Sunday 3 February 2013

Darussa 12 daga rayuwar Imam Hasan (AS)


Kasantuwar wata da muka fita na Safar, 28 gare shi, shi ne wafatin Imam Hasan (AS) a wata ruwaya kuma 7 ga Safar, da ma wani lokaci akan samu wannan sa~anin na ruwayoyi tsakanin Malaman tarihi na wilada ko wafatin Ma’asummin (AS), wato Manzon Allah (S) da kuma A’imma na Ahlul Baiti (AS) wanda akan asasin wa]annan ruwayoyi mutum zai ga mabiya Ahlul Baiti (AS) a wata nahiya sun tafi a kan ruwaya kaza wata nahiyar kuma sun tafi a kan ruwaya kaza,
alal misali dangane da wafattin Imam Hasan (AS) mafi yawan mabiya Ahlul Baiti (AS) da ke Ira}i, suna raya wannan munasaba ne 7 ga watan Safar.
A Iran kuma suna raya munasabar a 28 ga watan Safar ne, tare da munasabar wafatin Manzon Allah (S) a kan asasin wannan ruwaya ta 28 ga Safar. Wafatin Imam Hasan (AS) ke nan ya yi muwafa}a da wata da kuma ranar wafatin Manzon Allah (S) kamar yadda wiladar Imam Sadi} (AS) ta yi muwafa}a da wata da kuma ranar wiladar Manzon Allah (S) wato 17 ga watan Rabi’ul Awwal.
Imam Hasan (AS) shi ne Imam na biyu kamar yadda aka sani a jerin }idaya na Imamai 12. An haife shi ne a Madina 15 ga watan Ramadan shekara ya 3 bayan Hijira. Ya rayui tare da Kakansa wato Manzon Allah (S) shekaru 7 da watanni. Ya rayu tare da Mahaifinsa Imam Ali (AS) shekaru 37. Bayan shahadar Imam Ali (AS) ya rayu shekaru 10. Wannan kuma shi ne muddan Imamancinsa. Ya rasu yana da shekaru 47 a duniya, Hijira na da shekaru 50, kuma kamar yadda aka haife shi a Madina, a nan ya rayu, a nan kuma ya rasu, face kusan shekaru shida da ya yi a Kufa lokacin da Imam Ali (AS) na zaune a Kufar, bayan shahadar Imam Ali (AS) da wata shida ya bar Kufa ya dawo Madina. Saboda haka }abarinsa yana Madina ne, wato Ba}i’a kuma kabarinsa ya kasance abin girmamawa, da kuma ziyara ga Musulmi, musamman ma ga mabiya Ahlul Baiti (AS) har ya zuwa lokacin da Wahabiyya suka rusa ginin }abarinsa da na Imam Sajjad (AS), Imam Ba}ir (AS) da kuma Imam Sadi} (AS). Wannan mummunan aiki da suka yi ya auku ne a 8 ga watan Shawwal shekara ta 1344 Hijiriyya. Bayan nan kuma suka ]auki matakai na hanawa da kuma ta}aita kai ziyara ga wa]annan bayin Allah (T) ta fuskoki daban-daban.
Imam Hasan (AS) ya halarci duka ya}o}in da Imam Ali (AS) ya yi, wato ya}in Jamal, Siffin da kuma ya}in Nahrawan, kuma wannan suna nasa wato Hasan saukakke ne daga sama wato Allah(T) ya yi wahayi ta hanyar Mala’ika Jibril, cewa ya fa]a wa Manzon Allah (S) ya sa masa suna Hasan, kuma ana yi masa kinaya da Abu Muhammad, Manzon Allah (S) ne ya sa masa wannan kinaya. Kuma yana da la}ubba da yawa amma wa]anda suka fi shahara su ne Mujtaba, Sib] da kuma Zakiyy. Kuma ya kasance yana da ’ya’ya 15 maza 8, mata 7. Sai kuma abun da ya shafi wasu ~angarori na rayuwarsa, domin su kasance darussa gare mu da za mu yi }o}arin aikatawa ko kuma da]a }aimi wajen aikata su.
