Saturday 9 February 2013

Bankwana da watan Ramadan


Inna Lillahi Wa Inna Ilahi Raji’un! Na rabuwa da kuma tafiyar wannan babban ba}o mai girma da kuma daraja da ya ba}unce mu, wato watan Ramadan. Wannan wata na Ramadan, wata ne wanda gabanin zuwan sa bayin Allah (T) ke shau}insa (begensa) da kuma murna da farin ciki.
Don haka nan idan watan ya zo }arshe sukan kasance cikin damuwa da ba}in ciki dama yin kuka saboda zafin rabuwa da shi, wato saboda falaloli da kuma darajoji da ke cikin watan, da kuma irin zau}iyyat da halawat da kuma ma’anawiyyat na ibadodi da suke samu a cikin watan. Shi ya sa in muka duba kamar yadda aka ]an yi bayani a shekarar da ta gabata na bankwana da watan Ramadan.
Za mu ga cewa a duk watanni 12 da ake da su na Musulunci, babu wani wata wanda aka samu ruwayoyi daga Manzon Allah (S) da kuma A’imma na Ahlul Bait (AS) na bankwana da shi da kuma umarnin yin haka face watan Ramadan, wanda wannan ka]ai ya isa ya nuna falala da kuma darajar watan Ramadan. Wadannan ruwayoyi ko addu’o’i na bankwana da watan Ramadan, akwai wa]anda aka samu daga Manzon Allah (S), akwai kuma wa]anda aka samu daga Imam Sadi} (AS) da kuma Imam Ali Zainul Abidin (AS). Ga mai bu}atar ganin wa]annan addu’o’i yana iya duba littafan I}bal na Sayyid Ibn [awus. Kuma in son samu ne mutum ya karanta addu’o’i bankwan ]in dukkansu, wato wa]anda aka ruwaito daga Manzon Allah (S) da kuma Imam Sadi} (AS) da Imam Zainul Abidin (AS) in yana da iko a kan haka, in bai da ikon yin haka, sai ya karanta abin da ya sau}a}a masa. To tambaya a nan ita ce, wane lokaci ake biya wannan addu’o’i ta bankwana da watan Ramadan? Daren }arshe ne ko ranar }arshe na watan? An yi irin wannan tambaya ga ]aya daga cikin A’imma na Ahlul Baiti (AS). Amsar da ya bayar ita ce cewa daren }arshe na watan Ramadan ake son biya addu’ar bankwana. Har ma ya }ara da cewa idan ana tsoran watan zai yi nu}usani ne, sai a biya a dararen guda biyu, wato daren 29 da kuma daren 30. Wannan a kan asasin abin da aka fi so ke nan, amma misali da a ce mutum bai samu biyawa ba a }arshen daren watan Ramadan. To yana iya biyawa a ranar }arshe na watan ko a daren Idi ko ranar Idi.
Baya ga wa]annan addu’o’i na bankwana daga aka samo daga Ma’asumai (AS). Akwai wasu ladubba ko ayyuka da Malaman Irfan suka yi bayani, wa]anda ake son mutum shi a }ashin kansa ya aikata a ranar }arshe ta watan Ramadan ko bayansa.
Ga biyar daga ciki:- 1- Godiya ga Allah (T) ga wannan babbar ni’ima da ya yi masa, na nuna masa farkon watan Ramadan, kuma ya nuna masa }arshensa. Domin in mutum ya yi tunani zai ga akwai masu mutune da yawa wa]anda ba su samu wannan ni’imar ba. Wato Allah (T) bai raya su, ya nuna masu watan ba. Ko kuma wasu Allah (T) ya nuna masu farkon watan amma ba su ga }arshensa ba. Saboda wannan ni’ima da Allah (T) ya yi wa mutum, sai ya gode masa ta hanyar sujudu-shukur ko salatu-shukur. Wato sujudar godiya ko Sallar ta godiya. Haka nan ya gode mwa Allah (T) na muwafa}a da ya yi masa na ayyuka na ibadodi da ya ni’imata shi, kuma ya ba shi ikon aikatawa a cikin watan. Domin in mutum ya yi tunani zai ga wasu, sun kasance a cikin watan, amma ba su da lafiya wanda ya shiga tsakaninsa da aikata wa]annan ayyuka na ibadodi. Ko kuma ga su a cikin watan, amma sune cikin gafala ko kasala na aikata wa]annan ibadodi. Kuma duk lokacin da mutum ya gode wa Allah (T) kan wata ni’ima da ya yi masa, to ya bu]e wa kansa }ofar }ari ne. Wato kamar yadda Allah (T) yake cewa; “ Idan kuka gode zan }ara maku”.
