Kasantuwar
wannam wata da muke ciki, wato na Sha’aban a cikinsa ne aka haifi Hujjar Allah
a doron }asa, kuma Shugababn wannan zamani, wato Imam Mahdi (AS), kamar yadda
aka sani shi ne Imam na 12 a jerin }idaya na Imamai 12, wato shi ne Khalifan
Manzon Allah (S) na }arshe.
An
haifi Imam Mahdi (AS) a daren Juma’a, kuma daren 15 ga watan Sha’aban, a
shekara ta 255 bayan hijira, a wani gari da ake ce wa Samarra , wanda a yau yana cikin }asar Ira}i.
Saboda haka shekarun Imam Mahdi (AS) yanzu a duniya 1178. Imam Mahdi (AS). In
mutum ya lissafa daga haihuwarsa zuwa yanzu, zai ga haka.
Ta
yiwu wani ya yi mamaki, ko ya tambaya zai yiwu mutum ya yi tsawon rai haka?
Amsa, zai yiwu. Domin tarihi ya tabbatar mana akwai daga cikin mutane wa]anda Allah
(T) ya rayar da su shekaru masu yawa, wasun su Annabawa ne, wasu kuma ba
Annabawa ba ne. In mutum ya duba cikin littafi mai suna A’IMMATUNA juzu’i na
biyu akwai babi da ya yi kan
wannan al’amari da ya shafi tsawon rai na Imam Mahdi (AS), ya yi bayani mai
tsawo a kai. Daga }arshe kuma ya ba da misali na wasu da Allah (T) ya yi wa
tsawon rai.
Ga
misalan wasu da ya kawo; Annabi Nuhu (AS). Ya kawo wani Hadisi wanda aka samu
daga Imam Sadi} (AS) ya ce, Annabi Nuhu ya rayu shekaru 2500, daga ciki ya yi
shekaru 850 gabanin aiko masa sa}o, ya yi shekaru 950 wajen da’awa. (Wannan ma
ya zo a nasssin Al}ur’ani). Sannan ya yi shekaru 700 bayan halakar da
mutanensa”.
Wani
misali kuma da ya kawo shi ne Annabi Adam (AS). Ya kawo Hadisi daga Manzon Allah
(S) ya ce; “Baban mutane, Adam (AS), wanda ya rayu shekaru 930”.
Ya
kawo kuma misalin Annabi Idris (AS), wanda ya rayu shekaru 965. Annabi Hudu
(AS) ya rayu shekaru 962. Ga kuma misalin Khidir (AS), wanda Malaman Shi’a da
kuma Sunna mafi yawansu, sun tabbatar da yana raye, mu duba ko tun zamanin
Annabi Musa (AS) yake.
A
ta}aice dai abin da ake so a fitar a nan shi ne, tsawon rai na Imam Mahdi (AS)
ba wani ba}on abu ba ne a tarihin ]an’adam. Kuma ko dama ba hujjar wasu da suka
yi tsawon rayuwa kamar tasa, wato a ce
gabaninsa ba a samu wani ]an’adam da ya yi tsawon rai haka ba, to hujjar cewa
Allah (T) mai iko ne a kan
komai ya wadatar.
Shi
ya sa in mutum ya duba a wa]annan makarantu guda biyu, wato Shi'a da Sunna, zai
ga a mafi yawan al’amuran da suka shafi Imam Mahdi (AS) sun yi ittifa}i a kai.
Sa~anin da aka samu ka]an ne. Misali an haife shi, ko ba a haife shi ba. Ko shi
ma wannan, in mutum ya yi bincike zai ga cewa mafi yawan Malaman Ahlus Sunna
sun tafi a kan an haiife shi, kuma yana raye. In mutum ya bibiyi littafan Shehu
Usman [an Fodiyo, wa]anda ya rubuta dangane da Imam Mahdi (AS) zai ga ya
tabbatar da haka. Kuma a lokacinsa ya gina jama’a a kan haka. Wato a kan yana raye. Haka nan
wani Malamin Ahlus Sunnah mai suna Shaikh Abu Abdullahi Muhammad Ash-Shaffi’iy
ya fa]i a cikin littafinsa mai suna Al-bayan Fi Akhbaari Sahibuz-zaman. “Ha}i}a
Al-Mahdi ]an Hasan Askari ne, kuma yana da rai, kuma yana nan wanzajje tun
fakuwarsa har zuwa yanzu, kuma babu abin da zai hana wanzuwarsa, da dalilin
wanzuwar Isah da Khidir da Ilyas (AS)”. Wannan ke nan a ta}aice dangane da
kasantuwar Imam Mahdi (AS) a raye.
