Al-hamdu-lillah,kasantuwar wannan wata da muke
ciki,wato na zul hijja,a cikin sa ne,kamar yadda aka sani,18 gare shi,shekara
ta goma bayan hijira,wannan munasaba ta ghadir ta kasance.Kuma tun daga wancan
lokaci har ya zuwa yau dinmu wato yau shekara sama da dubu da dari hudu,mabiya
Ahlulbaiti [AS] a duk shekara a kuma sassan duniya dabam dabam suke raya wannan
rana ta ghadir ta fuskoki daban daban.
Misali raya ranar tayin wasu
ibadodi,kamar azumtar ranar,karanta wasu addu’oi da ake son karantawa a
ranar,dadai sauran ayyuka na ibadodi da sukazo a hadisai,da ake son yin su a
ranar,har wala yau mabiya Ahlulbait [AS] suna rayar da wannan rana,i tayin
tarurruka domin tunasar da juna dangane
da wannan rana ta ghadir dadai sauran ababe dake da alaka da ranar,Wanda irin
wadannan ayyuka na raya wannan rana ta ghadir,ba zaka jishi ko ka ganshi ba a
tsakan kanin ‘yan uwanmu musulmi Ahlus Sunnah ba.Duk da cewa shi wannan
al’amari na ghadir,ba abu bane daya shafi mabiya Ahlulbaiti ba kawai.A’a abu ne
da ya shafi kowa da kowa a wannan al’umma ta manzon Allah [S],Domin khutbar da
manzon Allah [S] yayi a ranar ghadir,wadda ta kunshi wadanda zasu kasance
khalifofi a bayansa.abune wanda ya shafi kowane musulmi. Baya ga haka kuma shi wannan
al’amari na ranar ghadir mutum zai iya tabbatar dashi sanka sanka dinsa, a
littafan Ahlus Sunnah, kai hatta wasu ibadodi da akeyi a ranar,sunzo a littafan
Ahlus Sunnah misali anan shine Azumin ranar ghadir,akwai hadisi da yazo a cikin
littafan Ahlus Sunnah akan shi,ga hadisin.An samo daga Abu Huraira yace, Manzon
Allah [S] yace “Duk wanda ya azumci ranar sha takwas ga watan zulhijja,za’a
rubuta masa azumin wata sittin itace ranar ghadir khum”........ wato har ya
zuwa karshen hadisin.Mu duba muga wannan hadisi,gashi dai daga masadir ne na
Ahlus Sunnah, amma da wuya kaji ambaton hadisin tsakan kanin malaman Ahlus
Sunnah, kuma mutum ya kwatanta wannan hadisi da wanda suke yawan kawowa na
Azumin Ashura,wanda wannnan ya isa ya nuna ma mutum cewa lalle wani abu ya auku
a tarihin wannan al’umma, wato an gina mutane akan abunda akeso a ginasu.An
kuma kautar dasu akan abunda akeso a kautar dasu.Wadanda suka yi riko da wannan
al’amari na ghadir,aka dauki matakai akansu dabam dabam na cutarwa da galla
zawa,mutum ya tambayi tarihi zai bashi amsa.Saboda haka wannan kadai ya isa ya
nuna banbanci n mahanga tsakanin shi’a da sunna,dangane da al’amarin ranar
ghadir.Wato a aikace zaka ga wadannan sun san da zamansa, kuma suna raya
shi.Akasin daya bangaren ba zaka ji ambaton haka ba,ballan tana su raya shi,
alhali mutum na mutuwa bayan an sa shi a kabari,daga cikin tambayoyin da za’a
yi masa akwai abinda yake da alaka da wannan al’amari na ghadir,wato bayan an
tambayi mutum waye Ubangijinka? Waye Annabinka?
Sa’annan sai a tambayi mutum waye Imaminka? Kuma wani abin lura anan
shine,wadannan tambayoyi suna nuna lalle al’amarin Imamanci ko Khalifanci yana da
alaka da akida ne,ba kamar yadda malaman Ahlus Sunna suka tafi akai cewa baida
alaka da akida.Wato baya cikin Usuluddin yana cikin Furu’uddin ne.Kuma ko baya
ga wannan mu duba irin su hadisai da suka zo,kan alamarin imamanci,misali
hadisin da ya zo cewa “Wanda ya mutu bai san Imamin zamanin sa ba,to ya mutu
mutuwar jahiliyya”Saboda haka,al-amarin imamanci ko khalifanci babban abune,a wannan addini,shiyasa,a mad-rasa din
Ahlul-bait, yana cikin usulid-din ne.kuma shi imamanci ko khalifanci,shine abu
na karshe da Manzon Allah[S]yayi,a sakon da ya isar tsawon shekaru 23.Domin
daga shi babu wani abun da ya sauka,mai matsayin wajibi,shiyasa bayan da Manzon
Allah ya Nasabta Imam Ali[as]A ranar ghadir,sai ayar Al-yauma akmal-tu
lakum-dinakum,ta sauka.Saboda haka isar da sakon imamanci ko khalifanci,tamkar
khatma na sakon da Manzon Allah[S] yazo da shi,Kuma ayyana Imam Ali[as]A
matsayin khalifa,a bayan Manzon Allah[S]ya kasance a matsayin rasmiyyan ne wato officialy,domin gabanin haka,a wajaje
da dama, a kuma lokuta dabam-dabam,Manzon Allah[s]yayi isha-rori da kuma hannun
ka mai sanda,na khalifa a bayan sa,shiyasa Manzon Allah na cewa zai bayyana
khalifan sa,sai wasu fuskoki suka bata rai,saboda sun san ko waye za a
bayyana.Kuma baya ga haka,A sahabban Manzon Allah baki daya,babu wani sahabi
wanda dajojin sa da fifikon sa,a ka ruwaito su daga Manzon Allah kamar Imam
Ali[S]wannan magana,Ahmad ibn hanbal ya fade ta.Misali ga wasu hadisai na Ahlus
sunna kan haka.Manzon Allah[s]yace “Bayana fitina zata kasance,idan haka ya
faru,to ku lizimci Ali dan Abi Dalib,domin shi mai rarrabewa ne tsakanin
