Sunday 3 February 2013

Bayani kan muhimmancin Akhla}.


A darasin daya gabata,an ]anyi bayani a ta}aice, kuma a dun}ule dangane da ilimin irfani da kuma cewa Akhla}, ~angare ne na shi wannan ilimin irfani,da kuma muhimmancin Akhla} da yadda kyakkyawan Akhla},  yake iya canza ma}iyi ya zama masoyi,kamar yadda aka bada misalai daga Manzon Allah [S] da kuma Aimma na Ahlul Bait [AS]
,wanda anan ne aka  kwana.Sai dai wani ]an tambihi, a nan shine lokaci bayan lokaci za a ri}a samun yankewar shi darasin,saboda rubutu na wafati ko shahadar Aimma na Ahlul Bait [AS] daya kasance, a kowane wata daga cikin wa]annan watannin 12 na musulunci,wanda akan kawo da, unwani  ]in ‘ Darussa 12’,alal misali,wata da muke fita na zul}i’idah  akwai wafatin Imam Ridah [AS],da kuma wannan watan na zulhijja,akwai wafatin Imam Ba}ir [AS],watan gobe kuma  wato Muharram akwai shahadar Imam Husain [AS] da kuma wafatin Imam Zainul Abidin [AS],da dai sauran watanni,  akan asasin wafatin ma’asumai ]in [AS].Saboda haka koda wani lokaci  ba’a ga cigaban darasin shi Akhla} ]in ba biye da juna to wannan shine dalilin.
Dawowa ga shi darasin Akhla},da yake har yanzu ana cikin shimfi]a da kuma gabatarwa na shi ilimin irfani da kuma muhimmancin Akhlak ne,akwai wata mas’ala muhimmiya da take da ala}a da ilimin irfani,wannan mas’ala kuwa itace,menene hukuncin yin Ta}lid  a cikinsa? Shin wajibi ne ko kuma bai halatta ba? Kamar yadda aka sani,a fannin ilimin  fi}hu,idan mutum shi ba mujtahidi bane,ba kuma muhta]i ba,to wajibi ne ya zamo yana ta}lid da wani daga cikin mujtahidai.Amma a fannin ilimin A}a’id,wato a}idah,bai  halatta  yin ta}lidi a ciki ba,to shifa ilimin irfani,meye matsayin ta}lid  a cikinsa? Wajibi ne ko bai halatta ba?A wata ma’ana ta daban,yadda za’a iya fahimtar abin da ake so a fitar a nan,a Madrasah ]in Ahlus Sunna a ~angaren fannin Tasawwuf,malaman Tasawwuf ]in sun tafi akan cewa dole ne mutum ya zama yana da shaihi ko malami domin sulukinsa zuwa ga Allah[T].To a Tasawwuf na imamiyyah,mene ne matsayin haka?dolene sai ya samu shaihi ko malami a sulukinsa zuwa ga Allah [T]? To wannan shi ake nufi da abinda aka ambata a baya na cewa wajibi ne yin Ta}lidi, a ilimin irfani ko ma bai halatta ba? Amsa anan itace malaman irfan a madrasah ]in imamiyyah akan wannan mas’ala sun kasu kashi biyu,wasu sun tafi akan cewa dole ne,wasu kuma sun tafi akan cewa ba dole bane.Daga cikin wadanda suka tafi akan cewa ba dole bane akwai Ayyatullah Bahjati,wanda kamar yadda aka sani yana daga cikin manya-manyan malaman Irfan a madrasah ]in imamiyyah a wannan zamanin,shekaru kusan uku da suka wuce Allah [T] yayi masa rasuwa.To,an sha tambayar sa dangane da wannan mas’alar, ga amsar da yake bayarwa.Ga misalin tambayar da aka yi masa; shin suluki zuwa ga Allah [T] yana bu}atuwa zuwa ga malami,in kuma ba malamin,to,menene abin da mutum zai yi? Ga amsar daya bayar, “Da sunan Allah ma]aukaki,malaminka shine iliminka,kayi aiki da abin da ka sani,zai isar maka daga abinda baka sani ba”.Akwai wani daya tambaye shi yake cewa;’nayi niyyar yin suluki zuwa ga Allah [T],ina son irshadi akan haka,shin wannan aiki yana bu}atuwa zuwa ga malami ko a’a? ga amsar daya bayar, “Da sunan Allah ma]aukaki,malaminka shine iliminka,ka aikata abin da ka sani da kuma lizimtar haka,zai kasance ya wadatar,domin duk wanda ya aikata abin da ya sani,to,Allah [T] zai gadar masa a bin da bai sani ba.”Wata tambayar kuma itace,Ni ina son suluki zuwa ga Allah [T],to wace hanya ce zan bi? Ga amsar, “Da sunan Allah ma]aukaki,in dai mutum da gaske yake yi,to barin sa~o [zunubi] ya wadatar dashi,a duk tsawon rayuwarsa,ko da kuwa zai rayu  shekara dubu ne”.A ta}aice dai wa]annan amsoshi da Ayatullah Bahjati ya bayar yana nuna cewa,idan mutum ya san ilimin irfani,ya kuma aikata ilimin,ya kuma nisanci zunubi,to wannan zai wadatar masa.
