Sunday 10 February 2013

Bayani kan Ijtihadi da Taklid.


Kamar yadda aka yi bayani a darasi na 3, cewa kasantuwar zuwan watan Ramadan gabatarwa da kuma shimafi]a da ake yi na wannan darasi na Fi}ihu za a dakatar a shiga babin Azumi, in ya so bayan watan Ramadan sai a kammala gabatarwar da kuma shimfi]a, bayan haka kuma sai a shiga babin farko, wato babin tsarki, bayan shi kuma babin Salla, da dai sauran babobi, insha Allahu daidai gwargwadon iko.

Saboda haka yanzu kammalawa ne na gabatarwa da kuma shimfi]a da aka yi a darasi na ]aya da na biyu. Wannan kuwa shi ne Ijtihadi da Ta}lidi. Idan mutum ya duba littafai na Risala Amaliyya, wato littafan Fi}ihu na fatawowin Mujtahidai na Madrasah ]in Imamiyyah zai ga mafi yawansu, kafin su shiga cikin babobin Fi}ihu, sai sun yi wannan gabatarwa ta Ijtihadi da Ta}lidi. Alal misali, mutum na iya duba Tahriril Wasilah ko Zubdah na Imam Khumaini ({S), zai ga haka. Domin a Fi}ihun Imamiyyah, dole ne Mujtahidin da mutum zai yi ta}lidi da shi a matakin farawa, ya kasance a raye. Wannan kuma yana ]aya daga cikin bambance-bambance da ke tsakanin Fi}ihun Imamiyyah, da kuma Fi}ihun Ahlus Sunna. Wato kamar dai yadda suke da bambanci a wajen masadir na istinba]in hukunce-hukunce.
Saboda haka shi wannan babi na Ijtihad da Ta}lid ya shafi mas’aloli ne da suka shafi Mujtahidi da Muhta]i da kuma Mu}allidi. Domin a Fi}ihu, mutane ko mukallafai sun kasu gida uku ne: Ko dai mutum ya kasance Mujtahidi; ko Muhta]i; ko kuma Mu}allidi. Saboda haka, wajibi ne ga kowane mukallaf wanda bai kai matsayin Ijtihadi ba a ibadodinsa da kuma mu’amalolinsa, ya kasance ko dai Muhta]i ko Mu}allidi.
1-MUJTAHID: Mujtahidi shi ne wanda yake da }udura (ikon) na fitar da hukunce-hukunce na Shari’a daga masadir, sune ‘Kitab’, ‘Sunna’, ‘A}al’, ‘Ijma'i’.
A Ahlus Sunna kuma, ban da wa]annan, akwai irin su {iyasi, Istihsan, Masalihil Mursala, da dai sauransu. Sai dai nan afuwan, wa]annan kalmomi ne wa]anda bayaninsu yana fannin Usulul Fi}ihu ne. Kuma Mujtahidi, akwai Mujtahid Mu]lak, shi ne wanda zai iya Ijtihadi, wato ya tsamo hukunce-hukunce a dukkan babobi na Fi}ihu. Akwai kuma Mujtahidi Mutajazziy, shi ne Mujtahidin da a wasu babobin na Fi}ihu yake iya fitar da hukunci, (ba dukkan babobi ba).
Misali, zai iya fitar da hukunci a babin Salla da Azumi, amma banda babin Zakka ko Hajji. Ko kuma zai iya yi a babin Aure, amma banda a babin Gado. A ta}aice dai, ba a dukkan babobin Fi}ihu zai iya istinba]i ba. To, tambaya a nan, shigen wannan Mujtahidi Mutajazziy, za a iya ta}lidi da shi? Fu}aha’u sun yi bayanin cewa, a babobin da yake iya fitarwa,za’a iya ta}lidi dashi.