2- Muhasaba:- Wato mutum ya zauna ya yi wa kansa hisabi, ta hanyar tafakkur (tunani) ya tambayi kansa, shin ya samu ci gaba a addininance, in an kwatanta da gabanin kamawar watan Ramadan da kuma yanzu da ya zo }arshe ko ya }are? Misali ala}arsa da Allah (T).  Ala}arsa da Manzon Allah (S), ala}arsa da Ahlul Baiti (AS), ala}arsa da gidan lahira. Ala}arsa da aikata addini wajen bin umarnin ko nisantar hani. Duk wa]annan da aka ambata, dama wa]anda ba a ambata ba, ya samu ci gaba ne a cikinsu ko akasin haka? Domin kamar yadda wani Malamin Irfan yake cewa; “Duk wanda watan Ramadan ya kamo }are, bai samu tasirantuwa da hasken watan Ramadan ba, to ya sani duhun zunubansa sun wuce hasken wannan wata mai haske mai haskakawa.” Kuma ita muhasaba, in son samu ne, mutum ya kasance kowace rana yana yin ta, misali ko da safe ko da yamma, ko kafin ya kwanta da daddare, ko kuma bayan ya tashi Sallar Tahajjud, wato mutum ya yi wa kansa hisabi dangane da kyawawan ayyuka da kuma munanan ayyuka da ya aikata a ranar. Bayan muhasabar, sai ya gode wa Allah (T) na muwafa}a da ya yi masa na aikata kyawawan ayyuka, munanan ayyuka kuma da ya aikata ya nemi Allah (T) ya gafarta masa.
A ta}aice dai yi wa kai hisabi kowace rana, yana daga cikin ayyuka da ke da gayar muhimmanci da mutum ya kamata ya lizimta wa kansa. Domin ya zo daga Imam Kazim (AS) yan cewa; “Baya daga cikin wanda bai yi wa kansa hisabi kowace rana”. Kuma shi hisabi ma kai kamar yadda Malaman Irfan suka yi bayani, ya kasu kashi hu]u:- 1- Akwai hisabi Yaumiyya (na kullum). 2- Akwai hisabi na Usbu’iyya (na mako). 3- Akwai hisabi na Shahariyya (na wata). 4- Akwai hisabi na Sanawiyya (na shekara). Wato in son samu ne mutum ya sunnata wa kansa, yin wa]annan hisabobi guda hu]u na kowace rana shi ne wanda aka yi bayaninsa a sama. Na kowane mako shi ne mutum kowane mako. Misali, kowace ranar Juma’a, mutum ya yi wa kansa hisabi na abin da ya aikata daga waccan Juma’ar zuwa wannan Juma’a na kyawawa ko munanan ayyuka. Na wata kuma shi ne misali }arshen kowane wata ya duba ayyukan da ya aikata a watan? Na shekara kuma shi ne misali na watan Ramadan da aka yi bayani a sama da kuma ya dubi ayyukan da ya aikata, da kuma ci gaba ko rashin ci gaba da ya samu a addinance daga watan Ramadan da ya gabata, zuwa wannan na bana. A ta}aice dai lizimtar yi wa kai hisabi ta wadannan fuskoki da aka ambata, zai taimaka wa mutum sosai wajen mujahadarsa da kuma sulukinsa zuwa ga Allah (T).