gaskiya da karya”.A wani hadisin kuma,Manzon Allah[s] yace ma Ammar dan Yasir,
“Ya Ammar idan kaga Ali yabi wata hanya,mutane kuma suka bi wata hanyar da Ali
bai bi ba,to kabi hanyar da Ali yabi,kabar hanyar da saura mutane suka bi,domin shi ba zai fitar da kai
daga shiriya ba.”Har wala yau a wani hadisi kuma,Manzon Allah [s]yace “Zai
kasan ce tsakanin mutane,za a samu sabani da rarraba,zai kasance wannan[wato
imam Ali] da sahabban sa,su ke kan gaskiya.”da dai hadisai masu yawa,makamantan
wadannan,da suka zo a litafan Ahlus
sunna,da suke nuni ga matsayi na Imam Ali[as]Saboda haka koda ma ace,kamar
yadda Ahlus-sunna,suka tafi a kai,na cewa,wai
Manzon Allah[s]bai khalifan tar da kowa ba,ya bar al-umma ne ta zaba.To
ashe ire-iren wannan matsayi na Imam Ali[AS]wadanda Manzon Allah,ya fadi game
da shi,basu isa su can-cantar dashi ba,khalifan Manzon Allah?To ballantana kuma
shine Manzon Allah,ya nasabta.Saboda haka Imam Ali[AS] shi ne ka dai ya
cika sharuddan da shia da suna suka tafi
akai,na zama khalifa,in ka tafi akan nassi,ba zabin jama’a ba,to yana da nassi
akai,in katafi akan zabin jama’a ne,to shi jama’a ne suka zabe shi.Sboda haka
anan,wannan rubutu zai gudana ne Insha Allah akan wadannan ababe:
1.Muhimmancin ranar ghadir.
2.Abubuwan da suka auku ranar ghadir.
3.Tawili da kuma kwaskwarima da akayi ma
al’amarin ghadir a littafan Ahlus Sunna.
4.Ayyukan da akeyi a ranar ghadir.
5.Kafa hujja da A’imma na Ahlulbaiti [AS] da
kuma wasu daga cikin sahabbai da tabi’ai sukayi da hadisin ghadir akan wasu
mutane.
6.Illoli da suka auku kuma suke aukuwa a
wannan al’umma ta manzon Allah [S] saboda rashin aiwatar da al’amarin ghadir.
7.Wasu darussa da zamu koya daga al’amarin
ghadir. Yanzu
bayani a takaice dangane da wadannan ababe guda bakwai:
1.MUHIMMANCIN
RANAR GHADIR. Ranar
ghadir rana ce muhimmiya, a tarihin wannan
al-umma,da kuma tarihin al ummun
da suka gabaci wannan al-umma.Domin abubuwa da yawa na tarihin na tarihin
Annabawa sun aukune,a irin wannan rana
ta ghadir.Alal misali yazo akan cewa
Annabi Musa[as] a irin wannan rana ce ya bayyana wasiyyinsa,wato
khalifansa mai suna Yusha’u dan Nun.Haka nan ma Annabi Sulaiman a irin wannan rana ya bayyana wassiyyinsa mai
Sham’un.Haka nan yazo a kan cewa’yan-uwantaka da Manzon Allah[s]ya hada
tsakanin Muhajirin da Ansar,a irin wannan rana ce ta kasance.wato 18 ga watan
zul-hijja.Haka nan samun nasara dawasu daga cikin Annabawa sukayi kan makiyan su, da yawa haka ya auku
ne, a irin wannan rana.A takaice dai abubuwa da yawa sun auku,a tarihin
dan-adam ,a wannan rana.Amma abun mamaki da yawa abubuwan da suka auku,a irin
wannan rana a tarihi sai aka jir-kita-su,a ka nuna wai a ranar Ashura suka
faru.Hatta al-amarin yal-wata ma iyali da yin ado da dai sauran su,da akazo
dasu a ranar ashura.Asalinsu a ranar ghadir suka zo,amma aka canza.Ire-iren
wannan abubuwa na canza tarihi da yawan su sun aukune,a lokacin daular
bani-umayya.Saboda haka mutum zai iya cewa ba a bisa hatsari bane,Manzon
Allah[s]ya bayyana ma wannan al-umma tasa wadanda zasu kasance khalifofi a
bayansa.,wato a wannan rana ta 18 ga zul-hijja,in mutum ya dubi abubuwan da
suka auku a tarihi a ranar,wato na Annabawan da suka gabata.Haka nan kuma daga
cikin muhimmancin ranar ghadir.An tambayi Imam Sadik[as] “Shin Musulmi suna da
wani idi banda ranar jumma’a da babbar sallah da kuma karamar sallah?sai Imam
Sadik yace:Na am wanda ma ya fisu daraja,sai wanda ya ruwaito hadisin ya
tambaya:wane idi ne wannan?sai Imam Sadik[as]yace
masa.Ranar da manzon Allah[s]ya Ayyana Imam Ali[as]a matsayin khalifa a
bayansa,i tace ranar 18 ga zil-hijja.”Saboda haka, a ido-din da ake dasu a
Musulunci ,to idin ghadir shine mafi girmansu da kuma daraja.Haka nan wannan
rana ta ghadir sanan-niya ce a sama,wato tsakan-kanin Mala’iku,a sama ana cema
ranar “YAUMUL AHDUL –MA’AHUD.”A takaice dai
ranar ghadi rana ce mai daraja da kuma falala mai tarin yawa.ya mazo
daga Imam Ridha[as]yace, “Da ace mutane sun san hakika nin falalar da ke cikin
ranar ghadir da Mala’iku sunyi musafaha dasu
a kowace rana sau goma.”Saboda muhimmancin al-amarin ghadir zamuga,
Malamai na mad-rasa din Ahlul-bait[as]da yawa sun rubuta littafai akai.Ga
sunayen wasu littafai daga ciki.1-Asrarul ghadir na Muhammad Bakir
al-ansariy.2-Idul ghadir fil Islam na Allama Amini.3-Ghadir fil kitabi wa sunna
wal-adab shima na Allama Amini.Da dai sauran littafai masu yawa akan haka. 2-Abubuwa da suka
auku ranar ghadir:-Sanin abubuwan da suka auku a ranar ghadir dama abubuwanda suka auku gabanin ranar da kuma
