Sunday 3 February 2013

Bayani kan Ruhin mutum.


Darussa guda uku da suka gabata na Akhla}, dukkansu suna matsayin shimfi]a da kuma gabatarwa, a wannan darasi na Akhla}. A wannan darasi ne za a shiga ainihin Akhla} ]in. Da farko dai mene ne Akhla}, a fannin Ilimi na Irfan? Ma’anar Akhla},


 shi ne, “Sura ba]iniyya na mutum.” Wato siffa ta ba]ini (~oye) ta mutum. Domin shi mutum yana da ~angarori guda biyu a halittarsa. Akwai ~angaren ruhinsa, akwai ~angaren jikinsa. To ~angaren ruhinsa shi ne sura ko siffa ba]iniyya ]insa. |angaren jikinsa kuma shi ne sura ko siffa zahiriyya ]insa.
To shi fannin Akha}, yana bayani ne ko mu’amala da ~angaren ruhin mutum, wato ba]ininsa na halitta, kamar yadda fannin Likitanci yake bayani ko mu’amala da ~angaren jikin mutum, wato zahirinsa na halitta. Kuma ita siffa ko sura ta ba]inin mutum, za ta iya kasancewa ]ayan biyu, ko dai kyakkyawa, ko kuma mummuna. Shi ya sa in muka duba za mu ga fannin Akhla} yana da ~angarori guda biyu. |angaren kyawawan Akhla} da kuma ~angaren munanan Akhla}.
To, tambaya a nan a cikin wa]annan ~angarori guda biyu wanne ake farawa? A cikin Istilahohin ilimin Irfan akwai abin da suke cewa “Attakhalliy }abla Tahalliy.” Wato ma’anarsa tsarkakuwa ko wofintuwa daga munanan ]abi’o’i gabanin siffantuwa ko kamantuwa da kyakkyawan siffofi. Wannan kuma ba kamar yadda wasu daga cikin Malaman Falsafa wa]anda ba Musulmi ba, suka tafi a kan cewa wai ]abi’o’in mutum ba su canzuwa, saboda dalilai biyu. 1. Wai kamar yadda mutum ba zai iya canza halittarsa ta zahiri ba. Misali in shi mai tsawo ne a halitta ya dawo gajere, ko kuma gajere ya koma mai tsawo. To haka ma na ba]ini ba su canzuwa.
2. Wai kyawawan ]abi’u za su iya samuwa ne kawai, idan an tum~uke ko cire fushi da kuma sha’awa kwata-kwata daga cikin zuciya; wannan kuma abu ne da ba zai yiwu ba. Shi ne aka ba su amsa da cewa.
Da a ce ]abi’o’i ba za su canzu ba, to da babu hikimar aiko da Annabawa da kuma saukar da littafai, tunda manufarsu ita ce su canza mutum. Saboda haka tun da Allah (T) ya aiko da Annabawa da kuma littafai, wannan ya nuna mutum zai iya canzawa. Amsa ta biyu da aka ba su ita ce. Wa ya ce masu an kallafa wa mutum ya tum~uke ko cire fushinsa da kuma sha’awarsa baki ]aya? Abin da aka kallafa masa shi ne ya daidaita su, su dace da Shari’a da kuma hankali.
Natija dai a nan ita ce ]abi’o’in mutum za su iya canzuwa idan ya yi sa’ayi a kai daga munanan ]abi’u zuwa kyawawan ]abi’u. Kuma a nan mutum shi yake da za~i na kyautata ba]inin halittarsa (wato ruhinsa), ko kuma ya munana shi, wato akasin zahirin halittarsa (wato jikinsa), mutum bai da za~i na canza shi. Misali yana da }afa biyu, ya canza ya koma }afa hu]u, ko kuma hannunsa guda biyu, ya canza ya koma hannu uku da dai sauransu.
Kuma kamar yadda jikin mutum ke kamuwa da cututtuka, to haka nan ma ruhin mutum na kamuwa da cututtuka. Ko kuma kamar yadda jikin ke samun datti da kuma }azanta, to haka nan ruhin mutum na iya samun datti da }azanta. Kuma kamar yadda jiki yake da magunguna na cututtukan jikinsa, ko kuma abubuwa na wanke dattinsa, kamar sabulu misali, to haka nan ma ruhi ma yana da magunguna na cututtukansa da kuma abubuwan da ake wanke shi in ya yi datti, saboda haka mutum na iya zama mutum a gangan jiki, amma a ruhin ya zamanto ba mutum ba. Wato sakamakon cututtuka da kuma }azanta na ruhinsa. Sai su mai da shi halitta daban. Misali a ruhance ya zamo dabba ko Shai]an.
