Saturday 9 February 2013

Darussa 12 daga rayuwar Imam Khumaini [KS]


Watan jiya,wato watan jimada sani shine wata wanda aka haifi Imam khumaini a cikinsa,domin an haife shine ran 20 ga watan jimada sani hijira na da shekara 1321,kuma ranar haihuwarsa tayi muwafa}a da ranar  haihuwar shugaban mataye baki ]aya,wato ‘yar Manzon Allah [S],sayyidah fa]ima [SA].
Dama kuma shi jikan sayyidah fa]ima[SA]]in ne,ta hanyar Imam Musa al-kazim [AS],wanda shi yasa ake ce masa al-musawi.Kuma rasuwarsa ta kasance 3 ga watan yuni 1989,amma a }idayar Hijiriyya 28 ga watan shawwal ne,1409.Wato yau shekaru 22 kenan cur da rasuwarsa.                                                                                                      To,kasantuwar wiladarsa da kuma wafatinsa sun yi kusa da juna a wannan }idaya ta Hijiriyya da miladiyyar ya zamanto zai yi kyau kawo wasu darussa daga rayuwar Imam Khumaini,wanda in muka aikata su a rayuwarmu zasu kasance insha Allah masu amfani gare mu duniyarmu da kuma lahirarmu.                   Koba komai duk wanda ya bibiyi tarihi da kuma rayuwar Imam Khumaini zai fahimci cewa lalle Imam Khumaini baiwa ce kuma kyauta ce ta musamman da Allah [T] ya bai wa alummar musulmi ta wannan zamani,kai hatta ma wa]anda ba musulmi ba,domin da yawansu bayyanar Imam Khumaini ya canza masu tunani dangane da yadda suke dubar  addinin musulunci,wanda sakamakon haka da yawa sun musulunta.                                                                                                                                                                                                 Ashe kenan sanin tarihi da kuma rayuwarsa wani abu ne wanda yake da gayar muhimmanci,saboda ma muhimmancinsa  za mu ga malamai da dama da suka zauna dashi,  suka kuma rayu tare da Imam Khumaini,da ma masana daga sassan duniya daban-daban sun yi rubuce-rubuce na littafai wasu ma mujalladat ne.Misali littafi mai suna ‘{abasat min hayatil Imam Khumaini’,wanda mujalladi hu]u ne.Da kuma misali littafi mai suna ‘Rajulun min ahli  }um’,wanda babba ne sosai,da dai sauransu;wanda yanzu haka a birnin }um akwai wani babban ]akin karatu [library],wanda duk littafan dake ciki littafai ne wa]anda suke da ala}a da Imam Khumaini,Ko littafan dashi ya rubuta,ko kuma wa]anda ya’yansa suka rubuta,misali su sayyid mustafa da kuma sayyid Ahmad.Ko kuma wa]anda wasu malamai suka rubuta dangane da Tarihin sa da kuma rayuwarsa.Saboda haka sanin tarihi da kuma rayuwar Imam Khumaini shi zai taimaka wa mutum domin yayi koyi dashi.Kamar yadda wani malami wanda ya rayu da tare da Imam Khumaini sama da shekaru 50,wato Ayatullah Nasiriy yake cewa, “na kasance na kan fa]a wa mutane a wasu lokuta,in kun kasance baku sami yin karatu gaban Imam khumaini ba,to kada ku haramta wa kanku yin koyi dashi,domin koyi da shi shima wani darasi ne wanda yake gina mutum ya zama salihi”.                                                                                                                                                                Saboda haka anan insha Allah za’a kawo wani sashen ~angaren rayuwar Imam Khumaini,ba duka ba.Domin kewaye ~angarori na rayuwar Imam wani abu ne wanda yake da wahala,koma ace ba zai yiwu ba,kamar yadda Ayatullah Nasiriy yake cewa, “a iyakar sanina har yanzu wa]anda sukayi rubuce-rubuce ko bayanai dangane da rayuwar Imam Khumaini basu kewaye duka ba,balle ba zai ma yiwu har abada a iya kewaye duka ba.” Akan asasin haka ga wa]ansu darussa game 12,amma a ta}aice:                                                                1.NIZAMINSA:Wato tsara alummarsa,Imam khumaini ya kasance komai