Sunday 3 February 2013

Darussa 12 daga rayuwar Imam Sadi} (AS) 2


Kamar yadda ya gabata a munasabar wafatin Imam Sadi} (AS) a shekarar da ta gabata, an tsaya ne a darussa na hu]u daga cikin rayuwarsa (AS, kuma aka ce insha Allah a wata munasabar wafatinsa za a ]ora a kai.

Darussan da suka gabata na rayuwarsa, su ne:-
1- Akhla} ]insa
2- Girmamawarsa ga Manzon Allah (S)
2- Ibadarsa
4- Iliminsa.
Yanzu za a tashi a darasi na biyar.
5-Jarabawoyinsa:- Imam Sadi} (AS) kamar yadda A’imma (AS) da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa suka fuskanci jarabawowi daban-daban, shi ma ya fuskanci jarabawowi daban-daban, ta kuma fuskoki daban-daban a zamaninsa. Amma jarabawowin duka za a iya dun}ule su, a kasa su gida biyu. Akwai jarabawar da ya fuskanta daga waje, akwai kuma wadda ya fuskanta daga cikin gida. Jarabawar da ya fuskata daga waje, ita ce ta fuskancin masu tafi da iko.
Da farko dai Imam Sadi} (AS) ya yi zamani da wa]annan dauloli guda biyu; Daular Umayyawa da kuma Daular Abbasawa. A lokacin Imamancinsa ne Daular Bani Umayya ta fa]i. Daular Banul Abbas ta hau. A Daular Umayyawa, ya yi zamani da Khalifofinta guda hu]u, su ne: 1- Hisham ]an Abdul-Malik. 2- Yazid ]an Abdul-malik. 3- Ibrahim ]an Walid. 4- Marwan ]an Muhammad.
A kuma Daular Abbasawa, ya yi zamani da Khalifofinta guda biyu su ne: 1- Saffah. 2- Mansur. To a cikin wa]annan Khalifofi na Umayyawa da Abbasawa da aka ambata, wanda ya fi cutarwa da kuma gallazawa ga Imam Sadi} shi ne Mansur. Wanda shi wannan Mansur ]in ya yi yun}uri da niyyar kashe Imam Sadi} (AS) ba ]aya ba, ba biyu ba. A wata ruwaya har sau biyar,  amma Allah (T) ya kare shi. Daga }arshe da haka ba ta yiwu ba, wato kashe shi da takobi. Sai ya sa a sa masa guba a inabi, ta hanyar gonarsa da ke Madina. Shi ya sa in mutum ya duba littafin tarihi na A’imma (AS), in mutum ya zo kan tarihin Imam Sadi} (AS),  zai yi wahala ka ga Malamin tarihin bai kawo fasali kan abin da ya gudana tsakanin Imam Sadi} (AS) da kuma Mansur ba. Amma sauran Khalifofin, da wuya ka ji an ambace su. Da yake a lokacin Daular Bani Umayyar ta yi rauni, ba wai kawai ta yi rauni ne ba, a’a, tana ya}in }watar kanta ne daga Banul Abbas da suka ]ago domin kau da su daga kan mulki. Saboda haka a lokacin sun shagaltu kan ya}i don dawwamar da kansu a kan mulki ne. Wato hankalinsu bai koma kan Imam Sadi} (AS) ba.
To wannan yanayi ne ya ba da dama ga Imam Sadi} (AS) wajen ya]a ulum na Ahlul Baiti fiye da sauran Imamai (AS). Shi ya sa in muka duba a Mazhabance ake cewa Mazahabar Ja’afariyya, wato daga sunan Imam Sadi} (AS), Ja’afar.
