Akhla}
~angare
ne na ilimin irfani,wato misali kamar yadda
ilimin fi}hu,yake
da manyan ~angarori guda biyu,wato Ibadat da Mu’amalat,
ilimin A}a’id
kuma yake da manyan ~angarori
guda biyar,Tauhid,Adl,Nubuwwa,Imama da kuma Ma’ad,to shima ilimin irfani yana da manyan ~angarori
guda biyu,sune AKHLA{,wanda wani lokaci
ake cewa IRFANIL-AMALIY,da kuma MA’ARIFA,wanda ake cewa IRFANIN-NAZARIY.
Wannan janibi na
akhla}
wasila ne,wato tsanine zuwa ga ma’arifa,wato sanin Allah[T] akan asasin zau}i
ko shu’uri,wato mutum da farko ya samu tsarkakuwa daga munanan ]abi’oi,bayan
haka ya siffantu da kyawawan ]abi’oi,to wannan
shine zai taimaka wa mutum ko kuma samun hanya wajen ala}antuwa
da Allah [T] da kuma damfaruwa da shi.Akan wannan asasin ne insha Allah, za’a soma gabatar da
darussa akan Akhla}.Wanda }ila zai iya ]aukan
lokaci ana gabatarwa. Amma
gabanin shiga cikin shi wannan darasin
na Akhla}, zai yi kyau da kuma muhimmanci yin
bayani ko da a dun}ule dangane da illmin
irfani.Ilimin irfani kamar yadda ake ce masa a madrasah ]inAhlul bait [AS].A
madrasah ]in Ahlus sunna, ana ce masa ilimin Tasawwuf,wannan
ilimi na irfani,ilimi ne mai zaman kansa,wato yana da is]ila-hohinsa
da littafan sa da kuma malaman sa.Alal misali ga wasu daga cikin fitattun
malaman sa da suka kasance a wannan zamani.Ayatullah Bahjati,Ayatullah sayyid Ali
Al-}adiy,Ayatullah
sheikh Hasan Ali Al-isfahaniy,Ayatullah mirza Jawad malakiy Attab-riziy da kuma Ayatullah Sayyid Abdul-Aa’la
Assib-ziwary.Dukkan wa]annan malaman da
aka ambata, bawai kawai malamai ne a fannin ba,a’a sun fitar da malamai masu
yawan gaske a fannin ilimin irfani,wato urafa’u.Ban da malaman da suka yi fice,
a wasu fannonin wanda in ka bincika tarihin rayuwar su, za kaga sun yi fannin ilimin irfani a ]aya
daga cikin wa]annan malaman.Misali anan shine ,Allama
Taba-taba’I,wato wanda yayi tafsirin almizan,yayi karatun irfani ne awajen
Ayatullah sayyid Aliy Al-}adiy,har ma yana
yawan cewa wannan uslubin tafsirin sa daga Ayatullah }adiy
ne.misali kuma,Imam khumaini yayi karatun ilimin irfani a wajen,Ayatullah Mirza
Jawad Attab-riziy da dai sauran wasu malamai fitattu, a wannan zamanin da suka yi
karatun irfani a wajensa. insha
Allah wani lokaci za’ayi rubutu dangane da wa]annan
malaman da aka ambata, domin sanin
tarihin su da rayuwar su da karamomin su, da dai makamantan su.Haka nan shi ilimin
irfani ba wai kawai ilmi ne da yake cin
gashin kansa bane.A’a ilimi ne da yake taimaka wasu fannoni ilimi wajen kamalar
su.Alal misali fannin ilmin fi}ihu,zamu ga a fi}ihu
an koyar da mutum yadda zai yi sallah.sharu]]an ta, da
abubuwan dake ~atata, amma abin da ya shafi ba]inin,ita
salla ]in,wato
ruhin ta,kamar khushu’i aciki,halartar
da zuciya acikin salla,ta’azimin Allah[T] da tsoronsa aciki,to duk wa]annan
dama wasun su, da ba’a ambata ba na ruhin sallah.shi ilimin irfani ne yake
bayanin su,haka ma sauran ibadodi kamar su Azumi,Hajji da dai sauransu,ruhin wa]annan
ayyukan,to ilimin irfani ne ke bayanin su.To kaga ke nan a nan ya taimaka wa
ilimin fiqhu wajen kamalar sa, a dun}ule abin da ake
nufi idan fiqhu yayi bayani dangane da zahirin wa]annan
ayyuka na ibadodi,shi irfani sai ya kammala da bayani dangane da ba]ininsu.Haka
nan kuma mu ]auki ilimin A}a’id,misali
Tauhid,za kaga ya koyar da mutum sanin Allah[T] ta hanyar siffofin sa,sunayen sa,
da dai makamantan su,Amma za kaga galibi
wannan yakan tsaya wa mutum a matsayin ii’ti}adi,ga misali guda ]aya, a tauhidi,za’a koyar da mutum
Allah mai jine,kuma mai gani ne.Amma samun
zau}in shu’urin cewa Allah[T] na ganin mutum, kuma yana jinsa wanda