nasa a cikin nizami yake,wato lokacin sa ne,alamarin sane,yadda yake tasarrufi da dukiya,duka a tsare suke.Kuma ya kasance ya na yawan kwa]aitar da ]alibansa muhimmancin su kiyaye nizami na lokutansu da kuma al’amuransu na yau da kullum,saboda ma gayar nizaminsa da lokaci,ya kasance agogo ne a gidan sa da kuma ]alibansa dama sauran jama’a,]aya daga cikin masu hidima a gidan Imam yana cewa,awowi 24 na Imam a tsare suke,ta yadda da sunga yana wani abu sun san }arfe kaza kenan;ta yadda da ]ayan su,da zai yi tafiya zuwa wani gari a tambaye shi mai Imam yake yi yanzu,in ya duba agogonsa zai ce ya na kaza ne,watau saboda gayar yadda suka kiyaye nizamin Imam na lokutansa.                                                                                      Kuma wannan nizami na Imam na lokutan sa, bai ta}aita ga ayyukansa na ibada ko bahasinsa na ilimi ko kuma ganawarsa da jama’a ba ,a’a hatta barcinsa da cin abincin sa a cikin nizami suke.Yazo akan cewa,wani lokaci a cikin gida idan an gama abinci akan zo ace masa an gama abinci akawo masa,sai ya duba agogo,yace saura minti kaza.A ta}aice dai wa]anda suke tare da Imam khumaini,duk lokacin da suka ga yana aikata wani abu,ibada ne,karatu ne,cin abinci ne,barci ne,ganawa da ba}i ne,sun san ko }arfe nawa ne,saboda Imam ko wane abu nasa yana ba shi lokacinsa.                                                                                               Akwai ma wani abin mamaki daya ta~a faruwa lokacin ya na gudun hijira a birnin Najaf,yazo akan cewa tsawon zaman da yayi a birnin Najaf na shekaru 15,kullum sai ya ziyarci kabarin Imam Aliy [AS].To, ta hanyar da yake bi zuwa ziyarar,akwai wani shago,watau kanti na sai da kaya,wanda akwai wani mutum da ya kan zo ya zauna wajen mai kantin suna hira,to yau da gobe,har ya kiyaye lokacin da Imam yake bi ta wurin,wata rana Imam yazo zai wuce sai shi wannan mutumin ya duba agogonsa sai yaga sa~anin yadda ya san Imam na wu cewa,sai ya tambayi mai shagon,}arfe nawa? Sai mai shagon yace }arfe kaza.Sai mutumin yace,haba! Na san wannan malamin kullum yana wu cewa nan }arfe kaza,sai ya fahimci agogonsa ne,ya samu matsala,akwai misalai da dama saboda gudun tsawaitawa,ba zai yiwu akawo ba. A ta}aice dai sa’a 24 na Imam a tsare suke.                                                                                                    2.IBADARSA:Imam Khumaini ya kasance mai yawan ibada,duk  wa]anda suka zauna tare da shi sun tabbatar da haka.Ga misalan wasu daga cikin ibadodinsa.                                                                                                               A-Tahajjud ]insa: watau sallar dare.Yazo akan cewa ya kwashe shekaru saba’in, bai ta~a fashin sallar tahajjud ba,watau a halin da yake zaune a gida da kuma halin tafiya.Kamar yadda yazo akan cewa,lokacin da yake dawowa daga gudun hijira watau daga faransa zuwa iran,to,a cikin jirgin sama lokacin daya saba yin Tahajjud yayi,sai aka ga kawai yana yi .Kuma ya tsayu da ita a halin tafiya da kuma rashin lafiya.Kamar yadda yazo,aka ce,wani lokaci an ]auke shi a motar Asibiti daga Qum zuwa Tehran,da lokacin Tahajjud ]insa yayi sai aka ga yana yi.Kai hatta ma jinyar da yayi ta rashin lafiyar wafatinsa,bai bar Tahajjud ]insa ba! Yazo akan cewa daren }arshe na rayuwarsa, da isha-ra yayi sallar tahajjud ]insa,wato saboda raunin da jikinsa yayi na jinya.A lokacin da yake isha-ra na salla ]in,likitocin dasu ke kula dashi sun ]auka ko wani abu yake bu}ata.’yar’sa tace  masu yana sallah ne.                                                    