Sunday 3 February 2013

Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) (1)


Kasantuwar watan da muka fita, wato Safar a cikinsa ne wafatin Manzon Allah (S), a 28 gare shi. Wannan a kan abin da Malaman Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) suka tafi a kai. Amma abin da Malaman Madrasah ]in Ahlus Sunna suka tafi a kai shi ne, 22 ga watan Rabi’ul Awwal.

Kuma kamar yadda aka sa~a a irin wannan munasabobi na wafatin Ma’asumai (AS) a kan gabatar da darussa a ta}aice daga rayuwarsu, domin su kasance madubi da za mu dubi kawukanmu, da kuma }o}arin ]abba}a su a aikace gwargwadon ikonmu.
Sanin tarihin ~angarori daban-daban na rayuwar Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS), wani abu ne wanda yana da gayar muhimmanci. Amma akwai wasu ~angarori na rayuwarsu, sanin su ya fi muhimmanci a kan sauran ~angarorin. Alal misali, sanin tarihin shekara ko wata ko ranar wafati ko wilada na Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS), ko kuma sanin shekarun da kowannensu ya yi a duniya, ko kuma adadin ’ya’yan kowannensu, da dai makamantansu. Wannan yana da muhimmanci. Amma muhimmancinsa bai kai kamar muhimmancin sanin Akhla} ]insu, Ibadodinsu, Zuhudunsu, Ala}arsu da Allah (T), mu’amalarsu da mutane, da dai makamantansu ba, domin jahiltar wancan wato sanin shekara, wata ko rana na wiladar su ko wafatinsu, ba zai cutar da mutan gobe }iyama ba, kamar yadda jahiltar sanin Akhla} ]insu, Ibadarsu, Mu’amalarsu da mutane, zai cutar da shi gobe }iyamah.
Kuma in mutum ya duba wancan ~angaren na sanin shekarunsu, ko lokacin wiladar su, ko wafatinsu, a kan samu sa~ani tsakanin Malaman wa]annan makarantun guda biyu (wato Shi’a da Sunna), ko kuma sa~ani a kai tsakankanin Malaman makarantun guda biyu. Misali, wannan munasabar ta wafatin Manzon Allah (S) in muka duba, za mu ga akwai sa~ani tsakanin Malaman wa]annan makarantu guda biyu. Malamnan Shi’a sun tafi a kan watan Safar, Malaman Sunna sun tafi a kan watan Rabi’ul Awwal.
To, in aka dawo a kowace Makaranta a cikinsu, sai ka ga wani lokaci a kan samu sa~ani. Misali a nan shi ne, na Malaman Sunna da suka tafi a kan wafatin Manzon Allah (S) watan Rabi’ul Awwal. Mafi yawansu sun tafi a kan 22, amma akwai cikinsu wa]anda suka tafi a kan wafatin 2 ga Rabi’ul Awwal ne. Haka nan Malaman Shi’a da suka tafi a kan watan Safar ne 28 gare shi, amma akwai ka]an da suka tafi akasin haka. A ta}aice dai, abin da ake so a fitar a nan, sanin wa]annan abubuwa yana da muhimmanci, amma muhimmancinsa bai kai kamar sanin Akhla} ]insu ba, da makamantansu. Shi ya sa a irin wa]annan munasabobi na wafatinsu aka fi }arfafawa kan wa]annan janibobi na rayuwarsu, domin su kasance darussa gare mu da za mu yi }o}arin aikatawa da kuma guzuri gare mu gobe }iyamah.
WAFATIN MANZON ALLAH (S)
Akwai abubuwan da suka faru gabanin rasuwar Manzon Allah (S) da kuma lokacin rasuwarsa da kuma bayan rasuwarsa. Shaikh Abbas Al-{ummy a cikin littafinsa Muntahal Amal (juz’i na ]aya) ya kawo wa]annan abubuwan da suka faru sanka-sanka, amma ga wasu daga cikin abubuwan da suka faru gabanin rasuwar Manzon Allah (S), mafi yawansu suna da ala}a da al’amarin Ghadir. Kuma kamar yadda aka sani tsakanin ranar Ghadir da wafatin Manzon Allah (S) kwana 70 ne, a cikin wa]annan kwanaki 70 abubuwa da yawa sun faru masu ]aci da zafi a zuciya.