Bayan da aka kifar da Daular Banu Umayya, Abbasawa suka hau, to Khalifanta na farko, wato Saffah, shi ma hankalinsa bai koma kan Imam Sadi} (AS) ba. {ila ko saboda Daular tana sabuwa. Kuma fa]an da suka yi domin kau da Bani Umayya, sun fake da sunan Ahlul Baiti ne domin su sami goyon bayan jama’a. Saboda  haka zai kasance abin kunya a wajensu, da hawansu a ga kuma suna fa]a da Ahlul Baiti. Amma bayan mutuwar Saffah, wanda ya gaje shi, Mansur sai ya fito da salon fa]a da Ahlul Baiti (AS) da kuma mabiyansu. Saboda haka a lokacin mulkinsa ya kashe mabiya Ahlul Baiti (AS) da yawa, ya kuma sa da damansu a kurkuku. Akwai ma lokacin da wani ya shiga wajensa cikin makusantansa sai ya same shi cikin damuwa da ba}in ciki, sai ya tambaye shi, wannan damuwar fa? Sai Mansur ]in ya ba shi amsa da cewa; “Na kashe ’ya’yan Fa]ima har kusan 100, amma ga Shugabansu nan, Imaminsu yana raye”. (Mu duba wannan abu). Sai mutumin ya ce masa wa kake nufi? Sai Mansur ya ce masa Ja’afar ]an Muhammad Sadi}. Sai mutumin ya ce masa; “To ai shi mutum ne (yana nufin Imam Sadi} (AS) wanda ibada da neman kusanci ga Allah (T) sun shagaltar da shi daga neman mulki ko khalifanci”. Sai Mansur ya ce; “Duk da haka dai na ]aukar ma kaina sai na kashe shi”. Mu duba irin wannan bushewar zuciya. Kuma wannan ba wani abu ya haifar da shi ba, face hassada. Duk da ko kasancewa ga shi a kan gadon mulki, amma kasantuwar cewa ya san zukatan mutane suna tare da Imam Sadi} (AS) ne, kuma a lokacin babu wani Malami wanda ya shahara ake kuma amsar ilimin daga wajensa kamar Imam Sadi} (AS). Domin ba wai kawai mabiya Ahlul Baiti suke karatu a wajensa ba. A’a har da ma manya-manyan Malamai na Ahlus Sunna, misali Abu Hanifa da kuma Malik ]an Anas. Shi ya sa Mansur a lokacin, saboda hassadarsa ga Imam Sadi} (AS) ta yadda ake ruwaito Hadisai daga wajensa, kusan kowane gari ka je a majalis na ilmi, sai dai ka ji ana Imam Sadi} (AS) ko Ja’afar ]an Muhammad ya ce. Sai ya bu}aci Malik ]an Anas, da ya rubuta littafin Hadisi, da nufin ya tattara mutane a kan amfani da shi. To shi ne ya rubuta littafin Muwa]]a. Amma shi Malik ya nuna bai yarda a kan ya tilasta mutane wajen amfani da shi ba. Daga cikin hujjojin da ya kafa masa, ya ce masa Sahabban Manzon Allah (S) sun watsu a sassan duniya daban-daban, ta yiwu akwai Hadisan da shi bai ji ba, amma dai manufar shi Mansur, yadda ya so, shi ne ya dushe wannan haske na ya]uwar Hadisai da aka ji daga Imam Sadi} (AS).
Da wannan ha}a tasa ba ta cimma ruwa ba, to shi ne ya ]auki matakai da kuma dabaru na ya ga ya kashe Imam Sadi} (AS). Ga mai bu}atar ganin wa]annan matakai da ya ]auka na kashe Imam Sadi} (AS) yana iya duba littafin Muntahul-Amal, Juz’i na biyu na Shaikh Abbas Al-kummy.
Sai kuma jarabawar da Imam Sadi} (AS) ya fuskanta cikin gida, wato daga wa]anda suke su mabiya Ahlul Baiti (AS) ne, ko a wata ma’ana ’yan Shi’a ne, wa]annan ~angarori kuwa su ne Zaidiyya, Isma’iliyya da kuma Gullat. Da yake wannan ba mahalli ne na bayanin a}idunsu ba, illa kawai nan a ta}aice bayani dangane da asalinsu.