B-Karatun Al}ur’aninsa: Yazo akan cewa a kowane rana Imam khumaini yakan karanta izu Ashirin,wanda yake nuna cewa a kowane kwana uku yake saukewa,Akwai ma wani a cikin masu yi masa hidima yana cewa so da yawa mu kanje wajen Imam cikin yini,domin ko yana bu}atar wani abu na hidima,sai mu same shi yana karatun Al}ur’ani.                                                                                                                                      C-Azkar ]insa:Imam ya kasance mai yawan zikiri,kamar yadda wanda ya zauna tare dashi mai suna Ansari Kar-maniy ya bayyana,yace,Imam bai ta~a gafala daga zikiri ba.Yaci gaba da cewa sau da yawa Imam Khumaini ko tafiya yake yi zaka ga akwai tasbaha a hannunsa ya na zikiri.                                                                D-Addu’oin sa: Imam ya kasance mai yawan addu’oi,musammam addu’oin ma’asurai,watau wa]anda aka ruwaito daga ma’asumai [AS].Tabbas haka ne,duk wanda ya bibiyi  wasu littafai da Imam ya rubuta,zai ga yana yawan kwa]aitarwa da kuma shajja’awa wajen karanta littafan addu’oi.Misali,Ansari  kar-maniy yana cewa, “sau da yawa mukan je wajen Imam a wasu lokuta na sashen dare,sai mu jishi yana biya addu’oi.Har ya bada misali da Du’a’u khumail.Imam ya kasance yana yawan kwa]aitarwa,na biya Du’a’u sha’abaniyya.ya kasance yana cewa itace addu’a,wanda baki ]aya A’imma [AS] sun lizimce ta.Asalin addu’ar,kamar yadda yazo a ruwaya,daga Imam Aliy [AS] ne.                                                  E-AZUMINSA:Har wala yau Imam ya kasance mai yawan azumi na nafila,watau baya ga azumin ramadan ,ya mazo akan cewa baki ]ayan darare na watan ramadan,ya kan shagaltu da salloli da kuma addu’oi ne.Har ila yau,yazo akan cewa idan Imam ya ]auki azumi baya bu]e baki har sai yayi sallar magariba da kuma isha’i da nafilfilinsu da kuma ta’a}ibat ]insu.                                                                                                 3.KUKANSA:Imam khumaini ya kasance mai yawan kuka saboda tsoron Allah [T] da kuma shau}i gare shi,har ila yau mai yawan kuka ne,saboda abubuwan da suka samu Manzon Allah [S] da kuma Ahlul-baiti [AS] wanda ya bibiyi tarihin rayuwarsa zai ga hakan.Ga misali lokacin Imam ya na birnin Qum,watau tun gabanin gudun hijira.Wata rana babban ]ansa watau sayyid mustafa,sai abokinsa ya ziyarce shi,sai ya kwana a gidan.Da tsakar dare,sai shi wannan ba}on ya tashi a firgice, saboda yadda yaji sautin kuka na tashi a cikin gidan,yana tunanin me nene ya faru? Sai ya ta da sayyid mustafa daga barci,domin yaje ya bincika menene ya faru? Sai sayyid mustafa ya shaida masa cewa ai babansa ne yake sallar tahajjud yake kuka.Haka nan Hurras dake gadin gidan,sukan fa]i makamancini hakan,cewa duk lokacin da yake sallar tahajjud su kan ji sautin kuka.Haka nan duk lokacin munasabar zaman makoki ta shahada ko wafatin ]aya daga cikin ma’asumai [AS] ya kan yi kuka,kuka mai yawa,musamman zaman makoki na wafatin Nana fatima [AS] da kuma na Ashura.Wa]anda suka zauna tare da shi sun ba da shaida cewa,duk lokacin da aka ambaci sunan Imam Husain [AS],idan Imam Khumain na wajen sai an ga hawaye sun gangaro masa.                                                                                                                                                                       4.ILIMINSA: A wannan fage na ilimi,Imam khumaini ba ma kawai ya }ware bane a dukkan fannoninsasss,a’a ya yi zurfi a ciki.Babban  hanyar da mutum zai san hakan itace ya bibiyi littafan da ya rubuta a fannoni daban-daban na ilimin addini,domin Imam khumain ya rubuta littafai da dama akan fannoni daban daban,misali fannin fiqhu Usul-fiqh Ilimul Rijal,Irfan da dai sauransu.Akwai ma wani littafi na irfan da ya yi sharhinsa mai suna Fususul-hikam,wanda wannan littafi ko a malaman irfan,ba kowa yake iya fahimtar sa ba ballantana ma ya yi sharhi a kai.                                                                                                                                                              