Saturday 9 February 2013

TARIHI DA KUMA DARUSSA DAGA RAYUWAR SAYYIDA ZAINAB [AS].


Rubutu ko bayani dangane da sayyida Zainab[AS] fage ne mai fa]in gaske.Kuma Malamai da dama sun rubuta littafai,game da tarihinta da kuma rayuwar ta,misalin wasu daga cikin littafan sune,Zainabul-Kubra na shaikh Ja’afar Najdiy.kasa-isus-zainabiyya na sayyid Nurud-din.
Zainabul-kubra minal mahdi-ila-lahadi.na sayyid Muhammad khazim.da dai sauran littafai masu yawa da malamai suka rubuta dangane da ita.Sayyida Zainab[as] an haife tane a Madina,5 ga watan jimadal-ula,shekara ta biyar bayan hijira.Akwai wasu zantuka akasin haka,amma dai wannan shi yafi shahara.Bayan da aka haife ta,aka je aka shaida ma Manzon Allah[s] nan take yazo wannan gida mai albarka na sayyida fa]ima [as]yace akawo masa ita,lokacin daya ]auke ta sai aka ga yayi kuka,kuka mai yawa,wanda har sai da hawayen sa suka zuba a kumatun sa masu al-barka.Sayyida Fa]ima tace wannan kukan fa?sai Manzon Allah yace mata “Lallai wannan yarin ya, za a jarrabe ta da jarabawowi kuma musibobi masu yawa zasu same ta d a kuma tsanan ce-tsanan ce,duk wanda yayi kuka saboda ita da kuma musibobin da suka same ta,to yana da lada ,kamar ladar wanda yayi kuka ga ‘yan uwanta”[wato Imam Hassan da Husain[as].kuma wannan suna nata Zainab saukakke daga sama,wato Allah[T]ne yayo wahayi ta hanyar malaika Jibril,cewa ya fa]a ma Manzon Allah a  sa mata suna zainab. Lokacin da Malaika Jibril ya isar da wannan sako,na sunan ta sai da yayi kuka.Manzon Allah ya tambaye shi miyasa yake kuka?Sai yace “Rayuwar wannan ya rinya zai kasance tare da musibobi da wahalhalu,tun daga farkon rayuwar ta har ya zuwa wafatin ta.”Haka nan anai mata la}abi da A}ila da kuma ummi Akiha,wato shigen la}abi na sayyida Fa]ima na ummi Abiha.          
                Sayyida Zainab[as] kamar yadda aka sani,mahaifin ta Imam Ali[as] mahaifiyar ta kuma Sayyida Fadima [as] itace ta ukku ga mahaifan ta,wata daga Imam Hassan,Imam Husain[as] sai ita,bayan ta kuma sai ummu-khul-sum,sai kuma Muhsin wanda Sayyida fadima[as] tayi ~ar insa,sakamakon hujumi da akayi ma gidanta.Sayyida Zainab[AS] ta rayu tare da kakan ta,Manzon Allah[S] da kuma mahaifiyar ta kimanin shekaru shidda.Tare kuma da mahaifin ta kusan shekaru 35,Tare kuma da ]an uwan ta Imam Hassan kusan shekaru 45.Ta kuma rayu tare da ]an uwanta Imam Husain kusan shekaru 5.Anan in mutum yayi tunani akan cewa,Sayyida Zainab ko da ace a rayuwar ta bata fuskanci wata jarabawa ba face ganin  wafatin As-habul kisa’a ]aya bayan ]aya.To wannan ka]ai ya isa ya  zama jarrabawa babba gar eta.Misali taga wafatin Manzon Allah[S],taga wafatin sayyida Fa]ima[AS],taga shahadar Imam Ali[AS],taga wafatin Imam Hassan[AS]taga shahadar Imam Husain[AS] Akwai  ma wani mafarki da Sayyida Zainab[AS] tayi,tun tana }arama,sai ta fa]a ma Manzon Allah mafarkin,da Manzon Allah yaji sai da yayi kuka.Mafarkin shine “Taga iska da guguwa sun taso wadda tasa duniya tai duhu,kuma iskar ta dunga ka]ani  daga wannan ~angaren zuwa wancan,sai naga wata itaciya mai girma sai na ri}e ta,saboda tsananin iska,sai iska ta tun~uke itaciyar.sai na ri}e wani reshe mai }arfi na itaciyar,sai ya karye,na rike wani reshen shima ya karye,na sake ri}e wani shima ya