Sunansa
MUHAMMAD, amma ya zo a kan cewa ana son sakaye sunansa a zamanin gaiba
(fakuwarsa), wato wannan zamanin da muke ciki, har sai lokacin da ya bayyana.
Sai dai a yi amfani da la}ubbansa wajen ambatonsa.
Sunan
Mahaifinsa kamar yadda aka sani, Imam Hasan Asskari (AS). Sunan Mahaifiyarsa
Narjis, kuma nasabarta tana tu}ewa ne da Sham’un, wato Wasiyyin Annabi Isah
(AS). Kinayar Imam Mahdi (AS) ita ce Abul {asim, wato dai kamar yadda ya zo a
wani Hadisi daga Manzon Allah (S) ya ce; “{arshen zamani wani mutum zai fito daga zuriyata, sunansa
kamar sunana ne, Kinayarsa kamar kinayata ce, zai cika }asa da adalci bayan ta
cika da zalunci”.
Haka
nan kuma Imam Mahdi (AS) yana da la}ubba masu yawa, amma wa]anda suka fi fice
su ne Al-mahdi, Al-{a’im, Al-Muntazar, Al-hujja da kuma Sahibuz-zaman. Yana da shekara biyar a duniya Mahaifinsa ya rasu, wato
ke nan yana da shekara biyar a duniya Imamanci ya koma gare shi. Bayan wafatin
Mahaifinsa, ya shiga gaiba ta farko wadda ake ce wa Sugraah, wato }aramar
gaiba. Domin gaiba ]in Imam Mahdi (AS) ta kasu }ashi biyu; akwai ta farko,
akwai kuma ta biyu, wadda ake ce wa kubra, wato babbar gaiba.
Gaiba
]insa ta farko ta ]auki tsawon shekaru 69, a cikin wa]annan shekaru ya kasance
yana da ala}a da Shi’arsa ta hanyar Jakadu guda hu]u. Ta hanyar wa]annan Jakadu
guda hu]u umurninsa ko haninsa yake fitowa zuwa ga Shi’arsa. Haka nan su kuma Shi’arsa ta hanyar su ne matsalolinsu da kuma tambayoyinsu
ke isa gare shi. Domin su Jakadun suna da dangantaka da shi kai tsaye, sai dai
a nan yana da muhimmanci a fahimce cewa su wa]annan Jakadu guda hu]u ba a
lokaci guda suka kasance ba. A’a sun kasance ne ]aya bayan ]aya. Na farko shi
ne Usman Bn Sa’id. Na biyu shi ne Muhammad [an Usman. Ya rasu a shekara ta 304
bayan hijira. Na uku shi ne Husain [an Ruh, ya rasu a shekara ta 326 bayan
hijira. Na hu]u shi ne Ali [an Muhammadd As-Samariy, ya rasu a shekara ta 329.
Bayan rasuwar wannan Jakadan nasa na hu]u, shi ne ya shiga gaiba kubra, a
lokacin yana da shekara 74 a duniya. Kuma tun daga wannan lokaci har ya zuwa
yau ]inmu, yana cikin wannan gaiba kubra ne, kuma zai ci gaba da kasancewa a
haka har ya zuwa lokacin da Allah (T) zai ba shi izni da ya bayyana. Allah (T)
ka gaggauta bayyanarsa.
Sabodaa haka rayuwar Imam
Mahdi (AS) ta kasu zuwa marhaloli guda hu]u. Marhala ta farko, rayuwarsa tare
da Mahaifinsa, wanda shekaru biyar ne. Marhala ta biyu gaiba ]insa ta farko,
wadda shekaru 69 ce. Marhala ta uku gaiba ]insa ta biyu, wadda ita ake ciki har
yanzu. Marhala ta hu]u lokacin da ya bayyana domin tabbatar da addini a bayan
}asa baki ]aya. Wadda zai kau da zalunci da azzalumai da kuma shimfi]a adalci
da gaskiya a duniya baki ]aya.
