Sunday 3 February 2013

Darussa 12 daga rayuwar Imam Ridhah [AS].


Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Zul }ada a cikinsa ne wilada da kuma wafatin Imam Ali ibn Musa Ar-Ridah[AS]suka kasance,domin yazo a tarihi cewa an haife shi ranar Alhamis 11 ga watan zul }ada a shekara ta 148 bayan hijira.Ya rasu 23 ga watan zul }ada shekara ta 203 bayan hijira.Amma a wata ruwaya,yazo a kan cewa rasuwarsa ta kasance a watan safar ne
.Shaikh Abbas Al-}ummiy  ya tafi akan 23 ga watan zul }ada, kamar yadda ya kawo a littafinsa na mafatihul Jinan.Har ya ci gaba da cewa sunna ne ziyarar Imam Ridha[AS]a ranar daga kusa ko kuma nesa.In mutum ya duba littafin mafatihul jinan zai ga ya kawo  ziyarori dabam-dabam na Imam Ridha[as].In mutum zai iya biya su duka a ranar yana da kyau,ko kuma ya karanta abinda ya sau}a}a masa na ziyarar.                                                                                                   Haka nan in aka duba za a ga cewa tsakanin haihuwar Imam Ridha[AS] da rasuwar Imam Sadi}[as]Kusan kwanaki 15 ne.Domin wafatin Imam Sadi}[as] a watan shawwak ne 25 gare shi,shekara ta 148,shi kuma wiladarsa 11 ga watan zul }ada shekara ta 148.Ya mazo a kan cewa Imam Sadi}[as] yayi fata da shau}in ha]uwa da Imam Ridha[as]domin  ya gan shi,har ambatonsa yayi da kalmar MALAM,tun gabanin a haife shi,kamar yadda zamu ga haka in sha Allah dangane da bayani na ilminsa.                                              Imam Ridha[AS]kamar yadda aka sani shine Imam na takwas a jerin Imamai 12,an haife shine a Madina,sunan mahaifiyarsa, [ahira,sunan mahaifinsa kamar yadda aka sani Imam Kazim[AS]kuma yana da la}ubba da yawa,amma  wanda  yafi  shahara  shine  wannan  la}abi nasa  na Arri-dha.An tambayi Imam Jawad[AS]cewa mi  yasa ake cewa babanka  Arri-dha,ya  ba da  amsa da cewa;Saboda ma}iyan sa sun yarda da shi,kamar yadda masoyan sa suka yarda  dashi.yace haka bai kasance  ga Imamai da suka gaba ce shi ba.Shekarunsa  a  duniya 55,muddan shekarun Imamancinsa 20,wato ya na da shekaru 35 a duniya Imamanci ya dawo gare shi.kabarinsa yana a khurasan ne,wato a }asar Iran.Kuma  yaro ]aya yake da shi shine,Imam  Jawad[as]idan mutum ya bincika zai ga cewa Imam Ridha[as]shine mafi }arancin’ya’ya, idan an kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa,in ka ]ebe Imam Hasan Al-askari[as]da yake yazo akan cewa shima yaro ]aya yake dashi,shine Imam Mahdi[AF].                        
Ga  adadin ‘ya’ya na kowane daga cikin A’imma na Ahlulbayt [AS].Imam Aliy [AS] ‘ya’ya 25,maza 11,mata 14.Imam Hasan [AS] 15,maza 8,mata 7.Imam Husain [AS] ‘ya’ya 7,maza 4,mata 3.Imam Zainul Abidin [AS] 16,maza 12,mata 4.Imam Ba}ir [AS] 7,maza 5,mata 2.Imam sadi} [AS] 10,maza 7,mata 3.Imam Kazim [AS] 36,maza 17,mata 19.Imam Ridah [AS] yaro namiji guda ]aya.Imam Jawad [AS] 4,maza 2,mata 2.Imam Hadi [AS] 5,maza 4,mace 1.Imam Hasan Al’askari [AS]yaro guda ]aya,shine  Sahibuz- Zaman,Imam Mahdi [AS].Allah Ta’ala ya  gaggauta  bayyanarsa.Sayyida Fa]imah [AS] 5,maza 3,mata 2.Sai kuma fiyayyen Halitta,wato  Manzon Allah [S] 7,maza 3,mata 4.                                                                    Sai dai tambihi anan shine,kamar yadda akan samu bambancin ruwayoyi na shekara ko wata ko rana na haihuwar ]aya daga cikin Ma’asumai [AS],ko kuma wafati,to,haka nan akan samu bambancin ruwayoyi na adadin ‘ya’yansu.Saboda haka babu mamaki mutum yaga wata ruwaya akasin yadda aka kawo adadin anan,wannan ruwaya na adadi da aka kawo,itace wadda mai littafin A’IMMATUNA ya tafi a kai.                                                                                                                                                                          
