Kasantuwar
ran 8 ga watan jiya, wato Rabi’ul Awwal shi ne ya yi daidai da wafatin Imam
Hasan Al-Askar. Kamar yadda ya zo a tarihinsa, ya rasu ne ranar Juma’a 8 ga
Rabi’ul Awwal Hijira ta 260. Imam Hasan Al-askari (AS) an haife shi ne a
Madina, a watan Rabi’us-Sani, sai dai an samu sa~ani dangane da ranar da aka
haife shi, da kuma nawa ga wata aka haife shi.
Allama Majalisi, watau marubucin
littafin Biharul Anwar ya ce abin da ya fi shahara shi ne, an haife shi ne
ranar Juma’a takwas ga watan Rabi’us Sani. Amma Shaikh Mufid ya tafi a kan 10
ga watan ne a shekar ta 232 bayan hijira.
Imam Askari (AS) kamar yadda aka
sani, shi ne Imami na 11 a jerin }idaya na Imamai 12, kuma ya rayu shekaru 28
ne a duniya. Ya rasu yana da ]a ]aya shi ne; Imam Mahdi (AS). Muddan
Imamancinsa shekaru shida ne, kuma ya yi zamani da Khalifofin Abbasawa guda uku
sune; Mu’utasim, Muhtadi da kuma Mu’utamad, kuma dukkansu su ukun nan, babu
wanda bai gallaza wa Imam Askari (AS) tare da yun}urin kashe shi ba, kamar
yadda haka zai zo nan gaba a bayanin jarabawowinsa, insha Allah (T).
Sunan Mahaifinsa kamar yadda aka
sani, shi ne Imam Ali Al-Hadi (AS). Sunan Mahaifiyarsa Salil. Idan mutum ya
bibiyi tarihin rayuwarta zai ga cewa ta kai matsayi ma]aukaki wajen kusanci ga
Allah (T) da kuma tsoronsa, kuma ta kasance makoma ga Shi’a ]in Ahlul Baiti
(AS) bayan wafatin Imam Hasan Al-Askari (AS). Akwai ma lokacin da Imam Ali
Al-Hadi (AS) yake cewa; “Salil tsarkakakkiya ce daga aibobi na zahiri da kuma
ba]ini”. A ta}aice dai ta kai mustawa Aliya a fagagen Addini. Misali a Ilimi,
Ibada, ta}awa da dai sauransu kamar yadda ya zo a tarihinta.
Imam Hasan Al-Askari yana da
la}ubba da yawa, amma wanda ya fi fice a ciki shi ne Al-Askari (AS), wannan
la}abi nasa na Al-Askari ya samo asali ne daga sunan wata unguwa da ya zauna
shi da Mahaifinsa a Samarra, wacce a yanzu tana }asar Ira}i ne. Asalin ita
wannan unguwa sansani ne na maya}a, wanda Khalifan Abbasawa mai suna Mu’utasim
ya kafa. Wato a wannan zamanin namu kamar a ce barikin soja.
Imam Hasan Al-askari yana da
shekaru hu]u da watanni, shi da Mahaifinsa Imam Hadi (AS) suka bar Madina zuwa
Ira}i. (Insha Allah idan an zo darussa 12 daga rayuwar Imam Ali Al-Hadi (AS) za
a yi bayani dangane da dalilin barinsu Madina zuwa Ira}i).
Imam Askari ya rayu tare da
Mahaifinsa shekara 22. Bayan rasuwarsa an birne shi a kusa da Mahifinsa. Saboda
haka }abarinsu yana nan a Samarra ne a }asar Ira}i, kuma daga wannan rana ta
rasuwarsa, wato 8 ga watan Rabi’ul Awwal shekara ta 260 bayan hijira, Imamancin
Imam Mahdi (AS) ya fara. Ya ma zo a kan cewa ana son ziyarar Imam Askari (AS)
da kuma Imam Mahdi (AS) a wannan rana ta 8 ga watan Rabi’ul Awwal. Saboda haka
rayuwar Imam Hasan Al-Askari za a iya kasa ta zuwa marhaloli guda biyu;marhala
ta farko daga haihuwarsa zuwa rasuwar mahaifinsa.marhala ta biyu rayuwarsa
bayan rasuwar Mahaifinsa, sai kuma abin da ya shafi wasu darussa daga cikin
rayuwarsa mai albarka.
