Kasantuwar watan Jimada Sani 3 gare shi ne wafati ko
shahadar Ummul A’imma, wato Sayyada Zahra (AS), amma wannan a ruwayar da ta fi
shahara, domin akwai ruwayoyi da suka zo akasin haka, rubutu ko bayani dangane
da tarihi ko rayuwar Sayyada Fatima (AS), wani fage ne mai fa]in gaske, wanda
ba za a iya cimma ma}urarsa ba,
domin idan mutum ya yi bincike zai ga cewa a
tarihin wannan al’umma, ko ma tarihin ]an’adam ba}i ]aya a ~angaren mataye, ba
a samu wacce Malamai daban-daban suka yi rubuce-rubuce na littafai dangane da
tarihi da kuma rayuwarta ba, kamar Sayyida Fatima (AS).
Alal
misali, akwai littafi mai suna ‘FA[IMATUZ-ZAHRA-BAHJATU-{AL-BIL-MUSTAFA (S)’
na Shaikh Ahmad Al-Hamdaniy, wanda in
mutum ya duba littafin zai ga akwai fasali da Malamin ya ke~ance, ya kawo
sunayen littafai na Malamai daban-daban
na wa]annan Makarantu guda biyu, wato Shi’a da Sunna, musamman ma na Shi’a da
suka yi rubutu dangane da Sayyida Fatima (AS). Misali tarihin da kuma rayuwar
ta, ko kuma wani ~angare na rayuwarta,misali iliminta ko kuma wa}i’a da ta auku, wadda take da ala}a
da rayuwarta,misali al’amarin fadak to
ire-iren wa]annan rubuce-rubucen a fasalin Malamin ya kawo sunayen littafai
]ai-]ai har guda 246 wa]anda aka buga. Sannan kuma ya kawo sunayen
littafai guda 44 wa]anda ba a buga ba. Ga mai bu}atar ganin sunayen wa]annan
littafai yana iya komawa ga littafin da aka ambata a sama, fasali na 40 shafi
na 679, zai ga sunayen wa]annan littafai da Malaman da suka rubuta su, da ma
inda aka wallafa su.
Sayyada Fatima (AS) kyauta ce ta
musamman da Allah (T) ya ba Manzonsa (S), wadda ta hanyarta ne zuriyyarsa suka
wanzu, wanda ko a yau akwai su da dama, wato zuriyyar Manzon Allah (S) a kuma
sassan duniya daban-daban akwai su. Na ji wani Malami a cikin jawabinsa yana
cewa, a yanzu a }iyasi, a}alla akwai jikokin Manzon Allah (S) a sassa
daban-daban na duniya sama da miliyan 50. Har ila yau akwai sashen Malaman
Tafsiri da suka tafi a kan cewa ayoyin da suka zo a cikin Suratul-Kausar sun ba
da tafsirin Kausar da cewa ana nufin
Sayyada Fatima (AS), da dai sauran zantuka na Malaman Tafsiri a kan ma’anar
Kausar. Ga mai bu}atar ganin wa]annan zantuka ]in yana iya komawa ga Tafsirin
Almizan na Allama Sayyid [aba-[aba’i, juz’i na 20.
Idan mutum ya bi ruwayoyin da suka
zo na Hadisai dangane da Asbabun-Nuzul na Surar, zai ga cewa ta sauka ne a kan
Mushirikan Makka kamar Abu Jahal da Walid ]an Mugira da dai sauransu, wa]anda
suke sukar Manzon Allah (S) lokacin da ’ya’yansa Al}asim da Abdullah (AS) suka
rasu, sai suna siffanta shi da cewa shi ‘Abtar’ ne Wal iya Zubillah, wato
ma’ana wanda bai da tsatso a bayansa, shi ne wa]annan Ayoyin na Suratul Kausar
suka sauka.
