Saturday 9 February 2013

Tarihi da rayuwar Shahid Ayyatullahi Sayyid Muhammad Ba}ir Sadr


Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Jimadal Ula, 23 gare shi ne a shekara ta 1400 Hijiriyyah, a miladiyyah kuma 9/4/1980 shahadar Ayatullahi Sayyid Muhammad Ba}ir Sadr, ta kasance, a daidai wannan lokaci akan yi tarurruka, musamman a Ira}i da kuma Iran, domin tunawa da shi da kuma shahadarsa, wanda a irin wa]annan tarurruka akan tunatar da juna dangane da tarihinsa, da kuma wasu ~angarori na rayuwarsa, da nufin su kasance darussa ga mahalarta da kuma wa]anda za su ji ko su gani daga baya.

A irin wa]annan tarurruka, a taron da aka yi na shekara 20 da shahadarsa, Lajnar da suka shirya taron mai taken ‘Mu’utamaral-alami-li-imami Shahidus Sadr’ suka bu}aci ]aya daga cikin manyan almajiransa mafi kusa da shi, wanda kuma ya kasance tare da shi a gidansa a watannin }arshe na rayuwarsa, mai suna Shaikh Muhammad Ridah Annu’umaniy da ya rubuta littafi dangane da tarihin Shahid Sadr da kuma rayuwarsa, musamman a fagen gwagwarmaya da azzalumai da kuma sa’ayi wajen kafa Hukuma Islamiyya a Ira}i. A kan asasin haka ya rubuta littafi juzu’i biyu, ya sa masa suna “SHAHIDUL-UMMA-WA-SHAHIDUHA”. Wanda a cikin wannan littafin ya kawo tarihinsa daidai gwargwado. Tun daga wiladarsa har ya zuwa shahadarsa, ibadarsa, ‘Akhla}’ ]insa, zuhudunsa, karamomisa da dai sauransu. Saboda haka abubuwan da za a kawo a nan na tarihinsa, da kuma sashen rayuwarsa, mafi yawansu daga wannan littafi aka ciranto.
Da farko dai Shahid Ayyatullah Sayyid Muhammad Ba}ir Sadr, an haife shi ne a Khazimiyyah, wato garin da kabarin Imam Kazim (AS) da kuma Imam Jawad (AS) suke ranar 25 ga watan Zul}a’ada shekara ta 1353. Nasabarsa tana tu}ewa ne ga Imam Musa Alkazim (AS). In mutum ya duba cikin wannan littafi da aka ambata a sama, juzu’i na ]aya zai ga ya kawo jerin sunayen wannan nasaba tasa, wane ]an wane, har ya zuwa Imam Kazim (AS). Kuma wani abin mamaki a jerin wannan nasaba baki ]ayanta daga Malami sai Mujtahidi, wato baki ]ayan mahaifansa da kakanninsa Malamai ne. Shi ne mai littafin yake cewa wannan wata baiwa ce da fifiko wadda ka]an ake samun haka cikin mutane.
Sunan Mahaifinsa Sayyid Haidar, Mahaifiyarsa kuma ’yar Ayatullah Shaikh Abdul Husain Ali Yasin ce. Ita ma kamar yadda ya zo a tarihinta Malama ce, abida, zahida. Yana da shekara biyu da wata bakwai a duniya, Mahaifinsa ya rasu. Su uku ne a wajen mahaifinsu, shi da kuma wansa Ayytullah Sayyid Isma’il Sadr da kuma }anwarsa wadda aka fi sani da Bintul-Huda, sunanta Aminatu. Ita ma shahada ta yi. Ranar da Saddam ya kashe Sayyid Muhammad Ba}ir Sadr a ranar ya sa aka kashe Bintul-Huda ta hanyar sa mata guba a shayi (tea) a kurkuku. Shi ne har ma na kusa da shi Saddam suka ce masa tunda ya kashe Sayyid Sadr ita ya }yale ta mana, sai ya ba da amsa da cewa, bai son ya yi kuskuren da Yazidu ya yi, ya kashe Husain, amma bai kashe Zainab ba. Mu duba wannan magana, shi ya sa a wannan zamani namu in mutum ya bincika zai ga cewa babu wani wanda ya kashe zuriyar Manzon Allah (S), wato jikokinsa kamar yadda Saddam ya kashe su. Ga mai bu}atar bincikawa yana iya duba littafin da aka ambata a sama.
