Monday 4 February 2013

Arba’in ]in Imam Husain [AS]


Ranar arba’in ]in Imam Husain [AS] rana ce wadda take da muhimmanci,musamman ma  ga mabiya Ahlul bayt [AS],kuma kiyaye ranar yana daga cikin alamomin mumini,kamar yadda haka yazo daga Imam Hassan Al-askari [AS],in da yace, “Alamomin mumini [wato ]an shi’a] guda biyar ne.
1.Yin salla raka’a 51 ko wace rana. 2.Ziyarar arba’in.3.Sa  zobe a dama. 4.Sa goshi a }asa [ta’afir]. 5.Bayyana karatun bismillah a sallah.”                                                                                                                                                                         Amma kafin bayani dangane da wannan hadisi da kuma  ranar arba’in ]in,zai yi kyau a ]an yi bayani a ta}aice dangane da matsayin adadin  arba’in  a  addinin musulunci.Adadin  arba’in  yana  da wani asrar gaibiyya a wajen Allah [T] da kuma tarkizi na musamman a wasu ayoyi na Al-}ur’ani mai girma,da kuma wasu hadisai da aka samo daga Manzon Allah [S] da kuma Ahlul bayt [AS],ga misalin wasu daga cikin wa]annan hadisai,an samo daga Imam Sadi} [AS] yace, “Idan mumini ya rasu,mutane 40 daga muminai suka halarci jana’izarsa,[cikin addu’ar da sukayi masa] suka ce ‘ya ubangiji! Bamu san komi dangane dashi ba sai alheri,kai ka  fimu saninsa, Allah [T] zai ce na zartar da shaidarku,na  gafarta  masa na abin da na sani da abunda ku baku sani ba.”.                                                                                                                               Haka nan kuma daga Imam Sadi} [AS] yace, “Babu wasu jama’a 40 da zasu ha]u  suyi addu’a  a kan wata bu}ata tasu face Allah [T] ya kar~a musu”.har ila yau daga Imam Sadik [AS] yace, “Duk wanda ya gabatar da muminai 40 gabanin addu’arsa,bayan haka ya gabatar da addu’a  ta bu}atarsa,to Allah[T] zai kar~a masa”kuma wannan wani abu ne wanda yake da gayar muhimmanci da falala,na kowannenmu ya sabawa  kansa  da yin haka,wato na addu’oi ga muminai  guda 40,in son sa mune a kowane dare  a }unut na witri,ko kuma bayan ya gama sallar tahajjud ]insa,in ba zai iyayi ko wane dare ba to a}alla duk daren juma’a  mutum ya lizimci hakan,domin yin hakan ya na da fa’idodi masu yawan gaske,kuma sunna ce daga cikin sunnonin ma’asumai [AS],alal misali yazo akan cewa sayyida fatima [AS] in ta gama sallar tahajjud ]inta, takan yi addu’oi  ga muminai na kusa da na nesa,shine har Imam Hasan [AS] yake ce mata “Na kan ji ki kan yi addu’oi  ga mutane,amma ban ji kina addu’a gare kiba”.shine tace masa, “ma}wabci gabanin gida”.                                                                                                         Haka nan kuma akwai hadisi da aka samo daga Manzon Allah [S] yace, “Duk wanda ya kiyaye wa al’ummata hadisai 40 da suka shafi al’amarin addininsu,baya  nufin  komai  face  yardar Allah [T] da kuma gidan lahira,to Allah zai  tashe shi ranar }iyama a matsayin  fa}ihi kuma Malami” wannan hadisin yasa  da yawa daga cikin malaman madrasah ]in Ahlul bayt [AS] da kuma ta Ahlus  sunna,  suka rubuta littafai na hadisai  40 domin samun falalar wannan hadisi,misali  anan  shine  littafin hadisi 40 na Imam khumaini da kuma littafin hadisi 40 na Imam Nawawi,in mutum ya duba littafin hadisi 40 na Imam khumaini, zai ga cewa a wajen gabatarwa na littafin yana cewa ya tattara wannan hadisai ne da fatan ya samu shiga cikin hadisin Manzon Allah [S] da yazo  akan cewa “wanda ya kiyaye wa al’ummata hadisai 40 da suke amfana  dasu,to Allah zai ta da shi ranar al }iyama  a matsayin