Sai kuma wa]anda suka tafi akan muhimmancin samun malami da mutum zai yi ta}lidi  da shi a wannan fagen na irfan,misalin su shine Ayatullah Sayyid Ali Al-}adiy,wanda shima babban malamin irfani ne,ya fitar da urafa’u da yawa a madrasah ]insa,ga abin da yake cewa,mafi muhimmancin abinda mutum yake bu}ata  ga sulukinsa zuwa ga Allah [T] shine ya samu malami  }wararre a ilimin irfan,kuma kamili a sulukinsa da kuma ]abi’unsa’.A wani waje  kuma yana cewa,idan mutum ya }are rabin rayuwarsa wajen neman irin wannan malami kamili na irfan,to bai yi hasara ba’.A ta}aice dai kuma a dun}ule a fagen ilimin irfan, a madrasah ]in imamiyyah mutum na da za~i,ko dai ya wadatu da karanta littafan irfan tare da aikatawa,ko kuma il-tizami da malaman irfani ko kuma ha]a duka  biyun,wato domin sulukinsa zuwa ga Allah [T].A nan ga sunayen wasu daga cikin littafan Akhla} da kuma suluki, da sashen malamai na imamiyyah suka rubuta;1-jami’u-ssa’adat,na shaikh Muhammad Mahdi Annara}y. 2-Durusun fil Akhla},na Ayatullah Mish-kini. 3-Tazkiyatun-Nafs,na Ayatullah kazim Ha’iriy. 4-Assuluki-ilallahi,na sayyid Abdullahi shubbar.5-Sairu-ilallahi,na ustaz sayyid Hasan. 6-Tahzibin-Nafs,na shaikh Muhammad kazim.7-kitabun- fil- Akhla}i- wal irfan. 8-A]]ari}u-i lallahi Ta’ala,na shaikh Husain Bahraniy. 9-Adabul-Arif,na shaikh ibrahim surar. 10-Al-}isasul irfaniyya,na Ridah Muhammad. 11-Risalatu-li}a’allah,na Ayatullah mirza jawad Attab-riziy.Da dai sauran littafai masu yawa wa]anda malaman imamiyyah suka rubuta a wannan fagen na ilimin irfani,wa]anda ba za  a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.
Kamar yadda aka bayyana a darasin da ya gabata cewa ilimin irfan yana da manyan ~angarori guda biyu,Akla} da kuma ma’arifa,wato sanin Allah,to  ko wanne daga cikin wa]annan ~angarori biyu, akwai hadisai masu yawa da suka zo daga manzon Allah [S] da kuma Aimma [AS] da suke nuni dangane da matsayi da kuma falalarsa.Alal misali,ga wasu hadisai da suka zo dangane da muhimmancin Akhla} da kuma matsayinsa a addinin musulunci;. 1-wani mutum yazo wajen manzon Allah [S] ya zauna gaba gareshi,yace ya Manzon Allah [S] me nene  addini? Manzon Allah [S] yace masa kyakkyawan Akhla}, sai mutumin ya dawo ta hagun Manzon Allah [S] yace,mene ne addini? Manzon Allah [S] yace masa kyakkyawan Akhla},sai kuma mutumin ya dawo bayan Manzon Allah [S] ya sake wannan tambayar, me nene addini? Manzon Allah [S] ya dube shi yace,shin baka fahimta ba,shine kada kayi fushi’. 2-An tambayi Manzon Allah[S] wane aiki ne yafi falala,yace kyawawan Akhla}. 3-Haka nan an  samo hadisi daga Manzon Allah (s) ya ce “Babu wani abu da ya fi nauyi a mizanin mutum (ma’auni)  ranar  }iyama  fiye da kyekkyawan akhla}.