Saboda haka kamar yadda aka ambata,in mutum ya duba zai ga Imam Ridah [AS] da kuma Imam Askari [AS] kowannensu na da ]a ]aya ne,wanda kuma yafi yawan ‘ya’ya a cikin A’imma [AS],shine Imam kazim [AS],domin yana da ‘ya’ya 36.Sai dai wani tsokaci anan shine,wa]annan ‘ya’ya mata na Imam kazim [AS] su 19 a wata ruwaya 21,dukkansu ba wadda ta ta~a yin aure har suka koma ga Allah[T].Malaman tarihi sun kawo dalilai na rashin yin aurensu,in Allah [T] ya kai mu munasabar shahadar Imam kazim [AS] za’a kawo wa]annan dalilai.Sai dai kasantuwar wannan wata da muke ciki na Zul }adah,Ranar farko na watan ne aka haifi Sayyida  Ma’asuma [AS],wato wadda  kabarin ta ke birnin -}um,ita ce kuma babbar ‘yar Imam kazim [AS].}an-wa ke nan take ga Imam Ridha[AS]saboda haka,Anan  tabarrukan  za’a kawo tarihinta a ta}aice.                                                                                                                          1.WILADARTA: Watau haihuwarta,an haife ta a madina,1 ga watan zul }adah,Hijira ta 173.                               2.NASABARTA: Mahaifinta shine Imam kazim [AS],sunan mahaifiyarta [ahira,wato mahaifiyarsu  ]aya da Imam Ridah [AS],kuma ita wannan mahaifiya tasu,[ahira bai war Allah ce mai yawan ibada, kamar yadda yazo a tarihinta.Ya mazo a tarihinta cewa,lokacin da ta haifi  Imam Ridah [AS] ta bu}aci a nemo mata mai raino,aka tambaye ta dalili,sai tace ibadodin da ta saba yi sun ragu,saboda haka tana bu}atar taimakawa wajen reno domin ta cike gi~in ibadodinta.Kakanta shine Imam Sadi} [AS].Yazo akan cewa tun gabanin a haife  ta yayi albishir da haihuwarta da kuma fa]in falalar ta da kuma  ziyarar  ta.                          Daga cikin falalar ta da Imam Sadik [AS] ya fa]i,akwai  cewa tana da matsayi a wajen Allah [T].Shi yasa wanda duk Allah [T] yayi wa muwafa}a da ziyarar haramin kabarinta dake birnin }um,a kofar shiga haramin  zai ga an rubuta “Ya Fa]ima ki ce ce ni a wajen Allah,domin ki na da matsayi a wajensa”.Allah Ta’ala ya saka mu cikin wa]anda zata ceta.                                                                                                         3.LA{UBBANTA: Tana da la}ubba masu yawa,amma biyun  nan su suka  fi  fice,sune Karimatu- Ahlulbayt  da  kuma Ma’asuma.Wannan la}abi na Ma’asuma yazo akan cewa Imam Ridah [AS] yayi mata la}abi da shi,wanda wannan yana alam ta, gayar kamalar ta da kuma matsayin ta.         4.FALALAR ZIYARAR KABARINTA: An samo daga Imam Ridah [AS] cewa duk wanda ya ziyarce ta,Aljanna ta tabbata a gare shi.Haka nan makamancin wannan Hadisin,an samo daga Imam Jawad [AS] cewa duk wanda ya ziyarce ta,Aljanna ta tabbata gare shi.                                                                                                     5.KARAMOMINTA: Ma’asuma [AS] ta kasance  ta na da karamomi masu yawa,tun tana raye da bayan wafatinta,kai har wannan zamanin namu kullum karamominta da]a bayyana suke.Za kaga masu ziyararta, zasu yi tawassuli da ita kan bu}atocin su,kuma ka ga Allah ya biya musu bu}ata.marasa lafiya zaka  ga an kawo su,ayi tawassuli da ita,ka ga Allah ya basu lafiya.shi yasa wani daga cikin malaman tarihi yake cewa babu wani daga cikin ‘ya’yan ma’asumai [AS] da yake da karamomi masu yawa kamar ta.Haka nan yau a doran }asa babu wata bai war Allah da take samun masu yawan ziyara kamar yadda take samu.Domin idan mutum yaje Haramin ta zai ga dare da rana maziyar ta ne,daga cikin karamominta daya bayyana  a  wannan  zamanin  namu  a shekarun baya,shine  akwai  gyaran  ainihin shi kabarin ta da akayi ,aka za~i manyan malamai daga ciki akwai Ayyatullah Najafi Almar’ashi,shine yake cewa babu wani abun daya canza na likkafanin ta da kuma jikinta,yace kamar kace yau aka sata.                                                                    
6.JARABAWOYIN TA: Ma’asuma [AS] ta fuskanci jarabawoyi masu yawa a rayuwarta,musamman a }arshen rayuwarta,misali  bankwana  da kuma zafin rabuwa da ]an uwanta Imam Ridah [AS] lokacin da zai bar madina zuwa khurasan,tafiya wadda ba zai dawo ba,kamar yadda ya shaida masu.Duk da sun yi  bankwana,amma  ta hau soron dakin na gidansu, tayi ta kallon Imam Ridah [AS] har ta dai na ganinsa,kuma wannan shine }arshen ganinta da Imam Ridha,a gidan duniya domin bayan haka basu sake ha]uwa ba.Ala}a da kuma sha}uwa na Imam Ridah [AS] da Sayyida Ma’asuma,kamar  ala}a  da kuma sha}uwa na Imam Husain [AS] da  kuma Sayyida Zainab [AS]ne. Bayan haka  ga kuma jarabawar mahaifinta, wato Imam kazim [AS] da ta gani na zamansa a kurkuku da kuma shahadarsa  a ciki, da dai sauran jarabawowi masu yawa da ta  fuskanta,wanda ba za’a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.                      
