Sunday 3 February 2013

Bayani kan Kalb {zuciya}.


A darasin daya gabata bayani ya gudana dangane da Tazkiyatus Nafs wato tsarkake rai.A wannan darasi bayani zai kasance ne,dangane da ~angarori biyu na tazkiyatus nafs.~angaren ba]ini wato zuciya da kuma ~angaren zahiri wato ga~u~~a,Da farko ~angaren ba]ini wanda shine tazkiyya na zuciya wato tsarkake zuciya,wanda in ya samu ]aya ~angaren zai iya samuwa wato ~angaren tazkiyya na ga~u~~a.
Kamar yadda yazo a hadisi daga Manzon Allah[S] yace, “A cikin jiki akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta ~aci dukkan jiki ya ~aci,wannan itace zuciya.”Wannan hadisi ya nuna mana idan zuciya ta gyaru wato ta tsarkaka,dukkan sauran ga~u~~a na jiki misali harshe,ido,kunne da dai sauran su suma zasu gyaru wato zasu tsarkaka.A saboda haka ne Malaman Ir-fan ko Tasawwuf suke }arfafawa da kuma muhimmar tar da al-amarin zuciya.Kuma in muka dubi yadda ambaton zuciya yazo a cikin Al-}ur-ani mai girma da kuma Hadisai da suka zo daga Manzon Allah[S] da kuma Ahlul bait[AS] babu wata ga~a daga cikin ga~o~in ]an Adam wanda ambaton ta yazo kamar haka.Wanda wannan ka]ai ya isa ya nuna matsayin zuciya a addinin musulunci,sai dai wani tambihi muhimmi anan shine, }alb wato zuciya da ake Magana anan da ma’anar ta na ma’anawi ne ba jis-miy ba wato jiki.Anan bayani zai kasance kan wa]annan ababe.
1-      Ma’anar  }alb wato zuciya.
2-      Muhimmancin zuciya a suluki zuwa ga Allah[T]
3-      Muhimmancin tsarkake zuciya.
4-      Hanyoyin tsarkake zuciya.
5-      Abubuwan da suke kai wa ga bushewar zuciya.
6-      Alamomin bushewar zuciya.
7-      Magance bushewar zuciya.
8-      Yadda zuciya zata dunga haskaka  ko tayi duhu.
9-      Makircin shai]an ga mutum dangane da zuciyar sa.                                                                     
1-Ma’anar }alb:}alb wato zuciya,ma’anar ta a luggace shine jujjuyawa, an ace mata haka saboda jujjuyawar ta a tunani,amma a is]ila -hance tana da ma’anoni guda biyu tana da ma’ana ta zahiri wato jis-miy,da kuma ma’ana ta ba]ini wato ma’anawiy.To ma’anar ta ta ba]ini shine malaman Irfan suke bayani akai,shi kuma ma’anar ta zahiri shine likitoci suke bayani da kuma kula dashi, tun da ya shafi ~angaren gangar jiki ne.Saboda haka idan mutum yaga ambaton zuciya anan,ba ana nufin ma’anar ta ta zahiri ba wato tsoka wanda aka sani tana jikin ]an Adam,a ~angaren jikin sa na hagu,wato a }irjinsa.A’a ana nufin ma’anarta ta ba]ini,wanda akan wannan asasi ta ma’anarta ta ba]ini zuciya itace mahallin imani,tsoron Allah,son Allah,ta}wa da dai sauran matakai suluki zuwa ga Allah[T]kuma a irin wannan ma’anar ta ba]ini ake nufin in ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,in ta ~aci dukkan jiki ya ~aci.