Wa]annan
Ayoyi na wannan Sura guda uku ne, ita ce mafi gajartar Sura a cikin Surorin
Al}ur’ani. In muka duba Aya ta }arshe cikin Surar, Allah (T) yana cewa, “Lallai
mai aibantaka shi ne Abtar.” Mu duba mu gani a yau wa za ka gani, ko ya ce shi
jikan Abu Jahal ne, ko jikan Wali ]an Mugira ne? Babu. Sai dai jikokinsu a
munanan ayyukansu, amma ba a jini ba. Amma jikokin Manzon Allah (S) fa,ga
sunan a sassa daban-daban na duniya,a
wa]ansu wajaje ma saboda girmamawa gare
shi suna da alama ko la}abi daga gani ko ka ji, ka san wannan jikan Manzon
Allah (S) ne, misali alamar ba}in rawani, ko ba}ar hula, ko sa alama koriya, da
dai makamantansu. Ko amsa la}abin Sayyid, ko Sharifi da dai makamantansu, ya
danganta daga nahiya zuwa nahiya.
Haka
nan kuma Sayyida Fatima (AS) kyauta ce ta musamman da Allah (T) ya bai wa
wannan al’umma ta Manzon Allah (S), domin A’imma na Ahlul Baiti (AS) wa]anda
Manzon Allah (S) ya bar wa wannan al’umma a matsayin Khalifofi a bayansa, kuma
in an bi su ba za a ~ace ba. To dukkansu in ka ]ebe Imam Ali (AS), sun kasance ’ya’ya
da jikokin Sayyida Fatima (AS) kuma idan
mutum ya bibiyi tarihin wannan al’umma ta Manzon Allah (S) zai ga cewa
gudummuwar da zuriyyar Sayyida Fatima (AS) suka bayar wajen raya wannan addinin
na Musulunci da kuma kare shi, ya fi na kowa, kuma wannan a dukkan fagage na
addini zai ga sun ba da gudummuwa fiye da kowa.
Alal
misali, a fagen ilimi ne, a fagen gwagwarmaya ne, a fagen suluki zuwa ga Allah
(T)ne. kuma a wannan zamanin mutum ya duba ya gani zai ga haka. Misali a Iran,
Sayyid Imam Khumaini, a Ira}I, Sayyid Shahid Muhammad Ba}ir Sadr, Ayyatullahi
Sayyid Ku’i, a Labanon, Sayyid Shahid Abbas Musawi, ga Sayyid Nasrullah. Mu ma
a wannan nahiyar tamu Alhamdulillah ga Sayyid Ibraheem Zakzaky (H). Mu duba
irin gudummuwar da ya bayar kuma yake kan bayarwa wajen raya wannan addinin da
kuma kare shi,a wannan }asa da muke ciki. Shi ya sa in mutum ya yi bincike zai
ga akwai Hadisai masu yawa da suka zo, da suke nuna muhimmancin girmama zuriyar
Manzon Allah (S) da kuma kyautata masu.
Ga
wasu daga ciki 1. An samo daga Imam Ali (AS) ya ce Manzon Allah (S) ya ce;
“Mutum hu]u ni zan cece su gobe }iyama, mai girmama zuriyyata, mai biya masu
bu}atunsu, mai kai-koma cikin al’amuransu a lokacin tsananinsu, mai son su da
zuciyarsa da kuma harshensa”.
2. An
samo daga Imam Sadi} (AS) ya ce Manzon Allah (S) ya ce; “Wallahi ba zan yi ceto
ga duk wanda ya cutar da zuriyya ta ba”.
3. Manzon
Allah[S] ya ce; “Cetona ya tabbata ga duk wanda ya taimaki Zuriyyata
da hannunsa da harshensa da kuma dukiyarsa”.
4. Manzon Allah (S) ya ce; “Ku so
Zuriyyata kuma ko girmamasu”.
5. An samo daga Imam Ridha (AS) ya
ce; “Dubi zuwa ga zuriyata ibada ce, (shi wanda ya ruwaito wannan Hadisi ya ce
wa Imam Ridha (AS) dubi zuwa ga A’imma daga cikin zuriyar ko kuma dubi zuwa ga
Zuriyar Annabi? Imam Ridha (AS) ya ce masa a’a, dubi zuwa ga dukkan zuriyyar
Manzon Allah (S) ibada ce, amma matu}ar su ba su bar tafarkinmu ba. Kuma ba su
caku]a da sa~o ba.” Da dai Hadisai masu yawa a kan haka. Wanda ba za a iya kawo
su ba saboda gudun tsawaitawa.