7.ILIMINTA:Sayyida  Ma’asuma [AS]  ta kasance mai yawan ilimi,akwai wani abin da ya ta~a faruwa,wanda ya nuna matsayinta a ilimi wannan abin ko shi ne akwai wani lokacin da wasu daga cikin mabiyan Imam kazim [AS] suka zo daga garinsu zuwa madina,domin su ga Imam kazim [AS] su gai she shi,su  kuma gabatar da wasu tambayoyi, da suka zo madina suka isa gidan Imam kazim [AS]sai suka samu bai nan yayi tafiya,sai suka rubuta tambayoyi  suka ba Sayyida Ma’asuma [AS] cewa in ya dawo ta bashi,kashe  gari sai suka dawo suka samu bai dawo ba,alhali su kuma suna son su koma garinsu a ranar,sai  Sayyida Ma’asuma [AS] ta rubuta masu amsoshin  tambayoyin, suka  amsa  suna farin ciki.Kan hanyarsu ta komawa sai suka ha]u da Imam kazim [AS] yana dawowa sai suka shaida masa ma}asudin zuwan su da kuma abinda ya faru sai Imam Kazim [AS] yace su kawo amsar takardar ya gani,bayan ya gani ya fa]i wannan kalmar sau uku, “ta fanshi babanta”.                                                                                   
8.IBADARTA: Ta kasance mai yawan ibada.Hatta in da take yin ibadar ta,salloli da makamantansu yana nan har yanzu a birnin }um ana ma kai ziyara wajen.                                                                                                     
9.WAFATINTA: Ta rasu tana da shekaru 30 a duniya,sababin rasuwar ta shine; ta bar madina ita da wasu ‘yan uwanta da nufin su tafi khurasan wajen Imam Ridah [AS], akan hanya a wani waje mai suna SAWA rashin lafiya ya kama ta,ta bu}aci a tafi zuwa }um,da suka isa kwanan ta 17 Allah yayi mata rasuwa.         Wannan dai a ta}aice kenan dangane da Tarihin Sayyida Ma’asuma[AS]                                                                                                                                                                                                              
Bayan haka,anan insha Allah za’a kawo darussa 12 daga rayuwar Imam Ridah [AS] da nufin ya zama madubin da zamu dubi kawukanmu dashi da kuma yin sa’ayi da kuma mujahada wajen ganin mun aikata su, domin su amfane mu duniyarmu da kuma lahirarmu.                                                                                                                1.IBADARSA: Imam Ridah [AS] ya kasance mai yawan ibadah,domin a zamaninsa babu wanda ya kai shi yawan ibadah,ga misalan wasu daga cikin ibadodinsa.                                       
A.SALLOLINSA: Imam Ridah [AS] ya kasance mai yawan salla,yazo a tarihinsa cewa ko wane dare ya kan yi salla ta nafila raka’a dubu,wato yana ]aya daga cikin Imamai guda hu]u wanda a tarihin rayuwarsu yazo akan cewa kowane rana suna salla raka’a dubu ta nafila.Wa]annan Imaman  kuwa sune,  Imam Ali [AS],Imam Husain [AS],Imam Zainul Abidin [AS],da kuma Imam Ridah [AS].ya ma ta~a ba wani daga cikin mabiyansa rigar sa,Imam Ridah [AS] yace masa, “ka kiyaye wannan rigar domin na yi sallah dare dubu da ita,ko wane dare raka’a dubu,kuma na sauke Alkur’ani  sauka dubu da ita”.Mu duba wannan yawan ibada, mu kuma kwatanta da kawukanmu mu ga gi~in dake tsakani.                                                                                                     Haka nan yazo a tarihinsa cewa da daddare ka]an yake bacci,mafi yawan darensa yakan raya da ibadodine,wasu dararen ma, baki ]ayansu yakan raya sune.An tambayi ]aya daga cikin matayensa dangane da ibadarsa,tace ya kasance idan  yayi sallar Asuba,yakan sallace  ta  a farkon lokacinta,ya kan yi  ta’a}ibat [Azkar bayan sallah]bayan haka yayi sujuda ba zai ]ago kai ba har sai rana ta keto.Akwai ma wani da ya ta~a  ganinsa bayan ya gama sallah,sai yaga yayi sujuda,sai yaji yana tasbihi,sai shi wannan mutumi ya shiga lissafa tasbihin, sai da ya lissafa guda 500,saannan yaga ya ]ago daga sujudar.                                                          
B.KARATUN - }UR,ANI-Imam Ridha[AS] ya kasance mai yawan karatun }ur’ani,domin yazo a tarihinsa cewa ya kan sauke shi a duk kwana ukku.Har ma ya kance;Da ina so in sauke }asa da kwana ukku da na sauke,amma in, ina karatunsa,duk ayar da na biya na kan tunani a kan me ta sauka?kuma yaushe ta sauka?Saboda haka nake sauke shi kwana ukku.’’Kuma yazo a tarinsa cewa,zantukansa baki ]aya da kuma amsoshin tambayoyi da aka yi masa,ya kan bada su, da Ayoyin Alkur’ani ne.Wato shigen }issar wata bai war Allah, mai suna FIDDHA,ta kasance tana yiwa Sayyida Fa]ima[AS]hidima ne,To yazo a tarihinta ta shekara 30 bata yi magana da wani abu ba face ayoyin Ayoyin Alkur’ani.Misali ko abu take so sai ta fa]e shi da wata aya da tayi kama dashi domin a fahinta.A ta}aice dai Imam Ridha[as]ya kasance mai yawan karatun Alkur’ani.Mu duba abinda aka ambata  a sama na rigar daya ba, ]aya daga cikin sahabbansa,yace masa ya sauke Alkur’ani da ita sauka dubu.
C.AZUMINSA: Imam Ridah [AS] ya kasance mai yawan azumi,kuma azumi na kowane wata basu ku~uce masa,wato ya kasance yana lizimtarsu, a zumin shahariyya[wata-wata] Sune Alhamis ]in farko na ko wane wata da kuma Alhamis ]in }arshe da kuma larabar farko ta goman tsakiya,ya kance duk wanda ya lizimci wannan azumin,to kamar yana azumin kullum ne.Kuma yazo a tarihinsa cewa in yayi azumi baya bu]e baki sai yayi sallah.
D.ADDU’O’IN SA:Imam Ridah [AS]ya kasance mai yawan addu’oi,akwai adduoi da yawa wanda aka ruwaito daga wajensa.Mai bu}atar wa]annan addu’oi  yana  iya samun littafin addu’a mai suna SAHIFATUR -RIDHA,wanda wani malami mai suna shaikh Jawad  }ayyumiy, ya rubuta.Ana samun sahifa ]in.                                                                                                                                                                                                                     Sai dai wani tambihi  muhimmi  anan shine;akwai wata addu’a da aka samo daga Imam Rida [AS] wanda yayi umarni da a din ga  biyawa, ga Sahibul-Amr wato Imam mahdi [AF].Saboda haka ya na da muhimmanci ga kowannenmu ya lizimci biya addu’ar a}alla ko wace juma’a,addu’ar akwai ta cikin littafin Mafatihul jinan,mutum ya duba ta gaban Dua’ul Nudba,to addu’a ta }arshen fasalin,to itace,zai ga ta soma da “Allahumma idfa’a,  an waliyyika wa khalifatuka……..