3- Afuwa:- Wato kamar yadda ake fata da kuma sa rai ga Allah (T) mutum ya fita watan Ramadan yana yafaffe, wato wanda Allah (T) ya yi wa afuwa daga laifukansa. To shi ma ya yafe wa mutune, musamman ma ’yan uwansa mabiya Ahlul Bait (AS) dangane da laifukan da suka yi masa. Kuma kamar yadda aka yi bayani a shekarar da ta gabata cewa Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance yakan yi haka a }arshen watan Ramadan, wato yakan yi afuwa ga duk wa]anda suka yi masa laifi. Domin kamar yadda ya zo Allah (T) mai afuwa ne kuma yana son afuwa. Akwai ma wani bawan Allah da yake cewa zai ji kunyar Manzon Allah (S) gobe }iyama a ce ga shi ya tsaya da wani mabiyin Ahlul Baiti (AS) ]insa, domin neman ha}}insa gare shi. Saboda haka wannan bawan Allah ya kasance kowace rana yakan ce; “Ya Allah! Duk wani mabiyin Ahlul Baiti (AS) da ake rubuta masa laifi saboda ni, daga yau na yafe masa”.
A ta}aice dai ]abi’a ta yin afuwa, wata siffa ce da ya kamata mutum ya siffata da ita. Domin idan mutum ya kasance mai yawan afuwa ga ’yan uwansa muminai, haka zai iya kasance masa wata wasila da Allah (T) zai zamanto mai yawan yi masa afuwa.
4- Tuba:- Wato a nan ana nufin mutum ya tuba ga Allah (T) da kuma neman gafararsa, saboda ta}aitawarsa da kuma rashin kyautatawa yadda ya kamata ga ayyukan ibadodi daban-daban da ya gabatar a wata na Ramadan. Misali Salloli, karatun Al}ur’ani, Azkar, Addu’o’i Ma’asurai da kuma wa]anda ba Ma’asurai ba. Ma’asurai sune wa]anda aka samo daga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS), da dai sauran ayyukan ]a’a kamar ciyarwa da sadakoki, a ta}aice dai ire-iren wa]annan ayyuka da Allah (T) ya azurta shi da aikatawa, to ya nemi Allah (T) ya gafarta masa, saboda ya ta}aita wajen aikata su, kuma bai yi su a ha}i}anin yadda Allah (T) yake so ba. Irin wannan tuba, ita ake ce wa tuba ta kususul-kusus. Wato ta za~a~~u-za~a~~un bayin Allah (T). Domin a wajen Malaman Irfan, sun kasa tuba kashi uku: 1- Akwai tuba ta Awwam. Ita ce tuba daga zunubai. 2- Akwai tuba ta kusus (wato za~a~~un bayin Allah). Ita ce tuba daga gafala, wato sukan tuba ga Allah (T) a lokutan da suke gafala daga tunanin Allah ko tunanin gidan lahira. 3- Tuba ta kususul-kusus (wato za~a~~un-zaba~~un bayin Allah (T) ita ce tuba, saboda ta}aitawa da kuma rashin kyautatawa a cikin ayyukan ibadodi da kuma sauran ayyukan ]a’a. Domin kamar yadda ya zo a Hadisi cewa akwai Mala’ikan da tunda aka halicce shi, wani sujuda yake yi, wani na ruku’u, wani yana tsaye, da dai sauransu. Amma duk da haka gobe }iyama za su ce; “Ya Allah! Ba mu bautata maka ba, ha}ikanin bauta”. Wato suna ganin sun ta}aita. To ina ga mutum? A ta}aice dai yana da gayar muhimmanci mutum ya ginu a kan wannan shu’uri, wato na ji da kuma ganin yana ta}aitawa ga ayyukan da yake yi. Domin ginuwa a kan wannan shu’uri yana da fa’idodi masu yawa. [aya daga ciki shi ne yana cire wa mutum ujub a ayyukan da yake aikatawa na ibadodi.