2-Muhimmancin zuciya a suluki zuwa ga Allah[T] wato kusanci zuwa gareshi,Zuciya tana da gayar muhimmanci a neman kusanci ga Allah[T]Ga wasu daga ciki A- Dukkan matakai ko ma}amomi na suluki zuwa ga Allah,to mahallin su a zuciya suke,kamar misalin da aka bayar a baya na ta}wa,imani,tawakkali…..B-Zuciya a matsayin shugaba take sauran ga~o~i kamar ido,kunnuwa hannuwa }afafuwa,harshe da daisauran su,a matsayin bayin ta suke,wato ita ke juya su,basu suke juyata ba.misalai anan shine idan mutum na zaune babu yadda za ayi }afafuwan sa, su tashi su kama tafiya in bashi yayi tunani a zuciyar sa akan bari ya tashi yaje waje kaza,haka nan kuma hannun sa ba zai ta~a wani abu ba,in ba yayi  tunan a zuciyar sa akan ya ta~a.to haka nan duk sauran ga~u~~an sa,ba zasu iya yin komi ba sai bayan mutum yayi tunani a zuciyar sa akan yayi.To anan ne mutum zai fahimci ha}i}anin ma’anar hadisin da aka ambata sama na cewa a cikin jikin mutum akwai wata tsoka in ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,in ta ~aci dukkan jiki ya ~aci,wato ma’ana in zuciya akwai tsoron Allah da kuma mura}abar Allah[T] to harshen sa,kunnuwansa,idanuwansa,da dai sauran ga~o~insa baza su sa~a ma Allah ba,saboda yasan Allah yana ganin sa yana kuma jinsa,zai kuma gamu dashi.Saboda haka sanadiyyar gyaruwar zuciyar sa, da kuma tsarkakuwar ta,sai sauran ga~o~in suma suka gyaru,to akasin haka kuma idan zuciya ba tsoron Allah ba tunanin gamuwa dashi,ga~o~in sa zasu kasance masu sa~a ma Allah[T]wato lalacewar zuciyar sai ya shafe su. C-Zuciya itace mahallin fafatawa tsakanin rundanar Allah[T] da kuma rundunar shai]an,kuma matu}ar mutum yana raye wannan fafatawa tsakanin wa]annan rundunoni guda biyu,zai ta gudana har ya zuwa saukar ajali.kuma wannan fafatawa da take gudana tskanin mutum da shai]an ita ake cema mujahada  a fannin ilimin irfan,kuma mutum zai tayin wannan mujahada ne,har ya samu sul-]a wato iko akan Naf’s ]insa da kuima shai]an.tanan  mutum zai fahimci cewa ashe matu}ar yana raye,shi mabu}aci ne ga mujahada,tun da yasan shai]an bazai ta~a }yale shiba.kuma muhallin da ake wannan fafatawa a zuciya ne,misali mujahada a wajen aikata addini ta umartuwa da umarce-umarcen sa, da kuma hanuwa da hane-hanen sa.D-Zuciya itace mahallin saukar kawa]ir wato tuna-nunnuka imma dai kyawawa ko munana,kuma nan ilimin ladunni yake sauka wato ilimin da Allah[T] kan ba wasu daga cikin bayinsa sakamakon ta}war su.haka nan ilhamomi na ayyukan ]a’a da Allah kanyi ma wasu daga cikin bayin sa duk a zuciya ne.E-Zuciya itace mahallin dubin Allah[T] wato kamar yadda yazo a hadisi  daga Manzon Allah[S] yace, “Allah[T] baya dubi ga jikkunanku ko dukiyoyin ku,amma yana dubi ga zukatanku da kuma ayyukan ku,”wanda ko da ace wannan ka]ai ne zuciya take dashi wato mahallin dubin Allah ya isa ya zama matsayi babba a wajenta,ata}aice dai zuciya tana da matsayi babba a wannan addini na musulunci,shiyasa ambaton ta yazo a wajaje da yawa acikin Al-}urani da kuma Hadisai.   
