Sunday 10 February 2013

Bayani kan Azumi 1.


Kamar yadda aka ce a darasin da ya gabata, cewa insha Allah (T) a wannan darasi za a kammala shimfi]a da kuma gabatarwa, da ma shiga cikin babobin Fi}hu. To kasantuwar mun shiga cikin watan Ramadan ,ya zamanto zai yi kyau da kuma muhimmanci mu shiga cikin babobin fi}hun, wato babin Azumi, in ya so bayan kammala babin Azumin sai a kammala ita waccan shimfi]a da kuma gabatarwa da shiga babin farko, wato babin tsarki. Saboda haka wannan darasi zai gudana ne a babin Azumi. Kuma saboda ya yi sau}i wajen gabatar da shi, an yi masa fasali 12 ne. Ga yadda suke.

1. Bayani dangane da hanyar tabbatar da watan Ramadan da kuma Shawwal.
2. Bayani dangane da niyyar Azumi.
3. Bayani dangane da Azumi ranar shakka.
4. Bayani dangane da abubuwan da suka wajaba mai Azumi ya kame daga gare su.
5. Bayani dangane da wanda ya yi abun da yake karya Azumi .
6. Bayani dangane da sharu]]an Azumi.
7. Bayani dangane da ramakon Azumi
8. Bayani dangane da abubuwan da aka karhanta wa mai Azumi ya aikata, da kuma abubuwan da aka mustahabbantar ya aikata.
9. Bayani dangane da rabe-raben Azumi
10. Bayani dangane da hukunce-hukunce na Azumin matafiyi.
11. Bayani dangane da kaffarar Azumi da kuma fidiya.
12. Bayani dangane da wasu mas’alolin Azumi na zamani.
Insha Allah a kan wannan fasaloli ne bayani zai guna dai dai gwargwadon iko.
Azumin watan Ramadan Allah (T) ya wajabta shi ga wannan al’umma ta Manzonsa ne a watan Sha’aban shekara ta biyu bayan hijira, kuma an wajabta shi ne domin samun ta}awa. Kamar yadda Alla (T) yake fa]i a cikin Suratul Ba}ra, Aya ta 183; “Ya ku wa]anda suka yi imani an rubuta Azumi a kanku, kamar yadda aka rubuta a kan wa]anda suka gabace ku, domin ku samu ta}awa”.
Kuma shi ‘Saum’ wato Azumi, ma’anarsa a luggace shi ne kamewa, amma a is]ilahance, yana nufin kamewa daga wasu ababe iyakantattu, a lokaci iyakantacce, da nufin kusanci ga Allah (T). Sai kuma bayani na wa]annan fasaloli 12 da aka ambata a sama.
1. Bayani dangane da hanyar tabbatar da watan Ramadan da kuma watan Shawwal. A Imamiyyah akwai hanyoyi guda biyar kamar yadda Fu}aha, wato Mujtahidai suka kawo, hanyoyin sune; i. Ganin watan da ido ko da ko wanda ya ganin shi ka]ai ne. ii. Jama’a masu yawan gaske su gani, da kuma watsuwar labarin gani, amma ya zamanto ya fa’idantar da ya}ini. Wato mutum ya zamo ya natsu, ya kuma samu ya}ini a kan hakan. iii. Cikar watan Sha’aban 30, ko kuma cikar watan Ramadan 30, wato idan Sha’aban ya cika 30 daidai, to washegari ko an ga wata ko ba a gani ba, washegari 1 ga watan Ramadan ne, wato za a tashi da Azumi. Haka nan idan watan Ramadan ya kai 30 washegari ko an ga wata, ko ba a ga ni ba 1 ga watan Shawwal ne, wato za a aje Azumi, domin watanni na Musulunci ba su yin 31ko 28, ]ayan biyu ne, ko dai su yi 29, ko kuma 30. iv. Shaidar adilai guda biyu na cewa sun ga watan. Wato ya zamanto su kasance su biyu, ba mutum ]aya ba.
