Wannan wata da muke ciki na zulhijja,bakwai gare shine
wafatin Imam Muhammad Ba}ir [AS] domin ya rasu ne ranar litinin 7 ga zulhijja shekara ta 114 bayan hijra.Ya
rasu ya na da shekaru 57 a duniya,muddan imamancinsa kuma shekara 19.Kabarinsa
yana madina ne,watau a Ba}i’a.Kuma
kamar yadda aka sani a jerin }idaya
na Imamai goma sha biyu,shine Imam na biyar.Kuma shi ]ane ga Imam Zainul Abidin [AS] ]an Imam Husain
[AS].
Ya rayu tare da kakansa ,watau Imam Husain [AS] shekara hu]u.Ya ma zo akan
cewa wa}i’ar
karbala a gaban idonsa ta gudana,wato yana wajen.Saboda haka duk abubuwan da
suka biyo bayan wa}i’ar
karbala na kai su sayyida Zainab [AS] zuwa kufa,daga nan zuwa sham,daga
nan kuma dawowa madina,da kuma abinda ita wannan tafiya da aka yi da su ta }unsa,na
cutarwa da kuma musgunawa,duk tare dashi aka fuskanci wa]annan matsaloli,lokacin yana da
shekara hu]u a
duniya.
Imam Ba}ir
[AS] yayi kama da Manzon Allah [S] sosai,shi yasa daga cikin la}ubbansa ana ce
mashi “SHABIH”Akwai ma ]aya
daga cikin sahabban Manzon Allah [S] wanda ake cewa Jabir ]an Abdullahi Al-ansari
[RA] da yace, Manzon Allah [S] yace mini “Ya jabir lallai zaka rayu har sai ka ga
wani daga cikin jikoki na da yayi kama dani,sunansa kamar sunana ne.Ana ce masa
Muhammad.Idan ka gan shi,ka isar da sallamata gare shi”.Sa’annan Manzon Allah
[S] yace masa, “Ka sani wanzuwarka bayan ka gan shi ka]an ne”watau tsakanin ganinsa dashi
,da kuma rasuwar sa ba nisa.Wa]annan
ababe da Manzon Allah [S] ya fa]a
ma sahabinsa,haka ko suka faru.Allah [T] yayi masa tsawon rai har sai da yaga
Imam Ba}ir
[AS],ya kuma isar da wannan sallama gare shi,kuma bayan daya ganshi bai jima
ba,Allah [T] yayi masa rasuwa.Har ma akwai fa]in
Jabir da yake cewa “Allah [T] ya jinkirta mani ajali na,har naga Ba}ir [AS] na isar
masa da sallamar kakansa Manzon Allah [S]”.Kuma
Jabir ]an
Abdullahi Al-ansari [RA] shine farkon wanda ya ziyarci kabarin Imam Husain [AS]
a karbala bayan shahadar sa da kwana arba’in.Tare dashi Jabir a wannan ziyara
akwai wani da ake cema A]a’a
,ya na daga cikin tabi’ai,sa’annan kuma da wasu daga cikin bani Hashim. Kuma kamar yadda yazo a littafan
tarihi,su Sayyida Zainab [AS],akan
hanyar su ta dawowa daga sham zuwa madina sun biyo ta karbala,sun iso karbala
ne 20 ga watan safar,watau ranar bisa ikon Allah [T] tayi muwafa}a da ranar
arba’in ]in
Imam Husain [AS].Saboda haka ko da su Sayyida Zainab [AS] suka iso kabarin Imam Husain [AS] sun samu su Jabir
[RA] a wurin.Haka wa]annan bayin Allah
[T] baki ]ayan
su suka zauna a wajen,su kayi juyayi da kuka da kuma zaman makoki har na tsawon
kwana uku,a wata ruwaya.Sa’annan suka kama hanya zuwa madina.Yazo akan cewa
lokacin da Sayyida Zainab [AS] ta iso
kabarin Imam Husain [AS] ta fashe da kuka tana fa]in