karye,bayan haka sai na farka daga barci,da Manzon Allah yaji wannan mafarki nata sai yai kuka yace mata,itaciyar da kika ri}e nine,Reshen farko da kika kama mahaifiyar ki,reshe na biyu mahaifin ki,reshe na ukku dan uwanki Hassan,reshe na hu]u ]an uwanki Husain.Duniya zatayi ba}i saboda rashin su. ”Wato wannan mafarki kinaya  na wafatin su ]aya bayan ]aya gareta.Saboda haka Sayyida Zainab ta Tashi gidan Nubuwwa da kuma Imaman ci,waton gaban Manzon Allah da kuma Imam Ali.Yama zo a tarin ta cewa,tun tana }arama wato a shekaru., Manzon Allah yak an zauna da ita,ya  karantar da ita,Haka nan ma Imam Ali ya kasance shima yana yi mata haka,Saboda haka a fagen ilimi ta kai mustawa- aliya.                                                                                                                                                                                                                                                    Sayyida Zainab ta zauna gaban mahaifin ta,har ya zuwa lokacin auren ta,wanda ta aura shine Abdullahi ]an Jaafar ]an Abi ]alib.Sunan mahaifiyar Abdullahi ]an Jaafar,Asmau ‘yar Umais,kuma an haife shine a Habasha,lokacin da mahaifin sa yake gudun hijira acan.SayyidaZainab tana da ‘ya’ya biyar sune,Ali,Aun,Muhammad,Abbas da kuma ummu khul-sum.biyu daga cikin su sunyi shahada a wa}iar karbala.sune,Muhammad da Aun.Sai kuma mijin ‘yar ta wato ummu khulsum,shima a wa}iar karbala yayi shahada,Sunan sa {asim ]an Muhammad ]an Jaafar. Sayyida Zainab ta zauna a gidan mijin ta har ya zuwa lokacin da Imam Husain zai bar Madina zuwa karbala,A lokacin ta koma gidan Imam Husain da zama,wato kafin fitarsa.Kuma yazo a tarinhin ta cewa,Lokacin auren ta da Abdullahi ]an Jaafar,Imam Ali ya gindaya wani shara]i Shine cewa,ya bata iznin fita zuwa karbala,tare da Imam Husain.Haka ko akayi da wannan lokaci yazo,ya bata wannan izni,bayan haka yace ma ‘ya’yan sa suma su fita domin su taimaka ma Imam Husain .yazo a tarihin sa shi a lokacin bai da lafiya shiyasa bai fita ba.Bayan da ta koma gidan Imam Husain kafin fitar sa,Abdullahi ]an Abbas, yazo ya same shi akan kada ya fita,Imam Husain, ya shaida masa cewa wannan wani abune wanda ba makawa,Abdullahi ]an Abbas yace tun da ba makawa akan fitar,to kada ya fita da iyalinsa dakuma mata.Imam Husain yace masa ya kai ]an Ammina,nayi mafarki da Manzon Allah cewa in fita tare dasu,to a lokacin da suke wannan tattau nawa,Sayyida Zainab tana jinsu,sai ta fashe da kuka tace,ya ]an Abbas yanzu kana bada shawara ga shuganmu cewa mu ya barmu, ya tafi shi ka ]ai,tace wallahi haka ba zai yiyu ba,zamu rayu tare da shi mu mutu tare das hi,yanzu a wannan zamanin muna da wanda ya kais hi.”jin haka Abdullahi]an Abbas ya fashe da kuka.Kuma wani abin lura muhimmi a nan shine,ala}ar sayyida Zainab da Imam Husain,wato akwai ala}a ta musammam,kuma tun tasowar su suna yara haka abun yake,Akwai ma lokacin da Sayyida Fa]ima ta lura da haka,cewa duk in da Imam Husain ya zauna sai Zainab ta zauna wajen,ta shaida ma Manzon Allah,wannan abu da ta lura das hi,,jin haka sai Manzon Allah yayi kuka,yayi mata bayanin irin musibobi da wahal-halu da Zainab zata fuskanta,da kuma yadda zata yi musharaka da Imam Husain wajen wahal-halu da zai fuskan ta.