Ayatullah shahid mu]ahhari yana cewa dangane da wannan littafi na fususul hikam,a kowane zamani wa]anda suke iya fahimtar sa [watau shi littafin] adadinsu bai wuce a }idaya su da yatsu ba.Haka nan fannin tafsiri na Al}ur’ani,shima akwai rubuce-rubucensa,da kuma muhadarori akai,duk da kasancewar sashen wasu surori ne da kuma ayoyi Imam Khumain ya yi tafsirinsu,ba wai dukkan al}ur’ani ba.Da mutum zai samu irin wa]annan littafan da suka }unshi tafsirin sa, ga wasu surori da kuma ayoyi,zai fahimci irin zuzzurfa ilimin da yake dashi na tafsirin Al}ur’ani,da kuma tunanin cewa da a ce ya rubuta tafsiri na Al}ur’ani baki ]aya,to da Allah [T] ne, ka ]ai ya san adadin juzu’o’in da zai kasance.                               Kyakkyawan misali anan shine mutum ya nemi littafinsa mai suna ‘Tafsirul Ayatil basmala’ na shi Imam khumain.zai ga cewa a tafsirin Bisimillah kawai sai da aka samu shafi ]ari da ashirin da ]aya.                             Haka nan fannin Hadisi, shima Imam ya rubuta littafi akai,wanda littafi ne sananne, kuma fitacce mai suna Al’arba’una Hadis;Hadisai 33 suna magana akan akhla},sauran 7 suna magana akan a}ida.A ta}aice dai Imam ya rubuta littafai da dama,wa]anda ko a yanzu akwai littafai a}alla guda 45 wa]anda an buga su,kuma ana samun su a kasuwa,banda wa]anda ba’a buga suba,ko kuma ana kan bugawa.                        Haka nan kuma wani ~angare da yake da ala}a da ilimin Imam shine uslubin karantarwarsa,wanda nasa uslubin yana da banbanci,in an kwatanta dana sauran malamai,kamar yadda wasu da su kayi karatu a wajensa suka bayyana.Ga misali guda biyu daga cikinsu.shaikh karimi yana cewa,uslubin karantar war Imam,wani abune wanda yana da ban mamaki kuma mai }ayatarwa.Tsawon wannan lokaci,kusan shekaru talatin da ‘yan kai,wanda na shafe ina karatu a gaban malamai masu yawa a hauzozin Qum da najaf ,uslubinsu na karantarwa da na Imam akwai banbanci.Imam ya kasance idan yana yi mana bayani na mas’aloli awani fanni na ilimi,ya kan yi wanda ya tattaro duk wani abu da yake da ala}a da mas’alar,wato bayani shamili kuma zuzzurfa,ta yadda yake,duk wanda yake zaune yake sauraron darasin,zai wadatu ga komawa ga wasu littafai ko bayanin wasu malamai domin }arin bayani.Haka wani da yayi karatu a wajensa mai suna khatim yazdi yana cewa’’Shekaru goma shabiyar da Imam yayi a najaf,na kasance tare dashi.Akwai wasu ababe da suka janyo hankalina gare shi.Na farko uslubin karantarwar Imam.Duk da kasancewar Imam babban malamin falsafane kuma malamin Irfani awannan zamanin,amma tare da haka in yana yi mana bayani a darussa na fa}hu,zai mana bayani gam sasshe,kai kace bai san kome ba in ba fi}hu ba.’’Ya ci gaba da cewa.Domin a fahimci abin da nike nufi ga misali;Idan }wararre a fannin ilimin falsfa,misali zai yi bayani dangane da mas’aloli na fi}hu ko kuma yayi tafsirin wasu ayoyi na Al }ur’ani,a guje za ka ga a cikin bayanansa ya kawo kalmomi na falsafa,amma idan Imam na bayani dangane da falsafa,to,falsafar kawai za kaji.Haka nan irfan, to irfan ]in kawai za kaji,haka nan fi}ihu da dai sauransu,wanda ta}aita kai acikin fannin ilimi lokacin bayani yana da wahala.’’A ta}aice dai uslubin karan tarwar Imam a ko wane fanni na ilimi,za a iya siffata shi da cewa’Al jami’I,Al mani’I,watau wanda ya tattara  komai,kuma ya hana duk wani abin da bai ciki shiga.