wannan zai iya kai wa ga shamakance mutum daga sa~a
wa Allah[T].To anan ilimin irfani ke taimakawa wajen samun haka.Kaga anan ya
taimaka wa ilimin A}a’id, wajen samun
kamalar sa.Wato in shi ya gina akan ii’ti}adi,shi kuma
irfani sai ya gina yadda zaka samu zau}i da shu’urin
wannan ii’ti}adin.To
haka nan ma a Nubuwwa,wato shi irfani zai taimaka maka wajen kyautata ala}ar
ka da Manzon Allah [S] a ba]inance,ba wai
kawai a matsayin ilti}adi ba.Haka nan
Ma’ad,yadda zaka dun ga shu’urin lahira kamar kana ganinta.Bawai a matsayin ilti}adi
ba.A ta}aice
dai a nan samun wannan shu’uri da kuma zau}i, ya taimaka wa ilimin A}a’id,
wajen kamalar sa.saboda haka kamar yadda aka ambata a baya cewa ilimin irfani,
ilimi ne mai zaman kansa,kuma mai taimaka wa wasu fannonin ilimi domin kamalar
su,
Manufa da kuma gayar wannan ilimi na irfani
shine ya kai mutum matsayin insa-niyyah da kuma ubu-diyya.Abin da ake nufi da
insa-niyyah anan shine, mutum ya zama insan[mutum] a ruhinsa,bawai hayawan
ba,wato[dabba] ba, domin mutum zai iya zama a zahirinsa shi insan ne, amma a ba]ininsa
ba insan bane, hayawan ne.To anan mutum zai fahimce yadda Imam khumaini a
littafan daya rubuta dangane da irfani yana yawan magana akan mutum ya zama
insan,har ma yakan ce zama insan yana da wahala.Akwai ma wani waje a cikin littafinsa na jihadul
Akbar, yana
cewa zama malami yafi sau}i kan zama insan,wannan magana ce ta Arifai.wato
mujahadar da mutum yake bu}ata wajen zama malami,bata kai mujahadar da mutum
yake bu}ata
wajen zama insan ba,wato mujahadar zama insan tafi wahala,insha Allah a darasin
Akhla},
za’a ]an
fa]a]a
bayani dangane da zama insan a ruhi.Hadafi na biyu na ilimin irfani,wato kai wa
ga matsayi na ubudiyyah,wato mutum ya zama Abd[bawa] na Allah[T],ba Abd na nafs
]insa
ba ko kuma Abd na shai]an,kuma idan
mutum ya kai wannan matsayin na ubudiyya,to ya kai matsayin da shai]an
be da sul-]a akansa,kamar yadda Allah[T] yake fa]i acikin
littafinsa,wato yake cewa shai]an ‘’bayina baka da sul-]a
akansu’’,wannan kenan dai a ta}aice dangane da
ma’anar ilimin irfani da abin daya }unsa da kuma
hadafinsa.
Dawowa gashi darasin
Akhla} ]in.Amma gabanin shiga cikin darasin Akhla} ]in, zai yi kyau yin
bayani dangane da muhimmancinsa da kuma hadisai da aka samo daga Manzon
Allah[S] da kuma Ahlul bayt[AS] da suke nuni ga matsayinsa da kuma falalarsa.muhimmancin
Akhla}
bai ta}aita ga
mutum shi }ashin kansa ba,ko
kuma rayuwarsa tsakanin mutane,a’a,hatta dabba in ka kyautata mata ko ka munana mata zai iya kasancewa
sanadiyyar shiga mutum Aljannah ko wuta.Alal misali }issar
wani mutum da yazo akan cewa yana jin }ishi sai yaje wata
rijiya ya ]ebo ruwa ya sha,bayan yasha sai ya juya zai tafi sai ga wani kare yazo yana lallagi na
alamun }ishi,sai
wannan mutum daya ga haka sai ya ]ebo ruwa a rijiyar
ya baiwa karen yasha.bayan wuce warsa,
sai Allah[T] ya yi wahayi ga
Annabin zamanin cewa ya fa]a
wa wannan mutumin,Allah ta’ala ya gafarta masa saboda wannan aiki da yayi, kuma
zai shigar dashi Aljannarsa.Haka }issar wata mata wadda ta kasance tana da mage,amma sai ta ]aure
magen bata ba ta abinci,ba ta kuma sake ta ba domin ta nemi abinda zata ciba.to
bayan rasuwar matar,yazo akan cewa Allah[T]
ya saka ta a wuta.to mu duba wa]annan }issar
da tazo a hadisan na mutanen biyu,wannan
sanadiyar kyakkyawar akhla}, ga kare ya shiga
aljannah,ita kuma sanadiyyar mummunan akhla} ga mage ta shiga wuta,idan wannan sakamakon akhla} ya kasance
ga dabba’ to ina ga sakamakon Akhla}, kyakkyawa ko mummuna
ga mutum ]an uwanka ,wannan ka]ai
ya isa ya nuna muhimmancin Akhla}.