fa}ihi kuma Malami”.da dai hadisai da dama da suka  zo  akan Tarkizi kan 40,wanda ba za a iya kawo su ba saboda  gudun  tsawaitawa.Dawowa ga wannan hadisi da  aka samo  daga Imam Askari [AS] na alamomin mumini guda biyar,alama ta farko,kamar yadda yazo a hadisin,shine  yin Raka’a 51 ko wace rana,wannan raka’a 51 ya ha]a da sallolin wajibi da nafilfilinsu da kuma sallar tahajjud  tare da shafa’i da witri,a warware  ga lissafin adadin raka’oin na sallolin wajibi,wato daga sallar Asuba zuwa sallar Isha’i, in mutum ya ha]a zai ga 17 ne,sai nafilfilinsu,sune  raka’a  2  gabanin  Asuba,raka’a 8  gabanin sallar zuhur,raka’a 8 gabanin sallar Asar,raka’a 4 bayan sallar maghrib,raka’a 2 a zaune bayan isha’i [watira].amma biyun nan yana matsayin  raka’a ]aya ne,sallar tahajjud raka’a 8,shafa’i 2 witri 1,in mutum ya ha]a  zai ga lissafin ya tashi 34,wato na raka’oi na nafilfilin,in mutum ya hada da wa]ancan raka’oi na wajibi 17, zai ga ya tashi akan 51,To,wa]annan raka’oi 51 sune  ake  so kowane mumini,wato mabiyin Ahlul bayt [AS] ya tsayu da yinsu kowace rana  ba tare  da yin fashi ba.ko da zata kai ace mutum bai samu yin su nafilfilin ba, saboda wani uzuri,to yazo akan cewa ana son mutum ya rama su.misali ace  bai  samu yin nafilfilin  zuhur da asar ba,ya na iya ramka su acikin yini ]in,ko kuma da daddare.in kuma bai samu yin nafilfilin dare ba, wato kamar maghrib ko isha’i,ko kuma  sallar tahajjud ]insa,to ya na iya ramka su a daren,ko kuma washe gari cikin yini.wato ya tsayu akan yin haka kowa ce rana ba tare da fashi ba.A in da kawai wa]annan nafilfilin suka fa]i shine a halin tafiya,a nan nafilfilin  zuhr  da  asar sun fa]i,amma sauran nafilfilin na sallar maghrib da isha’I da asuba,da kuma tahajjud,shafa’i da witri,su basu fa]i ba.Wato dai a halin tafiya nafilflin sallolin rana ne suka fa]i,amma nafilflin dare basu fa]i ba. kuma wa]annan raka’oi  51 mutum ya kwatanta su da raka’a dubu ]aya da Imam Aliy [AS],Imam Husain [AS],Imam zainul Abidin [AS] da kuma Imam Ridah [AS] suke yi ko wace rana ,zai  ga ]aya bisa 20 ne.kuma su wa]annan raka’oi 51,su ake cewa salloli  na yaumiyyah.Akwai  kuma salloli na usbu-iyyah,wato na mako,suma  an  ruwaito  sune daga Manzon Allah [S] da kuma Aimma na Ahlul bayt [AS],wato wa]annan kwanaki bakwai na mako,misali daga juma’a zuwa Asabar to kowace rana da kuma dare na wa]annan kwanaki na da nata sallolin,littafai da dama sun kawo wa]annan sallolin,misali  littafin Diya’us Salihin.ga wanda bai da wannan littafin ko Daren juma’a raka’a 2,ko wace raka’a  mutum zai karanta }ul-huwallahu 70.wannan an samo daga Manzon Allah ne.sai kuma ranar juma’a raka’a 8,ko wace raka’a }ul-huwallahu 1.Daren Asabar raka’a 4,kowace raka’a  bayan fatiha,sai kul-huwallahu 7,sai kuma ranar asabar raka’a 4,kowace raka’a bayan fatiha,}ul-ya Ayyuhal- kafirun sau 3 bayan sallama ta raka’a 4,sai mutum ya karanta Ayyatul -kursiyu sau ]aya,sai  daren lahadi  raka’a 6,ko wace raka’a bayan fatiha,}ul-huwallahu sau 7,sai ranar lahadi raka’a 2,raka’a  ta  farko bayan fatiha,Inna -A’a]aina sau 3,raka’a ta biyu bayan fatiha }ul-huwallahu sau 3,sai daren litinin raka’a 2,kowace raka’a bayan fatiha,Ayatul kursiyu,}ulhuwallahu,sai suratul fala}i da nasi,dukkansu  sau ]aya,bayan sallama sai  istigfari sau 10.sai ranan litinin raka’a 4,raka’a ta farko bayan fatiha Ayatul kursiyu ]aya,raka’a ta biyu bayan fatiha,}ul-huwallahu ]aya,raka’a ta uku bayan fatiha,suratul fala}i,raka’a ta hu]u bayan fatiha suratu Nasi,Daren talata raka’a 2,raka’a ta