Ayyatullah Shahid Sadr ya rayu shekara 47 ne a duniya, ya kasance yana da ’ya’ya shida, mata biyar, namiji ]aya, sunansa Ja’afar .Shahid Sayyid Sadr, Ya fara karatunsa a Kazimiyya a lokacin, kamar yadda ]aya daga cikin Malaman da suka koyar da shi a nan Kazimiyya ya ce; “Ha}i}a ya kasance duk fannonin da muke koyawa a wannan makaranta suna }asa da mustawarsa.”
Lallai duk wanda ya san Shahid Sadr, ko ya karanta tarihinsa, zai tabbatar da haka, cewa mutum ne wanda Allah (T) ya ba shi gayar haza}a da kuma basira. Alal misali ya zo a tarihinsa cewa ya kai matsayin Mujtahidi bai kai shekara 10 ba a duniya, wanda wannan ka]ai ya isa ya nuna cewa lallai wannan mutum ne na daban. Wato shigen mutanen nan ne da akan samu jefi-jefi a cikin tarihi, wa]anda a tarihi Allah (T) kan za~a ya ba su haza}a da basira ta musamman domin su kasance kyauta da baiwa ta musamman ga bayinsa.
Haka nan idan mutum ya duba rubuce-rubucen da ya yi da kuma sauyi da kawo  wasu fannoni na ilimi, misali a fanin Usulul-Fi}h, falsafa, fannin tattalin Arzi}i, a kan asasin mahanga ta Musulunci da dai sauran fannoni na Ilimi, zai fahimci irin wannan haza}a da basira da Allah (T) ya ba shi. Haka nan idan mutum ya dubi irin Malaman da ya fitar, misali su Ayyatullah Sayyid Shahid Ba}ir Hakim, Ayyatullah Sayyid Kazim Hairi, Ayyatullah Sayyid Kamal Al-Haidari da sauran Malamai da ba a ambata ba. Shi ma wannan ya nuna lallai baiwa ce da kyauta da Allah (T) ya bayar.
Ayyatullah Shahid Sayyid Ba}ir Sadr ba wai kawai a fagen ilimi ne ya yi fice ba. A’a akwai wani fage da ya yi fice a kai, wanda kuma ya bambanta su da mafi yawan Malamai da ke }asar Ira}i a lokacin. Wannan fage kuwa shi ne fagen gwagwarmaya. Wato gwagwarmaya domin tabbatar da Hukuma Islamiyya a }asar Ira}i. A wannan fage na gwagwarmaya domin tabbatar da addinin ya samu shahada shi da ’yar uwarsa Bintul-Huda da kuma da yawa daga cikin almajiransa.
