Sunday 3 February 2013

Darussa 12 daga rayuwar Imam Sadik [AS].1


Imam Sadi}[AS],kamar yadda aka sani shine imam na 6 a jerin I  mamai 12.kuma wannnan munasaba ce ta wafatinsa,domin  ya koma ga Allah [T] ne ranar 25 ga wannnan wata da muke ciki na shawwal,a shekara ta 148 bayan hijra.Ya rasu sakamakon guba da aka sa mishi a inabi,kuma ya rasu ya nada shekara 65, a wata ruwaya shekara 68
.Kuma wannnan yana ]aya daga cikin khususiyar Imam Sadi} [AS] wato na tsawon shekaru.Domin in mutum ya bincika zai ga cewa in ka ]ebe Imam Mahdi [AS],to duk Imamai da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa, basu kai wa]annan shekarun ba.Alal misali ga shekarun da kowane yayi a duniya.Imam Ali [AS] 63,Imam Hasan [AS] 48,Imam Husain [AS] 57,Imam Zainul Abidin 57,Imam Ba}ir [AS] 57,Imam Sadi} [AS] 65, ko 68 a wata ruwaya,Imam Musa Alkazim [AS] 55,Imam Ridah [AS] 51,Imam Jawad [AS] 25,shine mafi }arancin shekaru a raye,in an kwatanta da sauran A’imma [AS].Imam Hadi [AS] 41,Imam Askari [AS] 28,Imam Mahdi [AS] shi yana nan a raye har yanzu,Allah [T] ya gaggautar da  bayyanarsa.Haka kuma shekaru na Manzon Allah [S] a duniya 63,na kuma Sayyida Fatima [AS] 18.To anan in mutum ya duba,in ka ]ebe Imam Mahdi [AS]  ka dubi shekarun da wa]annan Ma’asumai su kayi a duniya ka kwatan ta dana Imam Sadi} [AS] za kaga ya fisu tsawon shekaru a duniya  shi ake nufi da waccen khususiyyar da aka ambata a sama.                                                          Haka nan khususiyya ta biyu,wadda Imam Sadi} [AS] ya ke~anta da ita in ka kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa shine,samun dama da kuma yana yi na koyar da ‘ulum’ na Ahlulbayt [AS],saboda a  lokacin a madina kawai yana da masu ]aukar karatu a wurinsa sama da mutum 4,000.Wanda dukkansu shi’arsa ne,wato banda wa]anda suke kan wasu a}idoji da kuma mazhabobi,wa]anda su ma suke karatu a wurinsa kamar yadda zamu ga haka nan gaba a wajen bayanin iliminsa.                                                                                                                                                                                                Khususiyya ta uku,a lokacin Imamancinsa ne daular Bani umayya ta fa]i da kuma hawan daular Abbasiyawa.Kabarinsa na madina ne a ma}abartar  Ba}i’a.Kusa da shi akwai kabarin Imam Hasan [AS],da na Imam Zainul abidin [AS],da kuma na Imam Ba}ir [AS],Imamai 6 kuma kabarinsu na Ira}i ne.Sune Imam Ali [AS],Imam Husain [AS],Imam Kazim [AS],Imam Jawad [AS],Imam Hadi [AS],da kuma Imam Askari [AS],sai kuma Imam Ridah [AS] shi kuma nasa yana Iran ne.Wannan kenan a ta}aice dangane da abin da yake da ala}a da wafatinsa.                                                                                                                                                