Sunday 10 February 2013

Bayani kan alakar limaman mazhabobin Ahlus-Sunnah da A’imma [AS].


Kamar yadda aka ambata a darasin da ya gabata cewa, wannan darasi na Fi}hu insha Allah, za a dinga gabatar da shi a bisa Usulubi na Fi}hul-Mu}arana ne, wato mu}arana tsakanin wa]annan Mazhabobi guda hu]u na Ahlus-sunnah; Hannafiyya, Malikiyyah, Shafi'iyya, Hanbaliyya. A ]aya gefen kuma da Ja'afariyya, amma za a }arfafa a Fi}hun Ja'afariyya ne.
Sai dai wani tambihi muhimmi kuma mai fa’ida  anan shine,su wa]annan shugabanni ko
 Limaman Mazhabobi na Ahlus-Sunnah guda hu]u da aka ambata a sama, watau Shugabaninsu duk sun  rayu ne a zamanin A'imma na  Ahlul-Bait (AS). Watau daga zamanin Imam Sadi}(AS) zuwa zamanin Imam Aliy Alhadi (AS) suka rayu.
Abu Hanifa ya yi zamani da Imam Sadi}(AS) ne, Malik shi ma ya yi zamani da Imam Sadi}(AS) ne, Shafi'i ya yi zamani da Imam Kazim (AS) da kuma Imam Ridha (AS), Ahmad ]an Hanbal ya yi zamani da Imam Kazim (AS) da Imam Ridha (AS) da Imam Jawad (AS) da kuma Imam Aliy Al-Hadi (AS). To, tambaya a nan shi ne tunda su wa]annan Shugabannin Mazhabobi na Alus-Sunnah sun yi zamani da A'imma na Ahlul-Bait (AS), wace irin ala}a suka yi da Imaman Ahlul-Bait (AS) da kuma mabiyan su A'imman (AS)? Sanin amsar wannan tambayar yana da muhimmanci, musamman ga 'yan uwanmu Musulmi mabiya Madrasa ]in Ahlus-sunnah. Misali idan mutum shi ]an Malikiyyah ne ko Hannafiyya zai ga yadda Imam Malik da Abu Hanifa suka zauna da Imam Sadi}(AS). Haka nan idan shi ]an Shafi'iyyah ne ko Hambaliyyah zai ga su ma yadda suka zauna da Imaman Ahlul-Bait (AS). Hanyar da mutum zai bi domin ya san amsar wannan tambayar ko, shi ne, karanta tarihin wa]annan Shugabanni na Mazhabobi guda hu]u, ]aya bayan ]aya.
Alal misali akwai littafi mai suna IMAMU SADI{ WAL MAZAHIBUL ARBA'A. Littafin Juzu'i uku ne. In mutum ya duba wannan littafi zai ga yadda ya kawo tarihin wa]annan limamai na Mazahib guda hu]u ]aya bayan ]aya. Da kuma yadda ala}arsu ta kasance da A'imma (AS) da kuma Almajiran A'imma(AS). Kuma wani abin mamaki, mafi yawan abin da ya kawo na tarihinsu ya cirantone  daga abin da mabiya na wa]annan Limamai na Mazahib suka rubuta. Amma amsar wannan tambayar a dun}ule shi ne cewa sun yi kyakkyawar ala}a da kuma mu'amala da zamantakewa da A'imma (AS) da kuma mabiyan su ne. Domin in da mutum zai yi bincike dangane da tarihi da kuma rayuwar wa]annan Shugabannin Mazhabobi hu]u zai ga cewa kowane ]aya daga cikinsu imma dai ko ka samu cikin wa]anda ya yi karatu a wajensu akwai Imam daga cikin A'imma na Ahlul-Bait (AS). Kamar yadda haka ya kasance ga Shafi'i da kuma Ahmad ]an Hanbal. Shi Ahmad ]an Hambal baya ga karatu da ya yi wajen Almajiran A'imma (AS) ya yi karatu ma wajen Imam Kazim (AS).