Shi ya sa da a ce mutum ]aya ne kawai ya ga wata, ba wanda ya gani sai shi. To a irin wannan yanayin shi ganin watan zai zama hujja a kansa ne kawai, amma ba a kan sauran mutane ba, inda yake zama hujja a kan sauran mutane, sai idan su biyu ne, kuma da shara]in su zama adilai, kuma maza ba mata ba, ko da ko matan su hu]u ne. Idan mutum ya duba cikin littafin Tahriril Wasila na Imam Khumaini ({S) zai ga wannan fasali na bayani na hanyar tabbatar da watan Ramadan da kuma Shawwal a mas’ala ta uku, inda ya ce; “Ba a la’akari wajen tabbatar da wata ga shaidar mata hu]u, ko namiji ]aya da kuma mace biyu. Ko namiji ]aya tare da rantsuwa (wato shi ka]ai ya gani, sai kuma a ce ya rantse da Allah a kan haka, duk ba a la’akari da haka)”.
A ta}aice dai a mas’alar ganin wata irin wannan shaida ta adilai biyu, ta ta}aita ga maza ne kawai, wato a Imamiyya, amma a Mazhabar Hanafiyya da kuma Hambaliyyah za a iya kar~ar shaidar mata a kan wannan mas’ala ta ganin wata.
Haka nan Imam Khumain ({S) yana cewa su shaidar wa]annan Adilai guda biyu ba a la’akari da cewa ganin watan nasu ya kasance lokaci guda, (wato a ce suna waje ]aya, a’a ko da a ce wannan yana nan unguwar, ]ayan yana waccan unguwar, ko kuma wannan ya gani a yanzu, ]ayan kuma daga baya, in dai a daren ne, in an yarda da adalarsu duka za a iya amsa). iv. Hanya ta biyar ta ganin watan Ramadan da Shawwal ita ce hukuncin Hakimu Shar’iy, wato Mujtahidi ya yi hukunci da ganin wata. Misali ya ce na yi hukunci a kan wata ya tsayu, kuma a irin wannan yanayi na hukuncin Mujtahidi a ganin wata, ya hau kan kowa idan ya ji, ko ya gani na ya tashi da Azumi ko kuma ya aje. Wato ba zai ta}aita ga masu Ta}lidi da shi ba, a’a hatta ma a kan wa]anda ba su ta}lidi da shi. In da yake ta}aita ga masu ta}alidi da shi kawai shi ne, sai idan fatawa ya yi, ba hukunci ba.
Haka nan tabbatuwar ganin wata, a wani gari bai sa wani gari su yi aiki da shi ba, sai dai idan sun kasance makusantan juna ne, ko kuma idan ‘Ufu}’ ]in su ]aya ne. Misali a ce lokacin su ]aya ne, ko kuma akwai kusancin lokaci sosai tsakaninsu. Wannan ke nan dangane da fasali na ]aya.
2. Bayani dangane da niyyar Azumi. Niyya shara]i ce ga Azumi, wato dole sai da niyya. Saboda haka da niyyar za ta ku~uce wa mutum saboda wani uzuri, ko dalili. Misali ya manta ne bai yi ba, ko ya gafala, ko kuma ya jahilci haka, sai daga baya ya tuna, ko ya sani gabanin Zawal, ko bayan Zawal na ranar. To, idan Azumin na wajibi ne, misali Azumin watan Ramadan ne, ya manta bai yi niyya ba, ko kuma ya jahilci cewa ashe watan Ramadan ya shiga, wato an ga wata jiya, to, wannan mantuwa da kuma jahilta, in gabanin Zawal ne ya tuna, ko ya sani. To nan take sai ya yi niyyar Azumin, kuma Azumin ya yi. Amma da shara]in shi wanda ya jahilci shigar watan Ramadan ]in, in bai yi abubuwan da suke karya Azumi ba. In ko ya yi, zai kame bakinsa ne, bayan Ramadan sai ya rama Azumi ]aya. Amma idan sai bayan Zawal ne ya tuna, ko ya sani cewa watan Ramadan ya shiga, to mahallin niyya ya }ubuce. Amma idan a Azumin nafila ne ba na wajibi ba, lokacin yin niyyar yana gudana har bayan Zawal, kai har ma zuwa gab da fa]uwar rana. Misali a ce mutum ya wayi gari bai ci komai ba, kuma bai yi wani abu da yake karya Azumi ba, har bayan Zawal kai hatta ma gab da fa]uwar rana, to, a nan in ya so yana iya yin niyyar Azumi na nafila. Kuma Azuminsa ya yi. Akasin in da Azumi na wajibi ne, in Zawal ya yi ba zai iya yin niyya ba.