5. ZUHUDUNSA
Watau gudun duniyarsa; shi ma wannan wani fage ne, wanda Imam ya kai mustawa ma]aukakiya a ciki. Duk wa]anda suka zauna tare da shi sun tabbatar da haka. Akwai ma fa]in ]ansa sayyid Ahmad cewa, “ba wai zar~a~~iya ba ce, na fa]in wa]anda suka zauna tare da Imam da suka siffanta da shi da cewa shi abidi ne kuma zahidi, wato mai ibada kuma mai gudun duniya. Duk wanda ya bibiyi rayuwar Imam sanka-sanka ta fuskoki daban-daban, zai ga cewa a kwai gudun duniya a ciki.
Akwai abubuwa da dama, idan mutum ya ji ko ya karanta zai ga abun mamaki sosai. Misali cewa Imam khumain har ya bar duniya bai mallaki gida da mota ba. Hatta  gidan da ya bar duniya a cikin sa, gida ne wanda ya ke haya a cikinsa, duk da cewa lokacin da aka kama hayar  gidan, masu gidan sun zo wajen Imam, suka nuna murnarsu da kuma jin da]insu da kuma godiya ga Allah (T) da ya yi masu wannan babbar ni’ima, suka nuna shi wannan gida sun bar wa Imam khomain har abada. Imam yace masu, abun da ya ke so a gurin su shi ne haya, in ko ba haka ba zai sa a bincika a wani waje. Kuma idan Allah (T) ya azurta mutum da ziyartar gidan, ba wai gida ne wanda ya kai ya kawo ba, a’a gida ne }arami wanda da yawa da suka ziyarci gidan, sai da suka zubar da hawaye, saboda yadda suka ga gidan da kuma kayan da ke ciki. Saboda gudun tsawaitawa, da an kawo rayuwar Imam sanka-sanka misali abincinsa, tufafinsa, da sauransu.
6. GWAGWARMAYARSA: Abin da ya shafi gwagwarmaya, baki ]aya masoya da ma}iya sun san Imam khomain a wannan fage na gwagwarmaya da zalunci da azzalumai da tsayawa wajen kafa hukuma islamiyya da kuma tsayawa wajen kare ta bayan kafuwarta. Kuma akan haka ya fuskanci jarabobi daban-daban a rayuwarsa, kama tun daga tsangwama ta fatar baki har zuwa ga ]aurewa a kurkuku zuwa ga yanke masa hukuncin kisa, da yake wannan sunna ce ilahiyya. Daga }arshe, da kashe shi bai yiwu ba, aka kore shi daga }asar, ya tafi gudun hijira }asan turkiyya. Da ga nan kuma zuwa ira}, da ga nan kuma zuwa kuwait, wanda su ko kwana ]aya basu yarda yayi a kuwait ba. Da kuwait ta }i yarda ya shiga }asar, ya wuce faransa. Kama-kama dai har Allah (T) ya hukunta dawowar sa }asar iran, hukuma islamiyya ta kafu }ar}ashin jagorancin sa. Bayan kafuwar hukuma islamiyya, matsaloli  sabbi daban-daban suka taso. Haka Imam ya kasance cikin gwagwarmaya da matsaloi daban-daban har zuwa rasuwar sa. A ta}aice dai duk wanda ya bibiyi tarihi da rayuwar Imam zai ga cewa baki ]aya rayuwarsa, tun daga farkonta har }arshen ta, ta gudana ne kan ginshi}ai guda uku.