Akwai wata rana, ya je wajen Imam Kazim (AS), sai ya ga wani abin da ya ba shi mamaki. Ga abin da ya gani da bakinsa, Ahmad ]an Hanbal ya ce, “wata rana na shiga gun Imam Musa ]an Ja'afar domin in yi karatu a wajensa, sai na ga maciji ya sanya bakinsa a kunnen Musa [an Ja'afar, kamar yana fa]a masa wani abu. Da ya gama sai Musa ]an Ja'afar ya fa]a masa wani abu, amma ni ban fahimci abin da ya fa]a masa ba. Bayan haka sai na ga macijin ya wuce. Imam Kazim (AS) ya ce masa, “ya Ahmad wannan ]an sa}on Aljanu ne, sun yi sa~ani kan wata mas'ala ce, shi ne ya zo domin ya yi tambaya a kai, na ba shi amsa.” Daga }arshe Imam Kazim (AS) ya ce masa, “ya Ahmad ina gama ka da Allah, kada ka fa]a wa kowa wannan abin, sai bayan rasuwata.” Shi ne Ahmad ]an Hambal ya ce, ni ko ban fa]a wa kowa ba wannan abin sai bayan rasuwarsa.” Mai bu}atar ganin wannan ya duba littafi mai suna ALKUNA WAL-AL-{AB juzu'i na biyu Na Shaikh Abbas {ummy, watau marubucin littafin Mafatihul Jinan.
Makamancin haka ya ta~a kasancewa ga Imam Aliy (AS), lokacin yana hu]uba a Masallaci, watau a Kufa. In mutum ya duba wannan littafi da aka ambata, ya kawo abin da ya faru sanka-sanka. Saboda haka wa]annan Limamai na Mazahib hu]u akwai ala}ar karatu tsakaninsu da A'imma na Ahlul-Bait (AS). Baya ga ala}a ta karatu da suka yi a wajen su, in mutum ya bibiyi tarihinsu, zai ga sun nuna gayar so da }auna da girmamawa da nuna goyon baya ga A'imma na Ahlul-Bait (AS). Wuce nan ma har da nuna fifikonsu a kan sauran mutane.
Wato irin kyakkyawar ala}a da suka yi da A'imma (AS) ta ~angarori daban-daban ya sa wasu daga cikin Malaman da suka yi zamani da su suna tuhumar su da Shi'anci, watau cewa su 'yan Shi'a ne. Ga Misalai, Ala}ar Imam Abu Hanifa da Ahlul-Bait (AS) a aikace, Imam Abu Hanifa ya yi karatu na shekara biyu wajen Imam Sadi}(AS) har ma wa]annan shekara biyun yana alfahari da su a rayuwarsa, domin yana yawan cewa, ba domin shekara biyun da ya yi karatu a gun Imam Sadi}(AS) ba, to da ya halaka. Domin karatunsa a wajen Imam Sadi}(AS) ya canza masa wasu ra'ayoyi nasa da kuma tunani, musamman ma yadda yake amfani da }iyasi wajen gina hukunci ko ba da fatawa. Imam Sadi}(AS) ya hane shi a kan haka, hani mai tsanani, har ma yake ce masa farkon wanda ya soma }iyasi shi ne Iblis, lokacin da aka ce masa ya yi Sujuda ga Annabi Adam (AS), sai ya ce ai ya fi shi, shi an halicce shi da wuta. Shi kuma da laka.
Imam Sadi}(AS) ya yi wa Abu Hanifa wasu tambayoyi domin ya wanke masa ra'ayoyi na }iyasi a al'amarin Addini. Ya ce masa ya Nu'uman (da yake sunan Abu Hanifa ke nan) wanne ya fi girma, kashe rai ko zina? Sai Abu Hanfa ya ce kashe rai. Sai Imam Sadi}(AS) ya ce masa, amma ga shi Allah (T) a wajen kashe rai yana amsar shaidar mutum biyu ne, yayin da Zina bai kar~a ba, sai shaidar mutum hu]u. Sannan sai ya sake ce masa tsakanin Sallah da Azumi wanne ya fi girma, sai Abu Hanifa ya ce Sallah. Sai Imam Sadi} (AS) ya ce masa to, me ya sa mai haila za ta rama Azumi, amma ba za ta rama Sallah ba? Daga }arshe Imam Sadi}(AS) ya ce masa ka ji tsoron Allah ka daina }iyasi a cikin Addini. Akwai ire-iren wa]annan munazarori da suka gudana a tsakanin Imam Sadi}(AS) da Abu Hanifa, amma ba za a kawo su ba, saboda gudun tsawaitawa.