1. IBADAR SA: Imam Hasan Al-Askari
(AS) ya kasance mai yawan ibada. Wa]anda suka yi zamani da shi, kuma suka zauna
da shi, sun tabbatar da haka. Kai hatta ma ma}iyansa sun yi furuci da haka. Ga
misalin wasu daga cikin Ibadodinsa. Akwai wani da ake ce wa Muhammad Shakiri ya
ce; “Imam Askari (AS) yakan zauna ya yi sujuda a wajen Sallarsa in je in kwanta
har in tashi daga barci, amma in samu bai ]ago daga sujudar ba”. Wato wannan
yana alamta tsawaitawarsa a sujuda idan ya yi.
Khalifan Abbasawa mai suna
Mu’utamad lokacin da ya sa shi a kurkuku sai aka fa]a masa ai kullum Azumi
yake, kuma kowanne dare baki ]ayansa yakan raya shi da Salloli. Akwai wani da
ake ce wa Muhammad [an Isma’il shi me ya fa]i makamancin haka. Ya ce; “Imam
Askari a kurkuku ya kasance mai Azumi kullum, ya kuma raya dare dukkansa. Ya
kasance bai shagaltuwa da komai face Ibada”.
Wa]anda suka tsare Imam Hasan
Al-Askari (AS) sun fa]a wa mai kula da kurkukun cewa ya }untata masa, kada ya
sassauta masa ko ya yalwata masa. Shi ne mai kula da kurkukun yake ce masu. “To
me zan yi masa alhali kun wakilta mafi sharri daga cikin mutane su biyu domin
su musguna masa da kuma }untatawa gare shi, amma yanzu sun zama bayin Allah (T)
waje Ibada na Salloli da Azumi?
Jin haka, nan take su wa]annan
jami’an Hukuma na Abbasawa suka sa aka kira wa]annan Gandirobobi guda biyu. Da suka zo, sai suka ce masu; “Menene sha’aninku dangane
da wannan mutum?” Sai suka ce masu. “To, mu dai tunda aka kawo shi wannan
kurkuku kullum Azumi muka ga yake yi, dare kuma baki ]aya yana Ibada. Ko magana
ma bai yi, ya shagaltu ne kawai da ibada”.
Jin
haka sai su wa]annan jami’an Hukuma na Abbasawa suka fice daga kurkukun a
fusace. Domin ganin cewa su wa]annan Gandirobobin guda biyu su suka fi kowa
mugunta da kuma bushewar zuciya, shi ya sa aka ji~inta masu }untata wa Imam
Askari (AS), amma sai aka samu akasin haka, wato sai suka tasirantu da zamansu
da Imam Askari (AS) har ta kai ga su ma suna aiki irin nasa na Ibadodi, wato
Azumi da kuma Salloli.
Imam Hasan Askari (AS) ya kasance
mai yawan Addu’o’i, musamman ma a }unut ]in Sallolinsa, kamar yadda ya zo a
tarihinsa. Akwai ma wata Adddu’a ya kasance yakan biyata a }unut ]in
Sallolinsa. Addu’ar ita ce “Allahumma wa }ad shamilana zaigul fitan…….” Malam
ma, wato Sayyid Zakzaky (H) ya kasance yana yawaita biya wannan Addu’a ]in a
}unut ]in Sallolinsa. Domin in mutum ya dubi wannan Addu’a zai ga ta }unshi
hali da kuma yanayi na fitinoni dakuma jarabawowi da al’ummar Musulmi, musamman
ma mabiya Ahlul Bait(AS) suke ciki a wannan zamani na gaiba da kuma neman
mafita daga wajen Allah (T).