To, ta yaya ake gane, ko sanin Mujtahidi? Ana sanin Mujtahidi ta hanyoyi guda uku: 1- Ko ta hanyar shaidar adilai guda biyu, wa]anda suke ma’abota ilimi da kuma gogayya; 2- Ko ta hanyar ya]uwar abin a tsakankanin ma’abota ilimi, wanda ta kai mutum ya samu ya}ini a kan haka; 3- Ko ta hanyar jarraba shi Mujtahidin. Wa]annan hanyoyi guda uku da ake sanin Mujtahidi da su, har ila yau sune ake bi domin sanin A’alam (Mafi sani) a tsakankanin Mujtahidai.
Wata mas’ala kuma ita ce, wa]anne hanyoyi ake bi domin sanin fatawar Mujtahidi? Hanyoyi guda uku ne: 1- Ko dai ta hanyar jin fatawar kai tsaye daga wajensa; 2- Ko ta hanyar na}altowa, ko ji daga adilai guda biyu, ko ma guda ]aya. Ba ma haka ba, Imam Khumaini ({S) ya ce, ko da daga mutum guda ]aya ne ya wadatar, in dai ana da si}a da kuma natsuwa da maganarsa; 3- Ko kuma ta hanyar komawa ga Risalah ]insu (wato littafin da Mujtahidin ya rubuta na fatawowinsa), amma da shara]in Risala ]in ta kasance amintacciya daga kurakurai.
2- MUHTA[: Muhta]i shi ne wanda ya wuce mataki na ta}lidi, amma kuma bai kai mataki na Ijtihadi ba, wato ba zai iya istinba]in hukunce-hukunce ba daga masadir da aka ambata a baya ba. Amma a lokaci guda kuma ya san fatawowin Mujtahidai daban-daban, da kuma inda suka sassa~a. To, a inda suka sassa~a ]in, shi Muhta]i zai yi aiki da abin da yake Ahwa]u, na fatawowin nasu. Misali, wani Mujtahidi ya ba da fatawar cewa aikata kaza haramun ne, wani Mujtahidin kuma ya ba da fatawar cewa aikata kazan ba haramun ba ne. To, a nan sai ya yi ihtiya]i na rashin aikata abu kazan. Ko kuma misali, wani Mujtahidi ya ce aikata kaza wajibi ne, wani Mujtahid ya ce aikata kazan mustahabbi ne. To, a nan sai Muhta]i ya yi ihtiya]i ya aikata abin.
Wata mas'ala kuma ita ce, ya halatta mutum ya yi aiki da Ihtiya]i ko da haka zai kai shi ga maimaita aiki. Misali, wani Mujtahidi ya yi fatawar cewa Sallar }asaru ga matafiyi, kilomita kaza, wani Mujtahidin kuma ya ce kaza. To, a nan sai mutum ya yi ihtiya]i tsakanin wa]annan fatawowin nasu guda biyu, ya yi Sallar }asaru ]in, kuma ya cika. Wato aiki guda ]aya, amma mutum ya maimaita shi sau biyu. To, yin haka ya halatta. Saboda haka zama a ajin Muhta]i yana da wahala, saboda na farko yana bu}atar mutum ya yi dogon bincike na fatawowin Fu}aha’u domin sanin inda suka sassa~a, don mutum ya yi aiki da Ahwa]u na fatawowin nasu. Na biyu kuma, yana bu}atuwar mutum wani lokaci ya maimaita aiki, kamar wancan misalin da aka bayar na }asaru da kuma cikawa.
Baya ga haka kuma, sanin wajajen Ihtiya]i ka]an ne suka sani. Saboda haka, da yawa daga cikin Malamai idan dai su ba Mujtahidai ba ne, sukan za~i zama cikin ajin Mu}allidai, domin ya fi sau}i. Akwai ma wanda ya tambayi Ayatullahi Khamene’i dangane da haka, ya ce wane ne ya fi, mutum ya yi aiki da Ihtiya]i ko da Ta}lidi (wato mutum ya zama Muhta]i ko Mu}allid)? Ga amsar da Ayatullahi Khamene’i ya ba shi: “Kasantuwar aiki da ihtiya]i ya dogara ne ga sanin wajajensa da kuma sanin kaifiyya ]in ihtiya]in, kuma wa]anda suka san haka ka]an ne. Kuma }ari ga haka, aiki da ihtiya]i yana bu}atuwa galibi ga cin lokaci (wato saboda wani lokaci akwai maimaiton aiki), saboda haka abin da ya fi shi ne yin Ta}lidi ga Mujtahidi, wanda ya cika sharu]]a.