Ga sunayen Shuhada’u 12 daga cikin almajiransa:- 1. Shahid Hujjatul-Islam Sayyid {asim. 2. Shahid Hujjatul-Islam Sayyid Muhammad Husain. 3. Shahid Hujjatul-Islam Sayyid Ali Akbar. 4. Shahid Hujjatul-Islam Shaikh Muhammad Yunus. 5. Shahid Hujjatul-Islam Shaikh Mahdi Samawi. 6. Shahid Hujjatul-Islam Sayyid Abdulrahim. 7. Shahid Hujjatul-Islam Sayyid Husain. 8 Shahid Hujjatul-Islam Shaikh Afifi. 9. Shahid Hujjatul-Islam Shaik Hassan. 10. Shahid  Hujjatul-Islam Shaikh Muhammad Ali. 11.Shahid  Hujjatul-Islam Sayyid Izzud-Din. 12. Shahid Ayyatullah Sayyid Kazim Shubbar, wanda wannan ma dattijo ne. Lokacin da Allah ya azurta shi da shahada yana da shekaru sama da 90, shi ya sa ake yi masa la}abi a lokacin da Shaikhul Shuhada’u, wanda wannan ya isa ya nuna gayar zalunci na Saddam a lokacin. A ce dattijo wanda ya kusan shekaru 100, Malami wanda ya kai matsayin Ayatullah, kuma jinin Manzon Allah (S) wato Jikansa za a kashe? Shi ya sa ya zo a tarihin shahadar Sadr cewa, yana yawan tunawa da shi da dai sauran Shuhada’u masu yawan gaske da gwamnatin Saddam ta kashe a lokacin. Ga mai bu}atar ganin sunaye da tarihi da kuma rayuwar wa]annan Shuhada’u masu yawan gaske yana iya duba littafi mai suna Shuhada’ul Ilmi-wal-fadhila-fil-Ira}”. In mutum ya duba littafin zai ga akwai Shuhada ]ai-]ai har 120 a ~angaren Malamai kawai.
Shahid Sayyid Sadr ya fuskanci jarabawowi masu yawan gaske, ta kuma fuskoki daban-daban, musamman ma ta fuskancin Hukuma, wato Saddam da gwamnatinsa a lokacin. Alal misali ga wasu daga cikin jarabawowin da ya fuskanta;
1. Kamu da ]auri.
2. Yun}urin kashe shi, ta fuskoki daban-daban.
3. |ata sunansa ta fuskoki daban-daban.
4. Sa ’yan le}en asiri gare shi ta fuskoki daban-daban na mutane da sanya wasu na’urori na zamani, masu na]ar bayani na ji da kuma gani.
5. Yi masa ]aurin talala na tsawon wata tara.
6. Cutarwa da kuma musgunawa ga mabiyansa.
7. Daga }arshe kama shi da azabtar da shi da kuma kashe shi.
Wa]annan wasu ke nan daga cikin jarabawowin da ya fuskanta ta ~angaren Hukuma a dun}ule. Amma a warware ga ]an bayani a kai.
1. Kamu da ]auri. Kamu na farko da aka yi masa shi ne na 1972, jami’an tsaro suka je gidansa da tsakar dare suka zagaye gidan domin su kama shi, sai ta bayyana masu ashe ba ya gidan, yana kwance a ]aya daga cikin Asibitoci na birnin Najaf, saboda rashin lafiya da yake fama da ita. Amma duk da haka suka bi shi Asibitin, suka kama shi suka sa masa sar}a wato Ankwa a hannu suka kai shi Kufa, a wani Asibiti da ake jinyar tsararru. Washegari labari ya bazu na an kama Sayyid Sadr, jama’a ko suka dinga tururuwa zuwa Asibitin da kuma kiran dole a sake shi. Ganin haka aka sake shi, amma asalin kamun domin a kai shi Bagdad ne.
Sai kuma na biyu wanda aka yi masa a 1977, bayan wata wa}i’a da ta auku, a cikin wa}i’ar an samu Shuhada masu yawa. Da yake Muzaharori ne aka yi na nuna bore da kuma tawaye ga gwamnatin Saddam a garuruwa daban-daban, musamman ma a Najaf.
Kamu na uku shi ne wanda aka yi masa a 1979. A daren da za a yi wannan kamun tun da yamma jami’an tsaro suka zagaye unguwar da yake da kuma layin da ke zuwa gidansa, wanda ke nuni ga dukkan alamu akwai abin da ke shirin faruwa. Shi ne wani daga cikin almajiransa ya je ya shaida masa ga abin da yake faruwa. Shi ne ya ce; “Ba matsala.” Ya ce; “Ai ni ina so ne ma su kashe ni, }ila wannan ya zama sanadiyyar farkawar mutanen Ira}i da kuma gwagwarmaya domin kafa Hukuma Islamiyya.”