Domin in mutum ya yi tunani sosai zai ga cewa dukkan jarabawowin da Manzon Allah (S) ya fuskanta a rayuwarsa, zafinsu da ]acinsu bai kai wa]anda ya fuskanta a cikin wa]annan kwanaki 70 na }arshen rayuwarsa ba. Domin in mutum ya dubi wa]ancan matsalolin zai ga mafi yawansu matsaloli ne na waje, amma wa]annan matsaloli ne na cikin gida, saboda haka jarabawarsu ta fi tsanani. Kuma kamar yadda aka sani Ma’asumin (AS), wato Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) akwai jarabawowi da suka yi tarayya a ciki, akwai kuma jarabawa da kowane Ma’asumi (AS) ya ke~anta da ita a zamaninsa. Kuma in mutum ya dubi tarihinsu ]aya bayan ]aya zai ga galibi, irin wa]annan jarabawowi ke~antattu, sukan zo ne }arshen rayuwarsu.
Alal misali, mutum ya dubi irin jarabawar da Sayyidah Fatimah (AS) ta fuskanta a }arshen rayuwarta, na hujumi da aka yi a gidanta, da kuma mas’alar gadonta da kuma Fadak, da dai sauransu.
Haka nan kuma mutum ya dubi jarabawowin da Imam Ali (AS), Imam Hasan (AS), Imam Husaini (AS), da dai sauran Imamai (AS) suka fuskanta a }arshen rayuwarsu. To, in mutum ya dubi rayuwar Manzon Allah (S) a irin wannan jarabawa ke~antatta zai ga babbar jarabawar da ya fuskanta ita ce, ta al’amarin Ghadir.
Mutum ya dubi abubuwan da suka faru gabanin Ghadir, da ranar Ghadir, da kuma bayan Ghadir, zai fahimci haka. Domin in mutum ya dubi tsawon shekaru 23 da aka aiko wa Manzon Allah (S) da sa}o na wahayi. To, babu sa}on da ya zo wanda Manzon Allah (S) ya nemi a yi masa afuwa wajen isar da shi, kamar wannan al’amari na Ghadir. Wato, saboda abin da zai-kai-ya-komo daga mabiya. Ile kuwa, lokacin da Manzon Allah (S) ya bijiro da al’amarin a tashin farko, sai fuskokin wasu da yawa suka canza.
Haka nan a ranar Ghadir da ya tabbatar da wannan al’amari, rasmiyyan a hu]ubar da ya yi mai tsawo, wanda a tarihinsa babu khu]uba mai tsawo kamarta da ya yi, wanda a cikinta ya bayyana wa]anda za su kasance Khalifofi a bayansa, adadinsu, da kuma sunayensu. Amma abin mamaki bayan khu]uba ]in aka samu wasu suka koma gefe suna }us-}us a tsakaninsu. Wani cikinsu ya ce Manzon Allah (S) ya yi hauka (wa’iyazu billahi), wani ya ce ba hauka ba ne son rai ne kawai. Sai wani ya ce koma hauka ya yi, ko son rai ne, to abin da ya fa]i ba zai yiwu ba. Saboda haka aka yi }ulle-}ulle cewa, to da shi da wanda ya na]a ]in a kan hanyarsu ta komawa Madina, a kashe su. Allah (T) ya tona asirinsu, ya kiyaye Manzon Allah (S) suka isa Madina lafiya.
Bayan da Manzon Allah (S) ya dawo Madina da kwana biyu, ya sa Bilal (RA) ya yi yekuwa ga Sahabbansa a kan su taru a Masallaci yana son ganin su. Da Manzon Allah (S) ya zo Masallacin ya hau mumbari, bayan ya yi yabo da godiya ga Allah (T), ya yi masu bayanin wasu daga cikin matsaloli daban-daban da ya fuskanta, ya kuma yi masu kashedi dangane da fitinonin da za su taso da kuma cewa su yi ri}o da nauyaya guda biyu, wato Al}ur’ani da kuma Ahlul Baiti (AS).