abun da ya biyo bayan ranar yana da gayar muhimmanci.Domin sanin wadannan bangarori ukku na ghadir,wato abinda
ya faru gabanin ghadir da ranar ghadir da kuma bayan ghadir,mutum zai fahimci
lallai babban jarabawa da manzon Allah[s] ya fuskanta,a tarihin rayuwar sa,itace
wannan al-mari na ghadir.Domin in mutum
ya dubi tsawon shekaru 23 da aka aiko ma Manzon Allah[S]da sako na
wahayi.To babu sakon da yazo wanda Manzon Allah[S]ya nemi ayi masa afuwa wajen
isar da shi.Sai wannan al-amari na ghadir.Domin yazo akan cewa lokacin da Manzo
Allah[s]ya bijoro da al-amarin,na cewa zai bayyanar da magajinsa,wato
khalifansa,gobe a ranar Arfa,sai
fuskokin wasu da yawa suka canza.Haka al-amarin ya kasance,har ya zuwa
saukar aya mai cewa “Ya kai wannan Manzo,ka isar da abinda aka saukar zuwa
gareka daga ubangijinka.Idan baka
aikata[haka]ba,to baka isar da[sauran]sakon ba.Kuma Allah zai kare ka
daga mutane.Lalle Allah ba ya shiryatar da jama’a kafirai.[suratul-ma’ida aya
ta 57]Bayan saukar wannan aya,nan take,sai
Manzon Allah[s] ya aika da a tsayar da mahajjata da suka wuce,da yake
ita ayar ta sauka ne bayan aikin hajjin bankwana da Manzon Allah[S]yayi,wato
bayan ya bar makka a kan hanyarsa ta komawa madina,sai ayar ta sauka a wani
waje da ake ce masa ghadir-khum.wasu ‘yan milamilai tsakanin su da birnin
Makka.Kuma shi wannan waje na ghadir-khum,wata mararraba ce da hanyoyi suka
rarrabu zuwa Madina,Masar,Sham da Iraki.To a wannan waje ne na ghadir khum,
Mala’ika Jibril[AS]ya sauko wa Manzon Allah[S]da wannan aya.Saboda haka sai ya
tsaya a wajen,ya kuma bada umarni na cewa,wadanda suka kama hanyar garuruwan
su,ace su dawo.misali wadanda suka kama hanyar sham,masar da dai sauran
su.Wadanda kuma basu iso ghadir khum din ba daga makka,ManzonAllah[S]ya tsaya
sai da suka iso.Ranar da wannan al- mari ya faru ranar Alhamis ne,18 ga watan
zul-hajji,shekara ta goma bayan hijira.Bayan da aka taru,adadin
wannan taro malamai sunyi sabani akai,akwai wadanda suka tafi akan cewa a dadin
ya kai sama da dubu dari, a kwai kuma wadanda suka tafi a cewa kasa da haka ne.koma
dai minene adadin, taro ne mai yawa.Kuma wannan taro ba rana daya aka yishi aka
tafi ba.A’a sai da aka kwashe kwana ukku
a wannan waje na ghadir khum,saboda haka abubuwa da yawa sun faru a cikin
waddannan kwanuka.Amma ga guda biyar daga ciki.1-KHUDUBA:Kafin hudubar,Manzon
Allah[s]yasa a kira sallah bayan nan ya jagoranci sallar Azahar,bayan kammala
sallah ya hau mumbari wanda aka yishi da siridda na dabbobi da dai sauransu,sa
annan yace ma Imam Ali[AS]ya hawo kan mumbarin,ta yadda kowa zai iya ganin
su.Bayan haka sai Manzon Allah yayi huduba mai tsawo,wanda a tarihin sa ba
huduba mai tsawo da yayi kamarta.Hudubar ta kunshi bangarori dabam dabam.Wanda
a cikin ta Manzon Allah[S]ya bayyana RAS MIYYAN wato OFFICIALY wadanda zasu
kasance khalifofi a bayan sa.Adadinsu da kuma sunayen su,su goma sha-biyu ne,na
farkon su Imam Ali [AS] na karshen su Imam Mahdi[AS]a cikin khudubar sunan Imam
Ali[AS] yazo a waje 40,kalmar Aimma waje 10,Imam Mahdi[AS]waje 20,da dai sauran
su.Har wala yau,a lokacin da Manzon Allah[s]ya ke khudubar akwai inda ya daga
hannun Imam Ali[AS]sama yace “Duk wanda na kasance shugabansa ne,to wannan ALI
ma shugabansa ne,Allah ka jibinci wanda ya jibin ce shi,ka ki wanda ya kishi,ka
taimaki wanda ya taimake shi,ka tabar da wanda ya tabar da shi.”2-Bayan wannan
huduba,Manzon Allah[s]ya sa ma Imam Ali[AS]Rawani, na muamman,sunan rawanin
SAHAB.Asalinsa na Manzon Allah ne [S]Mala,iku suka zo masa da shi a yakin
Badar.
3-WAKE:Bayan
haka wani mawaki sahabin Manzon Allah mai suna Hassan dan sabit ya nemi iznin
Manzon Allah[S]ya ba shi dama yayi wake kan wannan al-amari na ghadir,Manzon
Allah ya ba shi dama yayi waken,ga mai
bukatar ganin waken yana iya duba littafan da aka ambata sama. 4-BAI’A:Bayan
haka ,Manzon Allah[S]yasa ayi hemomi
guda biyu,domin yin bai’a,ya zauna a daya,yace Imam Ali ya zauna a
dayar,Haka aka ci gaba da yin wannan bai’a har kwana ukku,Domin kowa sai da
yayi, har da mata,amma da aka zo kansu Manzon Allah[s]ya sa akawo ruwa ne a
cikin kwarya,ko wace tazo, sai ta saka hannun ta a ciki.wato a matsayin tayi
bai ‘a.wani tambihi a nan shine,cikin wadannan mataye har da iyalin manzon
Allah[s]baki dayan su.Domin yazo akan cewa a wannan tafiya aikin hajji da su ya
tafi dukkan su.Haka nan yazo akan cewa,a cikin wadannan kwanaki ukku da ake wannan bai’a,Manzon Allah[s]yana yawan cewa,Ku taya ni murna,Allah ya keban ceni
da Annabta,ya kuma keban ce Ahlu-bai-tina da imamanci.