1. Neman ilimi da ilimantarwa.
2. Ibada domin kusanci zuwa ga Allah (T).
3. Gwagwarmaya domin kafa hukuma islamiyya da kuma kariya gare ta bayan kafata.
7. YUN{URINSA WAJEN HA[A KAN AL’UMMAR MUSULMI
Ha]a kan al’ummar musulmi yana daga cikin manya-manyan abunda Imam Khumain ya dinga kwa]aitarwa da kuma }arfafan musulmi a kai tsawon rayuwarsa, musamman bayan juyin islama  da aka yi a Iran. Kan haka ne ma ya ba da umarnin  }ir}iro da makon ha]in kai a watan maulidi, wato Rabi’ul- awwal, wanda ake yinsa ko wace shekara daga 12 ga watan zuwa 17 gare shi. Akan gayyato malamai daga sassan duniya daban-daban, da kuma mabiya mazhabobi daban-daban, wato ahlus-sunna da kuma shi’a, domin gabatar da jawabai  a mako ]in, da nufin fahimtar da juna da kusantar juna. Har ila yau idan mutum ya bibiyi jawaban Imam, musamman wa]anda yake aika wa lokacin aikin hajji, zai ga ya na }arfafa magana ne akan ha]in kan al’ummar musulmi da kuma nisantar rarraba.
8. MUJAHADAR SA
Wato fa]a da zuciyarsa da kuma shai]an domin samun sul]a, wato iko akan su, Imam ya kasance mai yawan mujahada. Kuma duk wanda ya bibiyi tarihinsa da kuma rayuwarsa, zai ga cewa lallai Imam khumain ya samu sul]a akan nafs ]insa da kuma shai]an. Wato shi yake juya nafs ]insa da kuma shai]an, ba su suke juya shi ba, kuma wannan shine babban hadafin mujahada, wato mutum ya kai matsayin da shi ya ke iko da zuciyarsa da kuma shai]an, ba su suke iko da shi ba, dama a ce mutum zai nemi  littafinsa na hadisai arba’in, ko ya duba in yana da shi, zai ga hadisi na farko da ya fara kawowa, shine hadisi wanda yake magana akan jihadin-nafs (ya}ar zuciya). In mutum ya duba zai ga yadda yayi dogon sharahi kan hadisin, wato bayani sanka-sanka kan mujahadar nafs. Domin samun iko akan zuciya da shai]an wani abu ne da yake da gayar mahimmanci, kuma yake da faidoji masu yawa, daga cikin faidojin, baya ga mutum zai kai matsayi na ubudiyya. Wato ya zama bawa na Allah (T) ba ya zama bawa na nafs ]insa ba ko shai]an.Haka nan kuma  zai taimakawa mutum wajen samun iko a tunanin sa, a lokacin ibadodi, wato ta yadda idan kana sallah, ko karatun al}ur’ani ko ka na biya addu’o’i ko ziyarori da dai sauran su, tunaninka ba zai je ko ina ba. Dama wa]annan tunani-tunanin  sukan zo ne ta wajen nafs da kuma shai]an.
