Watan sha’aban da muka fita,kamar yadda aka sani,a cikinsa
ne aka haifi Imam Mahdi [AF],saboda haka ne mabiya Ahlulbayt [AS] a sassan
duniya daban daban ke gabatar da tarurruka,domin tunatar da juna dangane da ~angarori daban
daban da suke da ala}a
da Imam Mahdi [AF].misali,wiladarsa,gaiba ]insa,shaksiyya
]insa,alamomin
bayyanarsa,bayanai da rubuce rubuce na malaman madrasah ]in Ahlus sunna dangane dashi,da dai
sauransu
.Akan asasin haka ya zama zai yi kyau da kuma muhimmanci kawo wasu daga
cikin bayanai da kuma rubuce rubuce wa]anda
shehu usman ]an
fodio yayi dangane da Imam Mahdi [AF]. Shehu usman ]an fodio [da yake
yadda sunan ya kamata ya kasance shine,shaikh bn fudi,amma kasantuwar galibi
haka ake fa]i
ko rubutawa] ya rubuta littafai masu yawa dangane da Imam Mahdi ] 1.AL-KABARUL HADI ILA AMRIL IMAMIL
MAHDI. 2.TAHZIRUL
IKHWA’AN MIN IDDI’AA’IL MAHDIYYATIL MAU’UDATI,AKHIRAZ ZAMAN. 3.ALAMATI
KHURUJUL MAHDI. 4.ULLUW
SHA’ANI MAHDI. 5.TANBIHUL-FAHIM
da dai sauran wasu littafai da ba za’a iya kawowa ba,saboda gudun tsawaitawa. Haka
nan ]an sa
Shaikh Muhammad Bello ya rubuta littafai hu]u
da suka shafi Imam Mahdi [AS].Ga biyu daga ciki: 1.KASHFUL
KAFIYYI FI AK-BARIL IMAM MAHDI. 2.AL
{AUL MUK TASAR
FI AK-BARIL MAHDI AL-MUNTAZAR. Haka
nan ‘yarsa mai suna Maryam,ita ma ta rubuta littafi [aya,da ya shafi Imam Mahdi [AS] mai
suna DARI{UL HI JRATI ILA MAHDI.Haka nan jikansa
mai suna Sa’id ]an
Muhammad Bello,shima ya rubuta littafan da suka shafi Imam Mahdi
[AF].Misali,daya ]aga
ciki shine SAHIHUL KHABAR FI AMRIL MAHDI AL-MUNTAZAR. Wannan
kuma banda wa]anda
almajiransa suka rubuta da kuma ]an
uwansa Shaikh Abdullahi.Wanda im mutum yayi zuzzurfan bincike zai ga cewa samun
nahiya a duniyar sunna,wa]anda
malamanta suka yi littafai da suka shafi Imam
Mahdi [AF] kamar wannan nahiyar da wahala.Mutum ya ]an bincika wasu }asashen musulmi na
duniyar sunna ya gani. Kuma
wani abun mamaki shine,idan mutum ya bibiyi
wa]annan
littafai da shehu ]an
fodio ya rubuta dangane da Imam Mahdi [AF],zai ga cewa sun yi muwafa}a da yadda
suka zo a madrasah ]in
Ahlulbayt[AS],misali kamar yadda ya kawo shekara da watan haihuwar Imam Mahdi
[AF] da nasabarsa da alamomin bayyanarsa da dai sauransu.kamar yadda za muga
hakan insha Allah nan gaba cikin rubutun.Saboda haka ne ma aka samu wasu a
wannan zamanin, nan da can,a bayanansu da rubuce rubucensu,da su kayi }o}arin kawo tawili
a wa]annan
rubuce rubucen na shehu ]an
fodio,domin ganin sun yi kama da yadda shi’a suka tafi akai.Wa]anda kuma basu
iya tawilantar dasu ba.sun nuna cewa shehu usman ]an
fodio ya dawo daga wadannan ra’ayoyin }arshen
rayuwarsa ne,domin idan mutum ya dubi malaman Ahlus sunnah da suka yi littafai
dangane da Imam Mahdi [AF] zai iya kasa su gida uku. 1.Akwai wa]anda abin da suka
rubuta yayi muwafa}a
da abinda shi’a suka tafi akai. 2.Akwai wa]anda abin da suka
rubuta yana kusa da abinda shi’a suka tafi akai. 3.Akwai wa]anda abin da suka
rubuta yayi karo da abinda shi’a suka tafi akai,misali kamar yadda wasu daga
malaman Ahlus sunna suka tafi akai na cewa Imam Mahdi, ba’a haife shi ba,ko