Abu Hanifa ya kasance ko tambayoyi ya zo yi wajen Imam Sadi} (AS) yana nuna girmamawa da kuma ladabi gare shi. An ce bai yi masa magana face sai ya ce, “in zama fansa gare ka ya ]an Manzon Allah(S).”
Haka nan lokacin da Zaid ]an Imam Zainul-Abidin  (AS) ya fita domin ya}ar Banu Umayya, Abu Hanifa ya shajja'a mabiyansa domin shiga cikin maya}an Zaid da kuma taimaka masa ta fuskoki daban-daban. Akwai lokacin da Abu Hanifa yake ce wa Almajiransa, “kun san me ya sa mutanen Sham suke gaba da }iyayya da mu?” Suka ce, “a'a.” Abu Hanifa ya ce masu, “domin sun san cewa da mun halarci ya}in da aka yi tsakanin Imam Aliy (AS) da Mu'awiyyah, da mun kasance tare da Aliy ]an Abi [alib.” A ta}aice dai irin wannan ala}a da kuma karkata da Abu Hanifa ya yi ga Ahlul-Bait (AS) ya sa aka samu wasu Malamai na Ahlus-Sunnah suna tuhumar sa da cewa shi Shi'a ne.
2. Imam Malik; shi ma ya yi karatu wajen Imam Sadi}(AS). Malik ba wai kawai ya yi karatu wajen Imam Sadi}(AS) ba. A'a ya tasirantu sosai a wasu abubuwa da ya gani a Majalisin Imam Sadi} (AS) na koyarwa. Misali, yadda ya ga Imam Sadi}(AS) yana gayar girmama Manzon Allah (S) in zai ambaci sunansa a wajen ba da Hadisi ko kuma idan ya ji an ambaci sunan Manzon Allah (S), ko kuma yadda Imam Sadi}(AS) ba zai fa]i Hadisin Manzon Allah (S) ba, face yana da alwala. Ire-iren wa]annan abubuwa sun yi tasiri ga Malik sosai, domin ta kai ma shi ma yana aikata haka.
       Ya  zo a tarihinsa cewa, ko tambaya aka zo yi a gidansa, in aka yi sallama yakan aika ya ji shin tambayoyin sun Shafi Hadisi ne? In aka ce eh, to in bai da alwala akan ga ya yi alwala kafin ya fito. Haka nan Malik ya kasance yana cewa, “na jajje wajen Ja'afar ]an Muhammad lokuta da yawa, duk lokacin da na je, sai in samu yana ]ayan uku, ko yana sallah, ko karatun {ur'ani ko kuma Azumi.” Mahallis-Shahid a nan shi ne cewarsa, na jajje a lokuta da yawa, watau wannan na alamta yawan ziyarar da yake kai wa Imam Sadi}(AS). Shi ma wannan ke nan a ta}aice na ala}arsa da Imam Sadi} (AS).
3. Imam Shafi'i. Cikin wa]annan Limamai na Mazahib hu]u, babu wanda aka tuhumta, tuhumta mai yawa na Shi'anci, watau cewa shi ]an Shi'a ne, kamar yadda aka tuhumi Shafi'i. Shi ya sa in mutum ya duba tarihinsa, akwai baitoci masu yawa na wa}e da ya yi domin raddi ga masu wannan tuhumar. Ga misali na wa]annan baitoci nasa “idan a Majalisi na karantarwa aka ambaci Aliy da Hasan da Husaini da Fatima Zakiyya, sai a ce mutum ya wuce gona da iri. A ce wannan fa]in Rafidawa ne (watau 'yan Shi'a, da yake lokacin haka ake ce masu), ni na barranta ga mutanen da suke ganin Rafidanci shi ne son Fatima.”