E.AZKAR [IN SA:Imam Ridah [AS] ya kasance mai yawan Azkar,ya mazo a tarihinsa cewa idan yayi sallar Asuba yakan zauna yayi azkar,wato tasbihi da tamhidi da takbiri da tahlili,[Subhanallah  -walhamdulillah wala ilaha illallah -wallahu akbar],da kuma salati ga Manzon Allah da Alayensa [AS],ya kan yi haka har rana ta keto.Wani tambihi anan shine idan mutum yayi sallar Asuba yana da gayar muhimmanci ya kasance bai koma bacci ba har sai rana ta keto,domin sunna ce ta Manzon Allah [S] da kuma Ahlulbayt [AS].Kuma akwai hadisai masu yawa da suka zo da bayani dangane da falalar da ke tsakanin ketowar Alfijir zuwa ketowar rana,da kuma kashedi  dayin  barci  tsakaninsu.Alal misali ga wasu daga cikin hadisan.An samo daga Imam Ba}ir [AS] yace, “Allah Ta’ala yana raba arziki tsakanin ketowar Alfijir zuwa ketowar  rana,saboda haka kashedinku  da yin barci tsakaninsu”.Haka nan an samo daga Imam Rida [AS] dangane da tafsirin wannan ayar “Fal mu}assimati Amra”.yace, “Mala’iku suna  raba  arzikin ‘yan Adam tsakanin ketowar Alfijir zuwa ketowar rana,duk wanda yayi barci tsakaninsu,to yayi barci daga arzikin sa”.Wato ba zai zamo daga cikin wa]anda za’a raba wa arziki na ranar ba.                                                                                         Har ila yau an samo Hadisi daga wajen Imam Ba}ir [AS] yace, “Iblis la’antar Allah ta tabbata gareshi yakan watsa [aika] rundunarsa lokacin ketowar rana da kuma lokacin fa]uwarta.Saboda haka ku yawaita Azkar [Ambaton Allah] a wa]annan lokuta guda biyu,kuma ku nemi tsarewar Allah daga iblis da rundunarsa,kuma ku nemi tsari ga yaranku a wa]annan lokuta guda biyu [watau safe da kuma yamma daga sharrori na zahiri da kuma ba]ini].                                                                                          Imam Ba}ir [AS] ya }arasa  hadisin da cewa domin wa]annan lokuta guda biyu lokaci ne na gafala.Haka nan yazo akan cewa Manzon Allah [S] idan yayi sallar Asuba yakan zauna inda yayi sallar yana Azkar har rana ta fito,Akwai ma hadisin da Manzon Allah [S] yake cewa “In zauna a In da nayi sallar Asuba, ina Azkar har zuwa hudowar  rana,yafi soyuwa gare ni akan in ‘yanta bayi guda hu]u”.                                                An samo dag Imam Hasan [AS] yace, “Naji Babana,Ali bn Abi [alib [AS] yana cewa,Manzon Allah[S] yace duk mutumin daya zauna,a  in da  yayi sallar Asuba yana Azkar har rana ta fito,to yana da ladar kamar wanda yayi aikin hajji,kuma Allah zai gafarta masa zunuban daya gabatar”.                    Haka nan daga Imam Ali [AS] yace, “ wanda yayi sallar Asuba ya zauna in da yayi sallar, har rana ta keto,to wannan zai kasance hijabi tsakaninsa da wuta”.A ta}aice dai akwai hadisai masu yawa da suka zo akan haka,shi yasa fu}aha suka tafi akan cewa makaruhi ne yin barci tsakanin ketowar Alfijir zuwa ketowar rana,ana so mutum ya raya tsakaninsu da ibada da kuma Azkar,karatun Alkur’ani,adduo’i, da dai makamantansu,haka nan idan rana ta fito mustahabbi ne kafin ya tashi daga wajen yayi nafila raka’a biyu,wato salatul Ishra},itama akwai hadisi akan haka wanda aka samu daga Imam Hasan [AS].Da fatan za’a kiyaye wannan tambihi domin samun falalar dake cikin lokacin,
                2-AKHLA} [INSA:Imam Ridha[as] a wannan fage na Akla}, a zamaninsa ba wanda ya kai shi ballantana ya wuce shi,ga misalan wasu daga cikin Akla} ]insa.
                A.TAWALIU’NSA,Imam Ridha [as]ya kasance mai gayar tawali’u,saboda ma yawan tawaliu’nsa,yazo a tarihinsa cewa mafi yawan lokuta shi yake yima kan sa hidima.Haka nan idan yayi ba}i da kansa ya ke yi masu hidima.Akwai lokacin da yayi ba}o,sun zauna suna tattaunawa,fitilar dake wajen sai ta ]an canza,wato haskenta ya ragu,da yake da daddare ne,to sai shi wannan ba}o yayi nufin ya gyara fitilar,sai Imam Ridha [as]ya tashi da kansa ya gyara fitilar.Sai yake cewa ba}on ; “Mu mutane ne wa]anda ba musa ba}inmu hidima.’’                                                                                                                                       Daga cikin tawali’unsa,yazo  akan cewa wani lokaci ko abinci zai ci yakan kira bayinsa domin suci tare.Shine wani daga cikin sahabbansa da ya ga haka,sai yace wa Imam Ridah [AS] “in zamo fansa gare ka,wa]annan ai da an zuba masu nasu daban su koma gefe suci.” Da yake yawancin bayin nasa launin jikinsu ba}i ne,wato ba}ar fata, kamar yadda yazo a ruwayar,sai Imam Rida [AS] ya bashi amsa da cewa, “Ai asasi  ubangiji ]aya ne,uwa ]aya,uba ]aya.sakamako  akan asasin aiki ne” [wato ba’a  launi ba].Haka nan daga cikin tawali’unsa,yazo a tarihinsa cewa wani lokaci ko da, ]aya daga cikin bayinsa ya kira domin yasa shi wani aiki,to idan bawan na cin abinci ne,yakan ce yaje ya gama sannan yazo.