Saboda haka a wannan zamani
na gaiba ta biyu, Imam Mahdi (AS) yana da Niyaba (wakilci) wadda aka ce wa
Niyaba amma, wato ta Fu}ha (Mujtahidai),
waccen kuma ta gaiba ta farko ta Jakadu guda hu]u da aka ambata ana ce mata
Niyaba Khassa. Duk da wannan wani fage ne na daban, bahasinsa na muhallinsa.
Ta yiwu a nan mutum ya yi
tambayar me ya sa Imam Mahdi (AS) ya kasance a gaiba? To a nan Malamai da dama,
musamman Malaman Shi'a sun yi rubuce-rubuce dangane da wannan maudu’i, wanda a
nan ba zai yiwu a iya kawo dogon bayani a kai ba. Amma ga mai bu}ata yana iya
samun littattafan da ako rubuta a kan haka. Misali littafin GAIBA na Shaikh
[usiy, ko kuma wasu littattafai na tarihin A’imma (AS). Misali, wani littafi da
aka ambata a sama mai suna A’immatuna ya
kawo bayani mai tsawo a kan wannan maudu’i, kuma da a ce mutum zai
bincika, ko ya karanci littattafan tarihi ya ga abubuwa da suka faru, gab da
rasuwar Mahaifin Imam Mahdi (AS) da kuma abinda suka biyo bayan rasuwarsa, zai
fahimci wasu daga cikin dalilan gaiba ]insa. Domin ya zo a kan cewa rashin
lafiya ta }arshe da Imam Hasan Askariy (AS) ya yi, wadda a cikinta Allah (T) ya
yi masa rasuwa, masu tafi da iko a lokacin sun yi ta bincike su gano inda ]ansa
Imam Mahdi (AS) yake da nufin su kashe shi, amma ba su samu nasarar haka ba.
Saboda haka bayan rasuwar
Imam Askari (AS) sai suka kamo matansa da kuyangunsa suka tsare da tsammanin ko
akwai mai ciki a cikinsu! Sun yi haka ne, wato yun}urin kisa da kuma tsarewa,
saboda Hadisai da suke da masaniya da su, wa]anda suka zo da cewa Imam na 12 shi
ne wanda zai kau da zalunci da kuma azzalumai a bayan }asa, ya kuma shimfi]a
adalci da kuma gaskiya a kanta, kuma sun tabbatar da Imam Hasan Askari (AS) shi
ne Imami na 11, sun ga shi yanzu yana gab da zai rasu, shi ne suka yi wannan
yun}urin na neman Imam Mahdi (AS) domin su kashe shi. Da ba su samu nasarar
haka ba, shi ne suka tsare wa]annan iyalinsa da tunanin ko ba a haifi Mahdi ba,
bayan rasuwar sa ne za a haife shi. Domin ya zo a kan cewa lokacin da aka haifi
Imam Mahdi (AS), Imam Hasan Askari (AS) ya ~oye maganar haihuwarsa, sai
Shi’arsa na kusa ya shaida wa. Saboda haka su masu tafi da iko suna cikin
]imuwa da kuma duhu kan haka. Wato ba su san cewa Allah (T) ya riga ya hukunta
ikonsa ba na cewa an haifi Imam Mahdi (AS) har ya rayu tare da Mahaifinsa
shekara biyar.
A ta}aice dai haihuwar
Imam Mahdi (AS) ta so ta yi kama da haihuwar Annabi Musa (AS), wato na cewa,
tun gabanin a haife shi, ana neman sa domin a kashe, amma Allah (T) ya yi
ikonsa, aka haife shi ya tashi a gidan wanda yake neman sa domin ya kashe,Allahu
Akbar !
Saboda haka shi Imam Mahdi (AS) tun gabanin a
haife, shi da kuma bayan da aka haife shi, masu tafi da iko na Khalifofin
Abbasawa suna neman sa ne domin su kashe shi. Allah (T) bisa ikon sa ya kare
shi daga mummunan wannan nufi nasu a lokacin,
Don hatta bayan rasuwar
Imam Askari (AS) a cikin kuyangunsa, akwai wata wadda suka ga tana da alamar
ciki, haka suka sa aka tsare ta, har tsawon shekara biyu, daga baya dai suka
sake ta. Ba su san cewa Allah (T) ya riga ya yi ikon sa ba.
