Sunday 3 February 2013

Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali Zainul Abidin (AS)


Kasantuwar watan da muka fita wato na Muharram, 25 gare shi ne wafatin Imam Ali Zainul Abidin (AS) a wata ruwaya 12 gare shi, saboda haka kamar yadda aka saba a irin wa]annan munasabobin na wafatin A’imma na Ahlul Baiti (AS) akan gabatar da darussa a ta}aice daga rayuwarsu da nufin su kasance madubi da za mu dubi rayuwarmu da kuma yin sa’ayi na Mujahada
wajen ganin cewa mun ]abba}a su gwargwadon ikonmu, shi ya sa ma aka fi }arfafawa a janibobin rayuwarsu da ke da ala}a da aikatawa kamar A}hlak ]insa, Ibadarsu, Ilminsu, Zuhudunsu, mu’amalarsu da mutane, jarabawowin da suka fuskanta a rayuwarsu ta fuskoki daban-daban, da dai sauran ~angarori na rayuwarsu.
Imam Zainul Abidin (AS), kamar yadda aka sani, shi ne Imami na hu]u a jerin }idaya na Imamai 12. An haife shi a Madina ranar Juma’a 5 ga watan Sha’aban shekara ta 38 bayan Hijira. Ana yi masa kinaya da Abu Muhammad yana kuma da la}ubba da yawa, amma wa]anda suka fi shahara sune ‘Zainul Abidin’ da kuma ‘Sajjad’. Ya rayu tare da Kakansa, wato Imam Ali (AS) shekaru biyu, tare kuma da Mahaifinsa, wato Imam Husaini (AS) shekaru 22, saboda haka lokacin da aka yi wa}i’ar Karbala yana da shekaru 22 ne a duniya, ya kuma rayu bayan shahadar Imam Husaini (AS) shekaru 35, wato wannan shi ne muddan Imamancinsa. 
Ya rayu a Madina, ya kuma rasu a Madina, sakamakon guba wadda Khalifan Umayyawa, Walid [an Abdulmalik ya sa masa. Kuma ya yi zamani da Khalifofin Umayyawa guda biyar, sune Yazidu ]an Mu’awiyya, Mu’awiyya ]an Yazid, Marwan ]an Hakam, Abdulmalik ]an Marwan da kuma Walid [an Abdulmalik. Kuma duk wa]anda aka ambata babu wanda bai cutar da kuma musgunawa ga Imam Zainul Abidin (AS) ba. Face ]aya daga cikinsu, wato Mu’awiyya ]an Yazidu, wanda sukan ce masa Mu’awiyya na biyu, al’amarin yana da ban mamaki wato rayyaye ne Allah (T) ya fitar da shi daga matacce, wato rayyaye a ruhi daga matacce a ruhi. Domin a ce ]an Yazidu (LA) ya zamo mutumin kirki wuce nan ya zamo mabiyin Ahlul Baiti (AS) abin da ban mamaki, amma ba mamaki ga al’amarin Allah (T). Ga ka]an daga cikin tarihin rayuwarsa, kamar yadda Ali Kaurani Al-Amiliy ya kawo a littafinsa mai suna ‘JAWAHIRUT TARIKH’, mujalladi na hu]u, shafi na 149.
Mu’awiyya ]an Yazid ya kasance ]an Shi’a wanda ya yi imani da Imama ]in Ahlul Baiti (AS) ya kuma yi iya iyawarsa a lokacinsa ya kuma yi layya da mulkinsa da kuma jininsa wajen ganin cewa ya mai da khalifanci zuwa ga ma’abocinsa na Shari’a, wato Imam Zainul Abidin (AS). Daga }arshe dai kamar yadda ya zo a tarihinsa da wannan sa’ayi nasa bai yiwu ba sai ya sauka daga khalifanci ]in. Wa]anda suka shiga tsakaninsa da wannan sa’ayin nasa, wato Banu Umayya, duk da cewa ]an uwansu ne na jini, amma suka kashe shi.