“WA AKAH,WA AKAH,WA AKAH!”. Imam Ba}ir [AS] an haife shi a madina,ya
rayu a madina,ya rasu a madina.An haife shi a ranar juma’a,a wata ruwaya ranar
litinin ]aya
ga watan Rajab,hijira na da shekara 57.Sunan mahaifiyarsa Fatima ‘yar Imam
Hasan.Yazo akan cewa shine ka]ai
wanda ya ha]a
irin wannan nasabar na cewa mahaifiyarsa itace Fatima ‘yar Imam Hasan [AS],mahaifinsa
Imam Sajjad [AS] ]an
Imam Husain [AS].Kuma ita wannan mahaifiyar tasa yazo daga Imam Sadi} [AS] cewa a zuriyar
Imam Hasan [AS] baki ]aya
babu mace kamar ta.Har ma siffan ta da
cewa ita Siddi}a
ce.Kuma idan mutum ya bibiyi tarihin rayuwarta zai ga akwai karamomi da yawa da
suka bayyana daga gareta.Alal misali ga wasu daga ciki: 1.Yazo
daga Imam Ba}ir
[AS] yace, “akwai lokacin da mahaifiyarsa tana zaune a jikin Katanga ,ashe
Katangar ta tsage ,zata fa]i.Ganin
haka sai mahaifiyarsa tayi ishara da hannunta ga katangar tace,a’a da ha}}in
Mustafa,Allah bai yi miki izinin
ki fa]i
ba”.Haka katangar ta tsaya a karkace sai da ta bar wajen ta fa]i.
2.Lokacin
da take ]auke
da cikin Imam Ba}ir
[AS] ta kan ji sautin Magana a cikin gida ana ce mata albishirinki da yaro mai
ilimi,mai ha}uri,ta
kan ji haka,amma kuma bata ganin mai maganar.
3.Haka nan
yazo akan cewa a daren da zata haifi Imam Ba}ir
[AS],wani haske ya bayyana wanda ya haskaka dukkan gidan, amma ikon Allah ba
mai ganin hasken daga ita sai mahaifinsa,watau Imam Zainul Abidin [AS],da dai
sauran karamomin ta wa]anda
ba za’a iya kawo su ba, saboda gudun tsawaitawa.
Imam Ba}ir [AS] anai masa kinaya da Abu ja’afar.Ya nada la}ubba masu
yawa,amma wanda yafi shahara shine wannan lakabi nasa na Al-Ba}ir.Kuma Manzon
Allah [S] ne ya yi masa wannan la}abi
da haka.An ruwaito daga Shaikh Sadu}
cewa an tambayi Jabir ]an Ju’ufiy me yasa
ake ce masa Ba}ir ? Sai yace, “saboda ya tsaga
ilimi tsagawa,ya bayyanar da shi bayyanarwa.A takaice wannan la}abi nasa na Al-ba}ir yana alamta yawan iliminsa da kuma fito da ba]ini
na ilimi
domin bayyanar dasu.Kuma tabbas idan mutum ya bibiyi tarihinsa a fagen ilimi za iga haka,domin hatta
sahabbban Manzon Allah [S] wa]anda
Allah yayi wa tsawon kwana da suka yi zamani dashi sun amfana da ilimin sa
kamar yadda zamu ga haka nan gaba,a bayanin iliminsa [AS].Imam Ba}ir [AS] yana da
‘ya’ya bakwai,maza biyar,mata biyu.Mazan sune,Imam Sadi} [AS],Ali,Abdallah,Ibrahim,da kuma
Ubaidullah.Matan sune,Zainab,da kuma ummu salma.Imam Ba}ir [AS] ya rayu tare da mahaifinsa
kusan shekaru 25.
Bayan wannan shimfi]a
na janibobi daban daban da suke da ala}a da Imam Ba}ir [AS],sai kuma
Darussa sha biyu daga rayuwarsa da aka saba gabatarwa a irin wannan munasabobi
na wafatin A’imma na Ahlul bayt [AS],da nufin su kasance madubin da zamu dubi
kawukanmu da kuma yin mujahada wajen ganin cewa mun ]abba}a su gwargwadon ikon kowannenmu.