1. IBADARSA: Imam Hasan (AS) ya kasance mai yawan ibada, kamar yadda aka samu haka daga Imam Zainul Abidin (AS) yana cewa Imam Hasan (AS) shi ne mafificin mutanen zamaninsa a wajen ibada da kuma zuhudu. Wato a wa]annan fagagen a zamaninsa ba wanda ya kai shi ballantana ya wuce shi ya zo a tarihinsa cewa idan yana alwala a kan ga ga~u~~an sa  na ma}ayartata kuma launinsa yana canzawa, aka tambaye shi dangane da haka, sai ya ce. Dole ne ga wanda zai tsayu gaban Allah (T) ga~u~~ansa su yi ma}ayartata kuma launinsa ya canza. Kuma ya kasance idan ya zo }ofar masallaci yakan ]aga kansa sama ya ce; “Ya Ubangijina! Ba}onka a }ofarka, ya mai kyautatawa mai munanawa ya zo maka, ka yafe mummunan da ke gare ni da kyakkyawan da gare ka, ya mai karamci”. Kuma Imam Hasan ya kasance idan yana karatun Al}ur’ani mai girma, duk inda “Ya Ayyayuhal-lazina Amanu”. Ta zo bai wuce wa sai ya ce; “Labbaikal Lahumma Labbaik”. Kuma ya kasance idan ya yi Sallar Asuba bai yin magana har sai rana ta keto, wato yakan lizimci Azkar, karatun Al}ur’ani da kuma Addu’o’i a tsakanin wa]annan lokacin kuma idan rana ta fito yakan mi}e ya yi Salla raka’a biyu, wato Salatul-Ish-ra}. Kamar yadda ya zo a tarihinsa, cewa ya yi Hajji ]ai-]ai har guda 25 dukkansu a }afa ya taka daga Madina zuwa Makka an ma ta~a tambayarsa cewa mai ya sa yake zuwa Hajji a }asa, alhali ba wai bai da dabbar da zai hau ba ne, ya amsa da cewa; “Ina jin kunyar Ubanjigina in tafi ]akinsa, ba ina tafe a }afafuwana ba”. Akwai ma lokacin da za su tafi aikin Hajji shi da Imam Husain (AS) daga Madina zuwa makka a }afa.
To, a kan hanya duk wanda suka ha]u da shi a kan dabba. Sai ya sauka saboda jin nauyin Imam Hasan (AS) da kuma Imam Husain (AS) ya ce suna a }asa shi kuma yana kan dabba, ire-iren wa]annan mata fa a kan dabba da suka ha]u da su. Sai su kuma abin ya yi masu }unci tafiya a }asa sai suka aika ]aya daga cikinsu ya samu Imam Hasan da kuma Imam Husain (AS) akan ko za su hau dabbobi. Domin mutane ba za su iya hawa dabbobinsu ba, matu}ar suna ganin su tafe a }asa. Sai Imam Hasan (AS) ya ce masu; “Lallai mun ]aukar wa kawukanmu tafiya ]akin Allah (T) a }asa da }afafuwanmu, saboda haka ba za mu samu hawa dabbobi ba,  sai dai ko mu bi wata hanya, ile ko haka aka yi Imam Hasan (AS) da kuma Imam Husain (AS) suka canza wata hanya, domin su ba da dama ga matafiyan, domin su hau dabbobinsu. A ta}aice dai Imam Hasan ya kasance mai yawan mujahada da kuma ibada.