Sai kuma bayani a ta}aice dangane da wasu ~angarori na rayuwarsa da nufin su zama darasi gare mu,wanda insha Allah in muka ]abbaka su a rayuwarmu,zasu kasance masu amfani gare mu duniyarmu da kuma lahirarmu.                                                                                                                                                                          1-AKHLA{-[INSA:
A-AFUWARSA,Imam sadi}[AS] ya kasance mai yawan afuwa,ba wai kawai ya kan yi afuwa ga wanda yayi masa laifi bane,a’a yak an ma nema masa afuwa a wajen Allah[T],misali;akwai wani mutum da yaje wajen sa sai yace ma Imam Sadi}[AS],wane,ko yace  kaza da kaza gare ka,wato marasa kyau,ciki har  da zaki,kamar yadda yazo a ruwayar.Sai Imam Sadi}[AS] yace ma kuyangar sa[baiwarsa] kawo min abin al-wala,data kawo sai yayi alwala,bayan haka yai sallah raka’a biyu.Bayan haka yai addu’a yace, “Ya ubangiji wannan mutumin ya ta~a ha}}ina,to,na yafe masa,kai ne mafificin yafewa,ka yafe masa kada ka kama shi,ko kayi masa hisabi saboda ni.”Shi wanda ya kawo wannan Maganar,sai yai tsammani,Imam Sadi}[AS] zai ma mutumin mummunar addu’a ne,amma sai yaga akasin haka,wannan babban darasi ne,gare mu.Haka nan an ruwaito cewa wani mutum cikin mahajjata sai jakar ku]insa ta fa]i,ya dudduba bai gani ba,sai ya ga Imam Sadi} [AS] yana sallah a masallacin Manzon Allah [S].To da yake bai san ko waye ba,kawai wal’iyazubillah sai yace shi ya ]aukar masa jaka.Sai Imam Sadi} [AS] yace masa cikin lausasawa,mene ne cikin jakar? Yace dirhami dubu ke ciki.Sai Imam Sadi} [AS] ya bashi dirhami dubun.Mutumin ya wuce kenan beyi nisa ba,sai ya ga jakar ku]in nasa,sai ya dawo wajen Imam Sadi} [AS] yana cewa ya yafe masa ,ya mi}a masa dirhami dubun,sai Imam Sadi} [AS] yace ba zai amsa  ba.Ya tafi ya bashi.Yace masa, “Duk abinda ya fita hannuna ,to ba zai dawo ba”.Shine wannan mutum abin ya bashi mamaki ,sai yaje ya tambaya,wai waye wannan? Sai aka ce masa Ja’afar Sadi}  ne.Shine ya tafi yana cewa haba,shi ya san wannan aiki  sai shi! Shine Imam Sadi} [AS] ya na yawan cewa, “Mu  Ahlul Baitin manzon Allah,]abi’unmu shine yin afuwa ga wanda ya zalunce mu”.Mu duba wannan }issa mu gani,zamu ga cewa A’imma [AS] ba wai kawai sun fuskanci jarabawowi wajen masu tafi da iko na zamunansu bane,a’a har da jarabawowi daga mutanen gari,in ba haka  ba.Don ba kaga kayanka ba,mutum na sallah sai kace shi ya ]aukar  maka.