Haka nan kuma kamar yadda yake wajibi yin niyya gabanin Azumi. To, haka nan dawwamar da niyyar Azumi cikin yini wajibi ne. Saboda haka da mutum zai yi niyyar fasa Azumi, wato ya a jiye Azumin, to a nan Azumin nan nasa ko na wajibi ne, ko na nafila ne, ya ~aci. Inda suka bambanta a hukunci shi ne, in a Azumin nafila ne, in ya dawo daga niyyar aje Azumi, wato ya yi niyyar ci gaba da Azuminsa in gabanin Zawal ne haka ya auku, to Azuminsa ya inganta, in ko Azumin wajibi ne, to ko da ya dawo da niyyar ci gaba da Azumi gabanin Zawal, to duk da haka Azuminsa na ranar dai ya lalace. Wannan ke nan dangane da fasali na biyu.
3. Bayani dangane da Azumin ranar shakka. Ranar shakka ita ce ranar da ake taraddudi, wato shakka cewa ranar }arshe ce ta watan Sha’aban, ko ranar farko ce ta watan Ramadan. To ita wannan ranar ba wajibi ba ne mutum ya azumce ta. Da mutum zai azumci ranar da niyyar cewa ranar a cikin watan Sha’aban take, sai daga baya ta bayyana masa ashe 1 ga watan Ramadan ne, to wannan Azumi ya wadatar masa.
Haka nan a cikin Tahriril Wasila, Imam Khumaini ({S) yana cewa; “Da mutum zai azumci ranar shakka da niyyar cewa idan ranar ta watan Ramadan ce, to Azumin wajibi ne a kansa, in kuma ba haka ba, to nafila ne a kansa”. Ya ce; “To haka bai nisanta daga inganta ba”. Wato ya inganta. Ya ci gaba da cewa; “In da zai azumci ranar da niyyar cewa na Ramadan ne, to wannan Azumin nasa bai yi ba. Ana Ramadan da kuma nafila, (wato ya tashi a tutar babu).
Matsalar ita ce idan ya yi Azumin da niyyar Ramadan kawai. Amma da zai yi Azumin da niyyar Sha’aban kawai, ko kuma da niyyar idan Ramadan ne, ko Sha’aban, to duk a wa]annan fuskoki guda biyu Azuminsa ya inganta, kuma ya wadatar masa a matsayin 1 ga watan Ramadan ]insa.
Haka nan da a ce a ranar shakku, mutum ya yi niyyar ba zai azumci ranar ba, sai a cikin yini ta bayyana masa cewa ashe Ramadan ya shiga, wato an ga wata jiya. To, a nan idan ya yi abin da yake karya Azumi, misali a ce ya ci abinci da safe, ko kuma a’a wannan labarin ya same shi ne bayan Zawal, ko da bai yi wani abu da yake karya Azumi ba, wato misali bai ci komai ba. In dai bayan Zawal ne ya ji, to, a wa]annan fuskoki guda biyu abin da ya hau kansa shi ne; wajibi ne ya kame baki da kuma duk ababen da suke karya Azumi, bayan watan Ramadan sai ya rama Azumi ]aya. Amma ko inda akasin haka ne, wato labarin ya same shi na ganin wata gabanin Zawal, kuma bai ci komai ba, ko yin wani abu da yake ~ata Azumi ba, to a nan abin da zai yi shi ne; sai ya yi niyyar Azumi, kuma ya wadatar masa. Wato ba zai yi ramuwa ba.
Haka nan Imam Khumaini ({S) ya ce da mutum zai yi Azumin ranar shakka da niyyar Sha’aban, sai ya manta ya yi wani abin da yake karya Azumi, misali ya manta ya ci abinci, sai daga baya ta bayyana masa ashe ranar ta Ramadan ce. To, wannan Azumin shi ma ya wadatar masa.
Amma a sauran mazahib na Ahlus Sunna sun sa~a a kan wannan mas’ala na cewa idan mutum ya yi Azumi ranar shakka, sai ta bayyana ashe Ramadan ya shiga. To, wannan Azumin ya wadatar masa, kuma ba zai yi ramuwa ba? To, a nan da Malikiyya da Shafi’iyya da kuma Hambaliyya, sun tafi a kan cewa, wannan Azumin bai wadatar ba, zai rama ne. Amma su Hanafiyya sun ce, ya wadatar masa, ba zai yi ramuwa ba. Wato dai kamar yadda Immamiyya suka tafi a kai. Amma dukkan Mazahib ]in, wato Imamiyya, Hanafiyyah, Malikiyyah Shafi’iyyah da kuma Hambaliyya, sun yi ittifa}i a kan wannan mas’alar, cewa idan mutum ya ci abinci a ranar shakka, sai ta bayyana ashe ranar ta Ramadan ce, to wajibi ne mutum ya kame baki, bayan watan Ramadan, sai ya rama Azumin. Wannan ke nan dangane da fasali na uku.