2. AKLA{ [INSA: Shi ma a wannan fage na Akla} babu wanda ya kai shi a zamaninsa, Malamai na wa]annan makarantu guda biyu wato Shi’a da Sunna duk sun tabbatar da haka ga misalan wasu daga cikin Akla} ]insa, akwai wani daga cikin mutanen Sham ya ga Imam Hasan (AS) yana tafiya kan dabba. Sai ya kama fa]a masa maganganu marasa kyau, a ciki har da zagi da tsinuwa. Imam Hasan (AS) bai mayar masa ba, sai da ya gama Imam Hasan (AS) ya same shi yana murmushi ya ce; “Ya kai wannan dattijo! Ina tsammani kai ba}o ne, ko kana da wata bu}ata a biya maka? In kuma inda za ka ba ka sani ba, ka fa]i a kai ka. In kuma ba inda za ka sauka, ka zo akwai masaukin da za a sauke ka”. Dai da sauran maganganu lausasa da Imam Hasan (AS) ya fa]a masa. Akasin shi abin da ya yi. Wato mai da kyakkyawa a kan mummuna.
Lokacin da wannan mutumin ya ji wa]annan maganganun na Imam Hasan (AS) sai ya fashe da kuka. Ya ce; “Lallai na shaida kai Khalifan Allah ne a doron }asa. A da kai da babbanka, babu wasu da nake }i kamar ku. Amma yanzu babu wani da na fi so a doron }asa kamar ku”. Sai ya yanke shawarar cewa zai sauka wajen Imam Hasan (AS). Tun daga lokacin ya zamo daga cikin mabiya Ahlul Baiti (AS).
Mu duba yadda kyakkyawar ]abi’a take iya canza ma}iyi ya zama masoyi. Shi ya sa kyakkyawar ]abi’a babban makami ce ga ma’abocin addini wajen kira ga tafarkin Allah (T) da kuma Ahlul Baiti (AS), kuma mu duba irin wa]annan jarabawowi da Imamai (AS) suka fuskanta daga mutanen gari, in ba haka ba mutum na tafiya ba li ba la ka kama zagin sa da kuma tsinuwa, kuma wannan duk aikin Mu’awiyya ne, shi ne ya sunnata wannan mummunar Sunna ya gina mutane a kai, musamman mutanen Sham. Kuma ya ba da umurni ga Gwamnoninsa akan su yi, kuma su gina mutane a kai. Wannan mummunan yanayi sai da aka kwashe shekaru masu yawa yana gudana, zuwan Umar [an Abdul’aziz ya hana wa]annan zage-zage da kuma la’antar da ake yi a masallatai ga Imam Ali (AS) da kuma Ahlul Baiti (AS), domin shi Mu’awiyya ba wai kawai ya gina mutanen Sham a kan la’antar Imam Ali (AS) ba ne, a’a ya ma gina su a kan ~ata shaksiyya ]insa, misali lokacin da mutanen Sham suka ji an kashe Imam Ali (AS) sai suka tambaya a ina aka kashe shi? Aka ce a masallaci. Suka ce a’a yana Salla ne da zai je Masallaci?
Mu duba irin wannan ~ata shaksiyya. A zamanin akwai wani da ya je Sham sai ya lura yawancin sunayen yara a Sham daga Walid, Yazid, Mu’awiyya da dai makamantansu, sai ya ji wani na kiran yaransa, yana cewa Ali, Hasan, Husain. Sai ya same shi ya ce; “Wani abin mamaki na ji daga gare ka”. Ya ce; “Menene?” Ya ce; “Tun da na zo garin nan sunayen yara ni kan ji Walid, Yazid, Mu’awiyya, amma kai sai na ji sunayen yaranka Ali, Hasan, Husain?” Sai wannan mutumin Sham ]in ya ce masa; “Haka ne. A nan Sham muna sa wa yaranmu sunayen Khalifofinmu ne, kamar Mu’awiyya Yazid, Walid…. Wani lokaci idan yaran sun yi laifi akan dake su ko a zage su. Ni sai na yi tunani sa wa yarana sunan Ali, Hasan, Husain, domin idan sun yi laifi in zage su, maimakon in sama su sunayen Khalifofinmu, domin kada in zage su”.