3-Muhimman cin tsarkake zuciya:Tsarkake zuciya yana da gayar muhimmanci domin idan ta tsarkaka,dukkan ga~u~~a  suma sun tsarkaka.kuma tsarkakuwar ta shi kan rayar da ita da kuma ga~o~in ta na ba]ini wato jinta,ganinta  da dai sauransu,domin mutum zai iya kasancewa a zahirance yana ji yana gani da kuma hankali,amma a ba]inan ce,bayaji,baya gani,bai kuma da hankali.Misali fa]in ‘yan wuta,Lau  kunna nas’mau, au na’a}ilu ma kunna fi as-habus-sa’ir.ma’ana  da ace muna ji ko muna hankalta da bamu kasance cikin ma’abuta wuta ba.saboda haka tsarkake zuciya kan sa jinta na zuci da ganinta ya zaman to suna aiki.sa~anin ko idan ba a tsarkake take ba,ya kan sa jinta da ganinta su makance.Haka nan tsarkakuwar zuciya,ya kan sa ibadodin da mu keyi ya zamanto suna da tasiri a zukatan mu,wato kamar salloli,karatun Al-}ur’ani,Azkar da dai sauran su.Haka nan tsarkakuwar zuciya ya kan taimaka ma mutum sosai wajen damfaruwa da Allah[T] da kuma damfaruwa da Manzon Allah[S] da Aimma[AS] har wala yau da kuma damfaruwa da gidan lahira.Haka nan tsarkakuwar zuciya ya kansa shai]an ya nisanci mutum,domin zai ga cewa bai da wani tasiri a zuciyar mutum.Haka nan tsarkakuwar zuciya yakan sa ta kasance a farke,wato ba cikin gafala ba.Haka nan zata kasance cikin haske ba duhu ba,da dai sauran abubuwa masu yawa,wanda tsarkakuwar zuciya ke haifarwa.
                4-Hanyoyin tsarkake zuciya:Malaman  irfan sunyi bayanin hanyoyi  da kuma matakai  na tsarkake zuciya,Amma ga guda ukku daga ciki,A-Nisantar zunubi,barin zunubi yana daga cikin babban hanyar tsarkakuwar zuciya,domin kamar yadda yazo a hadisi in mutum yayi sa~o to akan sa  ba}in ]igo a zuciyar sa,in ya sake asake sawa,haka haka dai in bai tuba ba za ai tasa masa ba}in ]igon har zuciyar ta zama ba}i}}irin.Shi yasa nisantar sa~o babban ginshi}i ne wajen kusanci zuwa ga Allah[T] domin shi sa~o ko zunubi dafine da kuma guba ga zuciya.Akwai ma hadisi da aka samo daga Imam Ali[AS] yace, “Babu wani ciwo da yafi tsanani ga zuciya kamar zunubi,”B-Mujahada:kamar yadda aka ambata a baya  cewa,zuciya fagene na fafatawa tsakanin mutum  da kuma shai]an da naf’s ]insa,wani lokaci ya samu galaba akansu  wani lokaci kuma su sami galaba akansa,To duk lokacin da akayi wannan ko kuwa tsakanin mutum da shai]an a zuciyar sa yayi kaye wato ya samu galaba,sai zuciyarsa ta da]a tsarkakuwa da kuma haskakuwa,sa~anin ko idan aka samu akasi wato aka kada shi,zuciyarsa zata da]a yin duhu ne.Saboda haka mujahada wajen siffantuwa da addini ta hanyar misaltuwa da umarce-umarce da  kuma hanuwa daga hane-hane,hanya c eta samun tsarkakuwar zuciya.kuma mutum ya gwada da }ashin kansa ya gani,duk lokacin da al-amari na wajibi ko mustahabbi ya bijiro ga mutum,kuma mutum yayi }o}ari ya aikata wajibin ko mustahabbin to sai yaji tasirin hasken haka a zuciyar sa,amma fa da shara]in iklasi wajen aikatawar.Haka abin yake idan abinda ya shafi barin haramun ne ko makruhi,mutum yayi mujahada wajen nisantar haramun ]in ko makruhin,shima sai yaji tasirin hasken haka