farko bayan fatiha,inna- Anzal-nahu sau 1,raka’a ta biyu bayan fatiha }uhuwallahu 7.Ranar talata raka’a 2,kowace raka’a bayan fatiha,wattini,}ul-huwallahu,fala}i da nasi,dukkansu sau ]aya.Daren laraba raka’a 2,bayan fatiha,kowace raka’a Ayatul kursiyu,inna Anzal nahu,iza-ja’a sau ]ai-]ai,sai kuma }ulhuwallahu sau 3,Ranar laraba raka’a 2,kowace raka’a bayan fatiha,iza-zul sau 1,sai kuma }ulhuwallahu sau 3.Daren Alhamis raka’a 6,kowace raka’a bayan fatiha }ul-ya Ayyuhal kafirun sau ]aya,sai }ulhuwallahu sau 3,bayan sallamewa  duka,wato raka’a  6  ]in,sai mutum ya karanta Ayyatul kursiyu sau 3,sai ranar alhamis raka’a 2,bayan fatiha kowace raka’a iza-ja’a da kuma inna -A’a]aina ko wace sau 5.                                                                                  To,irin wa]annan salloli su ake cewa sallolin usbu’iyyah,wato na mako.in mutum ya duba cikin littafin jamalul-usbu’i,na sayyid Ibn [awus da kuma littafin mir’atul kamal,zai ga duk sun kawo su.Su ma wannan ya na da kyau kowannen mu ya tsayu dasu,wato baya ga wancan raka’a 51 na yaumiyyah.   Sai kuma sallah ta shahariyya,wato ta wata;ita kuma yadda take shine;idan ka yi ta a daren farko na ko wane wata,sai kuma wani sabon wata a daren farko,haka nan in ka yi a ranar farko na wata,sai  kuma  wani  wata a ranar farko.shine ake ce mata shahariyya.mutum na iya duba sallolin a littafin Mafatihul Jinan babi na 2 fasali na 11.Ga wanda bai da imkaniyyar dubawa ga yadda sallolin suke.Daren farko na kowane wata raka’a 2,kowace raka’a bayan fatiha,sai ya karanta suratul An’am,idan mutum bai haddace ba yana iya amfani da Al’}ur’ani domin karanta suratul An’am ]in.sai kuma ranar farko ta ko wane wata,shima raka’a 2,raka’ar farko bayan fatiha,}ul-huwallahu 30,sai raka’a ta biyu bayan fatiha,Inna -Anzal nahu 30.Suma wa]annan sallolin an samo ne daga A’imma na Ahlul bayt [AS],suma wa]annan salloli na wata-wata ana son mutum ya tsayu dasu,wato ko wane wata daren farkonsa da kuma ranar farkonsa ya zamo mutum na yi ba tare da fashi ba,sai in da wani uzuri.                   Sai kuma salloli na sanawiyya,wato shekara- shekara,su kuma yadda suke,in ka yi su misali yau,to sai kuma wata shekara zaka sake yinsu.Irin wa]annan salloli sun zo ne jefi-jefi a cikin kwanuka  na shekara,wato ba kullum ake yinsu  ba.misalin irin wa]annan  salloli na sanawiyya sune kamar sallar ranar }arshe  ta shekara,ko kuma sallar daren Ashura,to ire-iren wa]annan salloli sune ake cewa salloli na shekara.misali sallolin da suka zo na daren Ashura,yanzu mutum ba zai sake yinsu ba,sai kuma shekara mai zuwa in Allah [T] ya kai mu wani daren Ashurar na shekara mai zuwa.Yanzu sallah ta sanawiyya dake gabanmu itace ta 17 ga watan Rabi’ul Awwal,wato ranar maulidin Manzon Allah [S],in mutum ya duba mafatihul jinan zai ga sallah ]in,kuma wa]annan watanni 12 na musulunci,in mutum ya bisu ]aya bayan ]aya zai ga ba wani wata wanda babu sallar sanawiyya a cikinsa.Shima wannan  wato sallah na shekara-shekara  ya na da kyau kowannen mu ya tsayu dasu.                                                                      Saboda haka in muka  duba  a wannan  nizami,wato  tsari zamu ga akwai salloli na yaumiyya,Usbu’iyya,shahariyya,da kuma sanawiyya,kuma duk wa]annan salloli an ruwaito sune daga Ma’asumai [AS].Saboda haka ya na da muhimmanci yin wa]annan salloli domin koyi dasu,kuma kamar yadda muka ga wannan nizami guda hu]u na salloli,to haka nan ma addu’oi na da nizami wato tsari na yaumiyya,usbu’iyya,shahariyya,da kuma sanawiyya. Haka nan ma shi Azumi yana da wannan nizamin guda hu]u,haka nan surori na Al}ur’ani suma suna da wannan nizami  guda hu]u,wato akwai surorin da ake son karantawa yaumiyya,akwai usbu’iyya,shahariyya da kuma surori na sanawiyya.insha Allah dukkansu za’a yi bayanin su a muhallinsu.                                                                                                                                        