4. Bayani dangane da abubuwa da ya wajaba mai Azumi ya kame daga gare su. Idan mutum ya duba a littafan Fi}hu na Imamiyya, zai ga kusan kowace Risala Amaliyyah sun kawo su. 1. Cin abinci. 2. Shan abin sha. 3. Jima’i. 4. Fitar da maniyyi. 5. Yi ma Allah (T) da Manzonsa (S) da kuma A’imma (AS) }arya da gangan. 6. Nutsar da kai cikin ruwa. 7. Wanzuwa da janaba zuwa ketowar Alfijir da gangan. 8. Isar }ura mai kauri zuwa ga ma}ogoro. 9. Yin amai da gangan. 10. Hu}na, wani nau’in magani ne wanda tura shi ake yi, wani lokaci na ruwa ne, wani lokacin kuma jamidi ne. To, wanda yake da matsala, wato karya Azumi shi ne Hu}na, na ruwa ba jamidin ba. Kuma }arin ruwa na ‘drip’ duk ya shiga cikin wannan hukunci, domin shi kamar cin abinci ne ta jijiya. Wa]annan sune abubuwa 10, wanda ya wajaba mai Azumi ya kame daga gare su. In mutum ya duba Tahriril Wasila ko Zubda zai ga Imam Khumaini ya kawo su da kuma bayani dangane da kowannen su.
Wani tambihi a nan shi ne, daga cikin wa]annan abubuwa guda 10 akwai wa]anda suka ke~anta da Fi}hun Imamiyya ne kawai, wato babu su a Fi}hun Ahlus Sunna, uku ne. Daga ciki akwai; 1. Yi wa Allah (T) da Manzo (S) da kuma A’imma (AS) }arya da gangan. A Imamiyya, misali a watan Ramadan, mutum ya ce Manzon Allah (S) ya ce kaza, alhali ya san bai ce ba, wato a kan }arya ya fa]i, to Azuminsa ya lalace, ko kuma mutum ya ce Imam wane, misali Imam Sadi} (AS) ya ce kaza, alhali a kan }arya ya fa]i, shi ma Azuminsa ya lalace. Kuma kamar yadda ya zo, Annabawa su ma sun shiga cikin wannan hukuncin, wato idan mutum ya ce Annabi wane ya ce kaza, alhali bai ce ba, a kan }arya ya fa]i, to shi ma Azuminsa ya lalace.
In muka duba a Mazahib na Ahlus Sunnah su ba su da wannan hukuncin, wato ya ke~anta a Imamiyya ne kawai. Sai dai nan a lura, ana fa nufin }aryar da mutum ya yi da gangan. Kuma yana sane ba wai a kan asasin ya hikaito ne daga wani ba. Ko ya ciranto daga wani littafi ba, in irin wannan ne, shi bai ~ata Azumi. Wanda ke ~ata Azumi shi ne mutum ya }ir}iri magana da kansa, ya ce Annabi ya ce, ko Imam wane ya ce, to shi ake nufi. Kuma wannan bai ta}aita da fa]i da baki ba, a’a ko da rubutawa ne, misali mutum ya rubuta cewa Manzon Allah (S), ko A’imma (AS) sun ce kaza, alhali a kan asasin }arya ne da gangan. Wato ba a kan asasin ya hikaito ba ne daga wani ko ya ciranto ne daga wani littafi ba. To shi ma Azuminsa ya lalace. Kai ko da ma ta hanyar ishara ne, kamar yadda Imam Khumaini ya fa]a. Ga misalin da ya bayar, da a ce mai tambaya zai tambaye shi, Manzon Allah (S) ya ce kaza, sai ya yi ishara da na’am, alhali a’a ne, ko kuma ya yi ishara da a’a, alhali na’am ne. To, Azuminsa ya ~aci. Saboda haka wa]annan hanyoyi guda uku, wato fa]i da baki ko rubutawa, ko ishara, idan mutum ya yi gangancin }arya da su ga Allah (T) da Manzon Allah (S) da kuma A’imma (AS) da ma sauran Annabawa (AS), in dai da gangan ne, to Azuminsa ya lalace.
