanan Akhla}. 3.yaya za’ayi mutum ya
samu ko ya siffanta da kyawawan Akhla}? A darasin daya gabata,an bada amsar
tambaya ta farko,bayan haka aka ce insha Allah a darasi na gaba za’a kawo
amsoshin sauran wa]ancan
tambayoyi guda biyu. Dangane
da tambaya ta biyu na wa]anne hanyoyi mutum zai bi domin ya tsarkaka daga munanan Akhla},idan mutum ya bibiyi littafan Akha},
kamar littafin Akhla}u Ahlul Bayt [AS],ko kuma littafi
mai suna, Ilajul –Amradu- Akhla-}iyyah;zai ga an kawo hanyoyi da matakai da mutum zai bi domin
tsarkakuwa ko wankuwa daga munanan Akhla}.Anan za’a kawo guda uku
daga ciki saboda gudun tsawaitawa. 1.Sanin
illolin munanan ]abi’u,domin su munanan ]abi’u sukan nisanta mutum daga
Allah [T],sukan nisanta mutum daga mutane,sukan kuma nisanta mutum daga
Aljannah.Ga kuma illoli da suke yiwa mutum,a addininsa da duniyarsa da kuma
lahirarsa.Domin ita mummunar ]abi’a,ba wai ga mutum ]an uwanka ba,a’a ko dabba mutum ya munana wa,zata iya kasancewa
sanadiyyar shiga wuta ga mutum,alal misali,}issar
wata mata mai mage da ta ]aure ta,ba ta bata abinci,bata kuma bari taje ta nema ba,wanda hakan
yayi sanadiyyar zuwanta wuta,insha Allah idan an yi nisa a cikin wannan darasi
na Akhla},za’a kawo illolin da munanan ]abi’u suke yi a addinin mutum da duniyarsa da kuma
lahirarsa,sanka- sanka. 2.Mujahada:Daga
cikin hanyoyin da mutum zai bi domin tsarkaka daga munanan ]abi’u shine mujahada,wato mutum
ya ya}i Nafs ]insa [ransa] da kuma shai]an,domin yaga ya tsarkaka daga wata mummunar ]abi’a
da yake tare da ita.Misali,mummunar ]abi’a ta riya,ko ujub,ko
hassada, ko rowa,da dai makamantansu.To,anan mutum zaiyi mujahada wajen ganin
cewa ya tsarkaka daga riya,ko ujub,ko hassada,ko kuma rowa.Shima wannan insha Allah nan gaba za’ayi bayanin
yadda mutum zai yi wannan mujahada,domin tsarkakuwa daga wadannan cututtuka na
zuciya da aka ambata,dama wa]anda ba’a ambata ba. 3.Mura}aba:Daga cikin hanyoyin da mutum zai bi domin tsarkaka daga munanan ]abi’oi,akwai hanyar mura}aba,wato shine mutum ya zamo yana shu’urin [jin]cewa Allah [T] yana ganinsa,yana
jinsa,ya san tunanin zuciyarsa,yana kuma tare da shi,idan mutum ya kasance ko da
wane lokaci,tunaninsa ya ginu akan wannan shu’urin na mura}aba,to ha}i}a ya samu hanya babba ta tsarkakuwa daga munanan ]abi’u, kuma wadda tafi tasiri fiye da biyun da aka ambata.Shima
wannan,wato yadda mutum zai gina shu’urin mura}aba a zuciyarsa,bayaninsa zai zo nan gaba.Wannan ke nan a ta}aice dangane da amsar tambaya ta
biyu. Sai
kuma amsar tambaya ta uku.Ta yaya za’ayi mutum ya siffantu,ko ya samu kyawawan ]abi’u? shima wannan malamam Akhla} sunyi bayani na hanyoyi da matakai da mutum zai bi,daga