Haka nan idan aka duba zuwa ga
darajoji da kuma matsayi na Sayyida Fatima (AS), za mu ga akwai Hadisai da dama
da suka zo a kan haka. Akwai ma sashen Malamai da suka rubuta littafai hususan
kan matsayinta da kuma darajojinta. Misali ga biyu daga cikin littafan. 1.
Fada’iluz-Zahra (AS) na [abrasi, 2.Fada’ilu Fa]imatiz-zahra (AS) na Hakim
Annaisaburi, da dai sauran su. Amma ga wasu Hadisai da suka zo dangane da
darajojinta da kuma matsayinta. Manzon Allah (S) ya ce, “Fa]ima Shugabar mataye
ce baki ]aya.” Sai aka tambaye shi Maryam ’yar Imran fa? Sai ya ce, “Ita Shugabar Mata ce, amma na zamaninta.” Haka nan ya zo cikin
littafin Kanzul Ummal da kuma Mizanul i’itidal, daga Manzon Allah (S) ya ce;
“Farkon wanda zai soma shiga Aljannah Fa]ima ce.”
Haka nan ya zo a kan cewa Fatima
(AS) ita ce Shugabar matayen Aljannah. Haka nan ya zo dai a cikin wa]annan
littafai da aka ambata, Manzon Allah (S) ya ce, Allah (T) yana fushi da fushin
Fatima (AS) yana yarda da yardarta. A wani Hadisi kuma Manzon Allah (S) ya ce;
“Duk wanda yake son Fatima (AS) ha}i}a yana so na, duk wanda ya fusata ta
ha}i}a ya fusata ni.”
A wani Hadisi kuma, Manzon Allah
(S) ya ce; “Da a ce kyau mutum ne, to da Fatima ce.” Da dai sauran Hadisai masu
yawa a kan fada’il ]inta. Kai ko dama a ce babu Hadisai da suke bayani dangane
da matsayinta, kasantuwarta ’ya ga Fiyayyen Halitta, mata ga Imam Ali (AS) Uwa
ga Imam Hasan da Husain (AS) ya isa ya zame mata babbar daraja da kuma matsayi,
ballantana kuma ga ‘nusus’ a kan haka, wato Hadisai da wasu ayoyi.
Da mutum ya duba da kyau zai ga
cewa komai na Sayyida Fa]ima (AS) tun daga wiladarta zuwa wafatinta ‘SAMAWIY’
ne. Wato ko dai daga sama ya zo, ko aka aiko da shi, ko kuma aka yo wahayinsa.
Ga misalai; Ya zo a Hadisai cewa ‘Nu]fa’ wanda ya kasance sabab na ]aukar cikin
Fatima (AS) ya kasance ne daga ’ya’yan itace da Manzon Allah (S) ya ci a
Aljanna, wa]anda suka kar~i haihuwarta daga Aljanna suka zo, su ne Mahaifiyar
Annabi Isa (AS), wato Maryam ’yar Imran, ’yar uwar Annabi Musa (AS), Kulsum,
Asiya ’yar Muzahim wadda Fir’auna ya kashe, da kuma Saratu matar Annabi Ibrahim
(AS). Ga mai bu}atar }arin bayani ko ganin haka. Ya duba littafin Muntahal Amal
juz’i na ]aya na Shaikh Abbas Al}ummy, wato marubucin Littafin Mafatihul Jinan.