B:KYAUTAR SA [AS]:Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan kyauta,wani daga cikin sahabbansa,ya shiga wajensa yace masa yana cikin matsala ta rayuwar,saboda haka yana son Imam Sadi}  ya taimaka masa da addu’a,sai Imam Sadi} [AS] ya aika akawo masa wata jaka da aka kawo ya mi}a masa,yace wannan jaka akwai dirhami ]ari hu]u,kaje ka biya bu}atarka  da shi, sai Imam Sadi} [AS] yace ka tafi da shi zan yi maka addu’ar.                                                                                                                                                                                                          Haka nan wani fa}iri ya ta~a zuwa neman taimako wajensa,sai ya bashi dirhami 400,sai fa}irin ya amsa ya tafi yana godiya.Sai Imam Sadi} [AS] yace wa khadiminsa je kace wa mutumin ya dawo .Sai wannan khadimin yace masa, baya tambaye ka ba,ka kuma bashi? Sai Imam Sadi} [AS] ya amsa masa  da cewa ; “Manzon Allah [S] yace mafificiyar sadaka itace wadda ta wanzar da wadata,sai Imam Sadi} [AS] ya mi}a masa zobe mai tsada.Kamar yadda yazo a ruwaya,yace masa duk lokacin da aka shiga cikin matsala ka sayar da zoben.                                                                                                                                                                              Kuma Imam Sadi} [AS] ya kasance yakan aika da kyauta ga wani ko ga wasu ba da sanin cewa daga wajensa bane.Misali,akwai wani ]an uwansa na jini lokaci bayan lokaci yakan aika da kyautar ku]i mutumin ya tambayi ]an sakon wannan da yake aiko wa da wannan sa}on lokaci bayan lokaci wa nene? Sai  ]an sa}on yace masa bai son a bayyana ko wanene,kawai sai wannan mutumin ya kada baki yace kai wannan mutumi na taimaka mana,amma ga Ja’afar ]an uwana ne,ga shi da ku]i amma ko dirhami ]aya bai taimake ni da shi ba.Mu duba kuma irin wannan jarabawa daga ‘yan uwa na  jini,shi yana }ule da Imam Sadi} [AS],alhali shi yake aika masa da wannan taimako.                                                                                                                Haka nan kuma yazo akan cewa Imam Sadi} [AS],idan dare yayi, lokacin da duhu yayi duhu yakan ]auki  kayayyaki na abinci,nama da ku]I, ya ]auka da kansa yana bin gidajen matalauta yana raba musu,basu san ko waye ba,sai bayan rasuwar Imam Sadi} [AS] suka ga abubuwan da aka saba basu  na agaji ya yanke,suka fahimci ashe Imam Sadi}[AS] ne, ke kai masu wa]annan kayayyakin.
C:TAUSAYINSA:Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan tausayi.Akwai wani daya shiga wajen Imam Sadi} [AS] sai ya gan shi launinsa ya canza,kuma cikin damuwa,sai mutumin yace masa lafiya? Sai Imam Sadi} [AS] yace masa; “na hana  hawa saman daki ,sai na shiga cikin gida  na ga ]aya daga cikin kuyangina ta hau ]auke da ]aya daga cikin yara na  da take reno,ganina  sai ta firgita ta ]imauta har wannan yaron ya fa]o ya kuma rasu.Wannan damuwa da kaganni  a ciki ba wai saboda rasuwar wannan yaron nawa bane, a’a yadda na ga ta firgita  hankalinta ya tashi shine tausayinta ya kama ni”.Daga }arshe Imam Sadi} [AS] yace mata ba komai har sau biyu.Yace kuma ta tafi ya ‘yanta ta saboda Allah [T].
2.GIRMAMAWARSA GA MANZON ALLAH [S]:An ruwaito cewa akwai wani daga cikin sahabban Imam sadi} [AS] ya kasance ya kan je majalisin Imam Sadi} [AS],sai aka kwana biyu bai je ba.Ran da yaje sai Imam Sadik [AS] yace masa,kayi kwana ki bangan ka ba.Sai yace masa haihuwa aka yimin,an sami da namiji,sai Imam Sadi} [AS] yace Allah yayi masa albarka,ya tambaye shi wane suna kasa mishi? Sai yace nasa masa Muhammad,jin haka sai Imam Sadi} [AS] ya sunkuyar da kansa }asa yana cewa har sau uku, Muhammad! Muhammad! Muhammad!!! Sannan yace; kaina da na iyali na da wa]anda suke a doron kasa baki ]aya,su kasance fansa gareka ya Manzon Allah [S]”.Daga }arshe yace masa. “Tunda kasa masa suna Muhammad,to kada ka zage shi,kada ka dake shi,kada ka munana masa”.Yace kuma ka sani babu wani gida a doron }asa wanda akwai mai suna Muhammad a ciki  face mala’iku  zasu dinga tasbihi kowace rana a gidan.Akwai ma Hadisi da yazo cewa talauci baya shiga gidan da akwai mai suna Muhammad.Mu duba ta’azimin sa ga Manzon Allah [S] na sun kuyar da kai,da yaji sunan Manzon Allah [S],da kuma abinda ya fa]a ma   wannan mutum daya sa ma ]ansa sunan Manzon Allah [S],yace kada kayi masa kaza da kaza,wato wannan yana alamta gayar girmamawar sa ga Manzon Allah [S].