Ta nan mutum zai fahimci maganar Imam Khumaini({S) da yake cewa zama Insan (wato mutum a ruhi) yana da wahala. Har ma yake cewa ya fi sau}i mutum ya zama Malami da ya zama Insan. Saboda Mujahadar da mutum yake bu}ata, ta ya zama Insan a ruhi, ta fi yawa kan mujahadar da yake bu}ata na ya zama Malami. Kuma ha}i}anin halittar mutum na ruhi mafi yawan mutane gobe }iyama ne zai bayyana. Wato cewa a ruhance shi mutum ne ko dabba ko kuma Shai]an. Saboda haka in mutum shi dabba ne, ko Shai]an a ruhance, haka za a ta da shi gobe }iyama da siffar dabbar ko kuma Shai]an. Kuma wa]anda suka san shi suna ganin sa za su gane shi. Misali a ce a ruhance shi a nan gidan duniya shi akuya ne, ko alade, ko biri, to gobe }iyama za a ta da shi da siffar akuya ]in, ko aladen ko biri ]in, kuma ana ganin sa wanda ya san shi a gidan duniya zai gane shi.
Ta yiwu abin ya ba mutum mamaki. To, ai ko a gidan duniya masu zanen katun za su iya zana mutum da siffar kowane irin dabba. Amma a zanen fuskar ka iya gane ko wane ne kuma ko ba gobe }iyama ba, a nan gidan duniya akan samu wasu bayin Allah (T) jefi-jefi da Allah (T) ya azurta su da kashafi na ganin ruhin mutane. Wato kamar yadda sauran mutane suke ganin gangar jikin mutum, to su ma haka suke ganin ruhin mutum a wacce irin halitta yake, dabba ne shi, ko Shai]an, ko mutum a ruhinsa. Ballantana kuma A’imma na Ahlul-Baiti (AS) da suke ganin komai a ha}i}aninsa.
Misali akwai wani aikin Hajji da Imam Sadi} (AS) ya je. To a aikin Hajjin sai yake ce wa wani daga cikin mabiyansa suna tare, “Me ka gani?” Sai ya ce; “Ga mutane nan da yawa”. Sai Imam Sadik (AS) ya ce duba da kyau, ya sake dubawa ya ce mutane ne. Sai Imam Sadi} (AS) ya yi masa wata addu’a, albarkacin wannan addu’ar, sai mutumin nan take ya samu kashafi na ganin ha}i}anin mutane, wato ruhinsu. Sai ya ga da yawa wasu dabbobi ne ashe ba mutane ba a ruhance. Sai abin ya ba shi mamaki. A ta}aice dai ha}i}anin ruhin mutane mafi yawa sai gobe }iyama zai bayyana, kuma shi ruhi shi ne ainihin mutum, ba gangan jikinsa ba.
Shi ya sa da za a tambaya a ce meye mutuwa? Mutuwa ita ce rabuwar ruhi da gangar jiki. Kuma shi ruhi yana da mafara amma bai da iyaka. Wato akwai lokacin da babu shi, Allah (T) ya samar da shi, amma bai da }arewa akasin jikin mutum, shi yana da iyaka. Misali jikin da mutum ya rayu da shi a wannan gida na duniya, ba da shi za a ta da shi gobe }iyama ba, wani jikin za a yi masa. Haka nan in za a kai shi Aljanna ko wuta wani jikin za a yi masa. Amma duk a wa]annan matakai na canje-canje na jikkuna, shi ruhin na nan, sai dai a saka shi cikin jikin da aka canza. Saboda haka shi fannin ilimin Akhla}, abin da ya }unsa ko maudu’insa shi ne kula da ruhin ]an Adam, wajen kyatatuwarsa ko munanuwarsa. Domin shi ]abi’ar ruhi kyau ko muni. Saboda haka daidai kyautatuwar ruhin mutum a wannan gida na duniya daidai kyan halittarsa gobe }iyama. Haka ma akasin haka. Wato daidai munanar ruhin mutum a wannan gida na duniya daidai munin halittarsa gobe }iyama. Saboda haka manufa ko gayar fannin ilimin Akhla} shi ne ya kai mutum ga kamalar ruhinsa, wato na siffata da kyawawan ]abi’o’i da kuma tsarkaka daga munanan ]abi’o’i.
