Kasantuwar
ba mu jima da fita daga wata mai albarka ba, wato watan Maulidin Manzon Allah
(S), kuma a darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) da ya gabata, in za a iya
tunawa mun tsaya ne a bayani dangane da Akhlak ]in Manzon Allah (S), wanda muka
kakkawo bayani kan kyautarsa a ta}aice da bayani a kan ha}urinsa da kuma
afuwarsa, shi ma a ta}aice.
A nan muka tsaya.
C.
TAUSAYINSA: Manzon Allah (S) ya kasance mai yawan tausayi ga mutane da kuma
wannan al’umma tasa, musamman ma ga Muminai, kamar yadda Allah (T) yake fa]i a
cikin littafinsa cewa; “Shi (wato Manzon Allah (AS) ga Muminai mai tausayi ne
mai jin }ai.” Tausayi ga mutane ta fuskoki guda biyu. Fuska ta farko tausayinsa
a fagen Addini. Fuska ta biyu tausayinsa a fagen duniya. Idan mutum ya bibiyi
rayuwar Manzon Allah (S) zai ga misali na irin wannan tausayi nasa ga mutane,
musamman ma tausayinsa a fagen Addininsu, tunda shi yana da ala}a da makomarsu
ta lahira. Misali lokacin da ya tafi da’awa a [a’ifa, dattawan [a’ifa suka sa
matasansu suka jejjefi Manzon Allah (S) da duwatsu. Haka suka aiwatar da wannan
mummunan aiki, har suka yi masa jina-jina. Shi ne Mala’ika mai kula da duwatsu
ya same shi, ya ce ya ba shi umurnin ya yi masu ruwan duwatsu. Shi ne Manzon
Allah (S) ya ce masa; “A’a, ina fatan ko su ba su musulunta ba, to a zuriyarsu
a samu wa]anda za su musulunta, su bauta wa Allah shi ka]ai ba tare sun ha]a
shi da wani ba.” A wata ruwayar kuma Manzon Allah (S) ya ce wata}ila su tuba,
daga baya su musulunta.
Haka nan a ya}in Uhudu bayan
abubuwan da suka faru, sun faru, wanda daga ciki akwai ji ma Manzon Allah (S)
da aka yi a kansa da fuskarsa da kuma ha}orinsa, wanda wannan abu ya jawo }unci
sosai a zukatan wasu daga cikin Sahabbansa; shi ne suka ce wa Manzon Allah (S)
ya yi addu’a a kan su, wato su ma}iyan da suka yi wannan mummunan aiki, shi ne
Manzon Allah (S) ya yi addu’a, amma akasin yadda su wa]anda suka bu}aci
addu’ar. A tunaninsu sai Manzon Allah (S) ya ce; “Ya Ubangijina!
Ka shiryar da su don su mutane ne da su ba su sani ba.”
Mu
duba irin wannan tausayi na Manzon Allah (S) a wannan wa}i’ar ta Uhud da kuma
[a’ifa, kuma akwai misalan irin haka da yawa a tarihin rayuwarsa. Kuma daga
cikin tausayinsa ga wannan al’umma tasa, akwai lokacin da yake cewa ba domin
kada ya matsa wa al’ummarsa ba, da ya umurce su da yin aswaki a kowace Alwala.
Haka nan ya kasance mai tausayawa ga iyalinsa. Kamar yadda ]aya daga cikin masu
yi masa hidima yake cewa; “Ban ta~a ganin, wani wanda yake da gayar tausayawa
ga iyalinsa kamar Manzon Allah (S) ba” Wannan kenan a ta}aice dangane da
tausayinsa.
D. TAWALI’UNSA: Manzon Allah (S) ya kasance mai gayar
}as}antar da kai. Ya zo a tarihinsa, saboda gayar Tawali’unsa. Mafi yawan
lokuta shi yake yi wa kansa hidima, kuma yakan taimaka wa iyalinsa a ayyuka na
yau da kullum na cikin gida. Akwai ma wani Sahabinsa da yake cewa, sun je
kasuwa tare da Manzon Allah (S), sai ya yi sayayya, sai ya yi nufin ya ri}e
abin da ya saya ]in, sai Manzon Allah (S) ya ce, a’a sai dai ya ri}e da kansa.