5-MU’UJIZA:Yazo akan
cewa a karshen yini na rana ta ukku,wata mu’ujiza ko aya ta bayyana.yadda abun
ya faru ko shine,wani mutum da a ke cema Haris al-fihiri,yazo wajen Manzon
Allah[S]ya ce masa “Ya ubangiji in wannan gaskiya ne daga wajen ka ne[wato nada
Imam Ali a matsayin khalifa]ka ai ko mana da duwatsu daga sama ko kuma kazo
mana da azaba mai radadi”An ce nan take a wajen,Allah[T]ya aiko dutse daga sama
ya samu kansa ,ya fita ta duburar sa,nan take kuma ya mutu.Wani abun mamaki
shine bayan da manzon Allah[s]ya gama huduba,sai wasu suka koma gefe
suna,tattaunawa kan wannan abu.Wani cikin su yace Manzon Allah yayi
hauka[Wal’iyazu billahi] wani yace ba hauka bane,son rai ne ka wai,sai wani
yace koma hauka yayi ko son rai ne,to abin da ya fadi ba zai yiyu ba.Saboda
haka akayi kulle-kulle ,na kashe Manzon Allah[S] kan hanyarsa ta komawa
Madina.Allah[T]ya tona asirin su,ya kiyaye Manzon Allah[s] ya isa Madina
lafiya.Bayan komawar sa madina akwai lokacin daya bukaci akawo masa tawada ya
rubuta, abinda in suka yi riko da shi a bayan sa ba zasu bace ba,nan ma aka yi
haya niya wani ya hana yace kur’ani ,ya wada cesu,ya shirya rundunar yaki
karkashin Usama dan Zaid,aka ki
tafiya.Ire-iren wadannan abubuwa da suka faru,tsakanin ghadir da wafatin
Manzon Allah[kwana 70 ne tsakani] suke nuna lalle al-amarin ghadir ya kasance
jarabawa babba ga manzon Allah [s].Domin in mutum yayi tunani sosai,zai ga cewa
dukkan jarabawowin da Manzon Allah[S]ya fus kanta a rayuwarsa,zafinsu da dacinsu a zuciya bai
kai wadanda ya fuskanta a cikin wadannan kwanaki 70 ba,na karshen rayuwarsa.Domin
in mutum ya dubi wadancan matsaloli zai ga mafi yawan su matsaloli ne na
waje,amma wadannan matsaloli ne, na cikin gida,saboda haka jarabawar sa tafi
tsanani.Wannan ke nan a takaice dangane da abubuwan dasuka faru aranar ghadir
khum. 3-Tawili da kuma kwas kwarima da
aka yima al-amarin ghadir a littafan Ahlus-sunna:-Idan mutum yayi bincike a
littafan Ahlus-sunna,kan al-amarin ghadir,zai ga babu wani abu
da aka yi masa tawili ko aka jirkita shi,kamar hadisin ghadir.Kasantuwar
in kari ko musa ,asalin aukuwar al-amarin bazai yiyu ba.Shi yasa aka dauki
matakai na tawili da kuma kwas-kwa-rima,ga hadisin ghadir.Baya ga haka kuma,in
mutum ya bibiyi Matanin hadisin ghadir a littafan Ahlus-sunna,zai ga sun yayyayen keshi,kaga nan an kawo wani yanki,can
an kawo wani sashe, wato gutsi-gutsi a kayi da shi.Shi yasa kammalalliyar
hudubar da Manzon Allah[S]yayi ,a ranar ghadir,baki daya babu ita a littafa n
Ahlus-Sunna,sai dai, kai tacin karo da yanki-yankin ta ,alittafai.Saboda haka
samun cikakkiyar hudubar,sai a littafan shia.Ga misalin haka,a littafin Hadis
na sunna.Mutum ya duba littafin Riyadhu-Salihin,babin dakemagana kan
girmama,Ahlu baitin Manzon Allah,Hadisi na farko a babin,An samo daga dan
Hibban,yace,mun tafi ni da Husain dan sabarata da Amru dan Muslim,zuwa ga,Zaid
dan Ar-kam.Lokacin da muka zauna gaban sa,sai Husain yace masa.Lalle Zaid ka
hadu da al-hairi mai yawa,kaga Manzon Allah[s]ka kuma ji daga gareshi,kayi yaki
tare dashi,kayi sallah a bayan.Saboda haka ya Zaid,ka fada mana wani abu da
kaji daga Manzon Allah[S]sai Zaid yace wallahi na tsufa,na manta wasu abubuwan
da naji daga Manzon Allah[S].Bayan haka sai ya ce masu,wata rana Manzon
Allah[S]ya tsaya a cikin mu ya na mai khuduba,a wani tabki na ruwa a nace masa
KHUM,yana tsakanin makka da madina ne.Yai godiya ga Allah,yai yabo ga reshi,yai
waazi kuma ya tunasar[wato a hudubar]saannan yace bayan haka:Yaku mutane,ni
mutum ne,yayi kusa Manzon ubangiji na
yazo in amsa masa[wato kusantowar
wafatinsa]Saboda haka na bar maku nauyaya guda biyu,na farkon su
littafin Allah,cikinsa akwai shiriya da haske.sa annan kuma yace,da
Ahlu-baitina,ina tunasar daku Allah game da Ahlu-baitina.”Muslim ne ya ruwaito
hadisin.kuma iyaka abunda
aka yanko daga khudubar ghadir ke nan,a hadisin.Can kuma wani Hadisin,a
binda aka yanko a hudubar shine,Manzon Allah yace a ghadir-khum,Man-kutu
maulahu,fahaza Aliyu maulahu.shi kuma abunda aka yanko kenan.A takaice dai haka
aka gutsutsura hadisin ghadir a littafan Ahlus-sunna.Dama ace abun ya tsaya ga
haka,A’a wadanda aka kawo a gutsutsure din,sai aka yi masu tawili ko aka canza su.misali wadannan hadisai biyu da aka kawo,Kalmar