Mu duba irin wannan mummunan tunani da aka gina su a kai. Kuma abin ba}in ciki da ban takaici, irin wannan gini da Mu’awiyya ya yi na gaba da }iyayya da rashin girmama Ahlul Baiti (AS) har yau ]in nan ma, akwai guggu~insa da kuma gubarsa tsakankanin wasu Musulmi, domin ni da kunnena na ta~a jin ana tattaunawa da wani Malami, mutumin Yaman a tashar Ahlul Baiti (AS), Alhamdulillah, yanzu mabiyin Ahlul Baiti (AS) ne, yake cewa gabanin fahimtarsa ga Ahlul Baiti (AS) an gina su a kan abubuwa da dama na rashin ganin girman Ahlul Baiti (AS) da }iyayya da su, musamman ma ya ce Imam Ali (AS). Ya ci gaba da cewa akwai lokacin da shi }ashin kansa, ya yi tunanin cewa da ma an kashe Imam Ali (AS) tun a ya}in Badar. Mu duba a ce a wannan zamani namu akwai masu irin wannan tunani?
Shi ya sa in mutum ya dubi madrasa ]in Ahlus Sunnah da kyau, zai ga ta ]oru, wato ta assasu ne a kan koyarwar guda biyu ko uku. Akwai koyarwar wadda ta ]oru a kan koyarwar Sahabban Manzon Allah (S), akwai kuma koyarwa wadda ta ]oru a kan koyarwar Bani Umayya. Akwai kuma ca ku]e tsakanin wa]annan karantarwa guda biyu, wato ta Sahaba da kuma Bani Umayya. Kuma in mutum ya duba tsakankanin Musulmi, zai ga tasirin wannan karantarwar a aikace. zai ga akwai sashen Musulmi, duk da yake ba su mi}a wilayarsu ga A’imma na Ahlul Baiti (AS) ba, wato ba su ganin Imamai 12 a matsayin Khalifofin Manzon Allah (S), amma za ka samu suna son su, suna kuma girmama su da ma neman tabarrukin su. Akasin kuma wasu sashen Musulmi za ka ga babu irin wannan girmamawa ga Ahlul Baiti (AS) ]in, ko kuma duk wani abu da yake da ala}a da Ahlul Baiti (AS) ba su cika son shi ba, ko da ba su fa]i a baki ba, a aikace ko a fuska mutum zai ga haka. Wanda irin wannan duk guggu~in koyarwar Bani Umayya ne, wanda su sun ginu ne a kan gaba da }iyayya da Ahlul Baiti (AS). Saboda haka anan kira ga ’yan uwa Musulmi na madrasa ]in Ahlus Sunna, dangane da mahimmancin bincike a kan al’amarin Ahlul Baiti (AS)wato mutum ya san su waye Ahlul-bait.  mai  Manzon Allah (S) Ya ce dangane da su, da dai sauran abubuwan da yake da ala}a da su.
Dalilin tsawaita bayani a nan shi ne, yadda wani lokaci mutum zai ji ko ya karanta cewa wani daga cikin A’imma (AS) misali Imam Hasan ko Imam Zainul-Abidin ko Imam Kazim wani ya zage su, dalili ko an gina su ne a kai. Amma sakamakon Akla} na A’imma (AS) sai ka ga wa]anda suka yi masu wa]annan munanan abubuwa sun koma masoyansu, kuma mabiyansu. Misali a nan shi ne na }issar shi wannan mutumin Sham da aka kawo da Imam Hasan (AS).