Zaidiyya, asalin wannan suna daga Zaid ]an Imam Zainul Abidin ne. An haife shi shekara ta 75 bayan hijira. Ya yi shahada shekara ta 120 bayan hijira. Ke nan shekarunsa a duniya 45. Ya yi zamani da Imamai guda uku. Mahaifinsa Imam Zainul Abidin (AS), ]an uwansa kuma yayansa, Imam Ba}ir (AS) ,da kuma ]an ]an uwansa, Imam Sadi}. Saboda haka wannan Mazhaba ta Zaidiyya ana jingina ta ne gare shi. Amma asalin Mazhabar ba shi ya }ir}ire ta ba, mabiyansa ne suka }ir}ira suka jingina masa. Domin su sun tafi a kan cewa wai Imam Ba}ir (AS) ba shine Imam ba,bayan Imam Zainul-Abidin,wai  Zaid ne.  Alhali in da mutum zai bibiyi tarihin Zaid, zai ga cewa ya yi i’itirafi da Imamancin Imam Ba}ir (AS) da kuma Imamancin Imam Sadi} (AS). Kuma wa]annan  Imamai biyu, sun yi masa shaida a kan haka. Ga misali na i’itirafi da Imamai biyu, wato Imam Sadi} (AS) da kuma Imam Ba}ir (AS).
Sadu} ya ruwaito a cikin littafinsa na Amaliy. Zaid ]an Ali ]an Husain (AS) ya ce; “Kowane zamani akwai wani daga cikin mu Ahlul Bait (AS), wanda Allah (T) kan aje shi Hujja ga halittarsa. Hujjar zamaninmu, shi ne ]an ]an uwana Ja’afar [an Muhammad. Duk wanda ya bi shi ba zai ~ace ba, wanda kuma ya sa~a masa ba zai samu shiriya ba”.
Haka nan a zamanin Imam Ba}ir (AS), akwai wani da ake ce wa, Muhammad ]an Muslim, ya ce; “Na shiga gun Zaid ]an Ali, sai na ce masa, akwai wasu mutane da suke riya cewa, kai ne ma’abocin wannan al’amari (wato Imami), sai Zaid ya ce, ‘A’a’. Bayan haka sai shi wannan mutumin ya tafi wajen Imam Ba}ir (AS) ya shaida masa cewa ga abin da Zaid ya ce masa. Sai Imam Ba}ir (AS) ya ce; “[an uwana Zaid ya fa]i gaskiya.”
Isma’iliyya kuma asalin sunan daga Isma’il ]an Imam Sadi} (AS) ne.Masu wannan A}ida sun tafi akan cewa, wai Imamanci a bayan Imam Sadi} ga Ismail ne, An haife shi shekara ta 110 bayan hijira. Ya rasu shekara ta 145 bayan hijira. Shekarunsa a duniya 35. Shi ne babban ]a namiji na Imam Sadi} (AS). Kuma wannan mazhaba ta Isma’iliyya ba shi ya }ir}ire ta ba. Shi ma an }ir}ira ne aka jingina masa, bayan ma rayuwarsa da shekaru. Kuma in mutum ya bibiyi tarihinsa, zai ga cewa bai yi da’awar Imamanci ba. Kuma ya bar duniya mahaifinsa yana mai yarda da shi. Amma kasantuwar cewa Imam Sadi} (AS) ya san bayan rasuwar akwai wa]anda za su yi da’awar Imamancinsa. Shi ya sa da Isma’il ]in ya rasu, ya sa a kira wasu daga cikin Sahabbansa, da suka taru, an ce sun kai wajen mutum 30, sai ya ce wa ]aya daga cikinsu ya kware fuskar Isma’il, ya kware fuskar tasa, ya tambaye shi yana raye ne ko ya rasu, ya ce ya rasu, haka ya dinga kiransu ]aya bayan ]aya, ya zo ya duba yana kuma tambayarsa, dukkansu suka tabbatar da cewa ya rasu. Bayan haka ya ce ya Allah ka shaida. Domin su masu wannan tunani na cewa wai Isma’il shi ne Imam bayan Imam Sadi} (AS), ]aya daga cikin Hujjarsu, ita ce, kasantuwar shi ne babban ]ansa namiji.