9. AKHLA{ [IN SA
Wato ]abi’o’in sa. Imam khomain ya kasance mai kyawawan ]abi’u ta ko wace fuska. Duk wa]anda suka zauna tare da shi sun tabbatar da haka. Ga misali:
a-      Ha}urinsa, Imam ya kasance mai yawan ha}uri. An cutar da shi ta fuskoki daban-daban, a kuma lokuta daban-daban a rayuwarsa, amma matakin da ya ]auka shine ha}uri. Har ma sau da yawa ya kan cewa ]alibansa, ko da sun ji wani na sukan sa, ko yana aibata shi, to, bai ce su ]auki wani mataki akai ba na musgunawa ko na ramawa ba.
b-      Tausayinsa, Imam ya kasance mai yawan tausayi ga mutane. Har ma yazo a kan cewa sau da yawa idan yana kallon talabijin (tv) aka nuna mutane suna cikin wahala da kuma halin }a}a-ni-ka-yi na talauci, ciwo ko rashin kwanciyar hankali, sai a ga yana zubar da hawaye akan haka.
c-       Tawali’unsa,Imam ya kasance mai yawan }as}antar da kai, saboda ma gayar }as}antar da kai, sau da yawa shi yake yima kansa hidima. Kuma a jawaban sa, ya kan siffanta kansa a matsayin ]alibi ko mai hidima. Ya ma zo akan cewa sau da yawa ya kan taimakawa iyalinsa a wasu ayyuka na cikin gida.
d-      Kyautarsa, Imam ya kasance mai yawan kyauta da kuma share wa mutane hawaye akan matsalolin su, idan sun kawo masa, shi ma wannan akwai misali da dama, amma ga guda ]aya, lokacin Imam yana najaf, akwai wani da ya samu Imam, ya kawo bu}atar wani da bai da lafiya, bayan haka kuma yana cikin matsala ta rayuwa. Da Imam ya ji sai ya kira ]aya daga cikin ]alibansa ya shaida masa cewa, in Allah ya kai mu gobe ya zo ya kar~i sa}o wajansa, ya kai ma mutumin. Wannan abu ya auku da daddare ne bayan sallar isha’i. Ikon Allah washegari sai labari shahadar babban ]ansa, wato sayyid Mustapha ya zo. Shi wannan da Imam yace ya zo ya amshi sa}o da safe, ko da ya doso gidan Imam da safe, sai ya ga cincirindon jama’a. Tun kafin ya iso sai ya tambaya lafiya?. Sai aka ce masa; Sayyid Mustapha ne ya rasu. Sai ya ce, “nan take na ]imauta, gwiwoyina suka yi sanyi, na isa gidan har aka yi jana’izar sayyid Mustapha. Bayan an dawo Imam na amsar ta’aziyya daga jama’a. Can misalin }arfe tara da minti goma, sai na ga Imam na kallo na, can sai ya ce min ya maganar jiya? Sai na tsaya ina tunani, saboda halin ka]uwa da juyayi da na ke ciki.  sai Imam ya ce maganar da na ce ka zo ka amshi sa}o ka kai wa mutumin. Sai Imam ya shiga ya ]auko sa}o na ku]i da wasu abubuwa ya ce in kai masa. A cikin wannan abu akwai darussa da dama, ]aya daga ciki shin ne yadda yake Allah (T) yayi ma babban ]ansa rasuwa. Amma bai manta da al}awari ba.
10. ALA{ARSA DA ALLAH (T)
Imam khomain ya kasance yana da gayar ala}antuwa da kuma ]amfaruwa da Allah (T). Akwai ma lokacin da aka bu}aci ]ansa, wato sayyid Ahmad, da ya yi bayani akan ala}ar Imam da Allah (T). Shine ya ke cewa, “lallai wannan wani abu ne wanda ba zan iya siffanta shi ba”. Ya ci gaba da cewa, “ha}i}a na yi iyaka }o}arina, na sa du da abokan mahaifina, kuma na tambayi mahaifiyata, dangane da wannan abu. Dukkan su sunyi ijma’I akan cewa lallai Imam yana da ala}a ta musamman da Allah (T), kuma yayi fana’i gare shi”. Ya ci gaba da cewa, sau da yawa masu gudanar da al-amura sukan zo wajen su lokacin matsaloli, ya kan ce masu, kada suji tsoro Allah (T)na tare da mu. Imam ya kasance mai gayar tawakkali ga Allah (T), mai gayar ya}ini da kuma si}}a ga Allah (T), mai gayar ikhlasi da kuma ta’azimi ga Allah, mai gayar so da kuma shau}i ga Allah (T). A ta}aice dai ala}ar Imam da Allah wani abu ne wanda ba za a iya bayani ba, kamar yadda ]ansa sayyid Ahmad ya fa]a.