Saboda haka Imam Husain ya bar madina tare da iyalin sa da kuma su Sayyida Zainab zuwa karbala,da yake wannan rubutu ne,na tarihi da kuma rayuwar sayyid Zainab duk abubuwan da za a kawo, na wannan wa}ia ta karbala zai kasance ne wa]anda suke da ala}a da ita ne kai tsaye.Saboda haka yana da muhimmanci mutum yasan abubuwan da suka faru ga Sayyida Zainab tun daga fitar ta madina tare da Imam Husain har ya zuwa dawowar ta madina,domin tsakanin fitar da dawowar kimanin watanni bakwai ne,wannan a dun}ule kenan,amma a warware,mutum yasan abun day a faru gar eta,a karbala, a kufa, a sham,da kuma abubuwan da suka faru a hanya daga karbala zuwa kufa daga kufa zuwa sham daga sham zuwa madina.A shekarar da ta gabata a irin wannan munasaba ta Ashura,anyi rubutu mai taken,GUDUNMAWAR MATA A WA}I’AR KARBALA an ]an yi bayani kan wadannan ~angarori da aka ambata a ta}aice.Wato na jarabawowin da Zainab ta fuskanta,tun daga fita madina zuwa dawowa madina,Kuma mutum yayi tunani a ransa bayan da wowarta madina ba tare da Imam Husain ba,ba wane,ba wane,ba wane.Hatta ita kanta ‘ya’yanta biyu aka kasha.Yazo a tarihinta cewa da suka iso madina,inda sayyida Zainab ta fara zuwa shine Masallacin Manzon Allah.Da ta isa masallacin ta dafa }ofar masallacin tace; “Ya kakana,ina yi maka ta’aziyyar ]an uwana Husain.”Saannan ta fashe da kuka.Bayan haka ta wuce gida.Bayan isar ta gida matayen madina suka cika gidan ta.Shine sayyida Zainab tayi masu bayani sanka-sanka abubuwan da suka faru a karbala a kufa da kuma sham,matayen su kai ta kuka.Da suka koma gidajensu suka fa]a ma mazajensu abubuwan da suka faru,wato kamar yadda Zainab tayi masu bayani,]an lokaci ka]an labara ya cika birnin Manzon Allah,akan asasin haka da yawa sukayi wa Yazidu tawaye.Shi yasa wannan yana ]aya daga cikin hikima da asrar na tafiya da mata da Imam Husain yayi zuwa karbala,wato saboda Tablig ]in wannan wakiar ,ga sauran mutane bayan shahadar su.kuma abun da ya faru kenan,domin ita wannan wa}ia ta karbala,duka abubuwan da akeji ko ake karantawa a littafai na abubuwan da suka faru,daga wajen su Sayyida Zainab aka ji.Domin duka mazaje an kasha in banda Imam Zainul-Abidin,shima dun bayada lafiya ne,duk da haka ma sunyi niyyar kashe shi, Allah yak are shi.Kuma ma mutum yayi tunani da ba wadannan mataye a karbala,Yaya za a san ha}i}anin abun daya faru a karbala,zai kasance ken an ta ~angare ]aya  za aji,wato ta ~angaren ma}iya,da suka yi wannan aikaka.Sayyida Zainab ta cigaba da zama madina har ya zuwa lokacin da Gwamnan Yazid na madina ya aika masa da cewa,in yana da bu}atar madina,to ya kori Zainab daga cikin ta,shine ya aiko da sa}o cewa a fitar da Zainab daga madina,mu duba mu gani birnin kakanta,da suka ]auki matakina fitar da ita Sayyida Zainab tace ba inda zata je.Shine wasu mataye daga cikin Bani Hashim suka same ta suka bata shawar  akan tabar madina,suka ce Yazidu zai iya yin