5- Khauf da kuma raja’a:- Wato tsoro da kuma fata, ko }auna ga Allah (T). Ana so ga mutum idan watan Ramadan ya zo }arshe, musamman ma daren }arshe, da ranar }arshe, ya kasance cikin wa]anda shu’uri guda biyu wato na khauf da kuma raja’a. Ya kasance yana tsoron wannan Azumi na watan Ramadan da ya yi da kuma sauran ayyuka na ibadodi da ya aikata a ciki, Allah (T) ya kar~a. Addu’o’in da ya yi Allah (T) ya kar~a, ko bai kar~a ba shi }ashin kansa, Allah (T) ya kar~a shi, a matsayin bawa na gari, ko bai kar~e shi ba. A lokacin guda da yake wannan shu’uri na tsoro ga Allah (T) kan wa]annan abubuwa da aka ambata. To daga }arshe sai ya yi tunanin raja’a, wato }auna da kuma fata na cewa yana ganin Allah (T) ya amshi Azuminsa, ya amshi ayyukan da ya yi na ibadodi ya amshi addu’o’insa, ya kuma kar~e shi a matsayin bawa na gari a wannan watan na Ramadan. Domin kyautata zato ga Allah (T) ga dukkan al’amura yana da muhimmanci mutum ya ginu a kai. Ya ma zo a Hadisi cewa; “Allah (T) yana cewa ina nan inda bawa yake zato na”. Wato in ka kyauta ta wa Allah (T) zato ga al’amura ko mutum ya munana zato a kai, to haka abin zai kasance. Saboda haka ana son mutum ya kasance mai yawan kyautata wa Allah (T) zato ga dukkan al’amuransa, na addini ne, na duniya ne, ko kuma na lahira ne. A ta}aice dai ana son mutum ya tarbiyyantu a kan wa]annan siffofi guda biyu, wato na tsoro ga Allah (T) da kuma }auna da sa rai gare shi, ga dukkan ayyuka na ibadodi da ya aikata da kuma sauran ayyuka na ]a’a da yake yi.
Wannan ke nan baki ]aya a ta}aice dangane da wasu ladubba, da Malaman Irfan suka yi bayani, wa]anda ake so mutum ya aikata idan watan Ramadan ya zo }arshe ko ya }are. Da fatan za a kiyaye, baya haka kuma ana so mutum ya kasance tsarkake, ya kuma ]ore a kan haka har ya zuwa wani wata na Ramadan in Allah (T) ya raya shi. Domin in mutum bai tsarkake wannan tsarkaka ba, to misalinsa zai zama kamar wanda ya wanke tufafinsa ne, ya kuma goge su, bayan haka kuma sai ya jefa su a kwata. Saboda haka tsarkakuwa da mutum ya samu daga zunubansa ta hanyar gafara da kuma afuwa da yake fatan Allah (T) ya yi masa a watan, to sai ya yi iyaka iyawarsa wajen nisantar zunubai na zahiri da ba]ini domin aikata zunubai yana da illoli masu yawan gaske a addinin mutum da  duniyarsa da kuma lahiyarsa. A ta}aice dai zunubi guba ce babba mai kisa ga ruhin ]an’adam da kuma }azantar da ruhin. Sannan kuma ana son mutum ya samu isti}ama da sabati ga wa]annan ayyuka na ibadodi daban-daban da ya aikata a watan Ramanda. Wato ya tsayu a kai har ya zuwa wani watan Ramadan ]in insha Allah.