Har yake ce masa ma’abocin abu shi ya fi cancanta da ya ]auki abinsa. Haka nan
ya zo a kan cewa, akwai lokacin da ya ziyarci Sahabinsa mai suna Sa’ad [an
Ubada. Da zai koma sai ya kawo dabba domin Manzon Allah (S) ya hau, sai ya ha]a
shi da ]ansa mai suna {ais domin ya raka shi. Sai Manzon Allah ya hau dabbar ya
ce wa {ais ]in ya hawo. Sai {ais ]in ya ce, a’a. Sai Manzon Allah (S) ya ce
masa ko dai ya hawo, ko ya koma. Wato saboda Manzon Allah (S) bai son ya
kasance shi yana tafiya kan dabba alhali shi kuma {ais yana bin sa a }asa. Wannan shi
ma ya nuna tawali’u na Manzon Allah (S).
Akwai ma wani lokacin da suna
tafiya da Abdullahi [an Abbas, sai ya kasance yana tafiya a bayansa, sai Manzon
Allah (S) ya ce masa ya zo daura da shi, sai abin ya yi wa Abdullahi [an Abbas
nauyi, amma kasantuwar ya ga haka Manzon Allah (S) yake so, sai ya zo daura da
shi ]in suka ci gaba da tafiya, wanda shi ma wannan yana alamta tawali’un
Manzon Allah( S).
Akwai lokacin da ya yi tafiya shi
da wasu Sahabbansa, sai suka bu}atu da su yanka dabba, sai wani cikinsu ya ce
shi zai yanka dabbar, wani ya ce shi zai jeme, wani kuma ya ce shi zai daddatsa
ta, sai Manzon Allah (S) ya ce; “Ni kuma zan nemo itacen da za a dafa”. Mu duba
tawali’u na Manzon Allah (S). Akwai misalai da dama na tawali’unsa ta fuskoki
daban-daban.
E.
KUNYARSA: Manzon Allah (S) ya kasance mai gayar kunya. Saboda gayar kunyarsa
sau da yawa akan yi masa abu ko abubuwa na cutarwa, amma sai ya kau da kai,
kamar yadda Allah (T) ya yi masa shaida a cikin littafinsa. “Lallai ne wannan
yana cutar da Annabi, amma yana jin kunyar ku”.
Ya kasance saboda kunyarsa, ko da
bai son abu ne sai dai a gane a fuskarsa. Haka nan ya zo a kan cewa saboda
kunyarsa bai dawwamar da dubinsa a fuskar wani. Haka nan ya kasance idan fa]in
wani abu gatsai yana da matsala, to yakan yi wa abin kinaya, wato domin
sakayawa. Kuma ya kasance saboda kunyarsa idan aka fa]a masa wani ya yi abu da
bai dace ba, in zai yi magana a kai bai cewa, me ya sa wane yake kaza? Ko yake
cewa kaza? Sai dai ya ce me ya sa wa]ansu mutane suke aikata kaza? Ko suke cewa
kaza?
F.
AMANARSA: Manzon Allah (S) ya kasance tun yana Makka gabanin aiko masa da sa}o,
jama’a kan kawo masa ajiyar kayyayakinsu gare shi. Shi ya sa lokacin da zai yi
Hijira zuwa Madina, cikin abubuwan da ya umurci Imam Ali (AS) da yi, baya ga
kwanciya a shimfi]arsa, shi ne na ba shi amanonin jama’a da suka kawo masa a
kan ya mai da masu. A lokacin har la}abi suka yi masa da Muhammad Amintacce.
Akwai lokacin da Manzon Allah (S)
yake cewa; “Wallahi lallai ni Amintacce ne a sama kuma amintacce a }asa”. Kuma
ya kasance saboda Amanarsa da kuma gaskiyarsa, ba kawai jama’a na kawo masa
ajiyar kaya ba ne, a’a, har }ararraki sukan kawo masa. Ko kuma al’amari ya taso, amma jama’a sai su duba menene matsayinsa? Sai su
tsaya a kai. Wannan ma fa tun gabanin aiko masa da sa}o.