Kuma ga wanda yake ma’abocin addini,kyakkyawan Akhla}
babbar hanya ce tayin da’awa,domin tafi yin tasiri ga ruhin mutum,in mutum ya duba tarihin
Manzon Allah[S] lokacin da ya soma da’awa a makka,da yawa sun musulunta ne
sakamakon Akhla} ]in
Manzon Allah[S].akwai misali da yawa,amma ga guda
]aya,yazo
akan cewa lokacin da manzon Allah[S] yana makka,to hanyar da yake bi zuwa
ka’aba, sai wani mutum ya ]aukar wa kansa zuba }ayoyi
a hanyar,in Manzon Allah[S] yazo wucewa sai ya kaudasu,wa she gari ya }ara
sawa,Manzon Allah[S] ya kawar,haka yayi tayi har lokaci mai tsawo,wata rana Manzon Allah[S] zai
je ka’aba domin yayi da’awa, kamar yadda ya saba ,sai bai ga }ayoyin
ba,kwana ]aya,kwana biyu haka,sai ya bincika aka ce masa
ai bai da lafiya ne,shine Manzon Allah[S] ya tafi har gidansa da nufin ya
gaishe shi,shine daya isa gidan yake ce masa,Abin
da nasaba gani akan hanya kwana biyu ban gani ba,sai na tambaya aka ce baka da lafiya ne, shine na zo domin in gaishe
ka,jin haka mutumin nan take yayi kalmar
shahada na shiga musulunci,mu duba yadda kyakkyawar Akhla} ya
canza shi,
Haka
nan kyakkyawar Akhla}, yakan
mai da ma}iyi ya zama masoyi,shima wannan akwai misali da
yawa daga rayuwar Aimma na Ahlulbayt [AS],amma ga guda uku,wata rana Imam Hasan[AS] yana tafiya sai wani mutumin sham ya ganshi,kawai sai ya kama zaginsa da
kuma la’antarsa[Wa’iyazubillah].Da yake mutanen sham haka aka ginasu,wato zagi da kuma
la’antar Ahlulbayt [AS] musamman ma ga Imam Ali [AS],domin ta kai ga cewa a hu]ubar juma’a, liman ba zai }areta ba sai yayi wannan la’antar ga Imam
Ali[AS] .Haka wannan mummunan aikin ya kasance
tsawon shekaru 70,zuwan umar ]an
Abdul-aziz ya hana wannan la’antar,ya maye wajen wannan la’antar da wata aya,[ga mai son ganin ayar ya duba cikin suratu-Nahal ayata 90,wato
Inna-llaha-ya’amuru bil-adli…….]wanda har yanzu masu khutbah na juma’a, a duniyar
sunna zaka ji suna biya ta.shi yasa idan
mutum ya dubi jawabin da sayyida Zainab [AS] tayi a kufa na wa}i’ar karbala,zai ga tana da bambanci akan wadda tayi
a sham.Domin su mutanen kufa sun san Ahlulbait[AS] da matsayinsu,sa~anin mutanen sham,basu san Ahlulbayt [AS]
ba,ballantana sanin matsayinsu.Mu dawo ga shi wannan mutumin da yayi zagi da
la’anta ga Imam Hasan [AS],yana tayi,Imam Hasan [AS] bai ce masa komai ba sai
da ya gama,Imam Hasan [AS] ya dube shi,
yayi murmushi yace ,ya kai wannan Dattijo! Ina tsammanin kai ba}o ne, ina zaka je,in baka san wajen ba, ka fa]i akaika? In kuma ba inda zaka sauka kazo a baka masauki,in kuma kana da bu}ata ka fa]i a
biya maka.yace in ma zai yiwu kazo ka ba}uncemu mana,ka zauna wajenmu kafin ka koma sham.jin wa]annan kalmomi na Imam Hassan [AS] nan take, sai
wannan mutumin ya fashe da kuka,sai yace wa Imam Hasan [AS],lallai na shaida kai
khalifan Allah [T] ne a doron }asa,kai
da babanka,ada babu wanda nafi }i kamarku,amma yanzu kai kafi soyuwa gare ni