Ilai ko da tsakar dare suka iso gidan domin su kama shi. Shi Shugaban jami’an tsaron ya ce wa Sayyid Sadr wai Hukuma ce take son ganin sa domin su tattauna. Ya ce bai da ~ukatar haka. Jami’in tsaron ya ce; “Ai ko babu makawa.” Sai Sayyid Sadr ya ce masa, “Ni dai in don haka ne ba zan je ba. Amma in kamu ne bisimillah.” Sai ya ce, “e kamu ne.” To a nan ne Sayyid Sadr ya yi masa jawabi kan irin zalunci da musgunawar da suke yi ma mutane. Daga }arshe bayan jawabin ya ce masa ya tashi su tafi.
Wasu ’yan uwa ma nan suka ce, sai dai a tafi da su, su ma ana cikin haka sai Mahaifiyar shi Shahid Sadr ]in, duk da cewa ta tsufa sosai da }yar take tafiya, amma ta fito ta ce wa jami’an tsaron, ita ma a kama ta a kai ta duk inda za a kai ]anta. Lokacin da ake wa]annan abubuwa, }anwarsa Bintul-Huda, har ta riga ta isa wajen motocin sojoji da ’yan sanda da suka zo, an ce adadin su ya kai sama da 300. Shi ne ta yi masu jawabi, take ce masu; “Ku duba duk da irin wannan muggan makamai da kuma yawanku, ]an uwana bai da makami, bai da sojoji, amma kuna cikin tsoro, in ku ba matsorata ba ne, me ya sa za ku zo da tsakar dare domin ku kama shi? To me kuke yi ma tsoro, ku tambayi kawukanku.” Ta juya ta dubi ]an uwanta Sayyid Sadr ta ce; “Ya ]an uwana! Ka bi su, Allah (T) zai kiyaye ka, zai taimake ka, wannan ita ce hanyar Kakanninka tsarkaka”.
Bayan an tafi da Sayyid Sadr, safiya na yi Bintul-Huda ta tafi {abarin Imam Ali (AS), ta ce; “Ya Kakana! Ya Amirul Muminin! An kama ]anka Sadr, ya Kakana ina kai kukana ga Allah (T) da kuma gare ka, dangane da wannan zalunci da musgunawa da ake yi mana.”
Bayan haka ta juya ga jama’a da ke haramin Imam Ali (AS) a lokacin. Ta ce; “Ya ku Muminai! Shin yanzu za ku yi shiru alhalin an kama Shugabanku an kulle a kurkuku, ana azabtar da shi? Me za ku ce wa Kakana gobe }iyama, in ya tambaye ku dangane da wannan shiru naku? Saboda haka ku fita ku yi Muzahara, ku nuna ba ku yarda ba.”
Nan take daga Haramin Ali (AS) aka fara Muzahara, aka shiga cikin gari. Ganin haka Hukuma hankalinta ya tashi aka sako shi, amma lokacin da aka sake shi ya ce, ba inda zai je sai an saki wa]anda aka kama tare da shi da kuma wa]anda aka kama a Muzaharar da aka yi. Ya zo a kan cewa a Muzaharar sun yi kame da yawa.
Bayan fitowar Sayyid Sadr ta bayyana ashe a wannan kamen sun so su kashe shi ne, kasantuwar juyin Musulunci da suka ga ya auku a Iran }ar}ashin Jagorancin Imam Khumaini ({S) don tambayoyin da suka yi masa lokacin da yake tsare suna da ala}a da Imam Khumaini da kuma shi wannan juyin da ya auku. Wannan ma yana daga cikin jarabawowin da Sayyid Sadr ya fuskanta, musamman daga wajen hukuma a lokacin, wato ala}antuwarsa da Imam Khumaini.
Kamar yadda aka sani, Imam Khumaini a lokacin gudun hijira ya zauna shekara 15 a birnin Najaf, a wannan zama da Imam Khumaini ya yi a Najaf, a lokacin an ce an samu Malamin yana da ala}a da Imam Khumaini a bayyane, to wannan jarabawa ce babba tsakaninsa da Hukuma.