cikin hanyoyin:
1.Sanin fa’idodi da kuma sakamako na kyawawan ]abi’u,domin sanin zai taimaka wa mutum wajen ganin cewa ya siffanta da
kyawawan ]abi’u. saboda kyawawan ]abi’u sukan kusanta mutum ga Allah [T],sukan kusanta shi
da mutane,sukan kuma kusanta shi ga Aljannah.Banda kuma fa’idodi masu yawan
gaske da mutum zai samu a addininsa da duniyarsa da kuma lahiyarsa sakamakon
siffantuwa da kyawawan ]abi’u.Domin kyakkyawar ]abi’a,ba wai ga mutum ]an uwanka ba,ko dabba mutum ya kyautata wa,haka na iya zama sanadiyyar
shigarsa Aljannah.Misali anan }issar wani mutumi
da yaji }ishi yaje ya samu wata rijiya ya sha ruwa,bayan ya sha ya juya zai
tafi sai ga wani kare,yazo bakin rijiyar yana jin }ishi,ganin haka sai mutumin
ya ]ebo ruwan a rijiya ya ba karen,to sai Allah[T] yayi wahayi ga Annabin zamanin,da ya
shaida ma mutumin,Allah zai shigar dashi aljanna sakamakon wannan aiki nasa.Mu
duba mu gani yadda kyautatawa ga dabba zai iya sanadiyyar shigar mutum aljanna
ko kuma munana mata,yana iya sanadiyyar shigar mutum wuta.To ina ga kyautata ma
mutum ]an’uwanka
ko munana masa.Hanyoyi da mutum zai bi a addini wajen
siffanta da kyawawan ]abi’u shine,ta hanyar mujahada,wato mutum yayi fa]a
da Nafs ]insa wajen ganin cewa ya siffanta da kyakkyawar siffa,kuma wannan
mujahada mutum zai yi tane ta fuskoki guda ukku:Na farko,mutum yayi mujahada
wajen ‘Iktisabin’ wato samun kyawawan ]abi’a.Na biyu,mujahada
wajen Ba}a’a’ wato wanzuwa da kuma isti}ama akan kyawawan ]abi’a.Na uku,mujahada wajen ‘Numuw’ wato cigaba wajen da]a kyautatuwa ga wa]annan kyawawan ]abi’u daya samu. Domin
su kyawawan ]abi’u,kamar yadda malaman Akhla} sukayi bayani,ana samun
su ko mallakar sune ta hanyoyi guda biyu: Hanya ta farko itace,ta ‘JuduL-lLahiy’
wato baiwa daga ubangiji,wani zaka ga tun tashinsa yana yaro, yana da ha}uri da kyauta,ko dai wasu kyawawan siffofi,wato yana da su ba tare da yayi
wata mujahada ba wajen samun su,To,wannan shine abinda malaman Akhla}, suke cewa ]abi’oi na ‘Judul-ILahiy’,Hanya ta biyu ta mallakar kyawawan ]abi’u, itace ta hanyar ‘Iktisabi’,wato mutum shi zai yi mujahada wajen
samun su kyawawan ]abi’un.Misali yayi mujahada idan
shi bai da ha}uri,ya zama mai ha}uri,idan shi mai yawan fushi ne,ya zama mai ha]iye
fushi,idan shi marowaci ne,ya zama mai kyauta,da dai sauran kyawawan ]abi’oi, da ba’a ambata ba.Shima wannan nan gaba insha Allah in an zo kan
bayani dangane da kyawawan ]abi’u, za’a yi bayani a warware, na irin mujahadar da kowanne yake bu}ata,domin siffanta da
siffar kamar yadda malaman Akhla}
suka bayyana.