Shi ma wannan suna nata, FATIMA,
saukakke ne daga sama, wato an yo wahayi ne a sa mata wannan suna. Haka nan
kuma ]aurin aurenta sai da aka yi a sama, sannan aka yi a }asa Likafaninta daga
Aljannah yake. Da dai sauran ababe nata samawiyya. Ya ma zo daga Ma’asumai (AS)
cewa; “Talauci ba ya shiga gidan da yake akwai mai suna Fatima (AS)”. Akwai
Hadisi da ya zo daga Imam Sadi} (AS) da ke nuni dangane da girmama sunan, da
kuma girmama wadda aka sa wa sunan. A ta}aice dai darajoji da falaloli na
Sayyida Fatima (AS) suna da yawan gaske
TARIHINTA
An
haifi Sayyida Fatim a (AS) a Makka, ranar Juma’a 20 ga watan Jimada Sani,
Shekara ta biyar, bayan aiko wa Manzon Allah (S) da sa}o. Akwai sashen Malamai
da suka tafi a kan cewa she}ara biyu bayan bi’isa ne. Amma su Malaman Ahlus
Sunna sun tafi a kan cewa she}ara biyar gabanin aiko Manzon Allah (S) ne aka
haife ta. Sunan Mahaifiyarta, kamar yadda aka sani, Khadijah (AS). Tana da shekara
biyar Allah (T) ya yi wa Mahaifiyarta rasuwa, domin ta rasu shekara 10 bayan
bi’isa. Har ila yau a wannan shekarar ce Allah (T) ya yi wa Abu [alib (AS)
rasuwa. Ya zo a kan cewa tsakanin rasuwar Khadija da Abu [alib (AS) kwana uku
ne. Shi ya sa shekarar aka yi mata la}abi da shekarar ba}in ciki. Bayan
rasuwarsu ne Manzon Allah (S) ya tafi [a’ifa domin isar da sa}o.
Wani ]an tambihi a nan shi ne,
Malaman Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) sun tafi a kan cewa ’ya’yan Manzon Allah
(S) baki ]aya an haife su ne gabanin aiko masa da sa}o, in ban da Sayyida
Fatima (AS) da kuma Ibrahim ]an Mariya. Su bayan bi’isa ne aka haife su. Har
ila yau akwai ayyukan da ake son aikatawa ranar wiladar Sayyida Fa]ima (AS),
daga ciki akwai Azumi, wato ana son mutum ya yi Azumi a ranar domin godiya ga
Allah (T) ga wannan babbar kyauta da ya bayar, da kuma yin Alhairai a ranar da
sadakoki ga muminai da kuma yin ziyara ga Sayyida Fa]ima (AS). Yadda ziyarar
take, mutum na iya komawa ga littafin Mafatihu. Har ila yau a irin wannan ranar
ne ta haihuwar Sayyida Zahra (AS) aka haifi Imam Khumaini, an haife shi ne 20
ga watan Jimada Sani a she}ara ta 1321 bayan hijira.
Sayyida Fatima (AS) tana da sunaye
da yawa da kuma la}ubba masu yawa. Imam Sadi} (AS) ya ce Fatima (AS) tana da
sunaye tara a wajen Allah (T), su ne: Fatima, Siddi}a, Mubaraka, [ahira,
Zakiyya, Radiyyah, Muhaddisa da kuma Zahra. A wata ruwaya, akwai Mardiyya, da
kuma Batul. Daga kuma cikin la}ubbanta, akwai Ma’asumma, Karima, Shahida,
Rashida, Sabira, Mu’azzama Mazluma da dai sauransu. Haka nan kuma tana da
kinaya da yawa, amma wa]anda suka fi fice su ne: Ummul A’imma da kuma Ummu
Abiha.
Ya zo a kan cewa Manzon Allah (S)
ne ya yi mata kinaya da haka. Manzon Allah (S) ya kasance yana girmama Sayyida
Fatima (AS) gayar girmamawa. Ya zo a kan cewa in ta zo wajen shi a gida yakan
tashi, ya ce ta zauna inda yake zaune. Haka nan Manzon Allah (S) ya kasance
idan zai yi tafiya, bayan ya bar gida, sai ya biya wajen Sayyida Fatima (AS) ya
yi bankwana da ita, sannan ya tafi, in kuma ya dawo daga tafiyar, sai ya biyo
gidan Fatima (AS), sannan ya wuce gida.
Sayyida Zahra (AS) ta tashi a
Makka, gaban Mahaifinta. Saboda haka dukkan tsangwama da wahalhalu da Manzon
Allah (S) ya fuskanta daga ma}iya a Makka wajen isar da wannan sa}o, a gaban
idonta suka wakana. Ya ma zo a tarihinta cewa, bayan rasuwar Mahaifiyarta
Khadija (AS), idan Manzon Allah (S) ya fita yin da’awa, kuma ma}iya suka yi
masa jina-jina, in har ya dawo gida, Sayyida Fatima (AS) ce ke wanke masa.