Domin
shi Imam Hasan Askari (AS) ]a ]aya kawai yake da shi, shi ne kuma Imam Mahdi
(AS). Bayan haka ta yiwu mutum ya yi tunani ko tambayar cewa, to menene fa’idar
Imam wanda yake fake? Wato cikn gaiba. Akwai fa’idodi masu yawan gaske, amma ga
guda uku daga ciki;
1.
Mujarradin kasatunwarsa a doron }asa, aminci ne, da albarka da kuma rahma ga
halitta kamar yadda ruwayoyi na Hadisai suka nuna.
2.
Shi Imam Mahdi (AS) kamar rana ce wadda girgije ya ~oye ta. Ana amfana da ita
ko da ba a ganin ta, kamar yadda Manzon Allah (S) ya gaya wa Sahabinsa Jabir [an Abdullahi
Al-Ansari lokacin da ya tambaye shi dangane da gaiba ]in Imam Mahdi (AS). Ya
ce; “Ya Manzon Allah (S)! Shin Shi’arsa za su amfana da shi a gaiba ]insa?” Sai
Manzon Allah (S) ya ce masa; “Eh! Ina rantsuwa da wanda ya aiko ni da Annabta,
lallai su za su haskaka da haskensa, za su amfana da wilayarsa gare shi, kamar
amfanar mutane da rana, ko da ko girgije ya lullu~e ta.
3.
Mas’uliyyar Imam Ma’asum (AS) a Madrasah ]in Ahlul Bait (AS) ya kasu kashi
biyu. Akwai mas’uliyya zahiriyya, akwai kuma mas’uliyya ba]iniyya. Mas’uliyya
zahiriyya ita ce tsare shi addini da kuma jaddada addini, wato aikata shi a
aikace da kuma }iyada siyasiyya, wato jagoranci, wanda su a Madrasah ]in Ahlus
Sunna wannan ne kawai suke la’akari da shi wajen shugabanci. mas’uliyyar
ba]iniyya ta Imam Ma’asum (AS), ita ce kamar shahadatul a’amal. Wato ayyuka da
ake kai masa na mutane, wato mabiyansa da ma wa]anda ba mabiyansa ba. Wasu ayyuka su faranta masa rai, wasu kuma su ba}anta masa rai.
Akwai kuma Nuzulul
Barakat da kuma Su’udul A’amal, wato saukar da albarkoki ta hanyarsa da kuma
kai ayyuka ta hanyarsa, da sauran su na mas’uliyya ba]iniyya. Kuma ko ba ma
wa]annan mas’uliyya ]in ba, Imani da kuma i’it}adi da kasantuwarsa, wato cewa
yana raye, ya na sa fata da kuma }warin gwiwa cewa insha Allah zalunci zai kau
daga doron }asa a watan wata rana.
Sai kuma abun da ya shafi
wasu ~angarori na rayuwarsa. Wato kamar ibadarsa, Akhlak ]insa, Zuhudunsa da
dai sauransu. Ta yiwu wani ya yi mamaki ko tunanin cewa tun da Imam Mahdi (AS)
mafi yawan rayuwarsa a cikin gaiba ne, ya aka yi aka san irin wa]annan
~angarori na rayuwarsa? Amsa a nan ita ce; idan mutum ya bibiyi tarihin Imamai
]aya bayan ]aya, wato tun daga Imam Ali (AS), har ya zuwa Imam Mahdi (AS), zai
ga babu wani Imam daga cikin Imamai da bayanin sa ya zo sanka-sanka a cikin
Hadisai da aka samo daga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS), kamar Imam
Mahid (AS).
Bayaninsa ya zo
sanka-sanka ta kuma kowace fuska, wato ta duk bayanai. Siffofinsa sun zo
‘khal}iyyan’ da kuma ‘khulu}iyyan’, wato na halitta da kuma ]abi’a. Saboda haka
hatta wa]annan ~angarori na rayuwarsa, kamar Ibadarsa, Akhlak ]insa da
Zuhudunsa, duk bayaninsu ya zo a Hadisai. Allah (T) shi ne mafi sani. Amma }ila
hikimar haka ita ce; idan ya bayyana, al’amarinsa zai kasance tamkar hasken
rana. Domin duk siffofinsa na halitta da ]abi’o’i ga su a Hadisai, kuma wannan
zamani ko lokaci da muke ciki ga dukkan alamomi lokaci ne na gab da bayyanarsa.