Ta yiwu wani ya yi mamakin abin, bacin gudun tsawaitawa da an kawo misalai na jarabawowi daban-daban da wa]anda suka ala}antu da Imam suka fuskanta daga gwamnatin Saddam , amma duk da irin wannan jarabawa ta ala}antuwa da Imam Khumaini, Shahid Sayyid Sadr shi ne Malami guda ]aya a cikin fitattun Malamai da ke binin Najaf a lokacin, ya fito a bayyane ~alo-~alo yana nuna goyon bayansa ga Imam Khumaini ({S), wuce nan ma ya ce wa almajiransa, su dinga halartar darasin Imam Khumaini, kuma baya ga haka al’amuran da suke gabatarwa na gwagwarmaya domin tabbatar da Hukuma Islamiyya a Ira}i, yakan tuntu~i Imam Khumaini a kai. Shi ya sa ranar da Imam zai bar birnin Najaf, Sayyid Sadr ya tafi domin su yi sallama da kuma bankwana da shi yake cewa; “Tafiyar Imam Khumaini daga birnin Najaf hasara ce babba gare ta”.
Haka nan bayan da aka yi juyin Musulunci a Iran ya fito a bayyane yana nuna goyon bayansa, ya kuma sa a yi Muzahara a garuruwa daban-daban a Ira}i domin nuna farin ciki da kuma goyon baya ga juyin. Duk da cewa shi wannan juyi na Musulunci ya auku ne shekara ]aya gabanin shahadarsa, amma ya ba da gudummuwa ta fuskoki daban-daban ga juyin. Ga mai bu}atar ganin gudummuwar da ya bayar da kuma jarabawowin da ya fuskanta domin ala}antuwarsa da Imam Khumaini ({S) da kuma tambayoyin da aka yi masa, lokacin da yake hannun jami’an tsaro da aka ce suna da ala}a da Imam Khumaini, ya duba littafin da aka ambata a sama.
Juyin Musulunci da ya auku a Iran a lokacin sai ya }arfafa wa mutanen Ira}i gwiwa, musamman ma’abota gwagwarmaya. Saboda haka, a lokacin sai mutane daga garuruwa daban-daban na Ira}i suka dinga zuwa gurin Sayyid Sadr a Najaf domin su yi bai’a gare shi. Ganin haka Hukumar Saddam hankalinta ya tashi, saboda gudun abin da ya auku a Iran na juyi kada ya auku a Ira}i. Sai suka fito da sabon salo na kashe Sayyid Sadr. Amma ta fuskar da ba za ta bayyana cewa Hukuma ce ta kashe shi ba. Wannan yun}urin na kisa sun yi ta fuskoki guda biyar, amma duk Allah (T) ya kare shi.
Ga fuskokin guda biyar. 1. Ha]a fa]an }arya. Abin da suka shirya shi ne, za a samu jami’an tsaro guda biyu kowanne da bindiga, daidai lokacin da Sayyid Sadr ya fito gida zuwa wajen karantarwarsa, su yi kamar suna fa]a da junansu, can sai ]ayansu ya harba bindiga, amma nufinsa ya yi saitin Sayyid Sadr domin ya same shi, wato daga baya sai a ]ora alhakin abin a kan kuskure ne, ba shi ya nufa ba.
 2. Yun}urin tarwatsa gidan da yake ciki ta hanyar bom da suka shirya a kan cewa bayan sun gano inda mai yin hidima a gidan yakan yo sayayya, sai ya zama a ha]a baki, bayan ya sai abin da ya saya an sa a leda, a ~oye sai a sa bom a ciki. Sun aiwatar da hakan, amma Allah (T) ya kiyaye.
3. Haifar da ambaliyar ruwa na da gangan, da yake ya zo akan cewa akwai dam a bayan unguwar da Sayyid Sadr yake, sai a sako dam ]in, duk da sun san cewa ba shi ka]ai zai shafa ba. Sun aiwatar, nan ma Allah (T) ya kare shi.