A ta}aice dai, in mutum shi ba Mujtahidi ba ne, zamansa a ajin Mu}allidai ya fi. Bayan haka kuma, akwai wani nau'i na ihtiya]i wanda sanin sa da kuma fahimtar sa yana da gayar muhimmanci. Shi irin wannan ihtiya]i ya kasu kashi biyu: Akwai Ihtiya] Wujubiy; da kuma Ihtiya] Istihbabiy. Ihtiya] wujubiy shi ne ihtiya]in da wata fatawa ba ta gabace shi ba da ta sa~a masa ko kuma ta biyo bayansa ta sa~a masa. To, shi irin wannan ihtiya]i na wujubiy in mutum ya ci karo da shi a Risalah ]in Mujtahidin da yake ta}lidi da shi, abin da ya hau kansa shi ne ]ayan biyu: Ko dai ya yi aiki da shi; ko kuma ya koma ga wani Mujtahidin da yana da fatawa a kan mas’alar ba ihtiya]i ba. Amma ya kasance Mujtahidin da zai koma masa kan ita mas’ala ]in ya zamanto A’alam, wato mafi sani a tsakanin su Mujtahidan.
Shi kuma ihtiya] istihbabiy shi ne wanda wata fatawa ta gabace shi, amma ta sa~a masa ko kuma ta biyo bayansa ta sa~a masa. Ko kuma amfani da kalima ta Aulawiyyah, kamar Mujtahidi ya ce ‘wal-aulal-ahwa]’, kaza. To, a irin wa]annan wajaje guda uku na Ihtiya]i Istihbabiy, mutum na da za~in ko dai ya aikata ihtiya]in ko kuma ya bar shi, wato ba dole ba ne mutum ya aikata shi. Sai dai in ya aikata haka ]in ya fi. Domin dai }arin bayani, mutum na iya duba littafin Tahriril Wasila ko Zubdah.
A mas’ala ta }arshe a babin Ijtihadi da Ta}lidi zai ga yadda Imam Khumain ({S) ya yi bayanin shi wannan Ihtiya] wujubiy da kuma Istihbabiy. Kuma kamar yadda aka ambata a baya cewa fahimtarsa yana da gayar muhimmanci, domin zai yi wahala ka samu babi daga cikin babobin Fi}ihu tun daga farkonsa har }arshensa a ce mutum bai ci karo da irin wannan Ihtiya]i ba na wujubi da kuma istihbabi, musamman ma ga masu ta}lidi da Imam Khumaini ({S). A Risalah ]insu akwai ihtiya]i fiye da sauran Risaloli na wasu Mujtahidai.
3- MU{ALLID: Mu}allidi shi ne wanda yake ta}lidi da ]aya daga cikin Mujtahidai. Ta}lidi kuma shi ne aiki wanda aka jingina shi ga fatawar Fa}ihi ayyananne. Saboda haka, idan mutum yana Imamiyyah, to wajibi ne a kansa, ba wai mustahabbi ba. A ibadodinsa da kuma mu'amalolinsa da suka shafi ~angaren Fi}ihu, ya zamanto akwai Mujtahid da yake bi a kai. In kuwa ba haka ba, ayyukansa ~atattu ne, kamar dai yadda Imam Khumaini ({S) da kuma sauran Mujtahidai suka yi bayani. Alal misali, mutum na iya duba littafin Tahriril Wasilah a babin Ijtihadi da Ta}lidi a mas’ala ta 24. Imam Khumaini ({S) yana cewa: “Idan mutum ya san cewa ya kasance a cikin ibadodinsa ya yi su ba tare da ta}lidi ba (wato bin wani Mujtahidi) a wata mudda ta zamani, amma bai san gwargwadon muddar zamanin ba, to in ya san abin da ya yi ba a kan ta}lidi ]in ba (misali Salla ko Azumi) da kuma muwafa}ar abin da ya yi a baya ga fatawar Mujtahidin da yake ta}lidi da shi a yanzu. To, in an samu wannan muwafa}a, to shi bai da matsala. In kuwa ba a samu wannan muwafa}a ba, to sai ya rama ayyukansa na baya.”