2. AKLA{ [IN SA: Imam Hasan Askari
(AS) a wannan fage na Akla}, a zamaninsa ba wanda ya kai shi balantana ya wuce
shi, domin su A’imma (AS) kowanne Imam a zamaninsa, to babu wani fage daga
fagage na addini da za a ce an samu wani ya kai shi ballantana ya wuce shi.
Mutum ya bibiyi tarihin Imamai ]ayan bayan ]aya a dukkan fagage na Addini zai
ga haka. Misali a fagen Ilimi, Ibada, Akhla}, Mujahada da dai
sauran su. Kuma wannan shaida ta fifikon Imamai (AS) ga mutanen zamaninsu a
fagagen na addini ba wai daga mabiyansu ba ne kawai, a’a hatta wasu daga cikin
Malaman Ahlus Sunnah da suka yi zamani da su sun tabbatar da haka. Wani abin
mamaki ma shi ne, hatta wasu daga cikin Malaman Ahlul Kitab, wato Yahudu da
Nasara sun yi shaida a kan haka, musamman ma a fagagen Ilimi, wanda da yawansu
wannan shi ne ya zama sanadiyyar musuluntarsu. Idan mutum na son ya ga irin
wannan shaida ta fifiko da Malaman Ahlus Sunnah da kuma Ahlul Kitab suka yi wa
Imamai (AS) da suka yi zamani da su, ya duba littafi mai suna A’IMMATUNA, zai
ga marubucin wannan littafin a tarihin Imamai 12 da ya kawo, na kowane Imami
daga cikin Imaman nan (AS). Wato tun daga Imam Ali (AS) zuwa Imam Mahdi (AS)
zai ga ya fitar da babi mai taken “zantukan Malamai gare shi”. To zai ga wannan
shaida ta fifikon kowane Imami a zamaninsa a dukkan fagage na addani. Ga wasu
misalai na Akla} ]in Imam Askari (AS)
A. KYAUTAR SA: Imam Askari (AS) ya kasance mai yawan
kyauta. Akwai wani mutum da abubuwa na rayuwa suka tsananta masa, shi da ]ansa,
sai shi wannan mutumin ya ce wa ]an nasa; “Abubuwa sun yi mana tsanani, mu tafi
wajen wannan mutum (yana nufin Imam Askari) domin an ce mutum ne mai yawan
kyauta”. Sai
]an ya ce wa Baban nasa; “To ka san shi ne?” Sai ya ce; “Ni ban san shi ba, ban ma ta~a ganin sa ba, ina dai jin labarin
sa ne”. Saboda haka sai suka tafi wajen Imam Askari (AS), to a kan hanya kafin
su isa, sai shi uban yake ce wa ]an nasa; “Ina ma dai a ce ya ba ni Dirhami 500
ka ga Dirhami 200 in sayi tufafi, Dirmahi 200 in biya bashi, Dirhami 100 kuma
in sai kayan abinci”. Sai shi ]an a cikin ransa, wato bai fa]a wa Baban nasa
ba, ya ce; “Ina ma dai ni ma ya ba ni Dirhami 300, Dirhami 100 in sayi dabbar
da zan dinga hawa, Dirhami 100 kayan abinci, Dirhami 100 in sayi tufafi”.
Da
suka isa gidan Imam Askari (AS) suka yi sallama da kuma bayanin matsalolinsu,
lokacin da za su tafi sai Imam Askari (AS) ya ba uban Dirhami 500, ]an kum ya
ba shi Dirhami 300. Wannan }issar ta nuna mana kyauta da kuma karama ta Imam
Askari (AS), domin kowannansu ya samu abin da yake fata da kuma burin samu a
wajen Imam Askari (AS).
Haka
nan akwai wani mutum da aka yi wa haihuwa a lokacin yana cikin }unci na rayuwa,
sai ya rubuta takarda ga wasu yana neman su taimaka masa, amma bai samu biyan
bu}ata ba. Sai ya yi tunanin cewa bari ma ya je wajen Imam Askari (AS) wata
}ila ya samu muwafa}a. Ya same shi ya shaida masa hali da yake ciki. Sai Imam
Askari (AS) ya ba shi Dirhami 400 ya ce ya yi ]awainiyar haihuwar da su, ya
kuma yi masa addu’a, ya ce; “Allah ya sa albarka ga abin da aka haifa.