Haka nan wata rana an ta~a tambayar sa dangane da Imam Aliy (AS). Sai ya ce, “me zan ce dangane da mutumin da masoyansa suka ~oye darajojinsa saboda tsoro, ma}iyansa kuma suka ~oye darajojinsa saboda hassada?”. A kuma raddin da ya yi na wannan tuhuma na cewa shi  Shi'a ne. Yana cewa “suka ce na Rafidance, a'a Rafidanci ba addinina ko A}idata ba. Sai dai ni na mi}a wula'ata ba tare da shakka ba, ga mafi alkharin Imami. In dai son Wasiyyi (watau Imam Aliy) shi ne Rafidanci, to lallai ni ne mafi rafidanci a cikin bayin Allah.” A kuma wani baiti na wa}e yana cewa “in dai Rafidanci (Shi'anci) shi ne son Ahlul-Bait (AS), to mutane da Aljannu baki ]aya su shaida cewa lallai ni Barafide ne.” Da dai wasu baitoci daban-daban da Shafi'i ya yi na nuna sonsa da girmamawarsa ga Ahlul-Bait (AS) wa]anda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.
4. Imam Ahmad ]an Hambal: Kamar yadda aka ambata a sama cewa, ya yi karatu a wajen Imam Kazim (AS) da kuma wasu daga cikin Almajiran A'imma (AS), akwai wata fa]a tasa da yake cewa, “ babu wani daga cikin Sahabban Manzon Allah (S) wanda darajoji suka zo a kansa kamar yadda suka zo ga Imam Aliy (AS)”. Mai bu}atar ganin wannan magana ta Ahamad ]an Hambal, ya duba littafin Suyu]i mai suna Tarikhul Khulafa'a, a fasalin da ke bayanin Imam Aliy (AS).                     Akwai wata rana da aka tambayi Ahmad ]an Hanbal, aka ce masa. Me za ka ce dangane da Hadisin da aka ruwaito cewa Aliy shi ne mai rabon wuta da Aljannah? Sai Ahmad ]an Hambal ya ce masu, kuna musanta Hadisin ne? Ashe ba a ruwaito daga Manzon Allah (S) yana ce wa Aliy ba, ba mai son ka face mumini, ba kuma mai }in ka face munafuki? Suka ce lallai akwai wannan Hadisin. Sai Ahmad ]an Hambal ya sake tambayar su. Mumini wane gida yake gobe }iyama? Suka ce Aljannah. Shi fa Munafuki? Suka ce wuta. Sai Ahmad ]an Hambal ya ce, “To lallai Aliy shi ne mai rabon wuta da kuma Aljannah.
Kamar yadda wasu suka sani, akwai wata fitina da ta auku a zamaninsa. Fitinar ita ce, wai Al}ur'ani makhlu} ne ko ba Makhlu} ba ne? A kan haka masu iko a wannan lokacin sun kashe mutane da yawa, wasu kuma an sa su a kurkuku. Shi Ahmad ]an Hambal yana ]aya daga cikin wa]anda aka sa su a kurkuku kan al'amarin. Domin shi mau}if ]insa shi ne Al}ur'ani ba Makhlu}ba ne. Dalilin kawo wannan }issar shi ne na amsar da shi Ahmad ]an Hambal ya bayar lokacin da wani ya tambaye shi a kan cewa, to mane ne hujjarsa a kan haka? Ya ce Hujjarsa ita ce, Ja'afar ]an Muhammad Sadi}(AS).
Haka nan kuma a Madrasah ]in Ahlus-sunnah Imam Ahmad ]an Hambal shi ne ya riskar da Imam Aliy (AS) a matasyin Khalifa na Hu]u. Wannan ya auku ne a mulkin Abbasawa, domin a mulkin Banu Umayya lissafin Khalifofi suna tsayawa ga uku ne, ba su sa Imam Aliy (AS) a ciki. Kuma wannan ma mutum ko da hankalinsa ya auna, zai ga haka. Wanda ake zagi da kuma la'anta a masallatai, wa'iyazubillah, ai ba a sa shi cikin lissafi ba. Haka nan kuma akwai littafi da Ahmad ]an Hambal ya rubuta dangane da falaloli da kuma darajoji na Imam Aliy (AS).