maula anan suka tafi akan cewa, wai tana nufin masoyi ko mai taimako,ba wai
shugabanci ba.Al-hali su wadanda akayi abun gaban su ,sun fahimce ta , a
matsayin shugaban ci.Kuma mutum ya auna da hankalin sa,ace manzon Allah ya tara
irn waddanan, jama’a waje daya,kuma cikin zafin rana,saboda ya shaida masu yana
son Imam Ali,saboda haka suma, su soshi.Haka nan kuma a daya hadisin,kalmar ,wa
Ahlu baitiy sai aka canza shi da Wa-sunnatiy,a wasu hadisan.Kai hatta ma,ayoyin
da suka sauka a ghadir khum,suma an canza Makan na Nuzul dinsu,wato wajen da
suka sauka.Wai Ayar Alyauma akmaltu lakum dinakum,a ,Arfa ne ta sauka.Ayar kuma
Ya ayyuhar Rasul ballig ma unzila ilaik.Wai a makka ta sauka.Al hali Suratul
Ma’ida,Ai Madaniyya ce ba Makkiyya ba.Da
dai abubuwa da dama da akayi tawilinsu ko aka canza su,dangane da,al-amarin
ghadir.Baya ga haka kuma,mu duba a farkon ai-amari,yadda aka dauki matakai na
hana rubuta hadisai na Manzon Allah[S] da kuma watsa su.Ba dun komi ba face
saboda danne wannan al amari na ghadir.Amma Allah[T]bisa ikonsa,ya hukumta
wannan al-mari na ghadir ba zai boyuba.Wannan kenan a takaice dangane da tawili
da kuma canje-canje da aka yima al-amarin ghadir. 4-Ayyukan
da akeyi a Ranar ghadir:-Akwai ayyuka na
Ibadodi ,da suka zo daga Manzon Allah[S]da kuma Aimma na Ahlul-bait[AS]wadanda
ake son yin su ,a daren ghadir da kuma ranar ghadir.Wanda wadannan ayyuka suna
da falaloli masu yawan gaske.A daren ghadir,akwai wata sallah mai,Raka’a goma sha-biyu,yadda ake yin sallar mutum na
iya duba littafin Ik-bal na sayyid ibn Dawus.Da yake babu ita acikin littafin
Matihul-jinan.Haka nan a daren akwai,
wata addu’a da ake biyawa.Ita ma mutum ya duba a littafin Ik-bal din.Sai kuma
ranar ghadir,ayyukan da suka zo sune:1-Azumi .2-Wanka.3-Ziyarar Imam
Ali[as].daga kusa ko nesa.4-Sallah raka’a biyu,yadda ake yinta mutum na iya
duba Mafatihu.5-Biya dua’un Nudba.6-karanta wata addu’a da aka samo daga shaikhul
Mufid,ita ma akwai ta cikin mafatihu.7-Taya juna murna,ta fadin cewa “Al-hamdu
lillahil-lazzi-ja’alana minal-mutamassikina,biwi-layati Amiril
ma’uminin,wal-aimma [as]”Da dai sauran ayyukan da ake son aikatawa a ranar.kuma
kamar yadda aka ambata wadannan ayyuka ,an samo sune daga Ma’asumin [AS] misali
yazo akan cewa an tambayi Imam Sadik [AS]mi ya kamata mutum yayi ranar
ghadir?sai yace.Azumi,ibada,yawaita yima Manzo salati da Alayen sa.Kuma kiyaye
irin wadannan ayyuka na Munasabobi yana
da gayar muhimmanci.Domin rashin kiyaye war zai sa mutum ya dun ga hasarar lada
mai yawa,misali wannan azumi da ake son yi a ranar,yazo a kancewa wanda yayi
shi,za a kan kare masa zunubin shekara sittin,a wata ruwaya kuma yana da lada
kamar ya kasance kullum yana azumi ne,a wata ruwayar kuma yana da lada kamar wanda yayi hajji da umra,sau dari.Mu
duba irin wadannan falaloli.Kuma idan
mutum ya saba yana kiyaye wadannan ayyuka na munasabobi,ko da sun zagayo,sai
uzuri ya hana shi aikatawa misali rashin
lafiya,tafiya da dai makaman tansu.To za’a ba mutum lada kamar ya aikata su.sabanin ko mutum idan
jefi-jefi ,yake yin su,shi ba zai samu irin wannan ladar ba.Saboda haka duk watan da ya kama ,mutum sai ya bincika
yaga wadanne munasabobi ne ke cikin watar.domin mutum ya aikata su.mutum ya dun
ga yin haka,har ya zama masa malaka wato
jiki.Misali yanzu munasabar da ke
gabammu itace ta yaumul-mubahala,wato 24 ga watan zul hajj.ita ma akwai ayyuka
da suka zo a ranar,mutum na iya duba mafatihu. 5-Kafa
hujja da Hadisin ghadir a kan wasu mutane da,Ahlul bait[as] sukayi.Idan mutum
ya bibiyi tarihin Aimma [AS]zai ga wani lokaci cikin lokuta,sun kafa hujja da
hadisin ghadir,misali Imam Ali[as]ya kafa hujja da shi, a wajaje dabam-dabam,misali
a ranar shura,a yakin jamal,a yakin siffin,a kufa,da dai sauransu,Haka nan ya
kafa hujja da shi a kan dai-dai kum mutane,wadansu sun tabbatar wasu kuma suka
boye.yai addu’a,akan su,kuma ta kama su,wato wadanda suka boye din,cikin su,akwai wanda ya
makance,akwai kuma wanda ya kutur-ce da dai sauran su,Haka nan Sayyida
Fadima[as]i tama ta kafa hujja dashi.Haka nan Imam Hasan da Imam Husain
[AS].Haka nan Ammar dan Yasir shima ya kafa hujja da shi a yakin siffin.Haka
nan Umar dan Abdul-aziz,shima ya kafa hujja da shi,da dai sauran mutane masu
yawa,da suka kafa hujja da hadisin ghadir,a kan cewa I mam Ali[as]shi ne