Bayan nan ya shelanta masu cewa, idan akwai wani daga cikinsu da ya san ya yi wa wani abu to ya tashi, domin yin }isasi (wato ramuwa). Sai wani daga can baya ya tashi ana ce masa Sawada [an {ais, amma a littafin Ahlus Sunna ana ce masa Ukashah. Ya ce, ya Manzon Allah (S) Babana da Mamata su zamo fansa gare ka, wata rana ka dawo daga [a’ifa muka ha]u kana kan taguwarka, ka ]aga sandar da ke hannunka sai ka same ni, ban sani ba, da gangan ne ko da kuskure ne. Sai Manzon Allah (S) ya ce; “Ina neman tsari ga Allah ya kasance da gangan na yi”. Shi ne sai Manzon Allah (S) ya ce wa Bilal, ya tashi ya je wajen Sayyidah Fatimah (AS) ya amso masa sanda ]in. Ya je ya amso ya kawo wa Manzon Allah (S). Sai Manzon Allah (S) ya ce wa mutumin ya zo domin ya rama. Ya ce, to ya kware cikinsa, shi ma lokacin cikinsa a kware ne. Sai Manzon Allah (S) ya kware cikinsa, sai mutumin ya ce Babana da Mamata su zama fansa gare ka ya Manzon Allah (S), za ka yi man izini in sa baki na a kan cikinka. Manzon Allah ya yi masa izini, bayan da ya sumbaci cikin Manzon Allah (S) ya yi Addu’a Allah ka tsare ni daga wuta albarkacin wannan jiki na Manzon Allah (S). Shi ne Manzon Allah (S) ya ce; “Ya Sawada! Za ka yi afuwa ne ko }isasi za ka yi?” Ya ce; “A’a ya Manzon Allah (S)! Zan yi afuwa ne”. Sai Manzon Allah (S) ya ce; “Ya Allah! Ka yi afuwa ga Sawada ]an {ais, kamar yadda ya yi afuwa ga Annabinka, Muhammad (S)”.
Wannan abu za mu ga akwai darussa da yawa a ciki. [aya daga ciki shi ne muhimmacin mutum ya bar duniya babu wani abu na mutane a kansa. Mu duba Manzon Allah (S), kuma Fiyayyen halitta ya ]auki irin wannan mataki kafin komawarsa ga Allah (T). To, ina ga mu. Shi ya sa yake da muhimmanci mutum ya zamanto bai cutar da ’yan uwansa Musulmi ba, musamman ma ’yan uwansa Mu’uminai, da zuciyarsa ko harshensa ko hannunsa. Cutarwa ta zuciya misalin su shi ne; kamar munana zato ko hassada. Na harshe kuma shi ne; kamar giba ko ba}ar magana. Na hannu kuma shi ne; kamar ta~a dukiyarsu ko jininsu. Domin gobe }iyama, kamar yadda ya zo a Hadisi, idan mutum ya cutar da mutane ta wa]annan fuskoki guda uku da aka ambata, to za a ]ibi ladan mutum ne a bai wa wanda ya cutar ]in, in kuma bai da lada sai a kwaso zunubinsa a sa wa mutum a littafinsa. Shi ya sa ya zo a kan cewa gobe }iyama in an ba da  littafan ayyuka, wani zai ga ladaddaki na ayyuka, da ya san bai aikata ba. Sai a ce masa, wannan lada ne na wani da ya munana masa zato ko ya yi giba da shi, da dai makamantansu.
Ta }issar wani bawan Allah da na karanta yana cewa da zai yi giba, to da zai yi da iyayensa ne. Ya ce, saboda ya san in ya yi giba za a ]auki ladarsa ne a bai wa wanda ya yi gibar da shi, to gwanda a ]ibi ladarsa a ba iyayensa da a ba wa wani. Shi ya sa yake da muhimmanci kafin mutum ya bar duniya ya zamanto ya kyautata ala}arsa da Allah (T), ya kyautata ala}arsa da mutane, wato babu wani abu nasu da zai tsayu a kansa ranar }iyama. Sannan kuma ya kyautata ala}arsa da kansa, shi ne mutum ya tsarkake kansa. Ta yadda ya zo duniya yana tsarkakakke, to ya koma ga Allah (T) yana tsarkakakke. Misali, kamar yadda ya zo duniya ga~u~~ansa suna tsarkakku, kamar harshensa, idonsa, kunnensa, hannunsa, da dai sauran su, suna tsarkakakke, to ya koma ga Allah (T) suna tsarkake. Domin su wa]annan ga~u~~a kamar yadda Imam Khumaini ({S) ne yake cewa, amana ce ‘Ilahiyya’ ga mutum, wadda Allah (T) zai tambaye shi a kai.
Dawowa ga abubuwan da suka faru gabanin wafatin Manzon Allah (S). Bayan wannan khu]uba da Manzon Allah (S) ya yi ta bankwana, ya shiga gida wajen Ummu Salma (RA) yana cewa, Ya Ubangiji! Ka amintar da al’ummar Muhammad daga wuta, ka sau}a}e masu hisabi. Ba a jima ba Manzon Allah (S) ya fara rashin lafiya.
