Kasantuwar
wannan wata da muke ciki wato Muharram,wata ne na zaman makoki wanda akan tunatar
da juna dangane wannan wa}i’a ta karbala,misali abubuwan da suka auku gabanin
Ashura da abubuwan da suka auku ranar Ashura,da kuma abubuwan da suka biyo
bayan Ashura da kuma darussan da zamu koya daga wannan wa}i’ar ta Ashura dadai
sauran ~angarori dake da ala}a da wannan al’amarin na Ashura,
wanda akan tunatar
da juna a kai,baya ga wannan akwai wani janibi mai muhimmancin gaske dake da
ala}a da wannan wa}i’ar ta Ashura.Wannan janibi kuwa shine GUDUMMAWAR MATA A
WA{I’AR ASHURA.Idan mutum ya bibiyi tarihin wannan wa}i’ar ta Ashura,tun daga
farkon ta har }arshen ta zai ga cewa
mata sun bada gudummawa mai yawan gaske a ciki.Kuma wannan gudummawa tasu ta
wanzu har ya zuwa wannan zamanin namu kuma zata ci gaba da wanzuwa.Alal
misali,zaman makoki wanda ya zama wata zaunanniyar sunna tun bayan shahadar su
Imam Husain [AS] wa]anda suka soma yin wannan zaman makoki
sune matan da sukayi musharaka cikin wannan wa}i’ar ta Ashura,wato su sayyida Zainab [AS] sun
soma yin haka a sham da kuma bayan isarsu madina kamar yadda zamu ga haka a nan
gaba Insha Allah.
Haka nan sa ba}a}en kaya a irin wannan zama na makoki su
suka soma yi.Wannan ya auku a madina har ma yazo akan cewa idan suna zaman
makoki Imam Zainul Abidin yakan sa a yi abinci a kai masu,kuma daga nan malaman
Imamiyyah suka tafi akan sunnah ]in sa ba}a}en kaya a lokacin makoki,domin kamar yadda aka
sani sunnah itace fa]in ma’asum ko
aikinsa ko kuma tabbatarwarsa,wato Imam Zainul Abidin [AS] ya gansu a wannan
shiga ta ba}a}en kaya baki ]ayan su,wato abinda ake so a fitar a nan
shine;wannan sunna ta shiga babin tabbatarwa. Haka
nan baya ga wannan daga cikin gidunmawar da mata suka bayar,shine Tablig ]in ita wa}i’ar.wato isar da ita ga
wa]anda basu kasance a wajen ba.Domin baki ]aya duk bayanan da akeyi dangane da
wannan wa}i’a
ta karbala ko rubuce-rubuce da akeyi
akai,to asalin shi daga wa]annan bayin Allah mata aka jishi,domin a wa}i’ai
kamar yadda aka sani duk wani namiji an kashe
shi,sai Imam Zainul Abidin ko shima dun yana kwance bai da lafiya.Wannan
yana ]aya daga cikin asrar da kuma hikima ilahiyya da yasa Imam Husain[AS] ya tafi da mata da kuma yara zuwa karbala,saboda bayan wa}i’ar ,su
isar da ita ga mutanen zamaninsu da kuma wa]anda zasu zo daga baya, na abubuwan
da idonsu ya gani,kuma kunnuwansu suka ji,da kuma abubuwan da suka fuskanta
bayan shahadarsu, a nan karbala ,kufa da kuma sham.kuma akan wannan asasi na tablig ]in wannan wa}i’a
ta karbala,wanda Sayyida Zainab[AS]
ta dun ga yi bayan komawarta madina,yasa Gwamnan madina na lokacin ya aikawa
Yazidu cewa,in yana bu}atar
madina to ya kori Zainab daga cikinta.wato saboda bayanan da take yin a wa}i’ar
karbala yana tasiri a zukatan mutane,wanda wannan tasiri ya kai ga hatta magoya
bayan Bani umayya,suka canza tunani,suka yi masu tawaye. A ta}aice dai Yazidu