Baya ga wannan, ga kuma matsalar Gullat da Imam Sadi} (AS) ya fuskanta. Ga mai bu}atar dogon bayani dangane da Zaidiyya da Isma’iliyya yana iya duba littafin Ayyatullah Subhani mai suna ‘Milal Wa Nihal’, ko kuma ‘Khulasar,’ sai mai suna ‘Mazahibul Islamiyya’. Dangane da kuma Gullat yana iya duba littafin Imamu Sadi} Wa Mazahibul Arba’a. Haka Imam Sadi} (AS) ya fuskanci wa]annan jarabawowi na cikin gida da waje har ya koma ga Allah (T).
6- Zuhudunsa:- Imam Sadi} (AS) ya kasance mai gayar guje wa duniya da kuma tarkacenta. A wannan fage na zuhu]u, a zamaninsa babu wanda ya kai shi, ballantana ya wuce shi. In mutum ya bibiyi tarihin rayuwarsa zai ga haka. Akwai littafin da aka jingina masa, cewa shi ya rubuta, sunansa Misbahu Shari’a. To akwai babi da ya fitar na zuhudu, wato gudun duniya.
7- Kukansa:- Imam Sadi} (AS) ya kasance mai yawan kuka saboda tsoron Allah (T). Ya ma zo a kan cewa saboda gayar tsoron Allah (T), in ya tashi yin Salla, a kan ga launinsa ya canza, jikinsa kuma na makyarkyata. Akwai ma lokacin da ya tafi aikin Hajji, shi da Malik ]an Anas, wato Shugaban Mazhabar Malikiyya, sai Malik ya ga duk lokacin da Imam Sadi} (AS) zai Talbiyya, wato Labbaikal Lahumma Labbaik, sai ya ji muryar Imam Sadi} (AS) tana yankewa. Sai Malik ya tambaye shi, me ya sa haka? Imam Sadi} (AS) ya ba shi amsa da cewa, yana gudun ya fa]i haka, Allah (T) ya ce masa La-Labbaika Wala-Sa’adaik. Mu duba fa mu gani, Imam Ma’asum a I’iti}a]inmu. Wato dai wannan ya nuna gayar tsoron Allah (T) nasa. Haka nan an ruwaito daga Sufyanu-sauri ya ce; “Wallahi na ga Ja’afar ]an Muhammad (wato a wajen aikin hajji) ban ga wani mahajjaci mai yawan kuka kamar sa”.
8- Hadisansa:- Imam Sadi} (AS) An samo Hadisai masu yawan gaske daga wajensa, domin a zamaninsa babu wani wanda aka ruwaito Hadisai masu yawa a wajensa kamar yadda aka ruwaito a wajensa. Akwai ma Malaman tarihi da suka tafi a kan cewa; A’imma (AS) baki ]aya, shi ne ya fi su yawan Hadisai da aka ruwaito daga wajensa. Wannan ko bai rasa nasaba da yanayi da kuma dama da ya samu na ya]a ilimi fiye da sauran A’imma (AS). Alal misali Abana ]an Taglib shi ka]ai ya ruwaito Hadisai 30,000, shi kuma Muhammad ]an Muslim ya ruwaito Hadisai dubu sha shida. Akwai ma lokacin da Imam Sadi} (AS) yake cewa; “Ku tambaye ni tun gabanin ku rasa ni, domin babu wani wanda zai ba ku Hadisi a baya na kamar Hadisina”. Kuma Hadisansa, ba wai kawai Malaman Imamiyya ne suka ruwaito ba, a’a har da Malaman Ahlus Sunna.