Akwai kuma }issar wani da ya tsaya
a kan hanyar da ya san Imam Askari (AS) yana bi. Lokacin da ya ga Imam Askari
(AS), sai ya yi masa bayanin halin da yake ciki na bu}ata, har ma yake rantse
masa ko Dirhami ]aya bai da shi, abin ma da zai ci a ranar bai da shi. Sai Imam
Askari (AS) ya ce masa; “Yanzu kana rantsuwa da Allah kan }arya, alhali kana da
Dirhami 200 ka ~oye su? Amma ni ba ina fa]in haka ba ne saboda kada in ba ka wani
abu”. Sai ya ba shi Dirhami 100. Mu duba Akhla} na Imam Askari (AS) da kuma
karamarsa.
Akwai kuma wani da ake ce wa Abu
Hashim Al-Ja’afari lokacin yana tsare a kurkuku ya rubuto wa Imam Askari (AS)
halin da yake ciki a kurkuku na matsaloli da kuma tsanance-tsanance, sai Imam
Hasan Askari (AS) ya rubuta masa cewa; “Yau za ka yi Sallar Azahar a gidanka”.
Ilai kuwa, kafin Azahar aka sake shi ya yi Sallar Azahar ]in a gidansa. Shi ne
Imam Askari (AS) ya aika masa da Dirhami 100, ya ce kuma in yana da wata bu}ata
kada ya ji kunya ya gabatar da ita zai samu biyan bu}ata insha Allah.
Mu duba ita ma wannan karama da
kuma Akhla} na Imam Askari (AS). Akwai misalai da yawa na kyautarsa, amma ba za
a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.
B.
AFUWARSA: Imam Askari (AS) ya kasance mai yawan afuwa da kuma kau da kai daga
masu cutar da shi. Akwai ma lokacin da yake fa]a wa wani daga cikin mabiyansa
cewa idan ya ji wani mai sukar sa ko zagin sa, ya wuce kada ya amsa masa ko
kula shi, ko ya nuna masa shi waye.
Akwai lokcin da Imam Askari (AS)
yana tsare a kurkuku, to ]aya daga cikin ma’aikatan kurkuku ya kasance mai
yawan gallazawa ga Imam Askari (AS), amma sakamakon Akhla} ]in da ya gani na
Imam Askari (AS) wannan ya canza masa tunani, sai da ya kai saboda girmamawarsa
ga Imam Askari (AS) da kuma jin nauyinsa bai iya ]aga ganinsa ya dubi Imam
Askari (AS). Wuce nan ma, daga baya ya zama cikin mabiyansa. Mu duba yadda
kyakkyawan Akla} ke canza }iyayya zuwa soyayya da kuma biyayya.
Akwai kuma lokacin da aka tsare
Imam Askari (AS) a kurkuku shi da wani ]an uwansa na jini da ake ce wa Ja’afar,
daga baya sai aka saki Imam Askari (AS) ban da Ja’afar ]in, shi ne Imam Askari
(AS) ya ce ba inda zai je idan ba saki Ja’afar ]in ba. Ganin haka shi ma
Ja’afar ]in aka sake shi. Da dai misali da yawa na Akla} ]in Imam Askari (AS)
ta fuskoki daban-daban.
3.
JARABAWOWIN SA: Imam Hasan Al-Askari (AS) duk da cewa ya rayu a duniya }asa da
shekaru 30, amma a cikin wa]annan shekaru ya fuskanci jarabawowi daban-daban,
ta kuma fuskoki daban-daban, musamman ma ta fuskacin masu tafi da iko. Domin
Khalifofin Abbasawa guda uku da ya yi zamani da su babu wanda bai }untata masa
ba da kuma yun}urin kashe shi, dama sa shi a kurkuku. Shi ya sa in mutum ya
bibiyi tarihin Imam Askari (AS) zai ga ya yi zaman kurkuku a lokuta daban-daban,
kuma ba wai kawai zaman kurkukun ba, a’a, har da umurnin cewa a gallaza masa.