Wannan shine bayani a ta}aice  dangane da alamar mumini na farko.Sai kuma alama ta biyu kamar yadda yazo a hadisin,wato ziyarar Arba’in ]in Imam Husain [AS] a 20 ga watan safar,wato kwanaki 40 bayan shahadarsa [AS],ya na daga cikin alamomin mumini wato mabiyin Ahlul Bayt [AS].Kuma ita wannan ziyarar, imma ta kasance daga kusa ne ko daga nesa,wato in mutum ya na da iko da kuma damar zuwa karbala domin ziyara ko kuma yin ziyarar daga garin da yake.A kan wannan asasin ne zamu ga mabiya Ahlulbaiti [AS] daga sassan  duniya  daban -daban da suke da ikon  zuwa  karbala,musamman ma wa]anda suke cikin kasar ira}i,suke tururuwa zuwa karbala domin wannan ziyarar ta Arba’in,wanda mutum zai iya dukan }irji a wannan zamanin namu, yace babu wani taro da yake tara mutane a doron }asa kamar wannan ziyarar ta Arba’in a karbala.                                                   Ta yi wu mutum yayi tunanin taron aikin hajji.To,duk shekara taron  bai  kai wa miliyan biyar,galibi miliyan biyu ne zuwa uku.To,amma mu duba taron jama’a na ziyarar arba’in ]in Imam Husain [AS] a karbala na shekarun bayan  nan da suka wuce, akan samu jama’a sama da miliyan 15,kuma ko wace   shekara  adadin  }aruwa  ya ke yi,wannan  aya  ce babba  ga masu tunani.Kuma wani abin lura shine wasu dake  cikin }asar Ira}i sukan  tako ne  da }afa daga garuruwansu,har ya zuwa karbala domin wannan ziyarar.Za ka gansu maza da mata yara da manya da ma dattijai.kuma a irin wa]annan hanyoyi na  zuwa  karbala  zaka  ga akwai bayin Allah [T] daban daban da suke gabatar da hidima ta fuskoki daban daban ga wa]annan matafiyan zuwa karbala,kuma dukkan wa]annan hidimomin kyauta suke gabatar dasu.Akwai masu bada abinci a hanyoyin,akwai masu bada masaukai,misali mutum ya yo tafiyan kwanaki  daga garinsu,ya na son ya huta kafin ya cigaba da tafiya,to, ga masauki fisabilillah.Akwai likitoci,ga masu gyaran takalmi,ga masu hanyoyi na sadarwa,wato tarho  shima  duk  kyauta  ga wa]annan matafiya zuwa karbala, da dai abubuwa da yawa daba a ambata ba na hidimomi, da wasu bayin Allah ke gabatarwa  fisabilillah.                                                   Ita ziyarar Imam Husain [AS] ta kasu kashi biyu,akwai ziyara mu] la}a,wato itace ziyara wadda bata ke ~anta da wani zamani  ayyananne  ba.Akwai  kuma  ziyara mak susa,wato ta ke ~anta da wani zamani ayyananne .To,ziyarar Arba’in ta na daga cikin ziyara mak susa.A wata ma’ana ziyara mak susa, ana  ce mata ziyara  sanawiyya,wato ta shekara-shekara.Domin idan kayi ta sai kuma wata shekara.Misali wannan ziyara ta Arba’in.Ziyarar Imam Husain [AS] mak susa,kuma sanawiyya guda 10 ne sune:             