Akwai lokacin da wasu suka zo wajensa suna tattaunawa har zance ya kai su kan magana dangane da Khalifanci. Suka ambaci Khalifanci na Abubakar, Umar Usman da kuma Khalifancin Imam Aliy (AS). Shi ne Ahmad ]an Hambal yake ce masu “ai shi Khalifanci bai }awata Aliy ba. Aliy shi ya }awata Khalifanci. Shi ne Ibn Abil Hadid, yake cewa dangane da wannan magana ta Ahmad ]an Hambal, wannan magana tasa abin da ta }unsa kuma take nunawa shi ne cewa wasu Khalifanci ya }awata su ne, amma Aliy ba shi da wata na}asa ko tawaya da yake bu}atar Khalifanci ya cika masa shi. Wannan ke nan a ta}aice shi ma dangane da ala}ar Ahmad ]an Hanbal da Ahlul-Bait (AS). 
Wa]annan abubuwa da aka kawo na ala}ar Shugabannin wa]annan mazhabobi guda hu]u da Ahlul-Bait (AS) da kuma mabiyansu an ciranto su ne daga Littafan Ahlus-sunnah, saboda haka, kira a nan da kuma Nasiha ga 'yan uwanmu Musulmi na Madrasa ]in Ahlus-Sunnah shi ne su duba su ga yadda Shugabanni na wa]annan Mazhabobi suka zauna tare da Imamai na Ahlul-bait (AS) da kuma mabiyansu. Sun zauna ne suna gaba da }iyayya da su, ko kuma ganin su a matsayin ba Musulmi ba? Ko kuma akasin haka ne? Watau sun yi kyakkyawar zamantakewa da su ne? Kuma a wannan zamanin hanyoyin bincikar abin da kowa yake a kai sassau}a ne. Saboda haka maimakon mutum ya ginu kan gaba da }iyayya ga mabiya Ahlul-bait (AS), mutum ya bincika ya gani a littafansu. Domin irin wannan gaba da }iyayya yana iya kai mutum ga halaka, musamman ma wannan zamani da muke ciki na kusantowar bayyanar Imam Mahdi (AS).
Akwai wani Malami, yana ]aya daga cikin Fitattun Malamai na Ahlus-sunna, ya rayu ne a }arni na goma, kuma ya rubuta littafai masu yawan gaske. Daga cikin littafin da ya rubuta, akwai littafi mai suna KASHFUL GUMMA. Littafi ne sananne, kuma ana samun sa. A mu}addimar littafin akwai abin da ya kawo dangane da abubuwan da za su kasance idan Imam Mahdi (AS) ya bayyana. Yana cewa, “ idan Imam Mahdi (AS) ya bayyana zai gusar da duk sa~ani da kuma ra'ayoyi a bayan }asa, zai dawo da Addini tsantsa. Kuma wasu sashen Musulmin zamaninsa za su yi }iyayya da shi a ~oye, kasantuwar yadda suka ga yana tafiya sa~anin yadda Malaman Mazhabobinsu suka tafi a kai, saboda i'iti}adin da suke da shi na cewa Allah (T) ba zai samar da wani da ya fi Limaman Mazhabobinsu Ilimi ba. Sai dai za su yi masa biyayya dole, saboda tsoron dam}arsa da kuma kwa]ayin abin da ke gare shi na dukiya.”
 Ya ci gaba da cewa zai dawo da Addini kamar yadda yake a zamanin Manzon Allah. Mu duba wannan bayani, domin wanda ya rubuta ba Malamin Shi'a ba ne, a'a malamin Ahlus-sunnah ne, kuma ya rubuta wannan littafin sama da Shekara 400 da suka wuce. Kuma wannan littafi nasa sananne ne a nan, kuma samun sa ga mai bu}ata mai sau}i ne, yana iya neman sa domin ya duba wannan magana da ma }ari a kai. Wannan ke nan baki ]aya a ta}aice, sai kuma darasi na gaba wanda insha Allah za a kammala wannan shimfi]a da gabatarwa da ma shiga cikin babobin Fi}ihun.



No comments:

Post a Comment