kome,akan haka yana iya maimaita wata karbala a nan.kuma su baza su yarda ace za azo a fitar da ita da }arfi ba  su }yale,sai duk abinda zai faru ya faru.Saboda haka sai Zainab ta yanke shawar ta bar madina ta koma misira da zama.Haka dai Sayyida Zainab ta ci gaba da rayuwa a irin wannan yanayi na jarabawowi dabab-dabam daga azzalumai masu tafi da iko,har ya zuwa rasuwar ta.Ta rasu ranar Lahadi 15 ga watan Rajab,shekara ta 62 a wata ruwaya 65 bayan hijira.Wato ta rayu kusan shekaru 60 ke nan a duniya.Kuma akwai sa~ani tsakanin malaman tarihi na ainihin inda }abarin ta yake,akwai zantuka ukku akai,wa]ansu sun ce a misira yake,wasu kuma suka ce a madina,wasu kuma suka ce a Sham ne,wannan shine wanda mabiya Ahlul Bait suka tafi a kai.Idan mutum yayi tunani zai ga haka zai iya yiwuwa,domin a Sali  an tilas ta mata barin madina  saboda yadda take bayyana ma mutane abubuwan da suka faru a karbala,wanda ya kai ga da yawa mutanen madina su kayi ma Yazidu  tawaye,tayi hijira ta koma misira,to ba mamaki makaman cin haka ya faru a misira,ganin haka Yazidu yasa a dawo da ita Sham,tun da alokacin nan fadar mulkin sa yake.Wannan kenan dai a takaice,sai kuma abunda ya shafi wasu ~angarori na rayuwar ta,da nufin su kasance Darussa garemu .
1-IBADARTA;Sayyida Zainab ta kasance mai yawan ibada,yama zo a tarihin ta cewa a ibada,baya ga Sayyida Fa]ima ba wadda ta kai ta.Haka nan yazo akan cewa bata ta~a fashin sallar Tahajjud ba,har ranar Ashura da daddare wato daren 11,Imam Zainul Abidin yace ya ganta tana sallar tahajjud a zaune.Domin a daren Ashura an ce ta raya shi baki ]aya da ibada,ba tayi bacci ba acikin sa,Aranar ashura kuma ga abubuwan da suka faru,amma duk da haka sai da tayi sallar tahajjud a daren,shine har Imam Zainul Abidin yake tambayar ta dalilin yin sallar ta a zaune tace masa; “Wallahi }afafuwana basu iya ]auka ta”wato saboda gajiya da yunwa da kuma }ishi.Kuma yazo akan cewa }arshen abinda Imam Husain yace mata da yake bankwana da ita a ranar Ashura,shine yace mata; “Ya ‘yar uwata kada ki manta dani a sallar dare”A ta}aice dai Sayyid Zainab ta kasance mafi yawan dararenta bata barci takan raya sune dasalloli da kuma karatun Al-}ur’ani.Haka nan nafilfili na salloli wajibai ta kasance madawwamiya akai,wato basu ku~uce mata,Imam Zainul Abidin yana cewa; “Duk da irin wahal halu da kuma jarabawowin da suka fuskan ta a tafiyar su daga kufa zuwa sham,yaga Sayyida Zainab duka nafifilin ta  na dare tana yin su”Saboda haka yana da gayar muhimman ci garemu tsayuwa da wa]]anan nafilfili musammam ma sallar tahajjud.ya kasance bata ku~uce ma mutum,ko dama mutum bai samu yinta da daddare ba, to ya rama ta acikin yini,kamar dai yadda yazo a hadis.Yazo a tarihin Imam khumaini cewa ya shekara saba’in bai ta~a fashin sallar tahajjud ba,Haka nan Sayyida Zainab ta kasance mai yawan Azkar da  Addu’oi,kamar yadda Fa]ima ‘yar  Imam Husain ta fa]i.