khalifan Manzon Allah,mubasharatan bayan sa. 6-Illolin
da suka auku,saboda rashin bin umarnin Manzon Allah[s]dangane da al-amarin
ghadir,wadannan illoli a bayyane suke.Duk abubuwan da suka faru a wannan Ai-
umma ta manzon Allah[S] tun daga farko har yau din mu,Asasi da kuma sabab din
aukuwar su,shi ne rashin aiwatar da al-amarin ghadir ne.misali da an ai watar
da al-amarin ghadir,mutum fajiri,fasiki irin
Yazidu[LA]zai iya zama khalifa,ballantana yayi abunda yayi.Saboda haka
illolin da haka ya haifar suna da yawa.Ga wasu daga ciki,1-An she, hakki daga
hannun masu hakki,da Allah[T]yaba,wato na khalifanci.Baya ga haka kuma aka
cutar da su aka gallaza masu,mutum ya bibiyi tarihin Aimma[as]daya bayan
daya,wato tun daga Imam Ali [as]har ya zuwa imam Mahdi[AS]yaga ko wannen su
yaddu aka cutar dashi ,aka gallaza masa,daga karshe kuma ko wannen su daga
wanda aka kashe da takobi[kamar Imam Ali da Imam Husain]sai wanda aka sama ma
guba,Abin mamaki ma shine Imam Mahdi[as]
tun gabanin a haife shi ana nemansa akashe shi.Wato shigen na Annabi Musa[as]
da Fir’auna.Baya ga haka kuma aka cutar da wadanda sukayi Riko da su,ta fuskoki
dabam-dabam,kisa ne,dauri ne, kora daga kasa,cutarwa- ta,fatan baki da dai
sauransu.in ma mutum bai san na zamanin da ba,to ya duba na wannan zamani da
yake ciki,yaga yadda ake cutarwa da gallazawa ga mabiya Ahlul-bait[as] a sassan
duniya dabam-dabam.2-Daga cikin illolin da wannan abu ya haifar,akwai gina
mutane akan jabun addini,wato ga ainihin koyar war Manzon Allah[s]akan
abu,sai a barshi,agina mutane kan wani
abu dabam,wato abinda ake
cema,IJTIHAD-MAKABILI-NAS.mutum ya duba tarihin khalifofi zai ga haka.Wanda
ire-iren wadannan abubuwa,Imam Mahd[as]ne kadai zai gusar da su idan ya
bayyana.Domin yazo akan cewa,duk wani abun da aka sa shi acikin addini wanda
babu shi a lokacin Manzon Allah[S]sai ya gusar da shi.Duk kuma wani abu wanda
akwai shi a addini,amma aka debe shi,to sai ya dawo da shi.Akwai mislai da
yawa,na gina mutane kan abun da ba dai dai ba,a lokaci guda kuma suna ganin
addini ne.Mu duba yadda aka gina mutane kan al-amarin Ashura,a duniyar
Ahlus-sunna.3-Daga cikin illolin da
wannan abu ya haifar,Akwai sabani da rarraba ga wannan Al-umma ta Manzon
Allah[s]Saboda haka duk wani sabani da rarraba da muke gani tsakanin musulmi,a
yau,da kuma wanda ya auku daga magabatan mu,to asasin abuda ya haifar
dashi,shine rashin aiwatar da al-amarin ghadir.4-Daga cikin illolin da wannan
abu ya haifar,akwai takai-tuwar ,amfana da wadanda Manzon Allah ya bayyana su,a
matsayin khalifofi a bayan sa ranar ghadir.Misali Imam Ali [as]ya rayu bayan
Manzon Allah[s]shekara talatin,mutum yayi tunani,wadannan shekaru 30,da Imam
Ali yayi su a khalifanci,kai tsaye bayan manzon Allah,wane irin gayar
amfanuwa,wannan al-umma zata samu,mu duba shekaru biyar da yayi na
khalifanci,irin natijojin da aka samu,duk ko da yayi sune cikin matsaloli dabam
dabam.misali Nahajul-Balaga,hudubobin sane da wasikunsa da zantukan sa,da yayi,
a wadannan shekaru biyar na khalifancin shi.Mu kuma duba ilimomi da
aka samo daga Imam Sadik da Imam Bakir [AS]saboda yana yi da suka samu na bada
ilmin.To me ake tsammani da ace wannan imamai 12 sun gudanar da khalifanci,irin
amfanuwa da za a yi dasu,wani abun mamaki su wadanda suka kwace khalifanci daga
wajensa, in ta kuke masu a fagen ilimi suna komawa ne gare su.mutum ya binciki
tarihi zai ga haka. 7-Darussa
da zamu koya daga wanna al-amari na ghadir,Akwai darussa masu yawan gaske a
cikin wannan ai-amari na ghadir,ga wasu daga ciki.1-Sallama ma hukuncin
Allah[T] wato yana da muhimmanci,mutum ya kasance,a rayuwarsa,mai sallamawa ga
abun da Allah[t]ya hukunta,misali wannan al-amari na ghadir,haka Allah[T]ya
hukunta,shi ya zabi wadannan bayin Allah,akan su kasance khalifofi bayan Manzon
Allah,saboda haka miya hau kan mutum,sallamawa,domin yin haka shine zaman
lafiyar mutum duniyar sa da lahirar sa.Domin ko a ranar ghadir din,akwai
wadanda suka zo suka samu Manzon Allah[s] suna tambayar sa,wannan abu daga
wajen Allah ne,ko daga wajen ka.Manzon Allah[s]yace masu daga waje Allah
ne.Amma wasu da yawa saboda Hassada ya kai su da inda ya kaisu.saboda
haka,akwai abun lura anan.2-Muhimmancin kyakkyawan karshe a rayuwa,in muka dubi
ranar da wannan al-mari ya faru.yadda kowannen su yayi bai’a ga Imam