Bayan da suka kashe shi, wato shi Mu’awiyya ]an Yazidu suka kama Malaminsa suka ce masa shi ya karantar da shi wannan abin ya kuma gina shi a kan son Ali (AS) da ’ya’yansa da kuma kautar da shi a kan yin khalifanci. Shi ne Malamin ya ce masu ba ni ba ne, abin a jininsa yake kuma ya ginu a kan son Ali (AS). Da yake Maman shi Mu’awiyya ]an Yazid ta yi zama gidan Imam Ali (AS), bayan shahadarsa ta koma gidan Imam Hasan (AS) kamar yadda yake a tarihinta. Kuma shi wannan Malami nasa, da Banu Umayya suka kama almajirin Abu Zarri (RA) ne. A ta}aice dai, kamar yadda ya zo a tarihinsa, wato shi Mu’awiyya ]an Yazid kwanakinsa 40 a kan mulki, bayan haka ya sauka. Kuma lokacin da aka kashe shi yana da shekara 20 ne.{abarinsa yana nan har yanzu,kuma akan ziyarce shi.
Rayuwar Imam Zainul Abidin (AS) za a iya kasa ta zuwa marhaloli guda biyu: Marhala ta farko, daga wiladarsa zuwa shahadar Mahaifinsa; marhala ta biyu, daga ranar Ashura zuwa wafatinsa. Ya rasu yana da shekaru 57. Sunan Mahaifiyarsa Maryam, Imam Ali (AS) ya sa mata wannan sunan da yake asalinta mutumniyar Farisa ce, wato Iran. Kuma ita ’yar Sarkin Farisa ne, wato Yaz Da Jir. Bayan aurensu da Imam Husaini (AS) cikin abin da Imam Ali (AS) ya ce masa, za ta haifa masa [a wanda yake mafifici a bayan }asa a zamaninsa.
Lokacin da albishir ya zo ga Imam Ali (AS) na haihuwarta, ya yi sujuda ta godiya ya kuma sa wa abin da aka haifa suna Ali. Kuma ya zo a tarihinta cewa tun kafin ta zo Madina, ta yi mafarki da Manzon Allah (S) bayan wannan kuma ta yi mafarki da Fatimah (AS). Lokacin da aka kawo su Madina, da ta ga Umar sai ta yi masa Farisanci, ya fusata ya ce ta zage shi zai ]auki mataki a kanta. Imam Ali (AS) ya ce masa, a’a kada ka yi inkarin abin da ba ka sani ba. Bayan haka Imam Ali (AS) ya yi mata tambayoyi da Farisanci ta ba shi amsa, da yake daga cikin khususiyar da A’imma na Ahlul Baiti (AS) suke da shi shi ne, babu wani yare da yake a doron }asa wanda ba su ji. In mutum ya bibbiyi tarihinsu ]aya bayan ]aya, zai ga haka. Saboda haka ga mai bu}atar ganin bayanin mafarkin da ta yi da Manzon Allah (S) da kuma Fatimah (AS) da kuma tattaunawar da suka yi da Imam Ali (AS) da Farisanci, ya duba cikin littafin ‘MUNTAHAL AMAL’ (juzi’i na 2), na Shaikh Abbas {ummiy, wato marubucin littafin ‘MAFATIHUL JINAN’. Sai kuma darussa daga rayuwarsa (AS):
IBADARSA (AS): Imam Zainul Abidin ya kasance mai yawan Ibada. Wannan la}abin nasa na Zainul Abidin ya samo asali ne saboda yawan Ibadarsa da kuma ruhin da ke cikin Ibadar. Ga wasu misalai daga cikin Ibadodinsa:
a.Sujudarsa: Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance mai yawan Sujuda saboda ma yawan Sujudarsa wannan la}abi nasa na ‘SAJJAD’ ya samo asali, kamar yadda hakan ya zo daga Imam Ba}ir (AS), ya ce: “Babana Ali bai tuna wata ni’ima da Allah (T) ya yi masa ba face ya yi sujuda ta godiya a kai, bai karanta wata Aya daga cikin Al}ur’ani ba alhali Ayar ta sujuda ce face ya yi sujuda, Allah (T) bai tun}u]e masa wani mummuna da yake gudu ko wani kaidin mai kaidi ba face ya yi sujuda a kai, bai gama wata Salla ta Farilla ba face bayanta ya yi sujuda ta godiya. Haka nan bai samu gyara tsakanin mutum biyu da matsala ke tsakaninsu ba face ya yi sujuda”. Saboda haka ake ce masa la}abi da Sajjad, wato wannan ya nuna sujuda ta godiya ba ta ta}aita da sujudar bayan Salla ba, a’a duk wata ni’ima da Allah (T) ya yi wa mutum ko kuma ya tunku]e masa wata musiba, to ya yi sujuda ta godiya ga Allah (T). Misali, ko da tafiya mutum ya yi ya dawo, to ya yi sujuda ta godiya ga Allah (T) da ya kai shi lafiya ya dawo da shi lafiya. Kuma kamar yadda aka sani godiya ga Allah (T) hanya ce ta samun da]i daga gurinsa (T), kamar yadda yake cewa cikin littafinsa: “Idan kuka gode, zan }ara maku.” Saboda haka, duk lokacin da mutum ya gode wa Allah (T) kan wata ni’ima da ya yi masa ta addini ko duniya, to kamar ya bu]e wa kansa }ofar samun }ari ne.
A ta}aice dai, rashin godiya ga ni’imar da Allah (T) ya yi wa mutum ko kuma sa~a wa Allah(T) a ni’imar, yakan sabbaba }wace ni’imar. Shi ya sa in mutum ya duba tarihin bayin Allah zai ga suna gode wa Allah (T) ga ni’imomin da ya yi masu ta hanyar ayyukan Ibadodi daban-daban. Misali, kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S) cewa, yakan tsaya wajen yin Sallar Tahajjud har dugadugansa su tsattsage. Da aka tambaye shi, me ya sa yake yin haka alhali Allah (T) ya gafarta masa? Ya ce: “Ba zan zamo bawa mai godiya ba.” Wato, wannan ya nuna mana lokacin da mutum ke yin Tahajjud ya zamanto yana shu’urin godiya ga Allah (T) da ni’imomin da ya yi masa.
b. Sallolinsa: Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance mai yawan Salla. Ya zo a tarihinsa cewa a kowacce rana yakan yi Salla ta nafila raka’a dubu ]aya, kuma ya kasance a wa]annan Sallolin nasa mai gayar khushu’i. Kamar yadda aka sani, khushu’i a cikin Salla ya kasu kashi biyu: Akwai khushu’i na ‘}alb’, wato zuciya; akwai kuma khushu’i na ‘badan’, wato jiki. Ga misalan wa]annan khushu’ai guda biyu a cikin Sallolinsa:
An samo daga Imam Ba}ir (AS) yana cewa: “Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance idan ya tsaya a Salla yakan tsayu kamar ka ce itaciya ce a tsaye, wato saboda rashin motsi.” Haka nan Abu Hamzatus Sumaliy yana cewa: “Na ga Imam Zainul Abidin yana Salla sai Alkyabbarsa ta goce a ]ayan kafa]arsa, bai sa hannu ya gyara ba har sai da ya gama Salla, sai aka tambaye shi a kan haka, wato me ya sa bai gyara ba? Sai ya ce masa: “Kaiconka! Ka san ko gaban wanda nake tsaye? Ai ba a amsar Sallar bawa face a kan asasin yadda ya halartar da zuciya a cikinta.” To, mu duba Sallolinmu mu gani ya muke wajen tsayuwa da wannan khushu’i na zuciya da kuma na jiki. Ya ma zo a tarihinsa cewa, saboda gayar khushu’insa a cikin Salla, in ya soma Salla bai jin duk wani abin da yake faruwa sai bayan ya gama Salla, sai ya ga ashe kaza da kaza sun faru yana Salla.