Kuma kamala kamar yadda aka sani ba ta da iyaka. Saboda haka mutum zai ta fama da kansa a wannan ~angare na Akhla}, har ya zuwa saukar ajalinsa. Wato ba ranar gamawa. Kuma shi al’amarin Akhla} wajibi ne Ainiy ba Kifa’iy ba. Wato dole kai za ka yi, wani ba zai ]auke maka ba. Kuma ba a sai da Akhla} a kasuwa ballantana mutum ya je ya sayo. Dole dai mutum shi a }ashin kansa zai yi mujahada wajen ganin ya siffantu da kyawawan ]abi’u ya kuma tsarkaka daga munanan ]abi’u.
Kulasar abubuwan da suka gabata su ne, an yi bayani dangane da mene ne Akhlak? Mene ne maudu’insa? Mene ne manufarsa? Wato gaya ]insa. Bayan haka yanzu za a shiga ~angaren farko na Akhla}. Domin a baya an ce yana da ~angarori guda biyu, kuma an fa]i ~angaren da ake farawa da shi. Saboda haka a nan insha Allah da wannan ~angaren za a fara. Wannan ~angaren a dun}ule a Is]ilahin fannin Ilimin Akhla} ana ce masa Tazkiyatu Nafs. Kodayake Tazkiyatu Nafs yana da ma’anoni guda biyu, akwai Tazkiyatu Nafs Mahmuda (abin yabo), akwai kuma Tazkiyatu Nafs Mazmuma (abin suka). Tazkiyatu Nafs Mazmuma, misali yabon kai ko kuma ko]a kai, wato irin wanda Allah (T) ya ce, “fala tuzakku amfusakum.” To, ba irin wannan ake nufi ba, wanda ake nufi shi ne Tazkiyatu Nafs Mahmuda, wato na tsarkakan rai daga munanan ]abi’u, wato irin wa]anda Allah (T) ya ce “}ad aflaha-man-tazakkaha.”
Da farko bayani dangane da muhimmancin Tazkiyatu Nafs yana da gayar muhimmanci, ta fuskoki daban-daban saboda ma muhimmancinsa akwai Malaman da suka rubuta littafai hususun a kai. Misali akwai littafi mai suna Tazkiyatu-Nafs, na Ayyatullah Sayyid Kazim Alhairiy. Yana ]aya daga cikin manyan Almajiran Ayyatullahi Sayyid Shahid Muhammad Ba}ir Sadr. Yana zaune a birnin {um ne. A shekarun baya kimanin shekara 17 akwai majalisi da yakan gabatar a Husainiyya ]insa. A Majalis ]in yakan karantar da Tazkiyatu Nafs, ban san ko har yanzu yana gabatar da wannan majalis ]in ba.
Haka nan idan mutum ya duba littafin Imam Khumaini na Jihadul-Akbar. Zai ga yadda ya }arfafa ko ya yawaita bayani dangane da Tazkiyatu Nafs. Shi asali wannan littafi na Jihadul-Akbar, Muhadarori ne, wa]anda Imam Khumain ({S) ya gabatar ga ]alibai a lokacin yana gudun hijira a birnin Najaf. Su ne aka tattara wa]annan muhadarori aka mai da su littafi. Ga wasu sassa na littafin da suke da ala}a da Tazkiyatu Nafs.  ya hau kan ]alibai, su yi iyakar iyawarsu wajen ganin cewa, sun sami kyawawan ]abi’u kuma sun tsarkake kawukansu.
“Wajibi ne ku gina kawukanku, ta yadda za ku iya shiryatar da mutane idan kun koma garuruwanku. Ana fata ga kowannenku a lokacin da ya gama makaranta, ya zamanto ya tsarkake kansa kuma ya gina kansa, ta yadda zai iya tarbiyyantar da mutane daidai da koyarwar Musulunci. Amma idan ba ku gyara kawukanku ba, Allah ya kiyaye lokacin da kuke karatu a makaranta kuma ba ku samu kyawawan ]abi’u ba. To, ko Allah (T) ya tsare. Za ku ~atar da mutane ne. Kuma za ku gabatar masu da mummunar sura ta Musulunci da kuma Malaman addini.”
A wani wajen kuma Imam Khumain ({S) yana ce wa; “Lallai ne Mas’uliyya mai nauyi kuma mai girma ta hau kanku. In ba ku tsaya da wannan mas’uliyyar ba kuna cikin makaranta, idan ya kasance ba ku damu da tsarkake kawukanku ba, abin da ya dame ku kawai ku san wasu mas’aloli na Fi}hu da kuma Usulul Fi}h, to lallai ko a nan gaba za ku kasance tushen cutar da al’umma, ta yiwu ku sabbaba ~acewarta. Allah ya tsare.”