kuma an haife shi yayi zamani ya wuce,da dai sauransu. Amma
idan muka duba shehu ]an
fodio,ya fuskanci jarabawa daban daban a zamaninsa,musamman bayan tabbatuwar
addini,na cewa shine Mahdi,domin an samu jama’a da dama a lokacin da suka tafi
akan cewa shine Mahdi.kuma babban abinda daya da]a
karfafa wa masu wannan ra’ayi,baya ga tabbatuwar addini }ar}ashin jagorancinsa,shine abinda
yazo a cikin wani littafi na Jalaluddin As-suyu]i
mai suna “AL-IR{UL
WARDIY FI AKHBAARIL IMAMIL MAHDI”.Na cewa Imam Mahdi zai bayyana ne a shekara
ta 1200 hijiriyya,ko kuma a shekara ta 1204 hijiriyyah.Ga shehu ]an fodio kuma ya
rayu ne a dai dai wancan lokacin ga kuma Allah [T] bisa ikonsa ya tabbatar da
addini }ar}ashin
jagorancinsa,ga kuma wannan hasashe na suyu]i.Saboda
haka akan asasin wa]annan
dalilai aka samu jama’a da dama suka ce ai shine Mahdin.Amma nan take shehu
yayi inkarin wannan abu da tsananin gaske,kuma ya rubuta littafai don gamsar da
mutane cewa bashi bane Imam Mahdi [AF],kamar yadda zamu ga haka a nan gaba.Saboda
haka bayan wannan shimfi]ar
insha Allah rubutun zai gudana ta fuskoki guda uku. 1.Bayanan
shehu ]an
fodio dangane da Imam
Al-Mahdi [AF]. 2.Inkarinsa
na cewa shine Mahdi. 3.Ala}arsa da Imam
Mahdi [AF]. 1.BAYANAN SHEHU [AN FODIO DANGANE DA IMAM MAHDI [AF].
Idan aka duba littafinsa mai suna NASIHATU AHLIZ
ZAMAN.Mutum ya duba fasali na bakwai a cikin littafin,wanda shine fasali na }arshe a littafin;taken fasalin shine,fasali na bakwai
cikin ambaton al’amarin Imam Al-mahdi,wanda shine halifa na }arshe”.A cikin fasalin shehu usman ]an fodio yana cewa, “ku sani yaku yan uwana,bayyanar
Imam mahdi [RA] wani al’amari ne wanda yake yankakke [wato tabbatacce],domin
hadisai akan haka sun kai haddin tawatur.kuma kasancewarsa daga zuriyar fa]imatu ‘yar Manzon Allah [S],shima abune yankakke
domin hadisai akan haka sun kai haddin tawatur”.A wani sashe na fasalin yana
cewa, “Ku sani ba makawa daga bayyanar Mahdi [AS],amma bazai bayyana ba har sai
}asa ta cika da zalunci da danniya,sannan ya
cika duniya da adalci,kuma koda ba abin
daya rage a kwanukan duniya sai yini ]aya,to Allah [T] zai tsawaita yinin,har wannan
khalifa ya ji~ince ta.kuma yana daga itrar Manzon Allah [S]
ne,daga ‘ya’yan fatima [RA], kuma mahaifinsa shine Al-hassan Al-askari ]an Imam Aliy An na}iy,]an Imam Muhammad At-ta}iy,]an Imam Aliy Arrida,]an Imam Musa Al-kazeem,]an Imam Jafar As-sadi},]an Imam Muhammad Al-ba}ir,]an Imam Zainul Abidin Ali,]an imam Hussain,]an Aliy ]an Abi Talib [AS]”. Haka nan kuma a wani sashe na
fasalin da yake bayani dangane da haihuwar Imam Mahdi [AF] yake cewa, “Haihuwarsa
[AS] ta kasance daren 15 ga sha’aban shekara ta 255,kuma yana wanzuwa [raye]
har zuwa lokacin da zasu ha]u da Isa ]an maryam [AS]”. Idan
muka duba,ko da daga wa]annan abubuwa da aka kawo,dukkansu sunyi muwafa}a da yadda suka zo a madrasah ]in Ahlulbayt [AS].Misali,yadda ya kawo nasabar
Imam Mahdi [AS],da kuma wata da shekarar haihuwarsa,da kuma cewa ba zai bayyana
ba har sai duniya ta cika da zalunci da danniya,da kuma bayyana shi a matsayin
khalifan Manzon Allah [S] na }arshe. Akwai ma in da yake cewa