Haka nan Imam Hasan (AS) ya kasance mai yawan kyauta. Akwai wani lokaci ya ji wani yana addu’a, yana cewa ya Allah ka azurta ni da dirhami dubu 10! Sai Imam Hasan ya je gida ya aika mai da Dirhami dubu goman. Akwai kuma wani lokacin da ya sai wata gona a kan Dirhami dubu ]ari hu]u, bayan wani lokaci sai labari ya same shi cewa, ai ko mutanen da suka sayar da gonar suna cikin matsalolin na rayuwa har ta kai ga suna bu}atuwa ga mutane. Sai Imam Hasan (AS) ya mayar masu da gonar kyauta. Akwai kuma wani loakaci Imam Hasan (AS) yana tafiya, sai ya ga wani bawa yana cin abinci, kusa da shi ga kare. Amma bawan in ya ci loma ]aya, sai ya jefa wa karen loma ]aya, haka dai sai Imam Hasan(AS) ya tambaye shi me ya sa yake yin haka? Sai bawan ya ce; “Ina jin kunya ina cin abincin, ban ba shi ba”. Sai Imam Hasan (AS) ya ji da]in wannan kyakkyawar ]abi’a tasa ga karen. Sai ya ce wa bawan ya dakata yana zuwa. Sai Imam Hasan (AS) ya je ga maigidan bawan ya sai bawan, da kuma gonar da ya ga bawan a ciki, ya shaida wa bawan cewa ya ’yanta shi, ya kuma ba shi gonar.
Akwai wani da ya ta~a zuwa wajensa. Ya tsaya gaba gare shi, ya ce; “Ya ]an Amirul-Muminin! Ina gama ka ga wanda ya yi maka ni’imomi, ga wani da yake husuma da ni wanda bai girmama tsoho, bai kuma tausayin yaro”. Imam Hasan (AS) yana jingine sai ya zauna da kyau. Ya ce; “Wanene wannan mai husuma da kai domin in taimaka maka?” Sai mutumin ya ce; “Talauci”. Sai Imam Hasan (AS) ya ce wa khadiminsa, ya kawo abin da ke akwai na ku]i, ya kawo Dirhami dubu biyar. Sai Imam Hasan (AS) ya ce wa khadiminsa ya ba mutumin, ya kuma ce masa; “Ina gama ka da wanda ka gama ni da shi, wato Allah(T), duk lokacin da wannan mai husuman naka ya dawo, to ka zo za a taimaka”. Wannan }issa duk da akwai ]an ban dariya na usulubin da mutumin ya bi wajen neman bu}atarsa, amma akwai darasi a ciki da za mu koya, wato na kyautar Imam Hasan (AS).
A ta}aice dai Imam Hasan (AS) saboda yawan kyautarsa ana ce masa mai kyautar Ahlul Baiti (AS), amma an ta~a tambayar sa me ya sa duk lokacin da aka zo aka tambaye shi wani abu sai ya bayar? Sai ya ba da amsa da cewa; “Ni ma ina tambayar Allah (T), ina jin kunya, ni kuma a tambaye ni ya zamanto ban bayar ba. Kuma na saba in Allah (T) ya ba ni nakan ba mutane, ina gudun in na daina abin da na saba, Allah ya yanke abin da ya saba ba ni”.
Haka nan baya ga yawan kyauta, Imam Hasan (AS) ya kasance mai yawan ha}uri da ma kyautatawa ga wanda ya munana masa. Misali na ha}urinsa. Ya zo a kan cewa Imam Hasan (AS) yana da wata akuya, wata rana sai ya ga }afarta a karye sai ya ce wa wani bawansa; “Waye ya aikata wannan gare ta?” Sai bawan ya ce; “Ni ne”. Sai Imam Hasan (AS) ya ce masa; “Me ya sa?” Sai bawan ya ce; “Saboda kawai in sa maka ba}in ciki?” Sai Imam Hasan (AS) ya yi murmushi ya ce; “Ni kuma zan faranta maka rai”. Sai ya ’yanta shi, ya ba shi kyauta mai yawa.