3.Mushahada da kuma Mura}aba:Daga cikin hanyoyin da mutum zai bi domin samun kyawawan ]abi’u shine,hanyar mushahada da kuma mura}aba na Allah [T].Mushahada shine,mutum ya zaman to koda wane lokacin yana
shu’urin [jin] Allah [T],kamar yana ganin Allah [T],domin in shi bai ganinsa to
Allah [T] yana ganinsa,wanda wannan shu’rin na cewa Allah [T] yana ganinsa
shine mura}aba,kamar yadda aka yi ]an bayani a baya.Domin idan
mutum ya kasance koda wane lokaci yana cikin wannan shu’irin na mushahada da
kuma mura}aba,to zai zamo hanya babba a gare shi da zai taimaka masa wajen siffanta
da kyawawan siffofi.Misali,tun da yasan Allah [T] yana jinsa,to duk abinda zai fa]i zai ga cewa ya fa]i gaskiya kuma tun da ya san Allah [T] yana ganinsa,to zai ga cewa ya
kasance mai ri}on amana,kuma tun da ya san cewa Allah [T] yasan abinda ke cikin
zuciyarsa,to zai ga cewa ya kyautata tunaninsa,ba zai yi tunanin da bai dace ba.Kuma
irin wannan shu’uri na mura}aba da kuma mushahada,idan mutum ya same shi,zai taimaka masa wajen ganin
cewa, ko da wane lokaci, yayi iya iyawarsa wajen ganin yayi wa Allah [T] ]a’a,da kuma kasancewa bai sa~a masa ba. Ta }issar wani malamin
irfani dana karanta, shi da Almajiransa.
Wata rana sai shi malamin ya ba almajiransa wani aiki, amma ya ce yana son kowa yayi in da ba a
ganin sa. Dukkan su sai suka tafi, kowa yaje
in da mutane ba su ganinsa ya aiwatar da aikin, sai guda ]aya daga cikin almjiran ne bai aiwatar ba.
Sai malamin ya tambaye shi, kai ya aka yi
kowa ya aiwatar kai baka aiwatar ba? Shine ya bada amsa cewa, ai duk in da ya je, Allah (T) yana ganinsa, shi yasa
bai yi ba. Shine malamin yace masa dama na yi maku jarabawa ne, in ga wanda ya
kai ma}am
(matsayi) na mura}aba da kuma mushahada na Allah (T).
4. Samun so da
kuma kusanci zuwa ga Manzon Allah (S), kamar yadda ya zo a hadisi, Manzon Allah
(S) ya ce; “Wanda na fi so daga cikin ku, wanda ya fi kusa dani gobe }iyama, shine wanda ya
fiku kyawawan ]abi’u”.
ginuwa akan wannan tunani na samun son Manzon Allah (S) da kuma
kusanci gare shi, yana daga cikin hanyoyin da za su taimakawa mutum wajen samun
kyawawan ]abi’u.
Saboda haka, ma’auni na yadda mutum yake a wajen Manzon Allah (S) shine
kyawawan ]abi’u,
dai dai kyawawan ]abi’un
mutum, dai dai son Manzon Allah (S) gare shi da kuma kusanci da shi gobe }iyama.
Kuma kyawawan ]abi’u,
koda ba domin fa’idodinsu da kuma amfanoninsu masu yawan gaske ga mutum ba, a
addininsa da kuma lahiransa,to ko da a duniyan ce,ya kamata mutum ya siffata
dasu. kamar yadda ya zo daga Imam Ali (AS) ya ce; “ko da bamu }aunar aljannah, ba mu
kuma tsoron wuta, ba mu fatan samun lada
da kuma gudn u}uba,
duk da haka ya kamace mu, mu siffantu da kyawawan akhla}.”
5. Daga cikin
hanyoyin da za su taimaka wa mutum wajen samun kyawawan ]abi’u, shine sanin cewa, jarabawa daga
wajen mutane wani abune wanda ba makawa ga mutum
matu}ar yana raye.Shi yasa Yazo a hadisi cewa: Mutuwa hutu ne ga mumini. Saboda
haka, samun jarabawa daga wajen mutane ta fuskoki daban-daban sunna ce ilahiyya wadda ba makawa, hadisai masu yawa
sun yi nuni ga haka, ga wasu daga ciki, akwai lokacin da Imam Zainul abidin
(AS) yake cewa wani daga cikin mabiyansa: mutane in ka barsu ba za su barka ba,
In ka watsar da su ba za su watsar da kai ba, sai yace wa Imam zainul abidin
(AS); ‘to ya zan yi?’ sai ya amsa da cewa: “ka basu daga mutuncin ka, saboda gobe
}iyama”.
Wato mutum yayi ha}uri
daga cutarwar mutane, saboda sakamakon
da zai samu gobe }iyama.