Akwai
ma lokacin da sa~ani ya auku tsakanin {uraishawa yayin ginin Ka’aba, wanda zai
sa Hajarul-Aswad, suka ce to duk wanda ya fara shigowa, to shi ne zai yi mana
hukunci. Ikon Allah! Sai ga Manzon Allah (S) ya shigo, duk baki ]ayansu suka ce
“mun yarda da duk hukuncin da ya yanke.” Shi ne Manzon Allah (S) ya ce
masu, to ga yadda za a yi. Nan take kuwa suka amince da wannan hukuncin na
Manzon Allah (S).
G.
GASKIYARSA: A wannan fagen hatta ma}iyansa sun yi masa shaida a kai. Akwai ma
lokacin da Abu Jahal yake ce wa Manzon Allah (S); “Mu ba mu }aryataka ba, amma
abin da ka zo da shi, shi ne muke }aryatawa”. Haka nan ya zo a kan cewa a ya}in
Badar, akwai wani da ya ha]u da Abu Jahal ya ke~ance da shi ya ce masa; “Ka
gani ba kowa daga ni sai kai, ka fa]a min gaskiya”. Muhammad mai gaskiya ne.Sai ya ce; “Muhammad mai gaskiya ne domin bai ta~a
yin }arya ba”. Haka nan Hira} ]an Sarkin Rum ya tambayi Abu Sufyan; “Shin kun
kasance kuna tuhumar sa da }arya gabanin ya fa]i abin da ya fa]i?” Ya ce;
“A’a”.
H. CIKA AL{AWARINSA: Manzon Allah (S) ya kasance mai
gayar cika al}awari. Akwai lokacin da suka yi al}awari da wani, sai da ya kwana
uku yana jiran sa. Sai bayan kwana ukun mutumin ya tuna ai ko sun yi al}awari
da Manzon Allah (S). Ko da ya zo wajen da suka yi al}awarin, sai ya samu Manzon
Allah (S) a wajen yana jiran sa. Wannan al’amarin ya auku tun a Makka ne, wato
gabanin aiko masa da sa}o. Shi ne har Manzon Allah (S) yake ce masa; “Ka wahal
da ni, tun kwana uku ina nan ina jiran ka”.
Mu duba irin wannan gayar tsarewa
da kuma kiyaye al}awari na Manzon Allah (S). Irin wa]annan ]abi’u na Manzon
Allah (S) daban-daban da ake gabatarwa, Amanarsa, Gaskiyarsa, Al}awarinsa,
Kyautarsa, Tawali’unsa, Ha}urinsa da dai sauran su, yana da muhimmanci su
kasance madubi gare mu da za mu dubi kawukanmu da su, mu ga ya muke wajen
]abi’antuwa da su da kuma siffanta da su. Shi ya sa watan Maulidin wata ne na
muhasaba a matsayinmu na ]ai-]aiku, da kuma al’ummance, watau kowannen mu ya samu
lokaci a cikin watan ya zauna shi ka]ai ya yi wa kansa hisabi. Ya tambayi kansa
ya yake wajen koyi da kuma siffantuwa da Manzon Allah (S) wajen ]abi’unsa da
ayyukansa da kuma zantukansa.
Haka nan kuma ya tambayi kansa ya
yake wajen aikatawa da kuma siffantuwa da sa}on da Manzon Allah (S) ya zo da
shi, wato Al}ur’ani mai girma? Wato ya yake wajen aikata Al}ur’ani? Wato
ala}arsa da Al}ur’ani ta wajen mujarradin karanta shi, haddarsa da kuma sanin
iliminsa? Misali ilimin Tajwidi, ilimin Nasik da Mansuk, ilimin Asbabun Nuzul
da dai makamantansu na ilimomin Al}ur’ani. Ya kasance ya ha]a wa]annan tare da
aikata shi Al}ur’anin? Shi ya sa idan mutum na karatun Al}ur’ani ana son ya
dinga lura da umurce-umurcen da yake karantawa, ya umartu da su?