a zuciyar sa,to wannan tasiri na haske da zuciya zata samu,wajen umartuwa da umarni na addini ko hanuwa da haninsa, to hanya ce ta samun tsarkakuwar zuciya,kuma wannan shine ma’anar fafatawa da ake bayani abaya,wato wadda take gudana tsakanin mutum da shai]an a zuciyar sa.domin shi shai]an duk umarce-umarce na addini, idan mutum na son ya aikata zai yi iyaka iyawar sa, yaga cewa mutum bai aikata ba,to duk lokacin da mutum ya yi }o}ari ya aikata,to yayi kaye ga shai]an kenan a wannan fafatawa,akasin haka kuma idan mutum bai aikata ba,to shai]an yayi kaye akan sa kenan.to haka nan abun yake,wajen hane-hane na addini,shima ko ya samu galaba akan shai]an,ta hanyar idan ya hanu ko kuma shai]an ya samu galaba akan sa,idan bai hanu ba.Saboda haka mutum koda wane lokaci dole ne ya kasance cikin mujahada har ya kai matsayi na “UBUDIYYA”wato zama abd[bawa] na Allah[T] idan mutum ya kai wannan matsayi,to ya kai matsayin da shai]an bai da sul]a wato iko akan sa,sai dai yayi abunda zai yi,amma zai zamo basu da tasiri a zuciya,kamar yadda Allah ma]aukaki yake fa]a ma shai]an “Bayina baka da sul]a akan su”C-Daga cikin hanyoyin tsarkake zuciya, akwai ayyuka na ibadodi,kamar salloli,karatun Al-}ur-ani,azkar,Adduo’i,azumi da dai sauransu,wa]annan misalai na ibadodi da aka ambata,abinci ne ga zuciya kuma sabulun wanki ne gareta,wato dashi take rayuwa dashi kuma take wankuwa,saboda haka duk lokacin da mutum ya yawaita karatun Al-}ur’ani da zikirori da salloli na nafil-fili,to tamkar yana tsarkake zuciyar sane,daga dattin zunubai da gafala da dai sauran su.
                5-Abubuwan da suke kai wa ga bushewar zuciya:Shima wannan malaman irfan,sunyi bayani akai, na wa]annan  abubuwa shima ga guda ukku daga ciki.A-Gafala:Idan zuciya ta kasance ko da wane lokaci tana cikin gafala daga tunanin Allah[T] ko tunanin mutuwa da abinda ke bayanta,misali  }abari,tashin }iyama,wuta……to irin wannan zuciya tana iya bushewa ta kuma }e}ashe,ya kasance duhu ya mamaye ta.B-daga cikin abubuwan da suke busar da zuciya akwai zunubi,wato zunubai su kansa zuciya ta bushe,ya zamanto ba haske acikin ta.shi yasa malaman irfan suna yawan }arfafawa sosai ga duk wanda yake son kama hanyar suluki zuwa ga Allah[T] da ya nisanci zunubi,domin illolin zunubi suna da yawa, addinin mutum da duniyar sa da kuma lahirar  sa.C-Daga cikin abubuwan da suke janyo bushewar zuciya akwai  yawan Magana ba tare da ambaton Allah ba.kamar yadda yazo a hadisi daga Manzon Allah[S] yace, “Kada ku yawaita magana ba tare da ambaton Allah ba,domin ya waita magana ba tare da ambaton Allah ba, yana }e}asar da zuciya,acikin mutane wanda yafi nisa daga wajen Allah shine mai }e}asarsar zuciya.”D-daga cikin ababen da suke janyo bushewar zuciya akwai tsawai ta buri,yazo a hadisi cewa, daga cikin abubuwan da Allah yace ma Annabi Musa[AS] lokacin da yake munajati dashi, “Ya Musa kada ka tsawaita burin ka a duniya,zuciyar ka sai ta }e}ashe,kuma mai }e}asar sar zuciya,manisanci ne gareni.” [i]                                    6-Alamomin bushewar zuciya,shima wannan malaman irfan sunyi bayanai akai,shima ga guda ukku daga ciki