B.KYAUTARSA:Imam Ridah  [AS]               ya kasance mai yawan kyauta da kuma sadaka.Saboda ma  gayar kyautarsa,da kuma sadakarsa,akwai wani da yayi zamani dashi,yake cewa “Duk wani wanda ku kaji yana riya cewa yaga wanda ya kai Imam Ridah [AS] kyauta da kuma sadaka,to kada ku gaskata shi.yazo a tarihinsa cewa a lokacin yana khurasan, yaba  da  baki ]ayan abinda ya mallaka ga matalauta.Haka nan ya kasance idan aka kai masa abinci,to kafin ya fara ci, yakan ce a kawo masa  kwano,sai  ya ]ebi abincin yasa a kwanon,sai yace akai ma miskinai.Haka nan daga cikin kyautarsa yazo akan cewa yakan sai, bayi ba don kome ba,sai don kawai ya ‘yanta su daga bauta.A kan asasin haka yazo akan cewa sai da ya’yanta bayi  dubu.                                                                                                                                                                                                                Akwai }issar wani da yazo aikin Hajji,sai ku]insa suka }are,ya zamanto abin da zai mai da shi Madina ba shi dasu,sai ya samu Imam Ridah [AS] ya shaida masa halin da yake ciki.Don haka yana ro}onsa ya taimaka masa da abinda zai koma garinsu,alabashi in ya koma yayi sadaka da abinda ya taimaka masa ]in.Sai Imam Ridah [AS] yace ya zauna,ya shiga gida ya ]auko ku]i dirhami ]ari biyu ya bashi,yace  masa  gashi yayi guzuri da shi da kuma biyan bu}atunsa.In ya koma garinsu ba sai yayi sadakar ba, da abinda yaba shi,da ma lokacin da wannan mutumin yazo, Imam Ridah [AS] yana tare da wani sahabinsa mai suna Sulaimanil  ja’afari,shine sai yace ma Imam Ridah [AS] “In zamo fansa gareka,ha}i}a ka kyautata ma wannan mutumin, amma  naga  da zaka bashi ka suturta fuskarka,me yasa haka?” Da yake kamar yadda yazo a }issar, da Imam Ridah [AS] ya shiga gida da ya ]auko ku]in da zai mi}a masa,sai ya mi}o hannunsa ta }ofa ya bashi,shine wannan sahabin sa yake tambaya akai.Sai Imam Ridah [AS] yace “Nayi haka ne saboda gudun kada in ga }as}ancin tambaya a fuskarsa,domin na biya masa bu}ata.Ba kaji hadisin Manzon Allah [S] da yake cewa ba,mai ~oye kyawawan aiki ya nada lada kamar wanda yayi Hajji saba’in”.Da dai misalai da yawa na irin kyautar Imam Ridah [AS] saboda gudun tsawaitawa ba za’a iya kawo suba.                                                                                         C.AFUWARSA:Imam Ridah [AS] ya kasance mai yawan afuwa ga wa]anda suka zalunce shi  ko kuma suka yi masa abin da bai dace ba,akwai wanda yayi masa abinda bai dace ba,shi da iyalansa,amma da Imam Ridah [AS] ya samu sul]a [iko] akansa  sai yayi masa afuwa.A ta}aice dai kyawawan ]abi’u, a zamaninsa  babu wanda yakai shi,kamar yadda wani wanda yayi zamani dashi mai suna Ibrahim ]an Abbas ya tabbatar.Yake cewa ni ban ta~a gani ko jin wanda yakai Imam Ridah]AS]kyawawan ]abi’u ba, ban ta~a ganin wani mutum  ya kawo masa wata  bu}ata, a wajensa bai biya masa ba.Kuma ban ta~a ganin yana  }yal-}yatar dariya ba,dariyarsa itace murmushi,da dai sauran Akhla}  na Imam Ridah  da ya jero.
3.ILIMINSA:A wannan fage na ilimi, shima a zamaninsa baki ]aya ba wanda ya kai shi,kamar yadda wani da yayi zamani da shi yake cewa, “Ban ta~a ganin wanda ya kai Ali bn Musa Ridah ilimi ba,kuma duk malamin da ya gan shi sai yayi masa wannnan shaida,irin shaidar da na  yi mashi”.Akwai ma lokacin da khalifan Abbasawa a lokacin mai suna Ma’amun, ya tara malamai na fannoni ilimi daban daban da malaman yahudawa da kuma nasara, akan suyi mu}abala da Imam Ridah [AS],baki ]ayansu.Daga }arshe kowannensu sai da ya tabbatar da fifikon ilimin Imam Ridah [AS] akansa.kuma irin wannan majlisi,shi Ma’amun ]in ya sha shirya yin haka,watau ita mu}abalar a lokuta daban daban.                                                    Akwai ma lokacin da Imam Ridah [AS] yake cewa, “Na kasance na kan zauna a rauda a cikin massallacin Manzon Allah[S]Malaman Madina masu yawa(da suke karantarwa amassallancin)idan ]ayansu wata matsala ta shige masu duhu ko kuma bai sani ba,sai suyi ishara  zuwa gareni da a zo a tambayeni,ni kuma sai in basu amsa.’’Haka nan Imam Kazim[AS] ya kance ma ‘ya’yansa “Wannan ]an uwan naku Ali, Malami ne na Ahlul baiti[as]ku tambaye shi dangane da mas’alolin addininku,Abinda ya fa]a maku to ku kiyaye,domin na ji babana, Ja’afar ]an Muhammad[as]ba sau ]aya ba, ba sau biyu ba,yana ce mani lalle Malami na gidan Manzon Allah[s]yana tsatson ka,ina ma dai na riske shi.Sunan sa yayi muwafa}a da na Amiru muminin.’’Mu duba shadar kakan sa Imam Sadi}[as]gare shi tun gabanin a haife shi.Ya ambace shi da kalmar MALAM.Ikon Allah tsakanin rasuwar Imam Sadi}[as]da kuma haihuwar Imam Ridha [as]kusan kwanaki goma sha biyar ne.                                                                                                                         Haka nan yazo akan cewa tafiyar da suka yi daga madina zuwa khurasan,Birni da }auye da suka yada zango jama’a kan zo suyi tambayoyi na mas’aloli na Addini,ya kan basu amsa,da kuma fa]a masu Hadisai na Manzon Allah[s]da kuma Ahlul-Bait[as]Saboda haka nema Ma’amun khalifan Abbasawa,abubuwan da yaji kuma ya gani daga Imam Ridha[as] na ibada da kuma ilmi,sai Ma’amun ]in,yace  wannan shine mafi ililmi a bayan }asa.mu duba shaidar  ma}iyinsa,watau wannan khalifa na Abbasawa,shaidar da yayi masa na fifikon iliminsa a doron }asa a lokacin.