a cikin fasalin, “shi Imam Al-mahdi yana daga cikin wanda wajibi ne abi
sunnarsa,domin shi yana daga cikin khulafa’ur Rashiduna Almahdiyyin,shine ma na
}arshensu”. Haka
nan ma awani sashe na fasalin yana cewa, “amma ayyana lokacin bayyanarsa,ace
sa’a kaza ko rana kaza ko shekara kaza,ba wanda yasan haka in ba Allah [T] ba”. Idan
kuma muka ajiye wannan littafin muka ]auko littafinsa mai suna AL-KHABARUL-HADI ILA
AMRIL IMAMIL MAHDI,a cikinsa ya kawo al’amura daban daban guda 10 wa]anda suke da ala}a da Imam Mahdi [AF].Misali,inda yake cewa,
“al’amari na shida sanin cewa lalle Mahdi [RA] yana raye”. Shehu ]an fodio ba kawai ya tafi akan Imam Mahdi yana
raye bane,wuce nan.ya tafi akan akwai yiwuwar a sadu dashi.mutum ya duba a
cikin littafin,al’amari na 10, ya kawo }issar wani bawan Allah [T] daga madrasah ]in Ahlus sunna,wanda ya ha]u da Imam Mahdi [AS],ga mai bu}ata yana iya duba littafin da yake }issar na da tsawo,kuma a }arshe shi wannan littafi in mutum ya duba zai ga
yadda shehu ya kammala wannan littafin da addu’ar cewa, “ya Allah ka }addara mana saduwa dashi,da kuma ha]uwa dashi ta ‘hissi’,wadda take tabbatuwa da
gangar jiki,kamar yadda ka }addara mana ha]uwa dashi ta ma’anawiy”. Wanda wannan
shima bai sa~a wa yadda malaman madrasah ]in Ahlulbayt [AS] suka tafi akai ba,wato na
yiwuwar ha]uwa da Imam Mahdi [AF].Ba domin saboda gudun fita
cikin maudu’in ba,da an kawo wani misali na wasu bayin Allah [T] daga madrasah ]in Ahlulbayt [AS] da suka samu baiwar ha]uwa da Imam Mahdi [AS]. Wannan
kenan dangane da bayanan da shehu ]an fodio yayi game da Imam Mahdi [AF].Mutum ya
kwatanta su da yadda suka zo a shi’a zai ga duk sun yi muwafa}a. 2.INKARINSA NA CEWA SHI NE IMAM MAHDI [AS]:
Kamar yadda ya gabata cewa wannan ya kasance
babbar jarabawa ga shehu a lokacin,domin a lokacin in mutum ya bibiyi tarihinsa
zai ga yayi iya iyawarsa ta hanyan rubuce rubuce,jawabai kai har ma da wake,domin a lokacin su mutane ne masu zau}in wa}e,domin ya gamsar dasu cewa shi ba shi ne Imam Mahdi
ba.misalin littafi daya rubuta akan haka shine mai suna TAHZIRUL IKHWAAN MIN
IDDI’AA’IL MAHDIYYATIL MAU’UDAH AKHIRAZ ZAMAN.In mutum ya duba littafin akwai
in da yake cewa, “kusani yaku yan uwa cewa bani ne Imam Mahdi [AS] ba,kuma ban ta~a da’awar cewa ni Imam Mahdi ne ba,na kan ji
haka a bakunan mutane,kuma na yi iyakar }o}ari na domin yi musu kashedi akan haka,kuma na
bayyana raddina akan haka a wallafe wallafena na Arabiyya da kuma Fulatanci”. A
wani waje a littafin yana cewa, “yaya zan yi da’awar ni Mahdi ne? alhali an
haife ni a Biladus Sudan a wani wuri da ake cewa ‘Marad’ kuma yaya zan yi
da’awar cewa ni Mahdi ne,alhali sunana bai dace da sunan Annabi [S] ba,domin
sunana Usman,kuma sunan mahaifina bai dace da sunan mahaifinsa ba,domin sunan
mahaifi na muhammad.kuma an riga an sani a cikin hadisan Annabi cewa Al-mahdi
sunansa ya dace da sunan Annabi” a wani waje kuma yana cewa “Imam Mahdi yana da
siffofi da kuma asrar,wanda ni bani dasu.”da dai sauran bayanai wanda saboda
gudun tsawaitawa baza a iya kawo su ba,wanda shehu ]an fodio yayi domin raddi ga masu irin wannan