.A-Daga cikin alamomin bushewar zuciya,akwai bushewar idanuwa wato ya kasance idanuwan mutum basu iya zubar da hawaye ko kuka saboda tsoron Allah ko tunanin ha]uwa das hi,ko tunanin mutuwa da abinda ke bayanta.wato kamar dai yadda yazo a hadisi,da aka samo daga Manzon Allah[S] “Bushewar idanuwa yana daga bushewar zuciya,bushewar zuciya yana daga zunubi.” Shigen wani hadisi da aka samo daga Imam Ali[AS] yace, “Idanuwa basu bushe ba face saboda }e}ashewar zuciya,zuciya bata }e}ashe ba face saboda yawan zunubi.”Har wala yau akwai hadisi da aka samo daga Imam Ba}ir[AS] yace, “Allah[T] yana da u}ubobi a zukata da jikkuna,bawa bai samu wata u}uba mafi girma ba,kamar }e}ashewar zuciya. “wato hadisin na nuna cewa,Allah kan yima bawa u}uba sakamakon mummunan aikin sa, imma a jikin sa, misali rashin lafiya ko a zuciyar sa,misali }e}ashewar ta.to acikin wa]annan u}ubobi guda biyu wannan shi yafi girma.domin rashin lafiyar jiki in mutum ya mutu shi ken an,amma rahin lafiyar zuciya kamar }e}ashewar ta,in mutum ya mutu bai tuba ba zai bishi har lahira ne. B-Daga cikin,alamomin bushewar zuciya akwai rashin kushu’i cikin sallah,da kuma rashin halartar da zuciya acikin ta ,wato ya kasance mutum na sallah,amma zuciyarsa na wani waje.ko kuma yana wasu ayyuka na ibadodi,misali karatun Al-}ur’ani,Azkar,biya adduo’i,ko biya ziyarori na Ma’asumin[AS] da dai suransu, amma zuciyarsa na cikin gafala na abubuwan da yake biyaw.Saboda haka rashin halartar da zuciya a ibadodi da rashin kushu’i, acikinsu na nuna acikin zuciya akwai matsala.C-Daga cikin alamomin bushewar zuciya akwai rashin tausayi,kuma tausayin nan bai ta}aita ga mutane ba kawai,a’a har ma ga wasu halitta,misali dabbobi,domin tausaya ma dabba yana iya sanadiyyar shigar mutum al-janna,kamar yadda yazo a }issar wani mutum da yaji }ishi,ya samu wata rijiya ya sha ruwa,ya juya zai tafi sai ga kare yazo yana jin }ishi,ya ]ebo ruwan ya bashi,sai Allah[T] yayo wahayi ga Annabin lokacin,akan cewa Allah[T] ya gode masa,zai kuma shigar dashi aljanna,kan wannan aiki nasa.mu duba mugani tausayawa ga dabba kenan,to ina ga mutum,shi yasa yana da gayar muhimmanci mutum ya zamanto mai tausayawa ma mutane a addinin su da kuma duniyar su,shi yasa idan irin wannan tausayi ya ginu a zuciyar mutum,cutarwar mutane gareshi,sakamakon bin tafarkin gwa-gwarmaya ko riko da Ahlul-bait[AS] bai damuwa dashi,tausayin su da yake ji na abunda zasu fuskanta a makoma,sai ya cire mai zogin cutarwar,yazo akan cewa a ranar ashura,an ga Imam Husain[AS] yana hawaye, aka tambaye shi dangane da haka,yace yana tausayin wa]annan mutanan ne,zasu shiga wuta saboda shi.Haka nan yazo a tarihin Imam khumain,wani lokaci idan yana kallon Tv aka nuna wani abin ban tausayi,kamar a nuno  yadda wasu suke cikin wata matsala ko wata musiba da ta same su,akan ga hawaye na zubo masa.In-sha Allah a darasi na gaba za a ]ora akai.



No comments:

Post a Comment