2-ILIMIN TA;Kamar yadda aka ambata a baya a wannan fage na ilimi Sayyida Zainab ta kai mustawa-aliya.Yazo a tarihin ta cewa lokacin da Imam Ali yake kufa da zama,ita take karantar da mata,musammam ma ~angaren Tafsirin Al-}ur-ani.Lokacin da Imam Ali yake kufa Akwai wa]anda suka same shi,suka ce masa,suna neman izni,ya bada dammar matayen su,su dunga zuwa wajen ‘yar sa domin sanin hukunce-hukuncen addini da kuma Tafsirin Al-}ur-ani.Akwai ma lokacin da Imam Ali ya shigo cikin gida sai yaji Sayyida Zainab tana tafsirin Suratul Maryam gasu matayen,tana yi masu bayanin ba}a}en farko na surar,bayan da suka tashi shine Imam Ali yake ce mata, wa]annan haruffa ishara ne na abinda zai same ki da ]an uwanki a karbala,kuma in mutum ma ya bibiyi jawaban da tayi a fadar ibn Ziyad[LA] a kufa da kuma fadar Yazidu[LA] a sham,zai ga yadda suke cike  da balaga da kuma fasaha.Kuma yazo akan cewa tana da Niyaba-kassa,ga Imam Husain bayan shahadar sa,wato mutane sun koma gareta  ga sanin hukunce-hukunce na addini,har ya zuwa lokacin da Imam Zainul Abidin ya warke.wanda wannan yana nuna zuzzurfan ilimin da take dashi na addinin musulunci.
 3-AKLA{-[INTA;-Shima a wannan fage ta kai matsayi ma]aukaki a cikin sa,Ta kasance mai yawan kyauta,wuce nan ma ta kasance mai fifita wasu  akan ta,yazo a tarihin ta cewa  tafiyar da akayi dasu daga kufa zuwa sham,abinci sau ]aya ake basu ko wace rana,to a haka Sayyida Zainab in an bata nata,take }a}}ara masu, ita kuma ta ha}ura.akwai lokacin da aka ganta tana  sallah zaune a tafiyar, aka tambaye ta kan haka,; “Tace ina sallah zauna ne saboda tsananin yunwa,da nike ji tun kwana ukku”wato saboda yadda take bada nata kason,kuma Sayyida Zainab ba wai ga abinci kawai take fifita wani akanta ba,A’a yazo akan cewa ko bulala za a fya]a ma wani cikin wa]anda suka yi wannan tafiya dasu,ta kan kare da jikin sa,wato dukan ya sauka a jikin ta.dun yazo  a tarihi cewa  duk wanda yayi kuka cikin yara ko manya daga cikin wa]annan bayin Allah,sai wa]annan azzaluman su kai mai duka.Baya ga haka kuma akwai lokacin da suka yi nufin kashe Imam Zainul Abidin,tace sai dai a fara kashe ta.da dai misalai masu yawa irin wa]annan da suka zo a tarihin ta.Haka nan daga cikin ]abio’in Sayyida Zainab ta kasance mai yawan dauriya.Shima wannan akwai misalai da yawa akai.mu duba yadda take dauriya ga yunwa da kuma }ishi,mu duba kuma duk da abubuwan da suka faru a karbala da kuma abinda ya biyo baya,amma ta kasance a fadar ibn Ziyad da kuma Yazidu ko gyazau.mu kuma duba isgili dabam-dabam  da maganganu marasa da]in ji da sukayi masu,amma duk da haka ta daure.wannan darasi ne babba  garemu.
4-ZUHUDIN TA;Shima a wannan fage na gudun duniya da kuma tarka centa,Sayyida Zainab ta kai mustawa aliya,Idan mutum ya bibiyi tarihin ta zai ga haka.wato duniya da abun duniya basu da tasiri a zuciyar ta, duk da irin gidan auren da ta zauna,domin mijin ta Abdullahi ]an Jaafar ya kasance yana da dukiya mai yawa.wato mai ku]i ne,yama zo a tarihin sa cewa akwai wanda ya ta~a zuwa wajen sa ya ranci dirhami miliyan ]aya.mu duba a wancan lokacin mafa kenan,Asalin yawan wannan dukiya tashi,shine albarkacin addu’a da Manzon Allah yayi masa tun yana }arami,wata rana manzon Allah ya gan shi yana was an }asa,ya kwa~a }asar  yana gina gida,wato shigen yadda yara sukeyi,shine Manzon Allah ya dube shi yace ya Allah  ka azurta shi ka yalwa ta masa.Saboda haka Sayyida Zainab ta kasance a gidan dukiya ne amma duk da haka ta rayu rayuwar ta gudun duniya.