Akwai lokacin da ya je Ka’aba yana Salla, bayan ya yi sujuda ma}iya suka ]auko
tumbin dabba, wanda ya ru~e yana wari suka sa masa a baya. Sai aka je aka shaida wa Sayyida Zahra (AS) ita ta zo ta
]auke masa. Daga irin wa]annan ayyuka da take yi wa Manzon Allah (S), wasu
Malamai suke ganin wannan kinaya da Manzon Allah (S) yake yi mata na Ummu Abiha
ya samo asali. Haka wannan yanayi ya ci gaba da gudana har zuwa lokacin da
Manzon Allah (S) ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina.
Kafin
hijirarsa, ya yi umurni ga Imam Ali (AS) da ya kwana a shimfi]arsa, da kuma
mi}a masu ajiyoyi da amanonin kayyayakinsu. Bayan nan ya zo Madina ya same shi
tare da iyalinsa. Haka kuma al’amarin ya auku bayan Imam Ali (AS) ya mi}a
amanoni da kuma ajiyoyi na mutane, sai ya kama hanya zuwa Madina tare da
wa]annan bayin Allah (T), su ne Sayyida Fatima (AS) da Fatima ’yar Asad, wato
Mahaifiyar Imam Ali (AS), da Fatima ’yar Hamza, da kuma Fatima ’yar Zubair ]an
Abdul Mu]allib, tare kuma da wasu mazaje guda biyu, su ne Ai’man da kuma wani
da ake ce wa, Abu Wa}idil-laisi. Haka suka yi hijira daga Makka zuwa Madina,
suka bar Makka da rana, ido na ganin ido suka kama hanya.
Bayan fitarsu, sai {uraishawa suka
aiko maya}a takwas a kan su bi su da umurnin cewa su kashe Imam Ali (AS). Suka
bi su, suka same su a wani waje da ake ce wa Dajanan. Da Imam Ali (AS) ya ga
haka sai ya tsai da tafiyar, ya ce wa wa]annan mazaje guda biyu da ke tare da
shi, wato Ai’man da Abu Wa}id, da su gurfanar da ra}uman da wa]annan bayin
Allah (T) ke kai, ya sa a ]aure ra}uman. Bayan
haka ya tafi wajen su ma}iyan da takobinsa, sa-in-sa ta magana ta gudana a
tsakaninsu. Daga cikin abubuwan da suka ce wai shi da wa]annan bayin Allah (T)
su koma Makka ]au’an ko karhan. Haka dai musayar maganganu suka gudana. Daga
}arshe abin ma ya kai ga gumurzu. Tunda suka ga Imam Ali (AS) ya samu ]ayansu,
wanda ya fi za}ewa, ya rafke shi, ya sassare shi da takobi, ganin haka sauran
maya}an suka tarwatse suka gudu. Bayan haka sai su Imam Ali (AS)
suka ci gaba da tafiya har suka iso Madina.
Ya zo a kan cewa lokacin da Manzon
Allah (S) ya iso Madina, bai shiga Madina ba. Ya tsaya a wani waje ne da ake ce
masa }uba, har a lokacin wasu suka ce masa ya shiga Madina mana, ya ce, ba zai
shiga ba har sai ]an Amminsa da kuma ’yarsa sun iso, haka kuwa aka yi. Sai da
suka iso, sannan Manzon Allah (S) ya shiga Madina. An ce lokacin da Imam Ali
(AS) ya iso Madina }afafuwansa sun kukkumbura sun kuma tsattsage, saboda ya zo
a }asa tun daga Makka har zuwa Madina, ba a kan dabba ba.
Insha Allah a kashi na biyu na
darussa daga rayuwar Ummul A’imma, Fatima (AS) za a ]ora a kai. Wato rayuwar
Sayyida Fatima (AS) bayan komawa Madina.
No comments:
Post a Comment