2. Nutsar da kai cikin ruwa. Wannan ma yana daga cikin abin da Imamiyya suka ke~anta da shi, wato babu hukuncinsa a Fikhun Ahlus Sunnah. A Imamiyya misali a watan Ramadan mutum ya nutsar da kansa a ruwa, to Azuminsa ya lalace. Misali a ce ya shiga kogi yana iyo, sai ya nutsar da kansa a ruwa. Ko kuma mutum ya samu ruwa ya sa kansa baki ]aya a ciki, ko da jikinsa na waje, shi ma Azuminsa ya lalace. Sai dai fa a lura a nan sosai, ba ana nufin ko da mutum ya zuba ruwa a kansa ba ne, ko kuma misali a }ar}ashin shawa, ruwa na zubo masa. Wannan duk ba matsala, kuma ba shi ake nufi ba. A’a abin da ake nufi kuma yake ~ata Azumi shi ne mutum ya nutsar da kansa baki ]aya cikin ruwa, ta hanyar iyo, a ruwa ko kuma ta wata fuska.
3. Wanzuwa da Janaba da gangan har Alfijir ya keto a watan Ramadan, ko kuma a ramuwar watan Azumin Ramadan, shi ma wannan ya ~ata Azumi. Shi ma wannan ya ke~anta da Fi}hun Imamiyya ne kawai, wato ba wannan hukuncin a Fi}ihun Ahlus Sunnah. Saboda haka a Imamiyyah idan janaba ta kama mutum a watan Ramadan sai ya zamanto da gangan bai yi wanka ba har alfijir ya keto, to Azuminsa na ranar ya ~aci. In ko a ramuwar Azumin Ramadan ne, haka ta faru, to ko da da gangan ne, ko ba da gangan ba, Azumin ranar ya ~aci. Amma idan a Azumin nafila ne, ko da da gangan mutum ya wanzar da janaba har alfajir ya keto, to bai ~ata Azumin ranar ba. Kamar yadda Imam Khumaini ({S) ya yi bayani a Tahariril Wasila. Saboda haka wannan hukunci ya ta}aita ne ga Azumin watan Ramadan da kuma ramuwarsa.
Kuma kamar yadda wanzuwa da janaba zuwa ketowar alfajir a watan Ramadan yake ~ata Azumin ranar, to haka nan wadda jinin hailarta ko nifasinta ya ]auke, sai ba ta yi wanka ba da gangan har alfijir ya keto, to ita ma ba ta da Azumin ranar. Shi ne Imam Khumaini yake cewa idan mai jinin haila da nifasi ya yanke, to, wajibi ne gare ta ta yi wanka. In ko ba ta yi ba da gangan, to Azuminta ya ~aci. Amma wanda ya rasa tsarkaka guda biyu; wato ruwa da abin yin taimama idan babu ruwa, ga shi kuma da janaba ko jinin hailarta ko nifasinta ya ]auke, to masu irin wannan larura haka za su ]auki Azumin, kuma Azuminsu ya inganta, amma wannan hukunci ya ta}aita ne idan a watan Ramadan ne, amma idan a ramuwar watan Ramadan ne, to Azumin ranar ya lalace, wato ya ~aci.
Wanda janaba ta kama shi a watan Ramadan da daddare ya halatta ya yi barci gabanin ya yi wanka, amma fa da tsammanin in zai farka. To da zai yi barci da tsammanin zai farka, sai bai farka ba har alfijir ya keto, to, ya zai yi? To a nan ]ayan biyu ne, in dama ya yi gina a kan cewa ko da ya farka ba zai yi wankan ba, ko kuma yana taraddudi in ya farka ya yi wanka ne, ko kar ya yi, a’a ya yi niyyar ko ya farka ba zai yi wankan ba. To duk a wa]annan fuskoki da aka ambata hukuncin wanda ya wanzu da janaba da gangan har alfijir ya keto, shi ramuwa da kuma kaffara ne suka hau kansa. Amma da a ce kafin ya yi barcin ya yi ginin ko niyyar cewa in ya farka zai yi wanka ne, sai kuma bai farka ba har alfijir ya keto, to wannan shi ba komai a kansa.
Insha Allah (T) a darasi na gaba za a ci gaba a cikin wannan babi na Azumi.

No comments:

Post a Comment