Ta }issar wani bawan Allah (T) yana Salla shi da almajiransa, sai wasu suka zo wajen wannan bawan Allah, da suka samu suna Salla sai suka ce, bari su je su dawo. Bayan Salla sai almajiransa suka ce ai ko sun ji zuwan su wane, sun ce za su je su dawo.sai bawan Allan yace “Ana Salla har kuka ji wasu sun zo sun ce kaza”. Ya ce masu; “To ku tashi ku sake Salla”. Wata }issa ta wani bawan Allah (T) shi ma ya yi Salla, bayan wani Limami, sai aka ga ya yanke Sallar ba a gama da shi ba. Shi ne bayan da aka gama aka tambaye shi, me ya sa haka? Ya ce, yaya zan bi Liman yana Salla alhali zuciyarsa na kasuwa. Aka je aka samu Liman aka ce ka ji abin da wane ya ce, ya ce tabbas haka ne, da nake ba da Salla ina tunanin in na gama zan je kasuwa in sayo kaza da kaza. Amma tambihi a nan shi ne, irin wannan Salla da ba khushu’i da ruhi a cikinta a Fi}ihance Sallar mutum ta yi, a Irfanance ne Sallar take da matsala. Insha Allah a darasin Akhla} in aka zo bayani dangane da ‘tazkiyya’ ]in Nafs, za a yi bayani dangane da ruhin Salla.
Haka nan Imam Zainul Abdin (AS) ya kasance idan Nafilfilin da ya saba yi suka ku~uce masa, a cikin yini yakan rama su da daddare, har ma an ta~a tambayar sa a kan haka, ya ce ba wajibi ba ne, amma yana da kyau in mutum ya saba aikata wani aiki na alheri ya dawwama a kansa. Kuma ya zo a kan cewa, aikin da Allah (T) ya fi so shi ne wanda aka dawwama a kansa komai }an}antarsa. Shi ya sa ya zo a kan cewa, mustahabbi ne mutum ya rama Salloli na Nafila da suka ku~uce wa mutum. Misali, a ce mutum bai samu yin Sallolin Nafila na Azahar da La’asar  ba, to yana iya ranka su da daddare ko kuma Nafilar Magrib da Isha’i, ko kuma Sallarsa ta Tahajjud, bai samu yin su ba, saboda wani uzuri to zai iya rama wa]annan Nafilolin a cikin yini,
c. Addu’o’insa: Imam Zainul Abidin ya kasance mai yawan Addu’o’i kuma idan mutum ya bibbiyi tarihin Imamai ]aya bayan ]aya, zai ga cewa babu wani Imami daga cikin Imamai da aka tattara Addu’o’insa kamar yadda aka tattara na Imam Sajjad (AS). Mutum ya duba Sahifah ta Imam Ali (AS) da Imam Hasan (AS), Husaini (AS) har ya zuwa Sahifah ta Imam Mahdi (AS), ya kwatanta da Sahifah Sajjadiyya, wanda kuma har yau har gobe ana kan tattara wa]annan Addu’o’in nasa. Shi ya sa in muka duba za mu ga akwai Sahifah Kamilah, akwai Jami’ah, wato mai }arin wasu Addu’o’i na Imam Zainul Abidin (AS), wanda mai Sahifah Kamilah bai kawo ba. Kuma littafin Sahifah Sajjadiyyah ya kawo Addu’o’i na Yaumiyya, Usbu’iyya, Shahariyya da kuma Sanawiyya da kuma Addu’o’i na bu}atoci na duniya da kuma lahira, ga kuma Munajatoti daban-daban wanda za su taimakawa mutum wajen ]amfaruwarsa da Allah (T). A ta}aice dai, littafi ne wanda ya kamata a ce kowanenmu ya kasance, akwai wata Addu’a ko Addo’o’i da zai lizimci karanta wa kowace rana ko dare a cikinsa.