An samo daga Imam sadi} (AS) ya ce; “Bai kasance a da ba, bai kasance a yanzu ba, kuma ba zai
kasance nan gaba, har zuwa tashin }iyama,
Annabi
ne ko mumini, face sai an samu wani yana cutar da shi. A wani hadisi makamancin
wannan da aka samo daga Manzon Allah (S) ya ce; “Bai kasance a da ba, ko a
yanzu, ko nan gaba, har zuwa tashin }iyama, ga Annabi ko mumini, face an samu wani ]an uwan sa na jini da ya
ke cutar da shi”.
An samo daga Imam
Ali (AS) ya ce; Manzon Allah (S) ya ce; “Da a ce mumini zai shiga wani rami
(wato saboda gujewa cutarwar
mutane) da Allah (T) ya salla]o masa wanda zai cutar da shi”.
A wata ruwayar da
aka samo daga Imam sadi} (AS)
ya ce; “Da mumini zai je ya hau tsororuwar dutse ya zauna (wato saboda gujewa matsalar mutane) da Allah (T) ya salla]o masa wanda zai
cutar da shi”.
A kuma wani
hadisi da aka samo daga Imam Ba}ir
(AS) ya ce; “Fari ya samu mutanan Annabi Hudu (AS), sai suka tafi wajen sa
domin yayi addu’ar Allah (T) ya saukar da ruwa. Suka je gidansa ba su same shi
ba, sai matarsa da ta fito, sai ta yi masu fa]a da hayaniya. Su ka ce, ‘to yana ina?’ ta
ce, ya tafi gona. Sai suka samu Annabi
Hudu (AS) a gona. Da suka isa sai suka ga duk idan ya yi kunya guda ]aya na shuka sai ya yi
nafila raka’a biyu. Ya dube su ya ce, ‘me nene bu}atar ku?’ su ka ce; ‘munzo wajen ka ne domin
wata bu}ata’, sai mu kaga abin da ya bamu mamaki’ sai ya tambaye su, me ya baku mamaki?
Suka ce; ‘Mun ga wata mata ta fito daga gidan ka, tana mana fa]a da haniya’. Sai Annabi
hud (AS) ya ce masu; ‘Ai matata ce, kuma duk da wa]annan ]abi’u nata, ina son ci gaba da zama da ita?’ Sai
ya ce masu, babu wani mumini face an samu wani da yake cutar da shi. Ni ina godiya ga Allah(T) da ya sanya mai cutar da ni,
yana }ar}ashin iko na ne, ba domin haka ba da Allah (T)ya salla]o min da wanda ya fita cutarwa”.
Akwai hadisai masu yawa ire-iren wa]annan masu nuni da
cewa cutarwar mutane ga mutum, wani abune wanda yake ba
makawa. Amma saboda gudun tsawaitawa, ba za a iya ci gaba
da kawosu ba. Sai dai mai bu}atar }arin
ganin wa]annan hadisai, yana iya duba littafi mai suna ‘mishkatil anwar fi guraril
akhbar
‘, na Abul-Fadhal at-tabrisiy. Shi ]a ne ga wanda yayi
littafin ‘Makarimul akhla}’ wato ta~-rasiy.
Tun da cutarwar
mutane ga mutum, wani abu ne lazim, matu}ar ya na raye, ashe ke nan siffantuwa da
kyawawan ]abi’u,
irin su ha}uri,
kau da kai, ha]iye
fushi, afuwa, kyawtatawa akan munanawa, da dai sauran kyawawan ]abi’o’I, wani abu ne
wanda yake da muhimmancin gaske, musamman ga wanda yake ma’abocin addini, domin
babbar hanya ce ta da’awa. Kuma wa]annan kyawawan ]abi’u,
mutum zai yi su ne saboda Allah (T) da kuma neman yardarsa, ba domin mutane su
yarda da mutum ba, ko su yaba maka.Domin mutane suna iya yaba maka yau, gobe su
soke ka. To, a nan mutum zai fahimci hikma da asrar na ikhlasi ga dukkan
ayyuka.