1.
IBADARSA:Imam Ba}ir
[AS] ya kasance mai yawan ibada.Ga misalan wasu daga cikin ibadodinsa.A -Azkar ]insa,ya kasance mai
yawan zikiri,kamar yadda aka ruwaito haka daga Imam Sadi} [AS] yace “Babana ya kasance mai
yawan zikiri.Na kasance in muna tafiya tare dashi sai in ji yana zikiri,in muna
cin abinci sai inji yana zikiri.Haka nan ko tattaunawa yake da mutane wannan
bai shagaltar dashi daga zikirin Allah [T].Na kasance ina ganin harshensa yana
yawan fa]in
“La ilaha illallah”.Imam Sadi}
[AS] yaci gaba da cewa,ya kasance yakan tara mu bayan sallar asuba,ya umurce mu
da yin azkar har rana ta fito.Wanda ya iya karanta Alkur’ani daga cikin mu sai
yace yayi karatun Alkur’ani,wanda bai iya ba sai yace yayi zikiri. B.Sallolinsa:Imam
Ba}ir [AS] ya
kasance kowace rana ya kanyi sallah ta nafila 150,duk da cewa mafi yawan
lokutansa ya kasance yana karantarwa ne da kuma amsa tambayoyin masu tambaya,na
kusa da kuma na nesa.Amma duk da haka kowace rana ya kanyi wa]annan
nafiloli C.Karatun Al}ur’ani:kuma
ya kasance mai yawan karatun Al}ur’ani,kuma
ya kasance mai yawan son sauraron karatun Al}ur’ani.Wani
lokaci ya kasance yakan sa wani daga cikin mabiyansa ya karanta masa Al}ur’ani,watau
domin ya saurara.Sai dai wani tambihi a nan dangane da karatun }ur’ani, shine yana
da gayar muhimmanci ga kowannenmu ya
zamanto yana da wani tsari na lokaci daya tsara ma kansa na karatun }ur’ani ta fuskoki
guda uku.Fuska ta farko ya zamanto akwai wani lokaci daya ke~e ma kansa na
karatun shi Al}ur’ani
kowace rana,ta yadda wannan zai sa ya sauke shi a}alla
kowane wata sau ]aya.Wato
kada ace wata ya kama har ya }are
bai sauke Al}ur’ani
ba.Kuma wannan sassau}a
ne in dai har mutum zai tsara lokacinsa.In ma saboda yawan shugul a cikin
yini,to mutum ya yasa karatun a cikin sallar Tahajjud ]insa.ko da ma bai haddace Al}ur’ani ba,to ya
dinga amfani da mus’hafi wajen Tahajjud ]insa.Domin
dai haka ya ba shi damar ya dinga saukewa sau ]aya
ko fiye da haka a kowane wata.Akwai wani da na sani a haka ]in
yakan sauke duk kwana uku.A
Tahajjud Raka’a 8,wato in ka ]ebe
shafa’i da wuturi da kuma raka’a 2 na bu]ewa.Da
yake yazo a hadisi cewa,a na son mutum yayi raka,a biyu kafin ya fara sallar
tahajjud ]in sa.Raka’a ta farko ana son mutum ya biya }ul-huwallahu ]aya,wato
bayan fatiha.raka’a ta biyu bayan fatiha }ul-ya ayyuhal- kafirun ]aya.bayan
sallama sai mutum ya Tashi,ya fara tahajjud ]insa. .Kaga kenan idan a
wata mutum sau ]aya
yake saukewa a kowane wata,to a wa]annan