d. Karatun Al}ur’anin Imam Zainul Abidin (AS): Ya kasance mai yawan Karatun Al}ur’ani. Akwai lokacin da yake cewa, da mutanen Gabas da Yamma za su mutu (wato mutanen duniya gaba ]aya) da ba zan yi kewa ba, matu}ar akwai Al}ur’ani tare da ni. Domin tabbas, duk wanda yake karatun Al}ur’ani (karatu wanda yake akwai halartar da zuciya a ciki), ba ya kasance mutum na karatun da harshe amma zuciyarsa na wani waje, wato yana tunanin wani abu ba abin da yake karantawa ba. To irin wannan karatu mai ruhi, yakan sa mutum tunaninsa ya fita daga wannan duniya zuwa wata duniya, wato daga duniyar ‘Mulk’ zuwa duniyar ‘Malakut’, kamar dai yadda ‘Urafa’u’ suka yi bayani. A ta}aice dai, Imam Zainul Abidin (AS) saboda yawan Ibadarsa da kuma yadda }afafuwansa suke tsattsagewa wajen Salla, Imam Ba}ir (AS) har kuka yake yi in ya gan shi wani lokaci, saboda tausayi. Ga mai bu}atar ganin wasu Ibadodinsa, yana iya duba littafin ‘MUNTAHAL AMAL’, juz’i na 2.
2. SHAJA’ARSA: Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance mai gayar jaruntaka, wanda ya bibbiyi tarihin rayuwarsa zai ga haka. Ya ma zo a kan cewa, a zamaninsa babu wanda ya kai shi a wannan fage na Shaja’a. Misali, daga irin wannan jarunkata tasa, shi ne lokacin da aka kai shi wajen Ibn Ziyad (LA) ya fa]a, ya fa]i, ya fa]a, ya fa]i, ya fa]a, ya fa]i, daga }arshe Ibn Ziyad ya fusata ya ce a je a kashe shi. Imam Zainul Abdin (AS) ya ce: “Ahaf! Ai mu ba ka san cewa kisa al’ada ne a wajenmu (wato abin da aka saba) ba? Kuma karamarmu a wajen Allah (T) ita ce shahada”. Domin shi Ibn Ziyad yana ganin waye zai fa]a masa irin wa]annan maganganu da Imam Sajjad (AS) ya fa]a masa.
Makamancin haka ma ya kasance a fadar Yazid (LA), shi ma ya fusata ya ce a je a kashe Imam Sajjad(AS). Daga cikin abin da Yazid ya fa]i, Imam Sajjad(AS) ya mayar masa akwai cewa da ya yi,”Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kashe Babanka, ya zubar da jininsa”. Imam Sajjad (AS) ya mayar masa da cewa: “Allah ya tsinewa wanda ya kashe Babana.” Maganganu masu tsawo sun gudana tsakaninsa da Yazid da kuma wani Malamin fada na Yazid wanda shi ma Imam Sajjad ya fa]a masa maganganu, majalisin nasu ya tsawaita, har lokacin kiran Salla ya yi. Da mai kiran Salla ya zo wajen cewa na shaida Muhammad Manzon Allah ne, sai Imam Zainul Abidin (AS) ya dubi Yazid ya ce: “Wannan Manzon mai daraja Kakanka ne ko Kakana? In ka ce kakanka ne, duk wanda suke wannan majalisi da ma mutane baki ]aya sun san }arya kake yi. In kuma ka ce Kakana ne, to me ya sa ka kashe Babana, saboda zalunci da }iyayya kuma ka ribace matayensa? Azaba ta tabbata gare ka ranar }iyama, idan Kakana ne zai yi husuma da kai.” Yazid ya sake fusata. Ladan ya gama kiran Salla, ya ce ya ta da I}ama saboda yadda Imam Sajjad (AS) ya kunyata shi ya kuma wawaitar da shi a majalisin.