3.IBADARSA:Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan ibada,yazo akan cewa a zamaninsa baki ]aya babu wanda ya kai shi yawan ibada,akwai ma fa]in Malik ]an Anas,wato shugaban mazhabar malikiyyah yace; “Na jajje wajen Ja’afar ]an Muhammad  lokuta da yawa,amma duk lokacin da naje sai in samu yana ]ayan uku; ko yana sallah,ko karatun Al}ur’ani,ko kuma yana Azumi”.Akwai kuma wani da ya ga Imam Sadi} [AS] ya yi sujuda a masallacin  Manzon Allah [S],mutumin yana zaune yana jin Imam Sadi} [AS] ya na tasbihi a cikin sujudar,sai wannan mutumin ya ]aukar wa kansa cewa,ko zai dinga }idaya wannan tasbihi da yake yi,yana ta }idayawa,sai da Imam Sadi} [AS] ya yi tasbihi 360  sannan ya ]ago daga sujudar.Akwai kuma wata rana Imam Sadi} [AS] yana karanta Al}ur’ani a cikin sallah sai aka ga yana yinsa ya canza,bayan da ya gama sai aka tambaye shi akan haka sai yace; “Ban gushe ba ina karanta wa]annan ayoyi na Al}ur’ani ba, har na kai matsayin da kamar ina jinsu mubasharatan daga wanda ya saukar dasu”.Haka ma Imam Sadi} [AS] ya ta~a kasancewa a wani wata na Ramadan ba shi da lafiya,amma duk da haka a daren 23 na watan yace akai shi masallacin Manzon Allah [S],haka ya dinga ibada duk da halin da yake ciki na rashin lafiya har wayewar gari.                                                                                            Akwai wata rana suna tafiya da wani mutum akan dabba kawai sai yaga Imam Sadi}[AS] ya sauko yayi sujuda,kuma ya tsawaita a sujudar,shine da ya ]aga kai daga sujudar sai  shi wannan mutumin ya tambayi Imam Sadi} [AS] dalilin haka.Sai Imam Sadi} [AS] yace masa yayi ne saboda godiya ga Allah [T] kan wata ni’ima da yayi masa,watau sujudu shukru.Kuma ita wannan sujuda ta godiya ana son mutum ya saba da yin ta a duk lokacin da Allah [T] yayi masa wata ni’ima,ko kuma ya tun ku]e masa wata musiba.Domin yin haka hanya ce ta da]a samun abinda Allah ya ba ka ko kuma da]a tsare ka daga abin da ya tsare ka,wato kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa idan kuka gode zan }ara maku.                      Haka nan yazo akan cewa duk lokacin daya tsaya zai yi sallah akan ga launin sa ya canza,kuma jikinsa na makyarkyata ba don komai ba sai saboda tsoron Allah [T] da kuma ta’azimin wanda zai tsaya gaba gare shi,wato Allah [T].                                                                                                                                                                 Haka nan kuma ya kasance mai yawan addu’oi,an samo addu’oi da yawa daga wajensa.Akwai ma wani malami daya tattaro addu’oin da aka samo daga wajen Imam Sadi} [AS] ya mai she shi littafi,yasa masa suna Sahifatu-Sadi}iyya.Ana samun littafin.Haka nan kuma Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan azumi,kuma ya kasance ya kan  kwa]aitar da mai azumi cewa idan mutum na azumi to ya kiyaye ruhin azumin.Alal misali ya kan ce; “Idan kana azumi to jinka da ganinka da harshenka suyi azumi [wato su kame] daga munanan abubuwa.Yace kada ranar da kake azumi ta zama kamar ranar da baka azumi.Wato ranar da mutum yake azumi ya da]a kame ga~o~insa daga sa~a wa Allah [T] fiye da ranar da bai azumi.Yazo akan cewa wata rana Imam Sadi} [AS] yana fa]in cewa “Na kasance lokacin ina saurayi,wato matashi,na kasance ina yawan ibada,har Babana yace min in sassauta.Domin  idan Allah [T] yana son bawa,to yakan yarda da ka]an daga wajensa”.A ta}aice dai Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan ibada ta kowace fuska,wato a salloli,karatun Al}ur’ani,Azkar,Azumi,Addu’oi da dai sauransu.