akan kowa a duniyar nan,yace wajenka
nake so in sauka.Haka ya zauna wajen Imam Hasan [AS] har lokacin da zai koma
sham.yazo akan cewa tun daga lokacin ya shiga cikin shi’a ]in Imam Hasan [AS].Na biyu yazo akan cewa wata rana
Imam Zainul Abidin [AS] ya fito sai wani mutum ya bishi yana zaginsa,nan take
mabiyansa da kuma bayinsa suka yun}ura
zasu auka wa mutumin,sai Imam Zainul Abidin [AS]yace masu a’a,sai Imam Zainul
Abidin [AS] ya dubi mutumin yace masa,Al-amarinmu ya ~oyu a gare ka,kana da wata bu}ata mu taimaka maka akai? Jin haka sai mutumin yaji
kunya,Imam Zainul Abidin[AS] ya mi}a
masa abayarsa,yace kuma abashi Dirhami dubu,to tun daga lokacin duk in da yaga
Imam Zainul Abidin [AS] sai yace lallai na shaida kai ]an
Manzon Allah[S] ne.Na uku yazo akan cewa akwai wani a madina,ya kasance yana
cutar da Imam kazim [AS] gayar cutarwa,domin duk in da yaga Imam kazim [AS] sai ya zage shi,ya
zagi Imam Ali [AS],sai sahabbansa suka ce masa kabarmu mu kashe wannan fajirin
mutumin,sai Imam kazim [AS] ya hana su,ya kuma tsawata akan haka gayar
tsawatawa.sai wata rana Imam Kazim
[AS] ya tambayi mutumin aka ce ya
tafi gona,sai Imam Kazim [AS] ya bishi gonar da kansa,lokacin daya shiga gonar da dabbar da yake kai,mutumin na ganinsa,yace kada ka taka mani shuka cikin
fushi,Imam Kazim [AS] yayi taka-tsantsan bai taka masa shukar ba,har ya isa wajensa,sai Imam Kazim [AS] ya
sauka daga kan dabbar yana jansa da maganan da kuma murmushi.Daga }arshe yace masa,nawa ka kashe a wannan shukar taka?yace dinari 100, yace to nawa kake tsammanin
zaka samu in ka girbe?yace ni bansan gaibi ba.sai Imam Kazim [AS] yace masa,ai
nace ne nawa kake tsanmani zaka samu,yace,to ina tsammanin dinari 200.Sai Imam
Kazim [AS] ya mi}a masa jaka, acikinta akwai dinari 300, yace masa
wannan shuka taka Allah yasa mata albarka,abinda kake tsammani zaka samu na dinari 200 in ka girbe,Allah yasa
haka.jin haka sai wannan mutumi ya sun baci Imam kazim [AS] yace masa ka yafe
mani duk abinda nayi maka,sai Imam kazim [AS] yayi murmushi yace masa ba
komai.sai ya juya ya tafi.Bayan haka In
da Imam kazim [AS] yake zama a masallaci
shi da sahabbansa,mutumin na komawa gida,sai yatafi masallaci ya zauna
wajen,shine su sahabban Imam kazim [AS] da suka ganshi sukace masa kai ya akayi
haka? Sai yace musu Allah [T] shine mafi sanin in da yake sa sa}onsa,Daga nan ya juya ya shiga addu’a, yana Allah ka
saka wa Abul Hasan [AS][wannan kinaya ne na Imam Kazim] da alheri,to lokacin da
Imam Kazim [AS] ya koma gida,sai yace ma wa]anda
suka nemi damar ya basu izini su kashe shi, baku ga yadda na gyara al-amarinsa
ba,kuma na tsaru daga sharrinsa,ga mai bu}atar
ganin wa]annan }issoshi
dama }ari yana iya duba littafi mai suna A’IMMATUNA,mu
duba yadda wa]annan kyawawan Akhla} na
Imaman da aka ambata suka canza ma}iya
suka koma masoya
No comments:
Post a Comment