9-Karamominsa:- Idan mutum ya bibiyi tarihin Imamai 12, wato tun daga Imam Ali (AS) har zuwa Imam Mahdi (AS), zai ga cewa kowannensu akwai karamomi ko mu’ujizozi da suka bayyana a rayuwarsa. Mutum ya binciki littafai na tarihin rayuwarsu zai ga haka. Saboda haka a nan za a kawo wasu daga cikin irin wa]annan karamomi da suka bayyana daga Imam Sadi} (AS)
1- Akwai wata rana da Imam Sadik (AS) ya taso daga Kufa zuwa Madina, to daga cikin wa]anda suka rako shi, akwai manyan Malamai da kuma wasu manyan Sufaye na Ahlus Sunna, irin su Ibrahim ]an Adhama, da kuma Sufayanu-Sauri, su wa]annan masu rakiya suna gaba, to a kan hanya sai suka ha]u da zaki, ganin haka sai Ibrahim ]an Adhama, ya ce; “Ku tsaya mu ga ya Ja’afar zai yi”. Da Imam Ja’afar  (AS) ya iso wajen, suka shaida masa ga zaki a kan hanya. Sai Imam Sadi} (AS) ya je wajen zakin, ya kama kunnensa ya janye shi daga kan hanya. Bayan haka sai Imam Sadi} (AS) ya dube su ya ce, da mutane sun yi wa Allah (T) ]a’a, ha}i}anin ]a’a, to da har kaya ya ]aukar masu, (wato zakin).
2- Akwai wani daga cikin Sahabban Imam Sadi} (AS) ya ce. Na kasance ina tafiya tare da Imam Sadi}n (AS) a Makka, sai muka ha]u da wata mata tare da yarinyarta suna kuka gaban wata saniya da ta mutu. Sai Imam Sadi} (AS) ya tambaya mene ne ya faru? Sai matar ta ce; “Na kasance ni da wannan yarinya tawa, muna rayuwa da wannan saniyar, ga shi ta mutu. (wato wajen amfani da nononta)”. Sai Imam Sadi} (AS) ya ce mata; “Kina so Allah (T) ya raya maki ita?” Shi ne Imam Sadi} (AS) ya yi wata addu’a. Bayan haka sai ya zunguri saniyar da }afarsa. Sai ga saniyar ta tashi.
3- Akwai wani lokaci da Khalifan Abbasawa, Mansur ya aika maya}a Madina, idan sun isa su kai hari gidan Imam Sadi} (AS) su saro masa kansa, da kan ]ansa, Musa (Imam Kazim AS). Sai Imam Sadi} (AS) ya samu labarin haka. Sai ya sa a kawo mai ra}uma guda biyu, ya ]aure su a kofar gi]ansa, bayan haka ya tara ’ya’yansa da jikokinsa, ya yi addu’a. Da maya}an suka isa }ofar gidan, Jagoran nasu ya ce; “Ku sare kawukan wa]annan mutane da suke tsaye (wato sai surar wa]annan ra}uman ta zama surar mutane) suka ]auki wannan kawuka suka kai wa Mansur, yana dubawa sai ya ga ai kawukan ra}uma ne, sai ya tambayi Jagoran maya}an, mene ne haka kuma? Sai ya ce masa, ai yadda ka ba mu umarni, mun je gidan muna zuwa sai na ga mutane biyu a waje a tsaye. Na ]auka Ja’afar ne da Musa. Nan take aka sare kan nasu. Shi ne Mansur ya ce masa ka ~oye labarin wannan abu, sai da Mansur ya mutu”.
A ta}aice dai akwai irin wa]annan karamomi ko mu’ujizoji masu yawa da suka bayyana daga Imam Sadi} (AS), wanda ba za a iya kawo su ba, saboda gudun tsawaitawa.
10- Zantukan Malamai dangane da shi:- 1-Abu Hanifa ya ce; “Ja’afar ]an Muhammad shi ne mafificin Fa}ihu da na gani.” Wani wajen kuma yana cewa; “Ban ta~a ganin mafi sani ba, kamar Ja’afar ]an Muhammad.” Haka nan akwai wani da ya tambayi Abu-Hanifan cewa, mene ne za ka ce dangane da wanda ya yi wa}afin dukiyarsa ga Imam, to wane Imam ne ya cancanta a yaba? Ya ce wanda ya cancanta, shi ne Ja’afar ]an Muhammad, domin shi ne Imam ]in gaskiya.