                                1.Ziyarar Ashura,wato 10 ga muharram.                                                                                                                                              2.Ziyarar Arba’in,wato 20 ga watan safar.                                                                                                                           3.Ziyarar ranar farko, ta watan Rajab.                                                                                                                                     4.Ziyarar 15 ga watan Rajab.                                                                                                                                                   5.Ziyarar 3 ga watan sha’aban,wato ranar haihuwar Imam Husain [AS].                                                                     6.Ziyarar daren 15 ga watan sha’aban.                                                                                                                                 7.Ziyarar daren lailatul }adr 19,21,23 na watan ramadan.                                                                                            8.Ziyarar daren idi }arama da kuma daren idi babba.                                                                                                     9.Ziyarar rana kun idi }arama da babba.                                                                                                                              10.Ziyarar ranar Arfa,wato 9 ga zul hijja.To dukkan wa]annan kwanaki da aka ambata, mustabbine ya ziyarci Imam Husaini [AS]a cikin su daga kusa ko nesa.                                                                                                Ba  yaga wannan ziyara ta shekara ta Imam Hussain[as]Akwai kuma ziyar  usbu’iyya wato mako mako.Itace duk ranar litinin.Ga mai bu}atar ganin wannan ziyara dama sauran ziyarori na Manzon Allah[s]da kuma Ahlul bait[as]na mako,ya duba cikin littafin mafatihu, babi na ]aya fasali na biyar.Baya  ga  wa]annan ziyarori mustahabbi ne yin ziyara a rana kun wilada da kuma wafati na Ma’asumai [AS],wato Manzon Allah [S] da kuma Ahlul bayt [AS],musamman  ma rana kun wafatinsu,wato ya na da kyau mutum ya sunnanta ma kansa wannan sunna ]in,ya kasance duk ranar wilada ko wafati na ]aya daga cikin ma’asumai, mutum ya kasance ya ziyarce shi ziyara ta kusa ko ta nesa.Domin yin haka yana ]aya daga cikin hanyoyin kyautata ala}a da Manzon Allah [S] da kuma  Ahlul bayt [AS] da kuma dan faruwa  dasu }al- biyyan,wato a zuci.A ta}aice dai kiyaye wa]annan rana ku na wilada da wafati na ma’asumai [AS] a matsayi na ]ai-]ai ku da kuma jama’a,yana da gayar muhimmanci.Ga wata da kuma ranar wafatin ko wanne daga cikin ma’asumai [AS]:1.Manzon Allah [S] 28 ga watan safar.                    2.Sayyida fatima [AS] 3 ga watan jimada-sani.                                                                                                 3.Imam Aliy [AS] 21 ga watan ramadan.                                                                                                                        4.Imam Hasan [AS] 7 ko 28[a wata ruwayar] ga watan safar.                                                                           5.Imam Husain [AS] 10  ga watan muharram.                                                                                                    6.Imam zainul Abidin [AS] 25 [a wata ruwaya] 12 ga watan muharram.                                                                7.Imam Ba}ir [AS] 7 ga watan zulhijjah.                                                                                                                               8.Imam Sadi} [AS] 25 ga watan shawwal.                                                                                                           9.Imam Kazim [AS] 25 ga watan Rajab.                                                                                                                        