4. Yun}urin kashe shi ta hanyar haifar da hatsarin mota da gangan, wato kamar yadda aka yi wa Hasan Albanna, nan ma Allah ya kiyaye shi.

5. Amfani da ]an kwangilar kisa. Suka bai wa wani wannan kwangilar, wata rana ya zo da shirin ya kawo ziyara ga Sayyid Sadr kuma yana son ya gana da shi a ke~ance bayan sun ke~anta da Sayyid, sai ya ji jikinsa na makyarkyata, hannunsa na rawa. Nan take sai ya tona asiri. Ya ce lallai shi Hukuma ce ta ba shi kwangilar kashe shi. Amma yana jin wani raurawa a jikinsa, amma bai san me ya sa ba. Ya ce shi ya zo ya tuba ga Allah (T), kuma yana so ya yafe masa.
Bayan da Hukumar Saddam suka ga duk wa]annan yun}urin kisa ta fuskoki daban-daban bai yi ba, sai suka yi wa Sayyid Sadr ]aurin talala a gidansa, ba su yarda shi da iyalansa su je ko’ina ba, ba su kuma yarda a zo gidansu ba. Suka sa jami’an tsaro, suna canjin aiki a gidansa, duk awa takwas. Wato saboda su tabbatr ba wanda yake zuwa wajensa, shi kuma da iyalinsa ba su je ko’ina ba. Haka Sayyid Sadr ya kasance a cikin wannan hali. Shi da iyalinsa, har sai da ta kai abincin da suke da shi ya }are, suka dawo }anzon da suke tarawa a baya shi suka dinga dafawa suna ci. Shi wanda ya rubuta wannan littafin da aka ambata a sama na rayuwar Sayyid Sadr da yake ikon Allah lokacin da aka yi wa Sayyid Sadr ]aurin talala shi yana gidan, saboda haka duk abubuwan da suka faru a watanni tara na ]aurin talala a gabansa aka yi. Ya ce, wata rana an dafa wannan }anzo sun ci shi da Sayyid Sadr sai Sayyid ya ga alamun ~acin rai a fuskarsa, ya tambaye shi lafiya? Sai ya ce; “Ina tunanin babban Malami kamar ka kuma Mujtahidi, amma ga abincin da yake ci”. Sai Sayyid Sadr ya ce masa; “To, wannan shi ne mafi da]in abincin da na ]an]ana a rayuwata, saboda wannan abin ya faru ne a tafarkin Allah (T) domin kuma neman yardarsa”.
Hukumar Saddam ta ga dai duk wannan bai yi mata ba. Sai ta sa aka yanke ruwan gidan, (wato famfo), aka yanke wutar lantarki, aka yanke tarho. Wa]annan abubuwa da aka ambata aka yanke su na tsawon kwana 15, wani abin ban takaici da kuma tausayi, Mahaifiyar shi Sayyid Sadr da ma a gidansa take, ga tsufa, ga shi kuma tana fama da rashin lafiya lokaci-lokaci, saboda haka lokaci bayan lokaci akan sayo mata magunguna. Wannan ]aurin talalan ya hana a sayo mata magunguna a cikin wa]annan watanni tara.
Lokuta daban-daban jami’an gwamnati sun zo wajen Sayyid Sadr domin gindaya masa wasu sharu]]a, in ya amince a janye wannan ]aurin talalar, amma Sayyid Sadr a duk wa]annan lokutan yakan yi watsi da wa]annan sharu]]an. In mutum yana son ganin wa]annan sharu]]an ya dubi littafin da aka ambata a sama zai ga duk wannan abin bai yi ba.