tunanin a lokacin. 3.ALA{ARSA DA IMAM
MAHDI [AF]:
Tabbas idan mutum ya bibiyi tarihi da kuma
rayuwar shehu usman ]an fodio zai ga yana da ala}a babba kuma ta musamman da Imam Mahdi
[AS].Akwai ma in da yake cewa, “Allah [T] yayi mani baiwa da sanin Imam Mahdi da koyi dashi”.idan
mutum ya duba tarihinsa zai ga ya kasance mai gayar tawali’u ga Imam Mahdi [AS].kuma
ya kasance mai gayar shau}i gare shi,akwai }asidodi na wa}e da yayi da harshen fulatanci na yabo da kuma bayanin
darajojin Imam Mahdi [AS].kuma akwai in da yake cewa, “wannan jihadin da nayi
da izinin Allah har sai ya dangana da zuwan Imam mahdi”.kuma yana cewa wannan
abu da yayi shimfida ne ga zuwan imam Mahdi [AS],kuma shehu usman ]an fodio ya bar wasiyya ga ‘ya’yansa da
jikokinsa da zuriyarsa baki ]aya da sauran jama’a, a lokacin cewa idan Mahdi
ya bayyana su kasance tare da shi, su kuma taimake shi,da kuma yin hijira zuwa gare
shi.Wannan wasiyya ta shehu ita ta san ya jikansa mai suna Hayatu ]an sa’id ]an muhammad Bello,lokacin da wani a Sudan ya bayyana
yayi da’awar cewa shine Mahdi [wato wanda ake cewa mahdin sudan,wannan ya faru shekaru
50 bayan rasuwar shehu ]an fodio],sai shi wannan jikan shehu ]an fodio ya bar sakkwato zuwa sudan da nufin
taimaka masa,har ma da ya sadu dashi yake ce masa “lalle na yi maka bai’a ni da
‘ya’yana da dukkan wa]anda suke tare dani”.Ya ci gaba da ce masa, “ha}i}a shehu usman ]an fodio yayi mana wasiyya da hijira zuwa
gareka,da taimakon ka da kasantuwa tare da kai idan ka bayyana”. Duk
da an samu malamai a sakkwato a lokacin da suka yi inkarin haka,na cewa abin ba
gaskiya bane,amma wannan abin da yake nunawa shine irin yadda shehu ya gina ‘ya’yansa
da jama’arsa, na su taimaka wa Mahdi [AS] idan ya bayyana.kuma mu duba yadda
shehu ]an fodio yayi tsayin daka wajen inkarin masu
cewa shine Mahdi,,misali akwai in da yake cewa “wanda yake riyawar ni ne Mahdi
da sannu zata bayyana ba haka bane,don na bayyana siffofin Imam Mahdi [AS]”.wannan
a wasu baitocin wa}e yake fa]in haka,a wani wuri a wa}en yana cewa, “ina garga]inku,kuma ina ro}onku don Allah mai girma, ku kame daga fa]in cewa ni ne Mahdi”da dai sauran bayanansa wa]anda ba za’a iya kawowa ba,saboda gudun
tsawaitawa.da suka nuna ala}arsa da Imam Mahdi [AS].Daga }arshe akwai darasi babba da zamu koya daga wa]annan rubuce rubucen na shehu usman ]an fodio dangane da Imam Mahdi [AS],shine
zuzzurfin bincike da yayi kan wanna abu,domin idan mutum ya bibiyi wadannan littafai
da aka ambata a sama wa]anda ya rubuta dangane da Imam mMahdi [AS],zai ga
ya dogara ne da masdarorin Ahlus sunna,domin kaiwa ga wannan sakamako.wato
bincike yayi mai zurfi,duk ko da }arancin wasa’il na ilimi da ake dashi a zamanin
da kuma rashin hanyoyin sadarwa,to, ina ga wannan zamanin da muke ciki mai cike
da wasa’il daban daban na ilimi da kuma hanyoyin sadarwa,saboda haka yana da
muhimmanci mu tashi tsaye domin amfanuwa da wa]annan wasa’il daban daban na ilimi,domin kai wa ga
irin wa]annan natijoji,da fatan Allah [T] ya amfanar damu da
abubuwan da aka karanta amin.
No comments:
Post a Comment