10.Imam Ridha [AS] 23 ga watan zul}idah [a wata ruwaya] a watan safar.                                                               11.Imam Jawad [AS] }arshen watan zul}idah.                                                                                                  12.Imam Hadi [AS] 3 ga watan Rajab.                                                                                                                    13.Imam Askari [AS] 8 ga watan Rabi’ul Awwal.                                                                                                               Wa]annan sune rana ku na wafatin su,wato rasuwarsu.                                                                                             Sai kuma na wiladar su,wato haihuwar su kamar haka:                                                                                          1.Manzon Allah [S] 17 ga Rabi’ul Awwal.                                                                                                                 2.Sayyida fatima [AS] 20 ga watan jimada sani.                                                                                                                3.Imam Aliy [AS] 13 ga watan Rajab.                                                                                                                      4.Imam Hasan [AS] 15 ga watan Ramadan.                                                                                                        5.Imam Husain [AS] 3 ga watan sha’aban.                                                                                                          6.Imam Zainul Abidin [AS] 5 ga watan sha’aban.                                                                                                            7.Imam Ba}ir [AS] 1 ga watan Rajab [a wata ruwaya 3 ga watan safar].                                                            8.Imam Sadi} [AS] 17 ga watan Rabi’ul Awwal.                                                                                                 9.Imam Kazim [AS] 7 ga watan safar.                                                                                                                    10.Imam Ridha [AS] 11 ga watan zul}idah.                                                                                                         11.Imam Jawad [AS] 10 ga watan Rajab.                                                                                                                             12.Imam Hadi [AS] 2 ga watan Rajab.                                                                                                                       13.Imam Askari [AS] 10 ga watan Rabi’us sani.                                                                                                      14.Imam Mahdi [AS] 15 ga watan sha’aban.                                                                                                      Haka nan baya ga ziyara a wa]annan  kwanaki na wafati ko wilada na ko wannensu,akwai yin juyayi, in na wafati ne,da kuma yin murna, in na wilada ne,da kuma mi}a ta’aziyya ga Manzon Allah [S] da kuma Ahlulbayt [AS]in na wafati ne,in kuma na wiladar ma’asumai ne,sai  ya mi}a murnarsa  ga Manzon Allah [S] da kuma Ahlul bayt [AS] duk sai bayan mutum yayi musu sallama.                                                         Insha Allah sauran  alamomin mu’umini  sai wata munasabar za’a ]ora.    

No comments:

Post a Comment