Ali[AS]akwai ma wadanda har taya shi murna sukayi cewa ya zama shugaban su da
kuma dukkak muminai.Amma kuma duk da haka daga baya mutum ya canza,wannan akwai
abun tsoro a ciki.Akwai kuma wadanda suke har bayan zaben sakifa,suna bayan
Imam Ali[as]suma daga baya suka canza.saboda haka mutum ya kasance mai yawan
tunanin akibar sa,a addinance yana da muhimmanci.3-Illar saba ma manzon
Allah[s] Idan mutum ya dubi,abubuwan da suka auku,ga wadanda aka yi wannan
al-amari na ghadir gaban idon su,abun yana da ban tsoro da kuma tada hankali,ga
kuma fadin Allah[T]wadanda suke saba ma,umarnin manzon Allah,su ji tsoron kada
fitina ta same su ko azaba mai radadi”mu duba irin fitinonin da suka gudana,a
lokacin.mutum ya binciki tarihi ,zai ga haka.mu duba,abubuwan da suka faru,a
madina lokacin da yazid ya halatta ta ga
mayakan sa kwana ukku,yadda aka ci mutuncin wadanda akayi wannan abu gaban idon
su,aka ma’ya’yan su fyade,akwai ma sahabin da suka shiga gidan sa duk da ya
tsufa sosai,amma haka suka kama shi suna fisge mai gemunsa daya bayan daya,da
dai sauran su.mutum ya duba cikin Tarihul-khulafa na suyudi zai ga haka.mutum
ya yi tunani da ba’a saba ma umarnin ManzonAllah ba,haka zai faru?wato na irin
wadannan fitinoni,da cin mutun ci. 8-Natijojin
da za a samu da an ai watar da al-amarin ghadir.Tabbas da an aiwatar da
Al-amarin ghadir,da an samu natijoji masu yawan gaske,a duniyan ce,da addinan
ce da kuma a lahiran ce.Aduniyance da an
samu zaman lafiya,yelwar arziki,izza akan wadanda ba musulmi ba,da dai sauran
su,na ni’imomin duniya.A addinan ce kuma da an samu fahimta sahihiya ta
addini,wato ba gurba-tacciyaba.kamar yadda mafi yawa ake akai yanzu.A lahiran
ce kuma mutum ya samu tsira,da ga azabar
Allah da kuma shiga cikin rahamar sa.Domin ba dadi ace mutum ya rayu a gidan
duniya,gobe kiyama ta bayyana masa akan cewa,abinda yake akai,ko kuma,wadanda
yayi riko dasu a matsayin khalifofin manzonAllah ,ba haka abun yake ba,Saboda
haka kira anan musammam ga ‘yan uwanmu musulmi Ahlus-sunna,da suyi bin cike a
littafan su,kan wannan al-amari na khalifanci.domin shine a sasi na sabani
tsakanin shia da sunna.kuma wani abun mamaki shine,hujjojin shia kan wannan
mas’ala ta khalifanci,zasu iya tabbatar da su a littafan sunni,misali cewa
khalifofi goma sha-biyu ne,ya na nan a cikin littafin hadis na Buhari,Muslim da
dai sauran su.Amma da mutum zai samu malamin sunni,yace yana son ya nuna mai hadisi da yazo daga Manzon
Allah,da yace,khalifofi a baya na gu da hudu ne,ba zai,iya nuna waba koda ko hadisin mai rauni ne.kada a manta
sunce manzon Allah bai khalifantar ba,wai ya barma al-umma ,ta zaba.shi kuma
wanda aka zaba na farko,da zai rasu sai ya ayyana magajin sa.mutum na iya
tambaya,to mai yasa shi bai yi koyi da sunnan manzon Allah,wato na ya barma
alumma ta zaba,shi kuma wanda aka ayyana da zai rasu,sai ya kafa kwamitin mutum
shidda,a kan su zaba,a tsakanin su,wanda aka zaba din bayan an kashe shi
,jama’a sukayo tururuwa wajen Imam Ali[as]su kace shi suke so a matsayin
khalifa,saboda haka Imam Ali[as]a cikin wadannan khalifofi shi kadai ne jama’a
suka zabe shi.wannan kuma wata ayane ga masu tunani.Ta yiyu wani yace a sakifa ba zabe akayi ba?mutum ya binciki abun da
kyau,zai ga mafi yawan sahabbai,basu wajen, daga baya sukaji labari, na abunda
ya faru.Shi kuma Muawiya shi ya nada kansa,da zai rasu ya nada dansa Yazid,tun
daga nan sai abun ya koma gado da kuma juyin mulki,wato in mutum nada maya ka,
sai yakauda wanda yake akai,domin ya hau.mutum ya duba wancan littafi na suyudi
da aka ambata ,zaiga wannan abubuwa da aka kawo.kuma wani abu shine,wannan
littafi na Tarihil-khulafa na suyudi,to mutum ya bibiyi,rayuwar wadannan
khalifofi na bani umayya da kuma banul-Abbas,ya gani zai ga cewa, Ayya ko
wadannan sune khalifofin Manzon Allah?Amma da ace anbi zabin Allah[T] da, duk
wannan abubuwan basu faru ba.kuma mutum yabi tarin Aimm[AS] yagani,ko wannen su
anyi mai shaida cewa a zamanin sa ba wanda ya kai shi,ballantana ya wuce
shi,wato ta kowa ce fuska,a ilimi ne
,ibada ne ,Aklak ne da dai sauran su .saboda haka da ace su sukayi khalifanci a
bayyane, da an samu natijoji masu yawa a wannan al-umma. 9-Abin
da ya hau kanmu dan gane da wannan al-amari na ghadir:-Abu na farko shi ne ya waita godiya ga Allah[T]