4. Manzon Allah (S)  ya ce; “mafi yawan abin da zai shigar da al’ummata aljannah , shine ta}’wa da kyakkyawan akhla}.
5. Manzon Allah (S) ya ce; “Mafi soyiwar ku zuwa gare ni da kuma wa]anda su ka fi kusa da ni a majalisina  ranar }iyama, sune wa]anda suka fi kyakkyawar akhla}”.
6. Manzon Allah (S) ya ce; Na hore ku da kyakkyawan akhla}, domin mai kyakkyawan akhla}, ]an aljannah  ne  ba makawa”.
7. Manzon Allah (S) ya ce; “Mai kyakkyawan akhla} yana da lada irin na mai azumi mai kuma }iyamullaili”.wato sallar dare
8. Manzon Allah (S) ya ce ; “Allah (T) yana son mai kyakkyawan akhla}, yana kuma  }in mai mummunan akhla}.
9. Manzon Allah (S) ya ce; “Ba za ku iya yalwatar da mutane da dukiyoyin ku ba, ku yalwatar da su da akhla} ]in ku.
10. Daga Imam sadiq (AS) ya ce; “Mumini bai gabata ga Allah (T) da wani aiki da yafi  soyuwa  gare shi, baya  ga wanda ya wajabta masa ba, fiye da ya yalwaci mutane da akhla} din sa.
11. Haka nan daga Imam sadiq (AS) ya ce; “Duk wanda ya ke son Allah (T) ya shigar da shi cikin rahamarsa, ya kuma sa shi a aljannarsa, to ya kyautata akhla} ]in sa.
12. An samo daga Imam Ali (AS) ya ce; “ko da ba mu }aunar aljannah, bamu kuma tsoron wuta, ba mu fatan samun lada, da kuma gudun u}uba, duk da haka da ya kama ce mu mu siffantu da kyakkyawan akhla}”.
Da dai  sauran hadisai masu yawa wa]anda aka samo daga Manzon Allah (S) da kuma Aimma na Ahlul bait (AS), wa]anda ba za a iya kawowa ba saboda gudun tsawaitawa.
Sai kuma hadisan da suka zo na akasin kyakkyawan akhla},wato mummunan akhla}, su ma ga wasu hadisai da suka  zo  akan haka da kuma  illolin mummnan  akhla}.
1.       Manzon Allah (S)ya ce;  “Mummunan akhla}  yana ~a ta aiki, kamar yadda kunu ya ke ~ata zuma.
2.       Manzon Allah (S) ya ce; “kashedinku da mummunan akhla}, domin mummunan akhla} na  kai mutum zuwa wuta.
3.       An samo daga Imam sadiq ya ce; “Mummunan akhla}  yana ~ata imani  kamar yadda kunu ke ~ata zuma.
4.       Daga Imam sadiq (AS) ya ce; “Duk wanda ya munana  akhla} ]in sa, to, zai azabatar  da kansa. Misali mai yin hassada, in mutum ya duba zai ga cewa ko da wani lokaci zai kasance ne hali na damuwa  da  kuma  ba}in ciki ga wanda ya ke yiwa hassadar”.
5.       An tambayi Imam Ali (AS) a cikin mutane wanene ya fi dawwama cikin ba}in ciki, sai ya ce, “wanda ya fisu munin akhla}”.
6.       Haka nan wani hadisi ya zo akan cewa wanda ya munana akhla} ]in sa, iyalinsa za  su }osa da shi. Misali ya zama mai yawan fushi ko rashin ha}uri da kuma kau da kai da dai sauransu. Wannan ke nan, shima a ta}aice, wato hadisan da suke  magana  dangane da mummunan akhla}.

Bayan haka nan akwai tambayoyi guda uku.
1.       Yaya za ayi mutum ya san aibobin nafs ]insa?. Wato ya san ko yana da mummunar akhla} ko bai da shi.
2.       Wa]anne hanyoyi mutum zai bi domin ya ku~uta, wato ya tsarkaka daga mummunan akhla}?
3.       Yaya za ayi ya samu ko ya siffanta da kyawawan akhla}?
Amsoshin wa]annan tambayoyin guda uku sune: tambaya ta farko wato yadda mutum zai san aibin nafs ]in sa a nan shine, malaman akhla} sun kawo hanyoyi da yawa da mutum zai bi domin ya san aibin nafs ]in sa, amma  ga hanyoyi uku:-
1.       Mutum shi }ashin kansa ya zauna yayi tunani , ya binciki kansa da kansa, wato muhasaba, ya ga wane  mummunan akhla}  yake da shi ko wani aibi na nafs yake da shi. Misali ya soma da zuciyarsa, shin yana da cututtuka na zuciya, kamar hassad, riya, ujub ko su’uzzann (mummunan zato) ga juna da dai sauran cututtuka na zuciya da zai binciki kansa.