Akwai ma wani da yake cewa bai ta~a ganin an tambayi Imam Ridha akan wani abu ba,face ya san abun,da dai misalai da yawa na ilimin Imam Ridha [as]wanda baza a iya kawo suba, saboda gudun tsawaitawa.
4.ZUHUDUNSA:Watau gudun duniyarsa,Imam Ridah [AS] a wannan fage ya kai mustawa aliya,wanda a zamaninsa babu wanda ya kai shi a wannan fage na gudun duniya,akwai }issar wata kuyanga [baiwa] ta khalifan abbasawa Ma’amun, tana zaune a gidan Ma’amun ]in ne,sai ya bada ita ga Imam Ridah [AS].Sai ta koma gidansa,shine take cewa lokacin da take gidan ma’amun tana cikin wal-wala da jin da]i na abinci da abin sha,da ku]a]e,amma da ta koma gidan Imam Ridah [AS] duk sai ta rasa wa]annan abubuwa na jin da]i.Tace,kuma baya ga haka a gidan akwai wata mata, aikinta shine ta dinga tada su sallar tahajjud [sallar dare],tace to wannan shi yafi tsanani gare ni [watau tashi sallar].Tace, “Ina ta fata da burin in bar gidan,daga }arshe Imam Ridah [AS] ya bada ni ga wani.Da na koma  gidansa  sai na kasance  kamar  an sani  a Aljannah.”                                                                                                                                                      Daga }issar wannan mata zamu iya fahimtar rayuwa ta zuhudu na Imam Ridah [AS].Akwai misalai da yawa,amma gudun tsawaitawa za’a ta}aita da wannan.
5.ALA{ARSA DA SHI’ARSA[mabiyansa]: Akwai wani da ake cema Musa ]an sayyar yace, “na kasance tare da Imam Ridah [AS],mun kusan isa [us [Mash-had] sai muka ga janaza.Sai Imam Ridah [AS]ya nufaci wajen janazar,sai yace min, “ya Musa ]an sayyar duk wanda ya raka janaza  ta ]an shi’a daga cikin shi’armu,to zai fita daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyar sa ta haife shi.” watau zai dawo bai da zunubi ko guda].                                                                                                                                                                                               Lokacin da aka zo za’asa Mamacin a kabari,kafin sa shi sai Imam Ridah [AS] ya ta~a  }irjinsa yace, “ya wane ]an wane  albishirin ka da aljannah,babu tsoro gare ka bayan wannan lokacin.” Sai shi wannan da ke tare da Imam Ridah [AS] yace in zama fansa gare ka,kasan wannan mutumin ne? Domin wallahi baka ta~a tako wannan }asa ba  gabanin yau.” Sai Imam Ridah [AS] yace masa, “ya Musa ]an sayyar,shin baka san cewa, mu  A’imma  ana  bijirowa  [kawo] da ayyukan  shi’armu  gare mu safe da yamma ba? Abinda suka ta}aita na ayyukansu,mu ro}a masu Allah ya yafe masu,abin da suka aikata mai kyau,mu ro}a masu Allah ya }ara masu.” A wannan al’amari zamu ga akwai darussa masu yawa a ciki ,amma ga guda uku daga ciki:
1.Ala}ar Imam na kowane  Zamani da shi’arsa,domin shi wannan mutum da yake tare da Imam Ridah [AS] yana mamakin ina yasan wannan mutumin, alhali bai ta~a zuwa wannan waje ba,wannan kuma yana nuna wilaya Tak-winiyya da kuma Wilaya Tashri’iyya  da A’imma [AS] suke dashi.Insha Allah wani lokaci za’a yi bayani dangane da wa]annan wilaya guda biyu na A’imma [AS] a muhallinsu.
2.Tausayin Imamin kowane zamani akan mabiyansa na zamaninsa,su duba in  an kai, aikin da bai dace ba ko kuma aka ta}aita,su ro}i Allah ya yafe wa mutum.
3.Wanda yake yana da gayar muhimmanci, shine mutum ya san da cewa,duk aikin da yake aikatawa mai kyau da kuma mara kyau,to akan kai shi ga Imamin zamaninsa.mu a wannan zamanin namu akan kai shi ga Imam Mahdi [AS] ne,saboda haka kowannen mu yayi tunanin ayyukan da yake aikatawa,ayyuka ne da in an kai ma Imam Mahdi [AS] zai yi farin ciki dasu ko kuma zai yi ba}in ciki dasu? Domin  tabbas kai ayyukan bayi  ga Ma’asumai [AS] wani abu ne wanda yazo a ruwayo yin hadisai masu yawa.Wanda shima wannan wani lokaci a muhallinsa za’a kawo wa]annan hadisai,saboda haka yana da muhimmanci kowannen mu ya lizimci ayyukan da zasu kyautata ala}arsa da Imaminsa,ba wa]anda  zasu raunana ala}arsa da shi ba.kamar fa]in wata magana ta Ayatullah Bahjati yana cewa, “kada mu dinga fa]i da harsunan mu,Allah ya gaggauta bayyanar Imam Mahdi [AS],amma kuma da ayyukan mu muna jinkintar da zuwansa.”