Saboda haka, in muka duba za mu ga abin na da ha]ari sosai, domin shi Fi}ihun Imamiyyah ba kamar Fi}ihun Ahlus Sunna ba ne cewa, in ka ga dama za ka iya zama ba ka bin Mazhaba, wato ba ka Malikiyyah ko Shafi'iyyah ko Hambaliyyah ko Hanafiyyah. Ko kuma in ka ga dama ka yi yawo tsakankanin Mazhabobi, wato in a wata mas’ala ka ji Malikiyyah ta yi maka zafi sai ka koma Shafi’iyya ko Hanafiyya.
To, a Imamiyyah ba haka ba ne, dole ga mutum idan dai shi ba Mujtahidi ba ne ko Muhta]i, ya zamo akwai Mujtahidin da yake ta}lidi da shi. Saboda haka, wannan yana da muhimmanci gare mu da yaranmu da suka taso, suka kai matsayi na taklifi, wato irshadinsu ga ita wannan mas’ala. Alal misali, akwai wanda ya tambayi Ayatullahi Khamene’i, ya ce, yarinyarsa za ta kai shekaru na taklifi nan da wani lokaci, to a lokacin zai zama wajibi a kanta ta za~i Mujtahidin da za ta yi ta}lid da shi. To, kasantuwar sani da fahimtar haka yana da wahala a wajenta, a taimaka mani da bayanin abin da ya wajaba in yi? Ga amsar da Ayatullahi Khamene’i ya ba shi: “Idan ita a }ashin kanta tunaninta bai kai ga haka na abin da ya hau kanta a Shari’a dangane da wannan al’amari ba, to abin da ya hau kanka shi ne ka sanar da ita da kuma irshadantar da ita a kai.”
Wani kuma ya tambaye shi cewa: “Wasu mutane in muka tambaye su wanda suke ta}lidi da shi, amsarsu ita ce ba mu sani ba, ko kuma su ce muna ta}lidi da Marji'i wane, amma kuma a lokaci guda ba su ganin kawukansu cewa lazim (dole) ne su koma ga Risalah ]insa domin su yi aiki da ita. To, meye hukuncin aikinsu? Ga amsar da Ayatullahi Khamene’i ya bayar: “Idan ayyukansu sun yi muwafa}a da ihtiya]i, ko suka dace da daidai, ko suka yi muwafa}a da Mujtahidin da suke bi, to ayyukansu sun inganta.”
Wani kuma ya tambaye shi, shin ya halatta mutum ya yi ta}lidi da Mujtahidin da bai rubuta Risalah Amaliyyah ba? Ya ba shi amsa da cewa: “In dai ta tabbata ga shi mukallafi cewa Mujtahidi ne wanda ya cika sharu]]a, to ba matsala a haka”.
Wani kuma ya tambaye shi, shin ya halatta ta}lidi da Mujtahidai na wasu garuruwa ko }asashe, ko da a ce ko mutum bai iya ha]uwa da su? Ga amsar da ya bayar: “Ta}lidi a mas’aloli na Shari’a ga Mujtahidin da ya cika sharu]]a, ba a shar]anta cewa dole ne Mujtahidin ya zamo a garin da mutum yake ba.”
Wata mas’ala kuma ita ce, ya halatta wa mutum ya yi canji daga wannan Mujtahidin da yake raye zuwa ga wani Mujtahidi da shi ma yake a raye, amma da shara]in su zamo daidai a ilimi. In kuwa ]ayan ya fi shi, to wajibi ne komawa gare shi, amma a bisa ihtiya]i wujubiy, kamar dai yadda Imam Khumaini ({S) ya yi bayani. Haka nan idan su Mujtahidan iliminsu ]aya, to mutum ya samu ya ]auki sashen wasu fatawowi daga wannan, wani sashen kuma daga wannan. Misali, a ibadodi yana bin fatawowin wannan, a kuma mu'amaloli yana bin fatawowin wannan.