A cikin wannan rashin lafiya Manzon Allah (S) ya ha]a runduna ta maya}a, domin zuwa ya}i a Rum }ar}ashin jagorancin Usamah ]an Zaid, kuma wannan runduna ta }unshi mafi yawan Sahabban da ke Madina, ciki har da Abubakar, Umar, Abu Ubaida,  da dai sauran wasu fitattun sahabbai. Saboda haka wasu suka koma gefe suna guna-guni, cewa ya za a sa yaro ya shugabance su? Domin a lokacin shi Usama yana da shekara 19 ne. Wannan abu ya koma ga kunnen Manzon Allah (S). Akwai ma wanda ya same shi kai tsaye kan al’amarin. A kan haka Manzon Allah (S), duk da yana cikin hali na rashin lafiya, amma haka ya zo ya yi magana a kai, ya ce kuma su tafi wannan ya}in. Amma abin ba}in ciki bayan da suka fita Madina, wasu suka dawo kuma ba a tafi ya}in ba. Manzon Allah (S) bai ji da]in wannan al’amari ba. In mutum ya duba littafin tarihi na Sunna da Shi’a zai ga haka, da ma maganar da Manzon Allah (S) ya yi kan duk wanda bai fita ba.
Bayan wannan da kwanaki Manzon Allah (S) yana cikin dai wannan rashin lafiya ta komawarsa ga Allah (T), wata rana ya ce a kawo masa tawada da al}alami ya rubuta abin da in aka bi ba za a ~ace ba a bayansa. Wani da ke wajen da ya ga wani ya tashi zai je ya kawo, ya ce ba a bu}ata, ai bai cikin hankalinsa (wa’iyazu billahi). Haka dai hayaniya ta auku, har ta kai ga Manazon Allah (S) ya ce, su tashi su tafi. Wannan yana nan cikin Buhari.
Bayan da rashin  lafiya ta kai ga Manzon Allah (S) bai iya fita Masallaci domin ba da Salla ba, nan ma matsala ta taso dangane da Limanci. Duk da wannan halin da Manzon Allah (S) yake ciki na gayar rashin lafiya, amma haka ya dafa Imam Ali (AS) da kuma Fadhlu [an Abbas ya je ya ba da Salla. Mu dubi irin wa]annan matsaloli da Manzon Allah (S) ya fuskanta ]aya bayan ]aya gab da rasuwarsa, wato cikin wa]annan kwanaki 70. Sannan kuma lokaci guda kuma Manzon Allah (S) yana da masaniyar cewa, abin da ya gudana a ranar Ghadir ba za a aiwatar da shi ba, kuma yana da masaniyar abubuwan da za a yi wa Ahlul Baiti ]insa (AS).
To, a irin wannan damuwa da kuma ba}in ciki na wa]annan matsalolin da suka faru da kuma wa]anda za su faru a bayansa ga Ahlul Baiti (AS) ]insa, Manzon Allah (S) ya koma ga Allah(T). Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Mu dubi irin wannan babbar jarabawar, domin kamar yadda aka fa]i da farko, wannan jarabawa ta fi ]aci da kuma zafi a zuciya. Kuma Manzon Allah (S) ya rasu ne a hannun Imam Ali (AS), kamar yadda Ibn Sa’ad ya ruwaito a [aba}atul Kubra ]insa. Wani ma ya ta~a tambayar Umar dangane da abu na }arshe da Manzon Allah (S) ya fa]i, sai Umar ya ce masa ya tambayi Ali (AS). Kuma Imam Ali (AS) shi ya yi wa Manzon Allah (S) wanka da kuma sa masa likkafani, kuma shi ne farkon wanda ya yi masa Salla, sannan aka yi masa kabari aka binne shi, }ar}ashin jagorancin Imam Ali (AS). Yayin da wannan yake faruwa wa]ansu Sahabbai suna Sa}ifa domin za~en Khalifa.
Wannan ke nan a dun}ule kuma a ta}aice dangane da wafaftin Manzon Allah (S). Ga mai bu}atar gani a warware, yana iya komawa ga littafin da aka ambata.