6.JARABAWOWINSA:Imam Ridah [AS] ya fuskanci jarabawowi masu yawa a rayuwarsa,kamar sauran A’imma na Ahlulbayt [AS] da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa.
Domin idan mutum ya bibiyi tarihin Imamai ]aya bayan ]aya, zai ga kowannensu ya fuskanci jarabawa iri biyu.ta farko jarabawa ta amma,ta biyu jarabawa ta khassa.Jarabawa ta amma itace jarabawar da dukkan Imamai sha biyu sun yi musharaka a ciki.Misali A- jarabawar }wacen tafi da iko daga gare su wanda ha}}insu ne,wanda Allah [T] ya basu. B-Zaluntar su da kuma mabiyansu da kuma sauran jama’a suna  ganin haka,amma babu yadda  za suyi. C- Tasarrufi a cikin shi Addinin.
Watau masu iko su }ago abu ko su jirkita yadda yake,su sa shi a cikin addini,kuma su gina mutane akan haka, har saboda  ginuwa akai mutane su ]auka Addini ne.Da yake nan ba muhallinsa ba ne da an kawo misalai akai.To,idan mutum ya duba wa]annan misalai guda ukun da aka kawo zai ga duk A’imma [AS] sun yi tarayya wajen wannan matsaloli da aka haifar.                                                                                                                  Jarabawa ta khassa itace wadda kowa ne Imami ya fuskanta shi }ashin kansa daga masu tafi da iko na zamaninsa,kuma a wata munasaba ta wafatin Imam Ridah [AS],za’a kawo jarabawa wadda ta ke~anta da shi.Wannan jarabawa itace ta “ Waliyyul-Ahd” watau na]a shi a matsayin khalifa mai jiran gado wanda khalifan Abbasawa Ma’amun yayi,wanda in mutum ya dubi abin a zahiran ce,zai ]auka ko abu mai kyau Ma’amun yayi,alhali abin ba  haka nan yake ba,a ba]ininsa makirci ne da kuma yaudara.Asasin wannan abu ya taso ne daga shi wannan khalifa na Abbasawa Ma’amun,lokacin daya  hau khalifanci yaga matsaloli sun yi masa yawa,ga matsalar ]an uwansa mai suna Amin,wanda yana ya}ar sa domin ya tunku]e shi shi ya hau.Ga kuma ta wa]anda suka yi masa tawaye daga sassa daban daban a lokacin,musamman ma daga ~angaren mabiya Ahlulbait [AS],Saboda abin da baban shi Ma’amun watau Harunar-Rashid, yayi na kashe Imam Kazim [AS] a kurkuku,ta hanyar sa masa guba.To,wa]annan matsaloli daya ga sun yi masa yawa,kuma matsalar da yafi jin tsoro daga cikin wa]annan matsaloli,ita ce ta  ~angaren mabiya Ahlulbait [AS],sai yayi tunani shi a }ashin kansa ba tare da yayi shawara da kowa ba,na  bari ya ]auko Imam Ridah [AS] daga madina ya kawo shi khurasan,lokacin itace  cibiyar tafi da ikonsa.Domin ya bashi mu}ami na khalifa mai jiran gado.                              Manufarsa ~oyayya itace domin ya kwantar da wancan tawaye da mabiya Ahlulbait [AS] sukayi a sassa daban daban, wanda  daga }arshe idan abubuwa suka lafa,komai ya koma dai dai na ikonsa sai ya kashe Imam Ridah [AS] ta hanyar sa masa guba.Wannan ‘plan’ ]in  shi  a }ashin kansa ya kitsa.Imam Ridah [AS] ne ya tona asirin haka.lokacin daya ha]u dashi yace masa,nasan manufarka.Sai Ma’amun yace masa mece ce manufata? Imam Ridah [AS] ya fa]a masa,nan take ya daburce  ya fusata,saboda ya san wannan abin bai fa]a wa kowa ba,amma gashi Imam Ridah [AS] ya fa]i,don hatta ‘yan uwansa na jini,lokacin da ya ba Imam Ridah [AS] wannan matsayi,sun  maganganu  me yasa  zai yi haka? Don bai bayyana wa kowa manufarsa ba.                                                                                                                                                        Bayan Ma’amun ya kitsa wannan tunani a zuciyarsa,sai ya fara ]aukar mataki na aiwatar dashi.Saboda haka sai ya aika aje madina a zo masa da Imam Ridah [AS].da ‘yan sa}o suka isa madina,suka samu Imam Ridah [AS] suka shaida masa sa}on Ma’amu,jin haka sai Imam Ridah [AS] ya tafi masallacin Manzon Allah [S] domin ya yi ban kwana dashi,saboda yasan }arshe yazo,kuma zamansa a birnin Manzo  ya }are.Saboda haka yaje kabarin Manzon Allah [S] yayi bankwana dashi,yana kuka sai ya fito masallacin,sai ya sake komawa domin sake bankwana,yana bankwana da Manzon Allah yana kuka.Har wani daga cikin mabiyansa,ya gan shi yayi masa sallama Imam Ridah [AS] ya amsa masa  sallamar,ya kuma ce masa ka ziyarce ni domin ni za’a raba ni da birnin Manzon Allah [S]. Zan rasu a can ina ba}o.Bayan haka ya koma gida ya tara iyalansa baki ]aya yayi masu jawabi.Acikin jawabin nasa yace masu “TO  zan  tafi  bazan dawo ba har abada,saboda haka mai  juyayi yayi juyayi,mai kuka yayi kuka a gare ni.”  