raka’o’i 8,sai ya biya izu biyu.wato
kowace raka’a ya dinga biya rubu’in izu .In kuma duk mako yake saukewa sai ya
dinga biya izu 8 a Tahajjud ]in,wato
a kowace raka’a ya biya izu ]aya kenan.Idan kuma
aduk kwana ukku yake saukewa ,sai ya dun ga biya izu 2o a raka’a 8 ]in,ko wace raka’a 2, izu
5,raka’a ta farko izu 3,raka’a ta biyu izu 2,kamar yadda wancan ]an’uwan ya
keyi,wanda na ambata a sama cewa yana saukewa a duk kwana ukku.Idan kuma
Tahajjud ]insa
ta samu matsala wani lokaci, sai ya biya abinda ya saba karantawa na Alkur’ani ]in a cikin yini. Fuska
ta biyu shine ya zamanto akwai lokacin daya ke~e
ma kansa na sauraron karatun Al}ur’ani.Alhamdulillah
a wannan zamani ga kasusuwa na CD ne da MP3 da makamantansu na makarantan Alkur’ani
daban-daban.Sai wanda mutum yake bu}ata,
kuma izu sittin cikakke.Sai mutum ya samu wanda yake bu}ata na makarantan,ya kasance lokaci
bayan lokaci,yana sauraron karatun, ya ]auko
sauraron karatun Alkur’ani ]in
tun daga suratul Ba}ara
har zuwa Nasi.Ta yadda dai a}alla
ko sau ]aya a
shekara ya sauke Alkur’ani, ta hanyar sauraro da kunnensa.Kuma nasan mutum zai yi
farin ciki gobe }iyama,kunnensa
yaba da shaida cewa ya sauke Alkur’ani dashi ta hanyar sauraro,banda kuma ladar
da mutum zai samu na falalar sauraron karatun Alkur’ani. Fuska
ta uku,ya zamanto akwai lokacin daya ke~e
ma kansa na haddar Al}ur’ani.In
kuma Allah [T] yayi masa muwafa}a
da haddacewa,sai lokacin ya mai dashi na biya haddarsa.Idan Kuma bai haddace
ba, kuma ya kai wata mustawa a shekaru,wato
shekaru sun yi nisa,to bai makara ba.Yana iya farawa koda ko aya ]aya ]aya ko fiye da
haka,yake haddacewa ko wace rana,idan ya tsayu akan haka,har ajalinsa ya sauka,to zai koma ga Allah [T] a matsayin
wanda yake da niyyar haddace Al}ur’ani,wanda
kuma wannan niyyar a bisa lu]ufi
na Allah [T] na iya zama sanadiyyar da Allah [T] zai sa mutumin cikin ajin
bayinsa mahaddata Al}ur’ani
gobe }iyama,sa~anin
ko in mutum na ganin shekaru sunyi nisa bai yi niyyar haka ]in ba.Saboda haka
mutum yayi niyya ]in,ya
fara.Kuma wa]annan
fuskoki guda uku da aka ambata,watau na karatun Al}ur’ani
da sauraron sa da kuma haddar sa, akwai hadisai masu yawa da suka zo daga Manzon
Allah [S] da kuma Ahlulbayt [AS] na falalar kowannensu,amma saboda gudun tsawaitawa
ba za’a iya kawo suba.Amma ga mai bu}atar
ganin wa]annan
hadisai yana iya duba littafin Mahajjatul Baida’a na Faidul-Kashani,wanda
littafin Ta’ali}i
ne yayi ga littafin Ihya’ul-ulumuddin na Gazzali.
2.