Misali, kana
kyautata wa mutum saboda Allah (T), sai wata matsala ta shiga tsakaninka da
shi. To, idan mu’amalar ka da shi, akan asasin ikhlasi ne, to baza ka damu ba
wajen ci gaba da kyautata masa, sa~anin ko idan mu’amalar ba akan ikhlasi ba ne, da an samu sa~ani shi ke nan, sai kyautatawar ta yanke. Ya ma zo a hadisi
cewa, mutum ya sadar ga wanda ya yanke masa. Ya bai wa wanda ya hana masa. Ya
yi afuwa ga wanda ya zalunce shi, kuma ma in mutum ya dubi wasu kyawawan ]abi’u da Manzon
Allah (S) ya samu mutanen jahiliyya a kai, kamar fa]ar gaskiya, ri}on amana, cika al}awari, sadar da zumunci, da dai sauransu,
musulunci ya tabbatar da wa]annan ]abi’un,
abin da ya }ara a
ciki shine ikhlasi. Wato wannan fa]in
gaskiyar, da ri}on
amana, da cika al}awari, da sadar da zumunci, da dai sauransu, to mutum yayi su saboda Allah (T),
ba domin kada a soke shi a ce ma}aryaci, mai cin amana, mai sa~a
alkawari, ko bai da zumunci ba.
Kuma in mutm ya
dubi Ayoyin da suka sauka a makkah, baya ga maganar a}ida da suke yi, wato tauhid, nubuwwah da kuma
ma’ad, da kuma }issoshi
na annabawa, zai ga suna magana kan akhla} ne, wanda
kuma an ga tasirin
akhla} ]in,a
lokacin da Manzon Allah (S) ya koma Madinah, a al’amarin ha]a ‘yan –uwan-taka tsakanin
muhajirin da kuma ansar. Kuma }arfin juriyar mutum a
bisa cutarwar mutane gare shi, yana nuna ikon sa, akan
nafs ]in sa
da kuma shai]an. Saboda haka, mujahada wajen samun
sul ]a
(iko) a kan nafs da kuma shai]an, wani abu ne wanda ya ke da gayar muhimmanci, kuma mafi }arancin kyautatawa da
mutum zai yi ga mutane ‘yan uwansa, musamman ma ‘yan uwansa muminai, shine ya
zamanto bai cutar da su ba da zuciyarsa ko harshensa ko hannunsa. In kuma su
suka cutar da shi, ya daure, ta wata mahangar, ni’ima ce gareshi saboda gobe }iyama, Allah (T) zai ba
shi sakamako akan wannan cutarwa da aka yi masa da kuma juriyar da yayi akai.
Domin sakamakon da Allah (T) zai ba bayinsa gobe }iyama,
sun kasu kashi uku:
1.
Sakamako da zai bayar na taklif da ya aza wa bayinsa, wato umurce-umurce da kuma hane-hane, wato
sakamako akan yadda kowa ya tsayu da wannan taklif.
2.
Sakamako akan jarabobin da ya
jarabta bayinsa da su,wannan jarabawa tana da fuskoki daban-daban; ]aya daga ciki shine: jarabawa na tsakanin mutum da mutane ‘yan uwansa.
3.
Sakamako na judiL-lLahi[wato bai
wa daga wajen Allah] wanda irin wannan sakamako ba kowa ke samun sa ba, wasu
daga cikin bayin Allah (T) ne yakan za~a, yayi masu sakamako
na musamman daga wajensa, saboda yadda suka tsayu da kuma kai wa gaya wajen tsayuwa da taklif, da kuma cin
jarabobin da suka yi, wanda Allah (T) yayi masu a wannan gida na duniya. Saboda haka cutarwar mutane a zahirance
mutum zai ga matsala ne, amma a ba]inance alheri ne.
Wannan ke nan dai a ta}aice dangane da hanyoyin da mutum zai bi domin ya tsarkaka daga munanan ]abi’u, da kuma hanyoyin da zai bi domin siffanta da
kyawawan siffofi.
No comments:
Post a Comment