A wani wajen kuma yana cewa; “Abubuwan da ya hau kan Malamai da kuma ]alibai na Addini, mai nauyi ne }warai, mas’uliyya ]in su ta fi mas’uliyyar sauran mutane.”
A wani wajen kuma Imam Khumaini yana cewa “na’am lallai mutum idan bai tsarkake kansa ba zahiri da kuma ~adini, karatunsa duk tsawaitar da ya yi, zai cutar da shi. Domin shi ilimi idan ya kasance a }asa wadda ba tsarkakkiya ba, to zai fitar da tsiro mummuna ne.”
A wani wajen kuma ya ce, “haka ne lallai ilimi haske ne, amma a zukata tsarkakku. Amma zukata wa]anda ba tsarkakku ba al’amarin ba haka yake ba. Lallai ilimin da mutum yake neman sa, saboda samun matsayi ko fice, irin wannan ilimi ba zai da]a masa komai ba, face nisanta daga Allah (T). Ko ilimin Tauhidi, idan ya zamo ba saboda Allah (T) da kuma neman yardarsa aka yi ba, to zai iya zama hijabi mai duhu. Hujub, ko hijabi - yana daga cikin Is]ilahohi na ilimin Irfan. Abin da ake nufi da shi, duk abin da zai shamakance mutum daga tunanin Allah (T). Kuma ya kasu kashi biyu, akwai Hijabai na duhu, akwai kuma hijabai na haske. Imam Khumain ({S) ya ci gaba da cewa, ko da a ce mutum ya haddace Al}ur’ani, amma manufarsa a haka ba Allah (T), to wannan hadda tasa ba za ta }ara masa komai ba face nisanta daga Allah (T).
 Idan ]ayanku ya yi karatu, ya sha wahala, ta yiwu ya zama Malam, amma yana da muhimmanci ku san akwai bambanci babba tsakanin Malam da kuma Muhazzab (watau wanda ya tsarkake kansa). Malaminmu, Allah ya ji}an sa yana cewa, yana da sau}i ka zama Malam, amma yana da wahala ka zama Insan”.
A wani wajen kuma yana cewa “kashedin ku, ku yi tsammani cewa, domin kun shagaltu da wa]annan karatuttuka na fannonin ilimin Addini, musamman ma ilimin Fi}ihu cewa yin haka ya wadatar. A’a idan babu ikhlasi a cikin wa]annan karatuttuka, to wa]annan ilimuka ba za su yi amfani ba. Idan ya kasance neman iliminku ba saboda Allah ba ne, Allah ya kiyaye, kuna nema ne saboda son zuciya ko neman matsayi a cikin jama’a, to ku sani lallai ba abin da za ku samu face zunubi da kuma musiba. Wa]annan is]ilahohi da kuke koya, idan ba ku ha]a su, watau gwama su da ta}awa ba, to duk lokacin da suka }aru za su cutar da al’ummar Musulmi, a duniya da lahira. Ilimin Tauhidi idan ba a gwama shi da tsarkake Nafs ba, zai kasance musiba ga ma’abocinsa. Wa]annan is]ilahohi busassu idan aka sa su a }wa}walwa, ba tare da ta}awa ko tsarkake Nafs ba. Ba abin da za su }ara face girman kai da kuma ru]u. Mummunan Malami, wanda ru]i da kuma girman kai ya mamaye shi, ba zai ta~a iya gyara kansa ba ko kuma ya gyara al’umma ba, ba sakamakon da za a samu face cutar da Musulunci da kuma Musulmai.”
A wani wajen a littafin Imam Khumaini ({S) yake cewa, “ba fa ina cewa ne kada ku yi karatu, ko kada ku sha wahala a fagen ilimi ba. Abin da nake nufi shi ne in fa]akar da ku a kan cewa lallai gyara kai yana bu}atar }o}ari mai dogewa; saboda haka ku yi aiki a wa]annan fagagen guda biyu, kuma ku sha wahala a kai (Watau fagen ilimi da kuma fagen gina Nafs). Kada ku karkatar da }o}arin a fage guda ]aya, watau fagen ilimi. Duk lokacin da kuka yi taku ]aya na neman ilimi, to ku gwama shi da taku ]aya na tsarkake nafs da kuma gyaran ta.”