11. ALA{ARSA DA MANZON ALLAH[S] DA KUMA AHLUL-BAYT (AS)
Shima wannan wani faga ne,wanda bayanin sa nada wahala.Baya ga ]abi’antuwa da kuma siffata da Imam Khumaini yayi,da ]abi’o’i na Manzon Allah da kuma Ahlul-bayt[AS] ya kasance mai kiyaye munasabobi na ranakun haihuwar su da kuma wafatin su.ya mazo akan cewa,hatta lokacin da yake gudun hijira a }asar faransa,ranar da wafatin sayyida Fa]ima[AS] ya zagayo,sai da ya gabatar da zaman makoki a gidan da ya zauna tare da wa]anda ke zaune dashi a lokacin.kuma yazo akan cewa tsawon shekaru 15 da yayi a birnin Najaf, lokacin yana gudun hijira a can,to kullum sai ya ziyarci }abarin Imam Ali[AS].a Akwai ma lokacin da sojoji sukayi juyin mulki a }asar,watau a Ira},sai suka sa dokanar hana fita,ga kuma Imam ya saba kullum sai ya ziyarci Imam Ali[AS] Babban ]ansa wato Sayyid Mustafa,yana ta tunanin yadda babansa zaiyi a ranar,to lokacin da Imam ya saba zuwa wannan ziyara,sai yaje ]akinsa bai gan shi ba,da kuma wasu ]akuna na gidan.Abin mamaki da Sayyid Mustafa ya ]aga kansa sama,sai yaga Imam Khumaini akan dakin ]in ]akinsa yana tsaye ya fuskanci }abarin Imam Ali[AS]yana biya ziyarar sa.Haka nan kuma Imam Khumaini ya kasance mai yawan kuka da juyayi na abubuwan da suka samu Ahlul bayt, musammam ma Imam Husain [AS]domin yazo a tarihin sa cewa duk lokacin da aka ambaci Imam Husain[AS] a gabansa to sai ya zubar da hawaye.A ta}aice dai Imam Khumain ya kasance yana da gayar ala}a a zahirance da kuma a ba]inance da Manzon Allah[S] da kuma Ahlul bayt[AS].
12. KARAMOMINSA
Da dama wa]anda suka zauna tare da Imam khumain, sun yi bayani dangane da karamomi daban-daban da suka gani wajen Imam. Har ma akwai fa]in  Ayatullahi sadu} da yake cewa, akwai lokacin da suka yi tafiya da Imam zuwa mash-had. To, a kan hanyarsu ta dawowa, jami’an tsaron da suke bincike akan hanyar su ka tsaida su, domin yin bincike. Ya ce, da yake wajen tsakar dare ne, sai ya kasance lokacin sallar tahajjud ]in Imam yayi, ya na so y yi alwala, amma babu ruwan alwala, saboda sahara ne. ya ce, kawai sai muka ga gefen mu, ga idon ruwa ya na ~u~~ugowa, sai Imam yayi alwala. Ayatullahi sadu} ya ci gaba da cewa bai sani ba, bayan sun bar wurin ruwan ya ci gaba da ~u~~ugowa ko ya tsaya. Mai bu}atar ganin haka yana iya duba littafi mai suna “Al-imam }udwa”; watau littafi ne da ya }unshi bayani daban-daban daga wa]anda suka zauna tare da Imam khomain. Daga cikin karamomin sa hatta rasuwar sa da kwanaki gabaninta, Imam ya shaida wa iyalansa, ‘yan’uwansa na jini da wasu da suke kusa da shi, wannan jinya ba zai tashi ba, zai koma ga Allah (T) ne.
Wannan kenan a ta}aice. Da fatan wa]annan darussan da aka kawo su amfanar da mu. Allah (T) ya bamu ikon aiki da su.

No comments:

Post a Comment