Akwai ma lokacin da suka ta~a
wakilta wani da ake ce wa Nahriri, ya tsare shi. Shi wannan Nahirir ]in ya kasance mutum ne maras tausayi, mai gallazawa
mutane. Shi ne a lokacin matarsa take ce masa ya ji tsoron Allah dangane da
Imam Hasan Askari (AS). Ta ce masa tana ji masa tsoro idan ya }untata masa wani
abu zai same shi. Maimakon ya amshi wannan nasiha tata, sai ma ya da]a }aimi.
Saboda bushewar zuciya, ya ce mata ai sai ya sa shi a cikin ]akin zakoki.
Wani
abin mamaki da Khalifofin Umayyawa da Abbasawa suka yi a lokacin su shi ne; a
kurkuku akan yi ]aki wanda ake sa zakoki a ciki, akan kuma yunwatar da su. To a
cikin fursunoni wa]anda aka yanke wa hukuncin kisa akan jefa mutum cikin ]akin
wa]annan zakoki a matsayin abincinsu. Mu duba irin wannan zalunci. To sai shi
wannan mutumin mai suna Nahriri ya nemi izinin yin haka daga masu tafi da iko
na lokacin, na a kan ya jefa Imam Askari (AS) cikin wannan ]aki na zakoki. Suka ba
shi izinin yin haka.
A bayan da ya je ya aiwatar da
wannan abin da ya yi nufi. Washegari sai ya zo domin ya ga abin da ya faru sai
ya tarar da Imam Askari (AS) yana tsaye yana Salla, wa]annan zakoki kuma na
gefensa! Allahu Akbar ! Ganin haka umurni ya zo a kan a saki Imam Askari (AS).
Mu duba wannan babbar karama ta Imam Askari (AS).
Baya ga wannan jarabawa da Imam
Askari (AS) ya fuskanta daga azzalumai masu tafi da iko na zamaninsa na zaman
kurkuku. Akwai jarabawa da ya fuskanta na sa masa ido da kuma kange shi daga
mu’amala da mutane, duk da cewa Imam Askari (AS) yana zaune ne a sansani na
maya}a, amma haka bai hana sa masa ido na le}en asiri ga dukkan mu’amalolinsa
ba. Wani abin mamaki ma shi ne, hatta zaman sa a cikin kurkuku, sai da aka ha]a
shi da ]an le}en asiri, da sunan cewa wai shi ma fursuna ne, amma a ~oye
aikinsa shi ne ya dinga tattara bayanai na zantukan Imam Askari (AS) shi da
mabiyansa da suke cikin kurkukun yana aiko wa masu tafi da iko.
Imam
Askari ne ya tona asirinsa ga mabiyansa. Wata rana suna zaune cikin kurkukun,
sai Imam Askari (AS) ya yi ishara gare shi, ko zai ]an fita daga waje. Bayan
fitar sa shi ne Imam Askari (AS) ya ce wa mabiyan nasa; “Wannan mutumin ba a
cikinku yake ba, saboda haka ku yi hankali da shi. Domin duk
abubuwan da kuke fa]i yana nan rubuce a takarda, takardar na nan cikin
kayansa”.
Nan take cikin mabiyan Imam wani
ya tashi ya duba kayansa, sai suka ga takarda }unshe da zantukansu. Wannan ma
wata karama ce ta Imam Askari (AS). Shi wannan mutumin ba wai kawai ya nuna shi
]an fursuna ba ne, a’a, ma ya nuna shi mabiyin Ahlul Baiti (AS) ne, shi ya sa
Imam Askari (AS) ya ce su yi hankali da shi, ba a cikinsu yake ba.