Haka nan hane-hanen da mutum yake
karantawa ya hanu? {issoshin da yake karantawa na Annabawa ya darastu da
darussan da ke ciki. Ayoyi na tsoratarwa da yake karantawa,ya tsoratu dasu, na
kwa]aitarwa ya kwa]aitu da su? Wato ya kasance yana karanta Al}ur’ani karatu
mai ruhi, ba karatu na gafala ba. Wato majarradin karatun lafuzzan ba tare da
tunanin wa]annan abubuwa da kuma halartar da zuciya ba. Domin kamar yadda akwai
ruhin Azumi, da kuma ruhin Salla, to akwai kuma ruhin karatun Al}ur’ani,
wa]anda abubuwan da ake ambata suna daga cikin ruhin karatun Al}ur’ani, wanda
in babu su, zai kasance kamar jiki ne babu ruhi.
Muhasabar da mutum zai yi wa
kansa, sa’annan ya tambayi kansa ya yake wajen koyi da siffantuwa na ]abi’o’i
da ayyuka da kuma zantuka na wa]anda Manzon Allah (S) ya bar wa wannan al’umma
nasa su yi ri}o da su a bayansa, wato Ahlul Baiti (AS). Wato kada ya zamanto
mutum ala}arsa da Imamai na Ahlul Baiti (AS) mujarradin i’iti}adi na
Imamancinsa, wato Khalifancinsu ga Manzon Allah (S), ya zamanto abin ya wuce
nan, ya kasance yana mai koyi da siffata da kuma bin su sau da }afa daidai
gwargwadon ikonsa.
Idan mutum ya bibiyi zantuka na
Imaman Ahlul Baiti (AS) zai ga cewa wannan shi ne babban abin da suka bu}ata
daga mabiyansu. Haka nan duk dai a wannan hisabi mutum ya tambayi kansa, ya
yake wajen Manzon Allah (S)? Ya kuma Manzon Allah (S) yake wajensa? Tunani a
kan wannan yana da gayar muhimmanci, domin ala}antuwa da Manzon Allah (S) a
wannan gida na duniya mutum ne yake gina shi. Saboda haka idan mutum ya kasance
yana raye, to dama ce babba gare shi na kyautata koyinsa da Manzon Allah (S),
domin mutum na mutuwa, dama ta }are. Saboda haka yake da muhimmanci yin tunani kan ya mutum yake wajen Manzon Allah
(S)? Wannan ko ta yin la’akari da kuma tunani na ayyukansa da ake kai wa Manzon
Allah (S). Domin kamar yadda ya zo a ruwayoyi na Hadisai, ayyukan da mutane
suke aikatawa a matsayi na ]ai-]ai akan kai wa Manzon Allah (S) ayyukan. Wa]ansu su faranta masa rai, ayyukan wasu kuma su ba}anta
masa rai. Akwai ma lokacin da Imam Sadi} (AS) yake ce wa mabiyinsa; “Ku daina
munana wa Manzon Allah (S). Sai ya ga duk hankalinsu ya tashi. Har wasu
suka tambaya, ta yaya muke munana wa Manzon Allah (S)? Imam Sadi} (AS) ya ce
masu; “Ba ku san ayyukanku ba ana kai wa Manzon Allah (S)? Wasu ayyukan su faranta masa rai, wasu kuma su ba}anta
masa rai”.
Saboda
haka kenan ayyukan mutum da ake kai wa Manzon Allah (S) idan kyakkyawa ne, zai
kasance kenan za su dinga faranta wa Manzon Allah (S) rai. Wannan kuma shi zai
sa ya kasance, Manzon Allah (S) ya zamto
yana son mutum. Kamar yadda ya zo a Hadisi daga Manzon Allah (S) ya ce; “Wanda
na fi so daga cikinku, wanda kuma ya fi kowa kusa da ni gobe }iyama shi ne
wanda ya fi ku kyawawan ]abi’u”. Kowannen mu yana son ya kasance kusa da Manzon
Allah (S) a gidan Aljannah, to wannan duk ya ta’alla}a ne da yadda mutum yake wajen Manzon Allah (S) a wannan gida na
duniya. Idan kuma akasin kyawawan ayyuka na mutum ne ake kai wa Manzon Allah
(S), wato munana zai kasance ke nan za su dinga ba}anta wa Manzon Allah (S)
rai, kuma haka zai kasance daga cikin dalilin da Manzon Allah (S) zai zamto bai
son mutum. Wannan
ke nan ta fuskacin ya kake a wajen Manzon Allah (S).