Haka nan ya kasance mai yawan tawa]i’u. Shi ma wannan akwai misalai da yawa a kansa. Misali guda ]aya a nan shi ne akwai wani lokaci yana zaune zai tashi ke nan sai ga wani ya zo wajensa ya yi masa maraba da zuwa ya ce; “Ka zo ke nan ga shi kuma zan tashi”. Ya ce; “Ka yi min izini in tafi?” Sai mutumin ya ce; “Na’am ya ]an Manzon Allah(S)”. Wannan ke nan a ta}aice dangane da Akla} ]in sa.
3. JARABAWOWI: Imam Hasan (AS) ya fuskanci jarabawowi masu yawa a rayuwarsa musamman ma a }arshen rayuwarsa. Wa]annan jarabawowi sun kasance ta fuskoki daban-daban. Misali ta fuskacin masu tafi da iko, mutanen gari da kuma mabiya. Musamman ma jarabawar da ya fuskanta ta fuskar mabiya wanda yana ]aya daga cikin dalilin da ya tilasta yin sulhu da Mu’awiyya, kuma kamar yadda aka sani jarabawowin da Imamai (AS) suka fuskanta sun kasu kashi biyu. Akwai jarabawar da dukkansu sun yi mushara}a a ciki, misali na }wace iko daga hannunsu, wanda ha}}i ne wanda Allah (T) ya ba su, akwai kuma jarabawa wanda kowane Imami ya ke~anta da ita a zamaninsa. Misalin ]aya daga cikin jarabawan da Imam Hasan (AS) ya ke~anta da ita a zamaninsa, shi ne wannan sulhu. In mutum ya bibiyi abubuwan da suka faru gabanin sulhu da lokacin sulhun da kuma bayan sulhun, zai fahimci jarabawa ce babba ga Imam Hasan(AS), kuma kowane Imami jarabawar da ya fuskanta a zamaninsa da kuma matsayar da ya ]auka kan jarabawar, da a ce Imamin da ya gabace shi ko ya biyo bayansa ya samu kansa a zamanin, to da shi ma matsayar da zai ]auka ke nan. Misali a nan shi ne da a ce Imam Husain (AS) shi ne Imam a zamanin Imam Hasan (AS), to, da matsayar Imam Hasan (AS) zai ]auka. Haka nan kuma da a ce Imam Hasan shi ne Imam a zamanin Imam Husain (AS), to da matsayar Imam Husain (AS) zai ]auka.
Insha Allah in an an zo kan sulhun za a yi bayani dangane da sabab ]in sulhun da sharu]]an sulhun da kuma abin da ya biyo bayan sulhun daga mabiyansa, wanda shi ma wani nau’in jarabawa ne ga Imam Hasan (AS)
4. KUKANSA: Imam Hasan (AS) ya kasance mai yawan kuka, saboda tsoron Allah (T) da kuma matakan da ke gaban mutum na mutuwa da kuma abin da ke bayanta. Ya zo a tarihinsa cewa idan ya tuna mutuwa yakan yi kuka, in ya tuna kabari yakan yi kuka, in ya tuna ranar tashin }iyama yakan yi kuka, in ya tuna tsallakewa kan sira]i yakan yi kuka, in ya tuna wuta yakan yi kuka. Mu duba Imam Ma’asum a IITI{ADINMU, yana kuka in ya tuna wa]annan matakai da ke gabanmu, to ina ga mu. Saboda haka wannan darasi ne babba gare mu wanda yake da muhimmanci mu ]abbaka shi wato ya zamanto mu ma muna kuka idan muka tuna wa]annan matakai da ke gabanmu, in ko har ba mu iya yin kuka idan mun tuna wa]annan matakai, to mu yi kuka dangane da rashin hakan. Domin kamar yadda ya zo a Hadisi bushewar ido dalilinsa shi ne bushewar zuciya, bushewar zuciya dalilinsa shi ne zunubi.
Insha Allah a wata munasabar za a ]ora a kai.

No comments:

Post a Comment