Mu duba irin wannan sa ido, har a
kurkuku ba a }yale shi ba. Saboda da ma gayar sa ido da ake yi masa, akwai
lokacin da Imam Askari (AS) ya bu}ata daga mabiyansa, idan suka gan shi ko suka
ha]u da shi, kada su yi masa sallama, ko su nuna shi domin amintuwa ga
kawukansu, kamar yadda Imam Askari (AS) ya ce. Daga nan mutum zai fahimci irin
gayar ’yan le}en asiri da aka turo wa Imam Askari (AS), wa]anda suke lura da
kai-komon sa, da kuma mu’amalarsa da mutane. Domin mujararradin ala}a da Imam
Askari (AS) a lokacin in an ga mutum yana iya fuskantar hukuncin kisa ko zuwa
kurkuku. Akwai ma lokacin da Imam Askari (AS) yake fa]a wa wani daga cikin
mabiyansa ko dai ya ~oye ala}arsa da shi, ko kuma ya fuskanci kisa.
A ta}aice dai Imam Askari (AS) ya
fuskanci sa ido daga masu tafi da iko fiye da sauran A’imma (AS) da suka gabace
shi.
Wata jarabawa kuma da Imam Askari
(AS) ya fuskanta wanda sauran A’imma (AS) ba su fuskance ta ba ita ce, na sa
ido da kuma bincike ga iyalansa lokaci bayan lokaci, domin a gane wacce ce take
da ciki? Saboda masaniyar da su wa]annan azzalumai masu tafi da a iko suke da
ita na cewa shi ne Imam na 11, kuma shi ne zai haifi Imam na 12, wanda zai kau
da zalunci da kuma azzalumai a doron }asa. A kan wannan asasi suka samo mata
}wararru na sanin cikin ’ya mace wa]anda suke da ciki, da nufin su sa ido ga
iyalinsa. Amma ta Allah (T) ba tasu ba. A irin wannan yanayi aka haifi Imam
Mahdi (AS).
Bayan haihuwar sa ma, al’amarin
haka ya ~oye gare su har ya shekara biyar a duniya gabanin wafaatin Imam Askari
(AS). Wannan jarabawa ce ga Imam Askari (AS), domin da aka yi haihuwar wa]anda
suka sani kawai sune wasu da suke kusa da shi sosai a cikin mabiyansa. Domin ko
abin a}i}ar[dabbar da
ake yankawa ta suna]
Imam Askari (AS) ya bayar a sayo a wani
waje ne,wato aka yanka acan. bayan wafatinsa ma akwai wata daga cikin kuyangun sa
da aka tsare kusan shekara biyu bisa tsammanin tana da ciki, sai daga baya suka
sake ta.
A ta}aice Imam Askari (AS) ya
fuskanci wannan jarabawa ta sa ido, fiye da kowane Imami, shi ya sa galibi
ala}arsa da mabiyansa ta rubutu ne. Su rubuto, ya rubuta masu. A nan za mu
kammala wannan rubutu da wata wasiyya da ya rubuta wa Shi’arsa a loakcin. Ga
Wasiyyar:- “Ina maku wasiyya da jin tsoron Allah (T) da kuma tsantseni cikin
addininku da kuma yin mujahada saboda neman yardar Allah (T) da gaskiya wajen
magana da ba da amana ga wanda ya ba ku amana daga mutum kirki da wa]anda ba
mutumin kirki ba. Da kuma tsawaita sujuda, da kyakkyawan ma}wabtaka, da wannan
Manzon Allah (S) ya zo. (Sannan Imam Askari (AS) ya fa]i abubuwa hu]u domin
kyautata ala}a ga wa]anda ba mabiya Ahlul-Baiti (AS) ba)”.
A ci gaban wannan wasiyyar sune;
“Ku yi Salla a masallatansu, ku halarci jana’izarsu, ku je gaida mara
lafiyarsu, ku ba da ha}}o}insu, domin ]ayan ku idan ya yi tsantseni a
addininsa, ya zama mai gaskiya a maganarsa, mai kuma ri}on amana, ya kuma
kyautata ]abi’unsa da mutane za a ce wannan ]an Shi’a ne. Wannan ko sai ya
faranta min rai”.