JARABAWOWINSA:Imam Ba}ir [AS] kamar yadda A’imma wa]anda suka gabace
shi da kuma wa]anda
suka biyo bayansa suka fuskanci jarabawowi daban-daban,ta kuma fuskoki
daban-daban a zamunansu,musamman ma ta fuskar masu tafi da iko,to shima ya
fuskanci irin wa]annan
jarabawowin.Daga cikin jarabawowin daya fuskanta ta fuskacin masu tafi da iko
akwai zaman kurkuku,domin in mutum ya bibiyi tarihin Imamai zai ga guda hu]u ne suka zauna a
kurkuku.Sune,Imam Ba}ir
[AS],Imam Kazim [AS],Imam Hadi [AS],Imam Al-Askari [AS].Wato kenan Imam Ba}ir [AS] shine
Imami na farko da masu tafi da iko suka kama da nufin sawa a kurkuku,kuma suka
sa.Wannan ya auku a mulkin Khalifan Umayyawa mai suna Hisham ]an Abdulmalik.Da
yake Imam Ba}ir
[AS] yayi zamani da khalifofin Umayyawa guda biyar,sune Walid ]an Abdulmalik,wanda
ya kekketa Alkur’ani, yace in yaje wajen Allah [T] yace Walid ne ya kekketa
shi.Wannan yana nan a littafan tarihi,musamman ma na madrasah ]in
Ahlus-Sunnah.,Sai kuma Sulaiman ]an
Abdulmalik,sai Umar ]an
AbdulAziz,sai Yazid ]an
Abdulmalik,sai kuma na }arshe
Hisham ]an
Abdulmalik.To,a cikin wa]annan
guda biyar, wanda yafi cutarwa da kuma gallazawa ga Imam Ba}ir [AS] shine Hisham.A
lokacinsa ne yasa aka ]auko
Imam Ba}ir
[AS] daga madina zuwa sham.Bayan an kawo shi sham,aka kai shi fada wajen
Hisham.Bayan tattaunawa da yayi dashi,daga }arshe
yace akai shi kurkuku.Zaman Imam Ba}ir
[AS] a kurkuku,sai ya zama sabab,ba wai kawai na samun canjin tunani ga wa]anda
suke cikin kurkukun ba,a’a ya zamanto sanadiyyar haka sun yi tamassuki da
wilaya ]in
Ahlulbayt [AS],watau sun zamo ‘yan shi’a.Aka je aka shaida ma Hisham cewa fa ga
abinda yake faruwa a kurkuku,sanadiyyar kawo wannan da ya yi. Jin haka sai
Hisham ya bada umurnin a fito dashi,a kuma mai da shi madina.Daga }arshe dai,shi
wannan Hisham ]in
shine ne sabab ]in
wafatin sa [AS] ta hanyar sa masa guba.Amma cikin wa]annan khalifofi na umayyawa guda
biyar da Imam Ba}ir
[AS] yayi zamani dasu,wanda yafi samun sau}i
da kuma samun damar karantarwa na ulum na Ahlulbayt [AS] a lokacinsa, shine
Umar ]an
AbdulAziz.Kuma shi Umar ]an
AbdulAziz ya yi wasu ababe ga Imam Ba}ir [AS],wa]anda su Banu
Umayya ba suji da]i
ba.Daga ciki akwai mai da FADAK na Sayyida Fatima [AS] ga Imam Ba}ir [AS],banda
kuma ha]uwa da
yake da Imam Ba}ir
[AS] in yazo madina,ga kuma hana la’anta na Imam Ali[AS] da yayi,wato wadda ake
yi lokacin a masallatai.Wanda daga }arshe
shi kansa Umar ]an
AbdulAziz Banu Umayya basu bar shi ba.Guba suka sa masa yayi sanadiyyar wafatin
sa, bayan mulki na shekaru biyu da wata biyar.
3.