Haka nan idan mutum na ta}lid da wani Mujtahidi, sai Allah (T) ya yi masa rasuwa, to yana iya komawa ga wani Mujtahidin da yake a raye, amma tare da kiyaye A’alam. Da dai sauran mas’aloli da suke da ala}a da ta}lid da Mujtahidai suka fitar a littaffan Risalolinsu, wanda ba za a iya kawo ba saboda gudun tsawaitawa. Ga mai bu}ata yana iya komawa ga Risalar Mujtahidin da yake wa ta}lidi domin }arin bayani.
Sai ]an bayani dangane da mas’alar Adala, wato takan zo jefi-jefi a wasu babobin Fi}ihu, musammman ma wajen ba da shaida kamar wanda aka ambata a baya na cewa, ]aya daga cikin hanyoyin sanin Mujtahidi ita ce shaidar Adilai guda biyu. Ko kuma misali shaidar Adilai a wajen ganin wata, ko shaida a wajen sakin aure, da dai misalan irin su, wanda akan shar]anta Adala ga masu shaidar.
To, Adala ita ce, ko na nufin wata siffa wadda take tabbatacciya ga mutum, wadda ta zamar masa malaka, wato jini da tsoka ko jiki, wadda ta kai ga tana tunku]a shi ga lizimtar ta}awa ta hanyar nisantar abubuwan da aka haramta da kuma aikata abubuwan da aka wajabta masa. Kuma hukuncin Adala na iya gushewa idan mutum ya aikata manyan laifuffuka ko kuma ya dage a kan aikata }ananan laifuffuka.
Amma idan mutum ya tuba hukuncin Adala ]in zai iya dawowa gare shi, wato wannan dai ya nuna bambancin Adala ko ta}awa, da kuma ‘Ismah’. Wato mutum na iya zama Adili ko mai ta}awa a wani lokaci, wani lokaci kuma sakamakon ayyukan da ya aikata marasa kyau, sai ta}awar ko Adalar ta gushe. Amma ita ‘Ismah’ ta Ma’asumi ba ta gushewa, wato ko da wane lokaci tana nan tare da shi.
Wannan ke nan dai baki ]aya a ta}aice dangane da kammalawa na ita wannan shimfi]a da kuma gabatarwa a wannan darasi na Fi}ihu. A darasi na gaba insha Allah za a shiga Kitabut Tahara.
Kasantuwar a Fi}ihu na Ahlus Sunna }ofar Ijtihadi a kulle take wajen su, shi ya sa abubuwa da yawa a wannan zamani na Masa'ilul Mustahadasa babu su a littaffansu na Fi}ihu, saboda haka ba su da fatawa a kai. Amma ko a Fi}ihun Imamiyyah abin ba haka yake ba, Fi}ihu ne mai rai, wanda ya ba da amsa, yake kuma ba da amsa ga dukkan sabbabbin abubuwa na zamani. Misali, mutum na iya duba littafi na Tahriril Wasilah na Imam Khumaini ({S) (juz'i na biyu), }arshensa, Imam ya fitar da babi wanda yake bayani dangane da hukunce-hukunce na sababbin abubuwa na zamani, wanda in mutum ya duba babin zai ga cewa duk da ci gaban wannan zamani, wasu fatawowi da Imam ya fitar ci gaban zamanin bai kawo nan ba. Amma ga amsoshinsu da Imam Khumaini ({S) ya bayar. Shi ya sa a Fi}ihance a wannan zamani namu, Fi}ihun Imamiyyah ne kawai zai iya tafi da shi, domin shi yana da amsa ga dukkan abubuwa na zamanin.
Akwai ma Malamai na Imamiyyah a wannan zamani da suka rubuta littafan Fi}ihu khususan kan Masa'ilul Mustahadasa. Alal misali, littafin Masa'ilul Mustahadasa na Sayyid Muhammad Sadi} Rauhaniyyah, da dai sauran wasu da fu}aha’u suka rubuta.

No comments:

Post a Comment