kan wannan babbar ni’ima, da yai mana na tamas-suki da wanna wilaya ta Ahlul
bait,da kuma Bara’a daga makiyan su.wannan ba karamar niima bace, musamman in
mutum yayi la’akari da nahiyar da muka taso a cikin ta.Abu na biyu ,shine mutum
yayi mujahada wajen ganin cewa,rayuwarsa tayi muwafaka,da koyar war
Aimma[as]dai dai gwargwadon ikon sa.Na ukku mutum ya saba ma kansa,da yin wasu
ayyuka na ibadodi,lokaci bayan lokaci da niyyar Allah [T]ya kai ladar gare
su.misali akwai wata sallah da akeyi ga Manzon Allah da Ahlul-bait,wato da
niyyar Allah ya kai ladar garesu,mutum na iya duba mafatihu,zaiga yadda ake
sallar.Ko kuma a munasabobi na wafatin
su ko wiladar su,mutum yayi wasu ayyuka da nufin Allah[T]ya kai ladar gare
su,misali ace ya sau ke Al-kur’ani,ko ya biya abinda ya saukaka,ko ,yai wata
kyauta,da dai makaman tan su.Domin irin yin wadanan ayuka, garesu yana daga cikin
kyatata,alaka da su.Na hudu,Yin wani abu domin raya wannan al-amari na
ghadir,tsakan-kanin mutane,misali,a’iyalin sa,’yan’uwan sa na jini,abokan
mu’amalar sa,idan shi dan makaranta ne ko dan kasuwa ko ma’akaci da dai makamantan su.Zai yi haka
ne dai dai gwargwadon ikon sa,ta hikima da kuma uslubin da za’a fahimce
shi.Domin ranar da Manzon Allah[S]yayi wannan khuduba,a ghadir khum,yace wanda
kenan ya sanar da wanda bai nan,uba ya sanar da dansa. 10-Ai’katuwar wannan al’amari na
ghadir.Kasantuwar wannan al’amari na
ghadir,bai gudana,a zahiran ce ba,wato a aikace ba,kamar yadda Allah[T] ya
hukumta,Manzon Allah kuma ya isar da sakon haka.To tambaya haka ya tada
Ai’mma[as] daga matsayin da Allah[T]ya basu,na cewa sune khalifofin Monzon
Allah a bayan sa.Amsa bai tada su.Dalilin yin wannan tambaya shine,so da yawa,malaman
Ahlus-sunna,suna yawan kawo haka,cewa
idan ance sune khalifofin Manzon Allah[S] ai ba suyi shugabanci ba.Kasantuwar
basu yi shugaban ciba,bai tada su daga matsayin suba na khalifofi,misali kamar
Allah[T]ya aika daAnnabi ga wasu mutane,sai ya zamanto ba wanda yayi imani da
shi,to haka ya tada shi daga Annabi?kuma kamaryadda ba mutane ne ke zabar
Annabi ba,to haka nan shima,khalifanci na Manzon Allah[S]Allah[T]yake zaba,ya
kuma zaba.Abinda ya hau kan kowa da kowa shine bin zabin Allah[T]In kuma mutum na shakka kan haka ko ya jahilci wannan
abu,to abun da ya hau kansa, yanzu shine yayi bincike,a littafan Ahlus sunna
bama na shia ba,kan wannan al-amari na ghadir.kuma koda ma hadisin da yazo a
cikin sahihul Buhari da Muslim na fadin ManzonAllah cewa khalifofi a baya na 12
ne,ya isa yasa mutum yayi tunani kuma ya tambayi kansa,to su waye wannan 12.In
mutum yace ai 12,ana nufin khulafai-rra-shidin,to
ai hudu ne,a ,Ahlus sunna,in kuma kace khalifofin bani umayyane,su 14 ne,in
kace khalifofin abbasawa ne,su,47 ne.saboda haka,inka hada adadin khalifofi na
umayyawa da Abbasawa da kuma khulafa guda hudu da suka gabace su,a dadin zai ta
shi,65.To kuma ga hadisi ingatance,yazo akan cewa khalifofi a bayana 12,shi
yasa mafi yawan malaman Ahlus suna,basu da fahimta guda daya ko matsaya guda
kan wannan hadisin.Zai yi kyau mutum ya
samu Tarikhul khulafa na suyudi,yaga yadda ya kawo zantukan fitattun malamam
Ahlus-sunna kan wannan Hadisi.ko kuma wani rubutu da akayi abaya mai
taken.Imama a mahangar Ahlul bait[as]da kuma Ahlus-sunna,an kawo waddanan
zantukan.To bayan duk matakai da aka
dauka na ganin cewa ,wadannan bayin Allah basu yi wannan khalifan ci,A zahiran
ce ba,wato basu rike iko ba.Wani abu wanda yake tabbatacce kuma saiya
auku,shine cewa,cika-makin wadannan khalifofi 12,wato Imam Mahdi[AF]i dan ya
bayyana sai wannan khalifanci ya
tabbata,a aikace,wato zai kasance,a lokacin duniya baki daya,zata kasance
kar’kashin ikon sa.To a lokacin zata bayyana ma wasu akan cewa,a she angina
mutane a tsawon tarihi kan wani abu dabam,wato akasin abinda Manzon Allah[S ]ya
bayyana,A ranar ghadir khum.Saboda haka wadanda suka haifar da wannan abu,mutum
zai iya ceawa sun zalinci kansu,sun kuma zalinci ‘yan’baya. Daga karshe babu abun da
zamu ce,face godiya ga Allah[T]da yayi mana wannan babbar ni’ima ta riko da
Ahlul-bait[AS]muna kuma rokon sa,ya rayar damu akai,ya karbi rayuwarma akai,ya
kuma tada mu a kai.Sauran ‘yan uwanmu musulmi, muna rokon Allah[T]kamar yadda
yayi mana,wannan ni’ima ta riko da Ahlul-bait [AS]suma yai masu.
No comments:
Post a Comment