Duk da kasancewa dai da wuya ya yi kamar watan Ramadan a sauran watanni, to ya zamanto dai akwai wani mi}idari na ayyuka ]in da zai lazimta wa kansa, kuma ya tsaya da su, ba tare da yankewa ba, sai da wani uzuri. Domin isti}ama da sabati a kan ibadodin da mutum ya lizimta wa kansa yana da fa’idodi masu yawa, daga ciki akwai; misali idan mutum bai da lafiya, ko ya yi tafiya, wasu shigul kamar ‘programms’ na gwagwarmaya. To kasantuwar wa]annan abubuwa da aka ambata, sai ya zama bai samu yin wasu ibadodi da ya saba yi ba, to za a rubutu masa lada na wa]annan ayyuka da ya saba yi kamar ya aikata, sa~anin ko akasin haka. Wato idan ya kasance ayyuka ]in jefi-jefi yake yi, wani lokaci ya yi, wani lokacin kuma ya kasance bai yi ba, wato bai tsayu a kai ba, to irin wannan ko da wa]annan abubuwa sun bijiro masa, kamar rashin lafiya, ko tafiya, ko wani shugul, to ba za a rubuta masa lada na ayyukan ibadodi daban-daban da za su dinga kusanta shi ga Allah (T) ba. Wa]annan ayyuka na ibadodi Malaman Irfan sun kakkasu kashi biyar sune:- 1- Yaumiyya (na kullum). 2- Usbu’iyya (na mako). 3- Shahariyya (na wata). 4- Sanawiyya (na shekara). 5- Umriyya (naso ]aya a rayuwa) kuma dukkan nau’ukan ayyuka na ibadodi kamar; 1- Salla. 2- Karatun Al}ur’ani. 3- Azumi. 4- Addu’o’i. 5- Azkar. 6- Ziyara na Ma’asumin (AS). 7- Muhasaba, ko wanne daga cikin wa]annan yana da wanda ake son yin kullum da mako da wata da shekara, wani kuma daga ciki ko da sau ]aya a rayuwa. Misali a nan shi ne Salla, in za a iya tunawa a Arba’ain ]in Imam Husain (AS) an kawo Salloli da aka samo daga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) wa]anda ake yi kullum da mako da wata da kuma shekara, wanda ba a kawo ba, ita ce Salla umriyya, wato wadda ake son mutum ya aikata ko da sau ]aya a rayuwarsa. In mutum ya bincika zai ga Imamai 12 na Ahlul Baiti (AS) kowannensu. Akwai Sallarsa, wato tun daga Imam Ali (AS) zuwa Imam Mahdi (AS) in mutum ya duba littafin Mafatihul Jinan ya kawo wa]annan Salla. To irin wa]annan Salloli, ana son mutum ya yi ta kowace Imami, ko da sau ]aya ne a rayuwarsa. To haka kuma ta ~angaren karatun Al}ur’ani in mutum ya duba baya ya sauka da ake son mutum ya yi a}alla sau ]aya wata. To akwai surori na Al}ur’ani da ake son karanta su kullum, misali Suratul Mulk, Suratul Sajada, Suratul Dhukan, Suratul Wa}i’a, Suratul Yasin, Suratul Lu}man, dukkansu in son samu ne ana son mutum ya karanta su kowane mako. Misalin su shi ne a daren Juma’a, akwai Suratul Kahaf, Isra’i, Shu’ara, Namli, {isas, {amar da dai sauran Surori in mutum ya duba littafin Mafatihul a ayyuka na daren Juma’a zai ga surori. Haka nan a ranar Juma’a ana son karanta Suratul Ali-imran, Nisa’i, Hud, Saffat da kuma Suratul Rahman.
Haka nan kuma surorin da ake son karantawa na kowane wata, akwai Suratul A’araf, Anfal, Taubah, Yunus da kuma Suratu Namli. Misali kuma Surori na shekara, shi ne Surar Ankabut da kuma Rum da ake son karantawa a daren 23 na watan Ramadan. To wa]annan Surori na Al}ur’ani na kullum, mako, wata, shekara, suna zaman kansu ne, wato ba su da ala}a da saukar da mutum ya saba yi. To haka nan addu’o’i akwai na safe da yamma da ta’a}ibat na Salloli na mako, kuma shi ne kamar wanda aka samo daga Imam Sajjad (AS) wato kowace rana da addu’arta. Kamar yadda mai Mafatihu ya kawo. Addu’ar wata kuma ita ce wadda mai Dhiyau Salihin ya kawo, in mutum ya duba zai gani tunda ga ]aya ga wata, har ya zuwa 30 ga wata, ita wannan addu’a ta shekara, ita ce kamar shigen na watan Ramadan, wanda wasunsu ana yi cikin yinin Ramadan, wasu kuma a dararen Ramadan.
Addu’a Umriyya kuma ita ce dukkan addu’o’i da aka samo daga Ma’asumai (AS) wato wa]anda suka zo a littafin addu’a. Mutum ya karanta ko wannen su ko da sau ]aya ne a rayuwarsa, wato a nan an nufin addu’o’i da bai lizimta wa kansa karanta su ba. A ta}aice dai irin wa]annan tsari na ibadodi ake son kowannenmu ]an uwa ne ko ’yar uwa ya tsara wa kansa ya kuma tsayu a kai har ya koma ga Allah (T).


No comments:

Post a Comment