Shi ne suka yi masa kamu na }arshe. Sun kama shi ne a ranar 5 ga watan 4 a 1980. Kafin ya bar gida, ya shaida wa jami’an tsaron cewa su ba shi dama ya yi bankwana da iyalansa. Shi ]an uwan da ya je tare da su ya ce, shi wannan bankwanan shi ne karon farko da ya ga ya yi haka. Da ma kwanaki gabanin wannan kamun Sayyid Sadr ya yi mafarki har yake shaida wa ]an uwan cewa yana ganin ma’anar mafirkin shi ne zai yi shahada ne, kuma a kusa. Ilai kuwa, kwana uku da wannan kamun aka kashe shi.
Bayan an azabtar da shi, sun kama shi kamar yau, washegari suka zo suka kama Bintul-Huda, amma da suka zo, sai suka ce mata wai Sayyid Sadr yake so ya gan ta. Shi ne ta ce masu; “In ma kamu ne, ko shi yake so ya gan ni, ko ma kisa ne, ba matsala, domin wannan ita ce hanyar iyayena da kakannina.”
Sai jami’in tsaron ya ce; “Ai ba haka ba ne, Sayyid Sadr ne kawai yake so ya gan ki”. Ta ce; “Wane ne bai san }aryarku ba?” Shi ne ta ce masu su ]an dakace ta tana zuwa. Ta shiga ta shirya, ta yi bankwana da Mahaifiyarta, da iyalan Sayyid Sadr, da kuma shi wannan ]an uwan da yake shi Sayyid Sadr ya bar masa wasiyyar cewa, duk lokacin da aka zo kama shi kada ya bi shi. Ya ce; “Domin idan ka bi ni aka kashe ka, abubuwa da yawa na tarihina, musamman na }arshen rayuwata zai ~uya”.
To, sai Bintul-Huda ta yi bankwana da wannan ]an uwan ta ce masa, “To wane, ]an uwana ya yi nasa aikin (wato Sayyid Sadr), ni ma zan tafi na yi nawa aikin, ina yi maka wasiyya da mahaifiyar nan tamu da kuma yaran ]an uwana, babu wani a nan gidan face kai. Sakamakon wannan aiki da za ka yi nan ga Uwata Sayyida Fatima (AS)”. Shi ne ]an uwan ya ce mata yana ganin kada ta bi su. Sai ta ce masa; “A’a, wallahi har sai na yi tarayya da ]an uwana ga dukkan wahalwahalun da zai fuskanta har kisa.” Ta fito ta bi su suka tafi.
Ranar 9 ga watan Afrilu 1980 da misalin }arfe 9:00 zuwa 10:00 na dare, aka ]auke wutar lantarki na Birnin Najaf baki ]aya. Ashe gawar Sayyid Sadr da kuma Shahidiya Bintu-Huda suka kawo. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Suka kawo gawar cibiyar jami’an tsaro ta Najaf, bayan haka suka je suka ]auko ]an uwan Sayyid Sadr na jini mai suna Sayyid Muhammad Sadi} Sadr suka kawo shi nan cibiyar suka ce masa wa]annan gawar Sayyid Sadr ne da Bintul-Huda an kashe su. Sai ya ce; “To ku ba ni su in je a yi masu wanka da likkafani”. Suka ce sun yi. Sai ya ce masu, to ai dole ne a yi masu Salla. Shi ne jami’in tsaron ya ce, to ya yi masu Salla. Bayan da ya gama masu Salla, sai shi jami’in tsaron ya ce; “Ko kana so ka gan su?” Ya ce; “Na’am”. Shi ne aka bu]e ya gan su. Ya ga duk ga kufan azabtarwa a fuskar Shahid Sadr da kuma Bintul-Huda, sannan suka ce masa yana iya ya fa]i cewa an kashe Sayyid Sadr, amma kada ya kuskura ya fa]i cewa an kashe Bintul-Huda, in ko ya fa]a hukuncinsa kisa.
Wani abin mamaki da kuma aya a nan shi ne, ranar da Saddam ya kashe Sayyid Sadr, wato 9 ga watan Afirilu, a irin wannan ranar ce gwamnatinsa ta kife. Allahu Akbar!

No comments:

Post a Comment