 5-JARABAWOWIN TA;Sayyida Zainab ta fuskanci jarabawowi masu yawa a tarihin rayuwar ta,mu duba yadda taga wafatin As-habul kisa’a ]aya bayan ]aya,da kuma irin jarabawar da kowannen su,ya fuskanta na matsaloli a }arshen rayuwarsa.misali hujumi gidan mahaifiyar ta da abun da aka yima ta lokacin hujumin.kashe Imam Ali.sama Imam Hassan guba,kashe Imam Husain,duk wa]annan abubuwa da aka ambata dama wa]anda ba a ambata ba a gaban idon ta suka guda na.Saannan kuma ga jarabawowi da ta fuskanta a wa}i’ar karbala bayan shahadar su Imamu Husain,wani abin lura da kuma tunani shine lokacin da akayi wannan wa}i’a ta karbala tana matsayin dattijuwa ne, tun da  a lokacin tana da kusan shekaru 60 ne a duniya,Amma mu duba saboda bushewar zuciya da kuma rashin kunya,irin nasu Yazidu da kuma ibn Ziyad lokacin da aka kai su fadar su, maganganun da suka yi mata.wanda a Haifa ta haife su.tun da a lokacin yazid ]in da ibn ziyad ba wanda ya kai shekaru 40.Saannan kuma mu duba jarabawowin data fuskan ta bayan dawowar su madina,mahaifar ta kuma barnin kakan ta,Manzon Allah, amma tana ji tana gani aka fitar da ita daga madina,wato akasa ta hijirar dole.Haka ta rasu a mahijir ta,Saboda haka rayuwar Sayyida Zainab tun daga farkon ta har }arshen ta cike da jarabawowi.Amma jarabawowin data fuskanta }arshen rayuwar ta su suka fi tsanani,wato na wa}i’ar karbala da kuma abinda ya biyo baya.Saboda tsakanin waki’ar karbala da kuma wafatin ta,kusan shekara ]aya da rabi ne,a wani zancen kuma kusan shekaru biyar.Shi yasa sanin irin jarabawowin data fuskanta a karbala,da kufa da kuma sham yana da muhimman ci,ga wasu misalai daga cikin ko wannen su.1-A karbala,ko da ace wani abu bai biyo, bayan wa}i’ar karbala ba,kasantuwar sayyida Zainab a gabanta aka kasha wa]annan bayin Allah ]aya bayan ]aya,domin a ranar babu wani gida daga cikin gidaje na bani Hashim,wanda ba a kasha wasu ko wani a gidan ba.alal misali gidan Imam Ali,Imam Hassan, Imam Husain,gidan Jaafar,gidan A}il dama ita kanta gidan Sayyida Zainab.Kuma mu duba gabanin shahadar wa]annan bayin Allah yadda su Sayyida Zainab tare dasu suka kasance ba ruwa ba abinci,kuma yara na wa]annan bayin Allah ko wannen su sai tambayar Sayyida Zainab yake ruwa,wanda haka yai mata }unci a zuciya,kuma mu duba irin ala}ar t a da Imam Husin tun  tana }arama,yau gashi a gaban ta, a kayi masa irin wannan kisa.Yama zo akan cewa lokacin da aka kashe kowa,wato cikin mazaje ya zaman to sai Imam Husain kawai,bayan yayi bankwana da iyalin sa da kuma su Sayyida Zainab aka ce ya duba dama ya duba hagu,yace wa zai kawo man dokina,jin haka Sayyida Zainab taje ta kawo dokin.Asalin wannan dokin na Manzon Allah ne,amma mu duba iko na Allah ya rayu sama da shekaru 50 bayan wafatin Manzon Allah.Bayan Imam Husain ya fita fagen daga,bayan wani lokaci sai ga doki ya dawo wajen su Zainab ba Imam Husain Inna lillahi wa-inna-ilaihi-rajiun,saboda haka Sayyida Zainab da sauran mataye da yara,suka fito daga cikin hemomin su suna kuka suna fa]in,´Wa Muhammadah,Wa Aliyya,Wa Fa]imah,Wa Hasanah,Wa Husainah.Insha Allah wani lokaci za a ]ora a kai.                   

No comments:

Post a Comment