4.ILIMINSA:Mutum zai iya cewa duk janibobin rayuwar Imam Sadi} [AS] babu wani janibi daya fi fice akai,kamar wannan janibi na iliminsa saboda ya samu yana yi na ba da ilimi da kuma ya]a shi fiye da sauran A’imma na Ahlulbayt [AS],har ma yana yawan fa]in cewa; “Ku tambaye ni gabanin ku rasa ni,domin babu wanda zai baku Hadisai a bayana kamar yadda nake baku Hadisan”.Akwai kuma in da yake cewa; “Na san littafin Allah [}ur’ani]  ciki da bai kamar tafin hannuna”.Akwai kuma in da yake cewa na san abinda yake cikin sama da abinda ke cikin }asa da abinda ke cikin Aljanna da kuma wuta da abinda ya kasance da kuma abinda zai kasance daga nan har zuwa sa’ar }iyamah”.                                                                Shugabannin mazhabobi guda biyu na madrasa ]in Ahlus Sunnah duk a wajen sa suka yi karatu,wato Abu Hanifa,shugaban mazhaban Hanafiyya.Akwai ma wata Magana tasa da yake cewa;ba domin shekaru biyu da yayi yana karatu gun Imam Sadi} [AS] ba,to daya halaka.Haka nan Malik ]an Anas wato shugaban mazhaban Malikiyya,shima yayi karatu a wajensa,ba wai kawai yayi karatu a wajensa bane,a’a ya tasirantu sosai da wasu abubuwa daya gani daga rayuwar Imam Sadi} [AS],misali,yadda yaga Imam Sadi} [AS] yana ta’azimin Manzon Allah [S] in zai ambaci sunansa a wajen bada hadisi ko kuma idan yaji sunansa ko kuma ba zai fa]i wani hadisi na Manzon Allah [S] ba sai yana da alwala,ire-iren wa]annan abubuwan sun yi tasiri ga Malik sosai,domin takai shima ya kwaikwayi haka daga Imam Sadi} [AS].Akwai ma lokacin da Imam Sadi} [AS] yace masa “Yana son sa.Yazo akan cewa duk lokacin da Malik ya tuna wannan Magana ya kanyi farin ciki,kuma ya gode wa Allah [T].                                           Kuma Imam Sadi} [AS] koyarwar da yayi,yayi ne a dukkan fannoni na ilimi kamar Tafsir,Tauhid,Fi}hu,Hadisi.A ta}aice dai babu wani fanni wanda Imam Sadi} [AS] bai karantar ba,kai hatta fannin ilimin kimiyya wato ilimin ‘science’ kamar Chemistry,Biology, da kuma Physics duk asalin su daga wajensa ne.Hatta malaman kimiyya magabatansu sun tabbatar da haka.Kuma a cikin almajiran Imam Sadi} [AS],wanda yafi fice a wannan ilimi na kimiyya shine Jabir ]an Hayyan.Mutum in yana son }arin bayani sosai kan wannan ilimin kimiyya da Imam Sadi} [AS] ya koyar, ya samu littafi mai suna A’IMMATUNA juz’I na ]aya ya duba.
Wannan kenan a ta}aice dangane da iliminsa sauran darussan takwas insha Allah a wata munasabar ta wiladarsa ,ko wafatinsa za’a ]ora akai.

No comments:

Post a Comment