Bayan haka ya raba masu ku]i,Dirhami dubu goma sha biyu.Lokacin da zai fita ya dubi ]ansa,guda ]aya da yake dashi watau Imam Jawad [AS] lokacin ya nada shekaru bakwai a duniya,ya kama hannunsa ya shiga dashi masallacin Manzon Allah [S], ya isa kabarinsa,ya kama hannun wannan ]a nasa ya aza a kabarin Manzon Allah [S] yace “to ya Manzon Allah [S] gashi nan ajiya  gare ka.” Haka ya bar madina birnin Manzon Allah [S],kuma ya bar mahaifiyarsa da kuma iyalansa baki ]aya,suka kama hanya dashi zuwa khurasan.[khurasan tana cikin Iran ne yanzu]                                                                                                            Don ma makirci da dasisa irin na Ma’amun,cikin umurnin daya ba wa]anda ya aika suzo da Imam Ridah [AS] har da ce masu,kada ku biyo dashi ta gari kaza da kaza,ya ambaci wasu garuruwa,watau duk  garin da ya san akwai ‘yan shi’a da yawa,yace kada a biyo dashi ta nan,daga ciki har da birnin-}um.Mu duba irin wannan dasisa da makirci,haka suka yi watanni har suka isa khurasan.Kuma duk wanda Allah [T] yasa yaga wannan waje,ko ya san yanda wannan yanki yake da Hamada da kuma tsanuka da zafin yana yi,wani wajen kuma sanyin yana yi, zai fahimci matsanancin wahalar da Imam Ridah [AS] ya sha a tafiyar.Domin zan iya tunawa zuwana  Iran na farko,kimanin shekaru goma sha bakwai  da suka wuce,lokacin da Malam ya tura mu karatu a birnin }um mu goma sha biyu,Allah yasa mun tafi daga }um zuwa mashhad a mota,tafiyar kimanin awa goma sha ]aya ce.To,a lokacin da ake tafiyar yadda naga tsaunuka daban daban,ga Hamada wani wajen,ga tsananin sanyi,akwai garin da muka biyo,dole tasa aka tsaya muka sa kayayyakin sanyi,sa’annan aka ci gaba da tafiya.To,lokacin abinda nake tunani a raina shine,yanzu a wannan yana yi na Hamada da tsaunuka da  sanyi da zafi tun daga madina har ya zuwa mashhad,watau khurasan aka biyo da Imam Ridah [AS].A irin wannan yanayi ne ‘yan uwansa na jini bayan shekara ]aya da tafiyarsa,suka kamo hanya daga madina da nufin su same shi a khurasan.Wa sunsu akan hanya Allah [T] yayi masu rasuwa aka binne su anan, har yanzu kabur-buransu  na nan,in mutum yabi ta hanyoyi zai gani,wanda wannan tafiya har yau har gobe,idan na tuna da ita,sai naji tasirinta a zuciyata.Wannan a ta}aice dai yana nuna irin wahalhalu da wa]annan bayin Allah suka sha a tafiyar.                                                                                           
Sayyida Ma’asuma [AS] akan hanyar su,ta zuwa khurasan,domin zuwa wajen Imam Ridha[AS] rashin lafiya ya kamata,wani waje da ake ce ma  Sawa.Ta tambaya,tsakanin nan da }um, far-sakhi nawa ne? Aka ce mata goma,tace to a }arasa da ita }um.Kuma wani abin ba}inciki da ban takaici da ya faru gare su,da suka iso wannan gari na Sawa.Shine Hujumin da akayi a kansu,wanda  ya  kai ga an kashe wasu daga ciki,wasu kuma aka ji masu ciwo.Wasu malaman Tarihi sun tafi akan cewa,wannan rashin lafiya nata,yana da ala}a da wannan mummunan abin da aka yi masu,mu duba mu gani zuriyar Manzon Allah [S] sun taso daga madina su kimanin 30 kamar yadda yazo a ruwaya aka tare su a hanya akayi masu wannan mummunan abu.Malaman tarihi sun yi tambaya kan wannan abu cewa,Ma’amun ne ya kitsa ayi wannan abu,ko ko su mutanen Sawa ne suka yi? Domin yazo a tarihi cewa su mutanen Sawa a lokacin, sun kasance suna gayar gaba da }iyayya da Ahlulbait [AS].Ko ma dai mene ne,musabbabin wannan aika-aika da akayi ma su Sayyida Ma’asuma[AS].To  yau ina Ma’amun ]in?ina mulkin nasa?ina kuma wa]anda  ya mulka? Bayan isar su Imam Ridah [AS] khurasan,Ma’amun ya gana dashi,ya shaida masa abinda yake bu}ata,na ya kasance  khalifa mai jiran gado.Imam Ridah [AS] yace masa a’a,sai Ma’amun yace masa ko dai ya amshi wannan matsayi na  Waliyyul-Ahd, ko kuma ya kashe shi.Imam Ridah [AS] ya amsa,amma da shara]in cewa ba zai zartar da komai ba.Wannan ya kasance babbar jarabawa ga Imam Ridah [AS] saboda yasan meye manufar Ma’amun kan wannan abu.                                                                sHaka Imam Ridah [AS] ya zauna a cikin wannan jarabawa,wadda sai da ta kai koda wane lokaci in ya dawo daga masallacin  juma’a, yakan ]aga hannu sama yace “Ya Ubangiji idan faraj ]ina yana ga rasuwata,to ka gaggauta wafatina.” An ce ko da wane lokaci yana cikin damuwa da kuma ba}in ciki har ya koma ga Allah Ta’ala.Daga }arshe Ma’amun Yasa masa guba a inabi,a wata ruwaya a rumman,wanda hakan yayi sanadiyar shahadarsa.Ya rasu yana da shekara 55 a duniya.Sauran darussan shida,insha Allah sai wata munasabar za’a ]ora akai. 

No comments:

Post a Comment