ILIMINSA:Imam Ba}ir
[AS] ya kasance a wannan fage na ilimi.malaman da su kayi zamani dashi,dama wa]anda ba suyi
zamani dashi ba,duk sun tabbatar da haka,cewa a zamaninsa baki ]aya ba wanda ya kai
shi ilimi.Domin hatta sahabban Manzon Allah [S],wa]anda
Allah yayi wa tsawon rai sun amfana da iliminsa.Ga misalan wasu daga
ciki,Abdullahi ]an
Umar,ga duk wanda ya bibiyi tarihin Abdullahi ]an
Umar a fagen ilimi,a littafan madrasah ]in
Ahlus-Sunnah zai fahimci abinda ake nufi a matsayinsa na fagen ilimi,amma duk
da wannan ilimin nasa,wani lokaci za’a zo mishi da tambayoyi na mas’aloli na
Addini,wa]anda
ya sani ya bada amsa wa]anda
bai sani ba sai yace “kuje ku tambayi
wancan saurayin,Yana nufin Imam Ba}ir
[AS],amsar daya fa]a
muku kuzo ku fa]a
mani,” haka nan,Sahabin Manzon Allah [S] Jabir ]an
Abdullah,wani lokaci in ya fa]i
wasu hadisai da yaji daga Manzon Allah [S],Imam Ba}ir
[AS] ya kan gyara masa wasu,yace ga yadda hadisin yake.Akwai misalai da dama
irin haka,kamar fa]in
wani malami da yayi zamani dashi,yace “ ban ta~a ganin wani wanda manyan malamai
suke gabansa kamar yara ba,sai Abu Ja’afar.Shine ya bada misali da wani babban
malami a lokacin mai suna Hakam ]an
Utaiba.Yace duk da matsayin sa a ilimi,ya gan shi a gaban Imam Ba}ir [AS] kamar
yaro gaban mai karantar da shi”.A ta}aice
dai,a lokacin sa hadisai na Manzon
Allah [S] da kuma Ahlulbayt [AS] sun ya]u
fiye da kowane lokaci a gabaninsa.Kuma
ko yanzu mutum ya duba littafan hadisai na madrasah ]in Ahlulbayt [AS] zai ga haka;wato hadisan
da aka samo daga Imam Ba}ir
[AS] da kuma Imam Sadi}
[AS] sun fi yawa,in an kwatanta da wa]anda
aka samo daga sauran Imamai [AS].
4.
AKHLAK-[INSA:Shima
a wannan fage kamar sauran fagagen rayuwarsa,a zamaninsa ba wanda ya kai shi ballantana ya wuce shi,ga misalan wasu
daga cikin Akla}-]insa.
A-Ha}urinsa:akwai wani
Ahlul-kitab daya fa]a masa Magana
]ai-]ai har guda uku,wa]anda
basu da da]in
ji ko karantawa ko rubutawa.Amma saboda amana ilimiyya ga ]aya
daga ciki,yace ma Imam Ba}ir
[AS] “kai ba}ara
ne.”Ya mayar masa da amsa cikin murmushi yace, “a’a ni Ba}ir ne”.Sai ya fa]i sauran munanan
maganganun guda biyu,Imam Ba}ir
[AS] ya mayar masa da amsa cikin murmushi,ganin haka sai wannan Ahlul kitab ]in abin ya bashi
mamaki, domin ya ga ya fa]i
maganganu wa]anda
yake tunanin, zasu fusata Imam Ba}ir
[AS],amma shi ya mayar masa da akasin abinda yake tunani.Daga }arshe dai ganin
wannan Akhla} na Imam Ba}ir
[AS] sai nan take ya tuba,ya musulunta.Mu duba irin wannan jarabawa,ace Ahlul-kitab,bama musulmi ba yayi irin
wannan.Mutum zai ji mamaki ta wani ~angare
kan haka,ta wani ~angare
kuma ba zai ji mamaki ba,saboda kafa suka samu na yin haka daga masu tafi da
iko;wato yadda suke zagin Imaman Ahlulbaiti [AS] a lokacin a masallatai,musamman
ma Imam Aliy [AS].Har wala yau daga cikin ha}urinsa
akwai wani mutumin sham,daya kasance yakan je majalisin Imam Ba}ir [AS]. ya fa]i sunansa gatsai
“ya Muhammad!”Ina zuwa wannan majalisi naka ne,ba wai don ina son ka ba,kuma ni
bani da wani da nake }iyayya
dasu kamar ku Ahlulbayt [AS],domin na
san }iyayya
daku shine ]a’a
ga Allah da kuma khalifah [mutanen sham
haka aka gina su a lokacin,wato }iyayya
da kuma gaba da Ahlul-bayt].Saboda haka abinda yasa nake zuwa majlisin
ka saboda fasahar maganarka da kuma balagar dake ciki.Bayan daya gama sai Imam Ba}ir
[AS] cikin murmushi ya mayar masa da jawabi mai ratsa zuciya.Nan take mutumin
ya samu canjin tunani daga }iyayya
ga Ahlulbayt [AS] zuwa wila’a garesu.Ya ma fasa
komawa sham ]in,ya
za~i ya zauna
wajen Imam Ba}ir
[AS].Ya bar wasiyyar cewa in ya rasu,Imam Ba}ir
[AS] yayi masa sallah.Akwai misalai da yawa irin wannan na ha}urin Imam Ba}ir
[AS] wanda wannan Akhla}
nasa na ha}uri,
ya zama makami babba na canza masu gaba da }iyayya
dashi zuwa ga masoya.