Kuma kasantuwar wannan wata da muke ciki, wato na Rabi’ul Awwal, wata na Maulidin Manzon Allah (S), wanda saboda so da kuma girmamawa ga Manzon Allah (S) mafi yawan al’ummar Musulmi na wannan }asa, dama na sauran }asashen Musulmi suke tarurruka daban-daban a cikin wannan wata, domin tunatar da juna, dangane da abubuwa daban-daban da suke da ala}a dashi.misali ayoyin da suka  bayyana lokacin haihuwarsa, rayuwarsa gabanin aiko masa da sa}o da kuma rayuwarsa bayan aiko masa da sa}o da kuma wahalhalun da ya fuskanta wajen isar da sa}on da kuma Hijirarsa daga Makka zuwa Madina, da kuma abubuwan da suka gudana bayan komawarsa Madina, wato ya}o}i kamar su Badar, Uhud da dai makamantansu. A ta}aice dai, wa]annan tarurruka sun }unshi bayani dangane da tarihinsa, da kuma rayuwarsa mai albarka.
Amma duk da haka, akwai sashen Musulmi da suke suka ga irin wa]annan tarurruka, wanda inda za su koma ga littafai na fitattun Malaman Ahlus Sunna da kuma zantukansu za su ga akasin haka. Ga bayanai na wasu daga cikinsu: Ibnu Taimiyya a cikin littafinsa mai suna I}tida’us Sira]il Musta}im, ga abin da ya ce: “Haka nan abin da mutane suka }ir}ira Imma saboda kwaikwayon Nasara ga haihuwar Annabi Isa (AS), ko kuma saboda nuna so da kuma girmamawarsu ga Manzon Allah (S), to Allah zai yi masu sakamako na lada a kan wannan so da kuma wannan Ijtihadi, amma ba a kan bidi’a ba.”
Idan kuma mutum ya koma ga abin da Suyu]i ya ce dangane da taron Maulidi. A duba a littafinsa mai suna Al-hawi-lil- Fatawi, ga Nassin abin da ya ce a littafin nasa: “A wurina asalin yin Maulidi, wanda shi ne taron mutane, da karanta abin da ya sau}a}a daga cikin Al}ur’ani da ruwayoyi na Hadisai, wanda suka zo dangane da haihuwar Manzon Allah (S) da kuma Ayoyin da suka bayyana lokacin haihuwarsa. Sannan bayan haka a ci abinci a watse ba a }ara komai a kai ba, to wannan bidi’a ce kyakkyawa, wadda za a yi wa wanda ya yi haka sakamako mai kyau, saboda abin da haka ya }unsa na girmamawa ga Manzon Allah (S) da kuma nuna farin ciki da kuma albishir ga wannan haihuwa tasa mai daraja.”
Haka nan ya zo daga Shafi’i, wato Shugaban Mazhabar Shafi’iyyah cewa, abubuwan da da aka }ir}ira na al’amura sun kasu kashi biyu: Na ]aya, abin da aka }ir}iro wanda ya sa~a wa Al}ur’ani ko Sunna ko Ijma’i, to wannan bidi’a ce, ~atatta. Na biyu, abin da aka }ir}ira na alheri wanda bai sa~a wa wa]annan abubuwa da aka ambata ba, to wannan abin da aka }ir}ira ba abin suka ba ne.
Bayan haka kuma akwai Hadisai wa]anda Muslim ya ruwaito cewa Manzon Allah (S) ya ce, duk wanda ya Sunnata Sunna kyakkyawa a cikin Musulmi, to yana da ladarta da kuma ladar wanda ya aikata a bayansa.” Ashe a taru a tunatar da kuma ilmantar da juna dangane da tarihin Manzon Allah (S), da rayuwarsa mai albarka, da wahalar da ya sha wajen isar da wannan sa}o da ya zo da shi, to Sunna kyakkyawa ce. Kuma idan muka koma ga fannin Usulul Fi}ihu za mu ga cewa }a’ida ga asalin abubuwa ita ce halasci, sai dai idan Nassi ya zo da yake nuni ga haramcinsa. A ta}aice dai, sukar Mauldi a wannan nahiyar tamu guba ce wadda ta zo mana daga baya-baya, a da babu ita.
Bayan haka watan Maulidi wata ne na muhasaba ga kawukanmu a ]ai]aiku da kuma al’ummance. Na ]aya, yaya muke wajen koyinmu da kuma kwafar mu ga Manzon Allah (S) ? Na biyu, yaya muke a wajen Manzon Allah (S), yaya Manzon Allah (S) yake a wajenmu? Na uku, yaya ala}armu take da Manzon Allah (S) a zahirance da kuma ba]inance.
Insha Allah za a ]ora bayani kan wannan.


No comments:

Post a Comment