Ya ma zo a kan cewa tun asali, shi Yazid bai so ya bar Imam Sajjad (AS) ya yi magana ba, ]ansa Mu’awiyya shi ya matsa masa a kan ya bar shi ya yi magana, shi ne Yazidu yake cewa ]an nasa; “Ba ka san wa]annan sun gaji ilimi da fasaha ba, kuma sun ]an]ani ilimi ]an]ana? ]an nasa ya ce duk da haka dai ka bar shi, sa’annan ya }yale shi ya yi magana.
3. AKHLA{ [INSA: Shi ma a wannan fage na Akhla} a zamaninsa ba wanda ya kai shi ballantana ya wuce shi. Ga misalan wasu daga cikin Akhla} ]insa:
a. Afuwarsa da kuma kau-da-kai daga wautar masu wauta. Akwai wani da ya ta~a zuwa ya samu Imam Sajjad (AS) ya ce, wane ya fa]i magangani marasa kyau game da kai. Sai Imam Sajjad (AS) ya ce tashi mu tafi wajensa, suka tashi suka tafi. Shi wannan mutumin ya ]auka zai je ne ya fa]a masa shi ma maganganu. Lokacin da suka isa, sai ya ji Imam Sajjad (AS) na ce wa mutumin, “In abin da ka fa]i ba gaskiya ba ne, to Allah ya gafarta maka”. Akwai kuma wani lokaci da wani ya zo yana ta fa]in maganganun da ba su dace ba ga Imam Sajjad (AS), sai ya yi kamar bai ji shi ba. Ya yi ta yi, ya yi ta yi, sai can mutumin ya ce; “Da kai fa nake”. Sai Imam Sajjad (AS) ya ce, da kai nake kau da kai (wato ina ji na }yale ne). Mu dubi irin wannan jarabawa ta tsokanar fa]a.
Haka nan akwai wata rana ya fita sai wani mutum ya ha]u da shi, ya zage shi. Bayin Imam Sajjad (AS) da kuma mabiyansa da ke tare da shi a lokacin suka zabura za su ]auki mataki kan mutumin, sai Imam Sajjad (AS) ya ce masu, a’a. Sai ya samu mutumin ya ce masa, al’amarinmu ya ~oyu gare ka, kana da wata bu}ata mu taimaka maka? Mutumin sai kunya ta kama shi. Sai Imam Sajjad (AS) ya ba shi mayafin da ke tare da shi, ya kuma ce a ba shi Dirhami dubu. Bayan haka shi wannan mutum duk inda ya ga Imam Sajjad (AS), ya kan ce masa: “Lallai na shaida kai ]an Manzon Allah (S) ne.”
Ya zo a kan cewa, akwai wani ]an uwan Imam Zainul Abidin (AS) na jini da ya ta~a samun sa yana Masallaci shi da Sahabbansa, ya fa]a masa maganganu da ba su dace ba. Imam Zainul Abidin (AS) ya yi shiru bai ce masa uffan ba. Ya gama maganganun da zai yi ya tafi. Sai da dare ya yi Imam Zainul Abidin (AS) ya ce masa; “Ya ]an uwana in abin da ka ce dangane da ni gaskiya ne, to Allah ya gafarta maka”. Ya yi mai sallama ya juyo. Sai ]an uwan nasa ya yi nadama kan abin da ya yi, har ya biyo shi yana kuka. Har yake ce masa wallahi ba zan sake yi maka abin da bai dace ba, sai Imam Zainul Abdin (AS) ya ce masa; “Na yafe maka duk abin da ka ce”.
Mu dubi yadda A’imma (AS) suka fuskanci jarabawowi ba wai kawai daga masu tafi da iko ba, a’a, daga mutanen gari da ma ’yan uwansu na jini. Insha Allah a wata munasabar za mu ]ora.



No comments:

Post a Comment