Domin kamar yadda ya zo a
Hadisai, gab da bayyanarsa, fitintinu da jarabawowi za su yawaita fiye da
kowane lokaci. Domin gab da bayyanarsa, zalunci zai kai mataki na }arshe, kuma
babi na }arshe, kuma idan ya bayyana, wata sabuwar jarabawa ce babba za ta fuskanci
duniya baki ]aya, Musulmi da wanda ba Musulmi ba. Domin idan ya bayyana, duniya
baki ]ayanta da ikon Allah sai ya du}ar da ita }ar}ashin Musulunci. Ba a na
nufin kowa zai zama Musulmi ba, a’a, zai zamo dai kowace nahiya a duniya za ta
kasance tana }ar}ashin iko na Musulunci. Sannan kuma zai dawo da fahimta da
kuma koyarwa ta Musulunci tsantsa kamar yadda yake a lokacin Manzon Allah (S).
Saboda haka duk wani abu
wanda yake akwai shi a cikin addinin Musulunci, amma aka fitar da shi, to zai
dawo da shi. Haka
nan kuma duk wani abu da aka sa a cikin addinin Musulunci wanda babu shi, to zai
fitar da shi. Wato a ta}aice dai kamar yadda aka ce zai dawo da addini tsantsa
kamar yadda yake a lokacin Manzon Allah (S). To nan
ne mutum zai fahimci cewa, lallai jarabawa ce babba za ta kasance ga mutane a
lokacin bayyanarsa. Kuma a lokacin babu wani }arfi da ya isa ya ja da shi, face
ya samu galaba a kansa da ikon Allah.
Bayan ya tabbatar da
addini a bayan }asa baki ]aya. To, lokacin duniya za ta numfasa, ta samu wani
irin aminci da yalwa ta arzi}i, da lafiya, da dai sauran alherai da kuma
albarkoki, wanda ba ta ta~a samu ba. A lokacin adalci zai shimfi]u ya mamaye
duniya, kamar yadda zalunci ya mamaye ta gabanin haka. Saboda haka yana da
gayar muhimmanci kowa ya yi wa kansa muhasaba, wato hisabi, ya tambayi kansa. Yaya ala}arsa take da Imam
Mahdi (AS)? Wato, ya Imam Mahdi (AS) yake a wajensa? Ya shi kuma yake a wajen
Imam Mahdi (AS)? Me yake yi ga Imam Mahdi (AS)? Da dai sauran tambayoyi
ire-iren wa]annan da zai wa kansa dangane da ala}arsa da Imam Mahdi (AS).
Insha
Allah shekara mai zuwa, in Allah (T) ya kai mu a munasabar wiladarsa, za a ]ora
a kan abin da
ya shafi ~angarorin rayuwarsa wa]anda aka ambata a sama.
Wani
Tambihi ka]an dangane da wannan wata da muke ciki, wato watan Sha’aban shi ne;
wannan wata na Sha’aban, wata ne da ake so mutum ya yi shiri da kuma yin
shimfi]a ga babban ba}o mai zuwa, wato watan Ramadan, kamar yadda bisa ]abi’a
da kuma al’ada, idan mutum zai yi babban ba}o, zai yi shirye-shirye domin zuwan
sa. To haka nan ake so gabanin zuwan watan Ramadan. Ana so mutum ya yi
shirye-shirye na musamman, wato shiri MA’ANAWI, ta hanyar tazkiyya ]in nafs
]inmu, wato tsarkake kawukanmu zahiri da kuma ba]ini da kuma lizimtar ayyuka na
ibadodi daban-daban, kamar yawaita Salloli, karatun Al}ur’ani, Azkar da
Addu’o’i da dai sauransu, ta yadda jikinmu zai saba sosai da tsayuwa da
wa]annan ibadodi kafin shigar watan, wanda wannan zai taimaka mana in mun shiga
watan Ramadan ]in, ba za mu samu wahala ba wajen tsawuwa da ibadodin da ke
ciki. Sa~anin ko a ce mun shiga watan ba wannan mu}addima ]in na tazkiyya ]in
nafs ]inmu, da kuma tsayuwa da ayyuka na ibadodi, wanda wannan zai shamakance
mu daga samun zau}i da halawa na ibadodi a cikin watan.
No comments:
Post a Comment