A.
Kyautarsa.Imam Ba}ir
[AS] ya kasance mai yawan kyauta.Akwai wani daya kawo kukan halin da yake ciki
na bu}ata.Yace,da
yana dashi,mutane suna tare dashi,amma
yanzu da bashi da shi sun waste sun bar
shi.Shine Imam Ba}ir
[AS] yace masa tir da ‘yan uwantakar da
in kana dashi,ana tare da kai,in baka dashi a yanke maka.Sai Imam Ba}ir [AS] ya bashi
dirhami ]ari
bakwai yace, “kaje ka biya bu}atar
ka da wannan,in sun }are
ka fa]a
mani”.Har wala yau daga cikin kyautarsa yazo daga Imam Sadi} [AS] yace “na
shiga wajen babana wata rana,sai na same shi yana sadaka ga matalautan madina
da dirhami dubu takwas.Haka nan ya kasance mai yawan ihsani ga ‘yan uwansa na
jini.Yazo a tarihinsa cewa,in suka zo wajensa ya kan basu ku]a]e,tufafi,da
kuma kayayyakin abinci.Har akwai lokacin da wata baiwarsa tayi masa Magana akan haka,yace mata, “meye
duniya in ba kyautata ma ‘yan uwa da abokai ba?” Akwai misalai da yawa na irin
kyautarsa,amma za’a ta}aita
akan wa]annan.
B.
Tawali’unsa.Imam Ba}ir
[AS] ya kasance mai yawan tawali’u.Ga misalin wani daga ciki.Yazo a tarihinsa
cewa da daddare a munajatinsa da Allah[T] yakan fa]i
haka “Ya Allah ka umurce ni,amma ban umurtu ba,ka hana ni,amma ban hanu ba,gani
bawanka gaba gare ka”.Mu duba,mu gani a matsayinsa na ma’asumi a I’iti}adin da muke
dashi,amma yana fa]in
haka,to ina gamu? Kuma wannan itace dama ]abi’a
ta bayin Allah [T],wato suna kusantar Allah,amma kuma suna ganin }as}ancin kansu da
kuma lalacewar su gaban Allah [T],saboda suna gaban wanda yake da kamala wadda
bata da iyaka.Saboda haka yana da muhimmanci ko wannenmu ya zamo mai yawan }as}antar da kai ga
Allah [T] da kuma bayinsa,musamman ma ga ‘yan uwansa muminai.
C.
Kukansa.Imam Ba}ir
[AS] ya kasance mai yawan kuka saboda tsoron Allah [T].Akwai wani da yaje aikin
hajji tare dashi,yaga yadda yake kuka har sautin kukan yana fita,sai shi wannan
mutumin yayi wa Imam Ba}ir
[AS] Magana,Sai Imam Ba}ir
[AS] ya kira shi da sunansa Aflah Ya Aflah! Ina ]aukaka
sautin kukana ne,domin Allah [T] ya gan ni ya dube ni da Rahma,domin in rabauta
da ita gobe }iyama.”Har
wala yau shi wannan dai da yayi aikin hajji da Imam Ba}ir [AS] yake cewa,akwai lokacin daya
ga yana sallah,da yayi sujuda,bayan ]agowarsa
daga sujada,sai yaga wajen duk ya ji}e
da hawayensa.Shima wannan akwai misalai da yawa akan haka,amma za’a ta}aita akan wannan.
No comments:
Post a Comment