A wani wajen kuma ya ce, “lokacin da kuka shiga makaranta, ya kamata ya kasance gabanin komai, ku himmantu da tsarkake kawukanku da kuma gina su. Wannan ya zamanto kun ba shi muhimammanci a tsawon zaman ku a makaranta. Har ya zamanto mutane sun fa’idantu da kyawawan ]abi’u da kuma siffanta da su. A lokacin da kuka shiga fagen aiki a cikin jama’a ku yi }o}ari gwargwadon ikonku. Ku gyara kawukanku gabanin ku shiga cikin al’umma. Idan ba ku damu da tsarkaka ba a yanzu, alhali kuna da isasshen lokaci, yaya za ku iya yin haka a nan gaba lokacin da mas’uliyyoyi masu yawa suka hau kanku? Ku gina kawukanku, gabanin dama ta ku~uce maku. Ku siffanta da kyawawan ]abi’u, kuma ku tsarkaka daga munanan ]abi’u. Ikhlasi ya zama jagoranku a karatu domin ku sami kusanci ga Allah (T), domin idan niyya a cikin ayyuka ba saboda Allah ba ce, to, wannan zai nisanta mutum daga }ofofi na Rahmar Allah (T).”
A wani wajen kuma a littafin Imam Khumaini ({S) yana cewa, “lallai wasu daga cikinmu abin da ya dame su, su san wasu ababe na ilimi. Sai su koma garuruwansu, domin su sami girma da kuma matsayi, saboda haka kashedin ku, ya kasance manufar ]ayanku a karatu shi ne domin ya samu matsayi ko girma. Saboda haka na hore ku da tsarkake kawukanku. Ta yadda in ]ayanku ya zama Shugaban mutane zai shagaltu da tsarkake rayukansu da kuma aiki domin gina su. Ya dai kasance manufarku hidima ga Musulunci da kuma Musulmai. Idan kuka shagaltu saboda Allah (T), kuka sha wahala a tafarkinsa, to Allah (T) shi ne mai juya zukata, sai ya soyantar da ku ga mutane, saboda haka ku yi jihadi a tafarkin Allah (T). Allah (T) ba zai bar ku ba tare da yi maku sakamako ba. In sakamakon bai kasance a wannan gida na duniya ba, to za ku samu sakamako a lahira. In Allah (T) bai ba ku sakamako ba a gidan duniya, to wannan ai shi ya fi, domin duniya ba ta da wani }ima.”
A wani waje kuma a littafin Imam Khumaini ({S) yana cewa, “yana daga cikin sa’adar mutum kada a jarrabe shi da ciwon da bai jin ra]a]insa domin cututtukan da mutum yake jin ra]a]insu za su tunku]a mutum zuwa ga neman magani, ko ganin likita ko Asibiti. Amma cututtukan da mutum bai jin ra]a]insu, mutum ma bai jin su. To, irin wa]annan cututtukan suna da ha]ari babba. To, cututtuka na zuciya shigen haka suke. Domin da a ce ana jin ra]a]insu kai tsaye, da sun tunku]a mutum zuwa ga neman maganin su. Girman kai da Ananiyya (Ninanci) da dai dukkan sa~o suna ~ata zuciya kuma suna ~ata ruhi, ba tare da jin ra]a]insu a jiki ba. A’a wuce nan ma wa]annan cututtuka ba wai kawai ba a jin ra]a]in su ba ne, a’a ana ma jin da]insu.”
Imam Khumaini ({S) ya ba da misali da Majlis na giba ko annamimanci. Watau a nan kamar yadda aka fa]i a baya cewa kamar yadda gangar jikin mutum ke kamuwa da ciwo, to haka nan ma ruhin mutum na iya kamuwa da ciwo. To, abin da Imam Khumaini ({S) ke cewa a nan. Ciwo na gangar jiki mutum kan ji zoginsa ko ra]a]insa, wanda wannan zai ingiza shi ya nemi magani, amma shi ciwon ruhi mutum bai jin wannan zogin ko ra]a]i, ballantana ya tun}u]a shi ya nemi magani. Misali ciwon zuciya na girman kai, ko riya ko yin giba. Ga su dai ciwo ne ma’anawi amma mutum bai jin zogin su. Shi ne Imam Khumaini ({S) yake cewa yana daga cikin sa’a da ]in mutum kada a jarrabe shi da irin wa]annan cuttuka. Wa]annan zantuka na Imam Khumaini ({S) sun nuna mana muhimmancin Tazkiyatu Nafs. Insha Allah a darasi na gaba za a kawo illolin rashin tazkiyatu nafs da kuma natijoji na Tazkiyatu Nafs.


No comments:

Post a Comment