2-Imam Malik ya ce; “Idonsa bai ta~a gani ba, kunnensa bai ta~a ji ba, wanda ya fi fifiko kan Ja’afar ]an Muhammad”. A ilimi ibada da kuma tsantseni. A wani waje kuma ya ce, Ja’afar ]an Muhammad yana daga cikin masu gayar ibada da zuhudu da kuma tsoron Allah (T).
3-Abdullahi Asshafi’iy ya ce; “Ja’afarus Sadi} yana da darajoji masu yawa.” Limamai masu yawa (wato na mazahib) sun ruwaito Hadisai daga wajen sa, misali, Malik ]an Anas, Abu Hanifa, Sufyanu-Sauri, Ibn Juraih, Shu’uba da dai wasunsu. A ta}aice dai akwai zantukan Malamai masu yawa, a kan fifikonsa a kan Malamai da sauran mutanen zamaninsa.
11- Wasiyyarsa:- Imam Sadi} (AS) ya yi wasiyyoyi masu yawa, wasu ga ]ai-]aikun mutane, mabiyansa da ma wa]anda ba mabiyansa ba, wasu kuma ga Shi’arsa, wasu ga ’ya’yansa da dai sauransu. Saboda gudun tsawaitawa ga wasu daga ciki:
 1- Wasiyyarsa da ya yi wa wani da ake cewa Abi Usama. “Ina yi maka wasiyya da jin tsoron Allah da tsantseni da mujahada, da fa]in gaskiya, da ri}on amana da kyakkyawar ]abi’a, da kyakkyawar ma}wabtaka. Ku kasance masu kira da ayyukanku, ku kasance }awa gare mu, kada ku kasance muni gare mu. Ina horonku da tsawaita ruku’u da sujada”.
2- A wata wasiyyarsa da ya yi wa wani daga cikin Sahabbansa ya ce; “Idan ]ayanku yana son ba zai tambayi Allah (T) wani abu ba face ya ba shi, to ya ]ebe tsammani daga wajen mutane baki ]aya. Ya kasance bai da wata fata ko }auna face ga Allah (T). In Allah (T) ya ga haka a zuciyarsa, to ba zai tambaye shi komai ba, face ya ba shi. Haka nan kuma ku yi wa kanku hisabi gabanin a yi maku (wato gobe }iyama), domin }iyama tana da matsayi 50, a kowane matsayi, shekara dubu ne.”
3- Sannan gab da zai rasu, ya sa a tara masa mutanen gidansa duka, da kuma ’yan uwansa na jini. Da suka ha]u baki ]aya, ya dube su, ya ce masu; “Cetonmu, bai samun mai wula}antar da Salla.” Da dai sauran wasiyyoyinsa masu yawa, wa]anda suke cikin littafan tarihin rayuwar A’imma.
12- Wafatinsa:- Imam Sadi} (AS) ya rasu 25 ga watan Shawwal, a shekara ta 148 bayan Hijira, sakamakon guba da aka sa masa a inabi. Ya rasu yana da shekara 65. A wata ruwaya 68. Kabarinsa na Ba}i’a ne a Madina. Amma ya zo a tarihinsa cewa, kafin rasuwarsa, ya yi jinya ta rashin lafiya, wadda ta kai ma ya samu rama sosai a jikinsa. Wata rana yana cikin wannan jinya, wani daga cikin Sahabbansa ya shiga wajensa, da ya gan shi, sai ya fashe da kuka. Sai Imam Sadi} (AS) ya ce; “Mene ne kake wa kuka?” Ya ce; “Saboda halin da na gan ka”. Sai Imam Sadi} (AS) ya ce; “Ka daina kuka, ai shi mumini komai nasa alheri ne. Ko da ko za a yanka shi gunduwa-gunduwa, alheri ne a wajensa, in kuma ya yi mulkin Gabas da Yamma na duniya alheri ne a gare shi.”
Wa]annan su ne cikon darussa 12 daga rayuwar Imam Sadi} (AS), da fatan su kasance haske gare mu gobe }iyama. Ba duhu da nauyi gare mu ba, idan ba mu aikata ba.
Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ali Muhammad.


No comments:

Post a Comment