Sai ta fuskacin kuma ya Manzon
Allah (S) yake a wajenka? Wannan ko mutum zai yi tunani, ya kuma dube shi ta
fuskoki daban-daban. Alal misali yaya sanin sa
ga Manzon Allah (S)? Yaya son sa ga Manzon Allah (S)? Yaya shau}insa ga Manzon
Allah (S)? Yaya damuwarsa ga cutarwar da aka yi wa Manzon Allah(S)? Da dai
sauran ala}o}in }albiyya (wato na zuciya) da Manzon Allah (S), to irin wa]annan
ala}o}i na ba]ini, wato kamar son sa, girmama shi, shau}insa na zahiri da kuma
ba]ini, wato kamar koyi da shi da kuma ]abi’antuwa da ]abi’o’insa, su ake so
mutum ya gina kansa a kai domin ala}antuwarsa da Manzon Allah (S). Kuma irin
wannan ala}a da Manzon Allah (S) ta zahiri da kuma ba]ini, mutum ya tambayi
kansa, a wannan muhasaba da yake yi wa kansa, shin ya ci gaba ne, ko yana nan a
inda yake? Ko kuma wa’iyazubillahi ya ci baya ne daga Maulidin bara zuwa
Maulidin bana? In mutum ya binciki kansa, zai ga dai ba zai fita daga ]ayan
ukun nan ba. Ko dai ya zamanto mai zaluntar kansa, wato ya ci baya ke nan, ko
kuma mai ta}aitawa, wato yana nan inda yake bai ci gaba ba, ko kuma ya ci gaba,
wato ya shiga cikin sabi}un, wanda haka ake so. Domin a fagen addini kullum ana
son mutum ya dinga ci gaba ne, ba ci baya ba. Ko kuma ya tsaya bai gaba. Shi ya
sa ya zo a Hadisi cewa a addini ana son mutum ya dinga duba wanda yake sama da
shi, ba wanda yake }asa da shi ba. Saboda wannan shi zai sa mutum ya }ara }aimi
akasin kuma a fagen duniya, shi kuma ana son mutum ya dinga duban wanda yake
}asa da shi, ba sama da shi ba. Wannan kuma shi zai sa mutum ya dinga godiya ga
abin da Allah (T) ya ba shi da kuma wadatuwa da shi. Wannan ke nan a ta}aice
dangane da muhasaba a watan Maulidi.
Haka
nan watan Maulidi wata ne na godiya ga Allah (T) na wannan babbar ni’ima da ya
yi mana na sanya mu cikin ’yan wannan al’umma ta Manzon Allah (S) a kan sauran
Annabawa. To, haka nan ya fifita wannan al’umma ta Manzon Allah (S) a kan
sauran al’umma da suka shu]e. Ya ma zo a wasu ruwayoyi na Hadisai cewa wasu
daga cikin Annabawan Allah (T) kuma Manzanninsa Ulul-Azim, sun yi fata da kuma
burin ina ma da su ’yan al’ummar Manzon Allah (S) ne, wato saboda falaloli da
kuma darajoji da suka gani na wannan al’umma a littafan da Allah(T) ya ba su
kamar Attaura da makamantan su. Saboda haka idan watan ya kama gabanin ya }are,
mutum ya samu wani lokaci ya yi salatus shukur ko kuma a}alla sujudus shukur
domin godiya ga Allah (T) na wannan babbar ni’ima da ya yi masa na kasantar da
shi ]an al’ummar Manzon Allah (S). Wannan ke nan dai a ta}aice. Insha Allah (T)
sauran wasu daga cikin darrusa na rayuwar Manzon Allah, kamar ibadarsa da
mu’amalarsa misali da iyalinsa, ma}wabtansa, ’yan uwansa na jini, da dai sauran
~angarori na mutane, Shaja’arsa, Zuhudunsa, Mu’ujizarsa da sauransu wajen cin
abinci, barci, tafiya, zama, sa tufafi da dai makamantan su.
In
Allah (T) ya kai mu wata munasabar za a ]ora a kai.
No comments:
Post a Comment