Bayan haka sai ya dawo ga ga~o~insa na zahiri kamar harshensa ya binciki kansa yana giba, ko fa]in }arya, ko anna-mimanci (wato ]aukar maganar wannan ya kai ma wannan), ko kuma suka da aibanta juna. Haka nan kunnansa yana yin abubuwa da suke haramun ko makaruhi da shi.
Haka nan idanuwansa, yana ganin abubuwan da suke haramun ko makaruhi da shi. Da dai sauran aibobi na nafs kamar yawan  fushi ko rowa da dai makamantansu.
2.       Hanya ta biyu ita ce hanyar mutane, wato duk wani mummnan akhla} da ka gani ga wani ko wasu, sai ka tambayi kanka kana da wannan mummnan akhla} ]in ko ba ka da su? Ko kuma abin da ya fito na suka da aibantawa daga ma}iyanka, domin shi ]abi’ar ma}iyi  a kullum shine ya nemi aibin mutum, domin ya aibanta shi da shi, wato ya soki shi, to mutum shi sai yayi amfani da wannan damar ya ga aibin, in yana da shi sai yayi }o}ari ya tsarkaka daga aibin. ko kuma ta hanyar masoyin sa, kamar mutum ya ke~an ce ka ya nuna maka aibobinka da kuma matsalolinka, wato dai da nufin nasiha. To anan sai mutum ya anshi irin wannan nasiha da farin ciki,da ma godiya ga wanda yayi masa, domin ya taimake ka ne. Misali kamar kai ne,kana  cikin  jama’a sai wani ya ga tasono ko wata ‘yar majina a hancin ka, ko wani datti a bayan rigarka, sai ya ]an ke~anceka, yace maka  ai ko hancinka akwai kaza da kaza, ko kuma bayan rigar ka, akwai kaza da kaza, ka duba sai ka ga haka ne, yadda mutumin ya fa]i. Ka ga ai murna za ka yi,kai masa godiya sannan ka gyara. Ka ga ke nan ya taimake ka.
[an tambihi a nan shine, sau da yawa za ka ga haka zai iya samun mutum, misali yana da wani aibi da ya ke yi wanda bai dace ba,ko kuma wata mummunar ]abi’a, ai masa nasiha akai, mai makon ya ji da]in haka a zuciyarsa, akasin haka  sai ya zama bai ji da]i ba. Ko kuma  ya dage akan abin da bai dace ]in ba, wato ya}i  gyara wa, alhali }in gyara aibin nafs ]in, ya fi muni akan wancan misalin da aka bayar na kaza da kaza a hanci, da kuma datti a taguwarsa, domin da zai mutu, nan take illarsa a wannan gida na duniya ne kawai. Sa~anin ko aibin nafs ko mummunar akhla}, idan mutum ya mutu bai gyara ba, to illar  haka  za ta bishi har lahira, ba wai za ta tsaya a gidan duniya ba.
Hanya ta uku da mutum zai bi domin ya san aibobin nafs ]insa, it ace hanyar malami masanin irfan, da kuma  baiwa ta kashafi na akhla} ]in mutane. Wato ba wai kawai masani ga akhla} ba, a’a Allah (T) ya yi masa baiwa da ganin mutane  a ruhinsu, wato a ba]inin su, wanda in ya ganka ba sai ka fa]a masa aibin nafs ]in ka ba, zai fa]a maka aibin da kuma matakan da za ka bi na mujahada domin magance aibin. To, samun irin wannan arifi, shi ya ke da wahala a wannan zamani namu, ba wai ba a  Samuba ba, sam sam.Kuma in mutum ya bibiyi tarihi na malaman Tasawwuf ,na Ahlus sunna da kuma malaman  Irfan na shia,zai ci karo da irin wa]annan bayin Allah, da Allah [T] yayi musu wannan bai wa ta kashafi,misalin irin wa]annan bayin Allah masu kashafi na imamiyya a wannan zamani namu, akwai Ayatullahi Bahajati,wa]anda suka zauna dashi sun tabbatar da haka. Insha Allah a darasi na gaba za’a kawo amsoshin sauran wa]ancan tambayoyi guda biyu.

No comments:

Post a Comment