Ya ci gaba da cewa; “Ku ji tsoron
Allah ku kasance masu }awatawa, kada ku kasance masu munanawa. Ku jayo mana
dukkan so. Ku tunku]e mana dukkan }i (wato mutum ya lizimci aikata abin da ya
san zai jayo so ga Ahlul Baiti (AS) domin abin da aka fa]i kyakkyawa dangane da
mu, to mu ma’abotansa ne. Abun da kuma aka fa]i mummuna dangane da mu, to mu ba
haka muke ba. Ku yawaita ambaton Allah (T) da kuma tunanin mutuwa da karatun
Al}ur’ani da kuma salati ga Manzon Allah (S). Ku kiyaye wannan wasiyya da na yi
maku. Amincin Allah ya tabbata gare ku”.
Wannan ita ce wasiyyar da Imam
Askari (AS) ya aiko wa mabiyansa. Kuma wannan wasiyya tasa ba ta ta}aita ga
Shi’ar zamaninsa ba, a’a, har da wa]anda suka zo daga baya. Saboda haka sai
mutum ya dubi wannan wasiyya kamar madubi, ya dubi kansa da ita. Abubuwan da
aka ambata duka ya dabba}a su, in haka ne sai ya gode wa Allah (T) da kuma da]e
tsayuwa a kan su, in ko ba haka ba ne. To sai ya yi }o}arin wajen ganin cewa ya
]abba}a su.
Bayan haka kuma akwai wata
wasiyyarsa da ya rubuta wa ]aya daga cikin manya-manyan mabiyansa, wato Ibn
Babawaihi Al}ummi, wanda yake shi Mahaifi ne ga Shaikh Sadu}. Ga wasiyyar;
“Inai maka wasiyya da tsoron Allah da tsaida Salla da ba da Zakka, domin ba a
}ar~ar Sallar wanda bai ba da Zakkah.
“Ina maka wasiyya ga yin afuwa ga
laifin da aka yi maku, da ha]iye fushi da sadar da zumunci da taimaka wa ’yan
uwa, da kuma sa’ayi ga bu}atocinsu a cikin tsanani da kuma sau}i da kuma ha}uri
ga mai wauta, da kuma neman ilimin addini, da kuma tabbata a kan al’amarin, da
kuma yawaita karatun Al}ur’ani, da kyakkyawar ]abi’a, da umurni da ma’arufi, da
kuma hani ga mun}ar, da nisantar alfasha dukkan ta. Na hore ka da Sallar dare.
Domin Manzon Allah (S) ya yi wasiyya ga Imam Ali (AS) ya ce masa; ‘Ya Ali! Na
hore ka da Sallar dare, na hore ka da Sallar dare, na hore ka da Sallar dare,
duk wanda ya wula}anta Sallar dare, to ba ya daga cikinmu’. Ka yi aiki da
wannan wasiyya tawa. Kuma ka umurci duk mabiyana da su yi aiki da ita. Kuma na
hore ka da dauriya da kuma jiran faraj[wato jiran Imam Mahdi]. Domin Manzon Allah (S) ya ce
mafificin aikin al’ummata shi ne jiran faraj, kuma Shi’armu ba za su gushe ba
cikin damuwa da ba}in ciki ba har sai ]ana ya bayyana, wanda Manzon Allah (S)
ya ba da albishir da zuwan sa, cewa zai cika }asa da adalci bayan ta cika da
zalunci da kuma danniya. Saboda haka
ka daure ka umurci Shi’ata, su daure, }asa ta Allah ce yana gadar da ita ga
bayin sa. A}iba kuma tana ga masu ta}awa. Amincin Allah ya tabbata gare ka da
kuma dukkan Shi’armu”. Wannan ita ce }arshen wasiyyar. Allah (T) ya ba mu ikon
aikatawa.
In Allah ya kai mu wata munasaba ta wafatinsa za a ]ora a
kai, insha Allah.
No comments:
Post a Comment