ya aika da umarni cewa a kore ta daga cikin madina.shi yasa in muka duba zamu
ga }abarinta ba a madina ba yake. Daga
cikin gudummawar da mata suka bayar a wannan wa}i’a ta karbala.Akwai kula da
kuma bada magani ga wa]anda suka samu raunuka,wanda zainab [AS] ta bada gudummawa babba a wannan fage.A
kan asasin haka ne ma a jamhuriyar musulunci ta Iran aka baiwa ranar da aka
haifi zainab [AS] sunan ‘Ranar masu kula da majinyata’,don tunawa da girmama
irin gudummawar data bayar wajen jinyar wa]anda suka samu raunuka a karbala.Daga cikin
gudummawar da mata suka bayar a cikin wannan waki’ar ta karbala itace }arfafa mazajensu da kuma ‘ya’yansu wajen
taimaka wa Imam Husain [AS].Ga misali matar Zuhair kamar yadda yazo a tarihi
zuhair a farkon al’amarin yaso ya kasance basu ha]u da Imam Husain [AS] ba,sai Imam Husain ya
aika yana kiransa, Lokacin da wannan sa}o yazo ga zuhair sai yayi ]an nauyin jiki ga amsa wannan kiran,sai
matarsa ta }arfafa shi akan
ya tafi ya amsa kiran Imam Husain [AS] yaji menene,bayan ya tafi ya dawo,ikon
Allah sai ya dawo da canjin tunani da kuma yankewa cewa ai shiga cikin rundunar
Imam Husain [AS],shine matarsa tace masa; “Allah [T] yayi maka za~i.Ina ro}on ka,ka tuna dani wajen kakan Husain [AS] ranar
}iyama”.Haka nan
zainab ta bada gudummawa mai yawa wajen }arfafa zukatan wa]anda sukayi musharaka a cikin wannan waki’ar ta karbala,musamman ma
mataye da yara a bayan shahadar su Imam Husain [AS].
Daga cikin gudummawar da mata suka
bayar a wannan waki’ar ta karbala akwai niyya da kuma azama wajen sadaukar da
kai domin taimaka wa Imam Husain [AS].Idan mutum ya bibiyi tarihin wannan
waki’ar,zai ga akwai matayen da suka yi yun}urin fafatawa da ma}iya,Imam Husain [AS] yace su koma.Misali wata
mata mai suna Ummi wahab,lokacin da mijinta ya fito yana fafatawa da ma}iya itama ta yun}uro domin ta shiga fagen faman a fafata
da ita,sai Imam Husain [AS] yace ta koma hema.Yace mata Allah ya saka da
alheri.Bayan shahadan mijin nata ta shigo filin daga tana share masa jini,tana ce
masa ; “Albishirinka da Aljanna,ina ro}on Allah da ya azurta ka da shahada ya sani
danshinka mu tafi tare”.Tana cikin fa]in haka sai Shimr ya bada umarnin a rotsa mata
kai,aka ko aiwatar da umarninsa na rotsa kanta.Nan take Allah yayi mata
rasuwa.Saboda haka itace farkon matar da aka kashe a cikin wannan waki’ar ta
karbala.Shine bayan da mahaifiyar wannan shahidi taga ]anta an kashe,ga matarsa an kashe,ta ]auki makami ta yun}uro domin ta shiga fagen fama ta fafata da ma}iya.Imam Husain [AS] yace mata ta
koma.Shine ta koma tana cewa ya Allah kada ka yanke fatana,wato na samun
shahada.Sai Imam Husain [AS] yace; “Allah ba zai yanke maki fata ba”.Da dai
misalai irin wannan da yawa,wanda ba za’a kawo ba saboda gudun tsawaitawa,wato
irin wannan gudummawar da mata suka bayar wa]anda aka ambata dama wa]anda ba’a ambata ba. Akwai
kuma dauriya da dakewa da sukayi na fuskantar wahalhalu daban daban ta kuma
fuskoki daban daban tun daga ranar Ashura har bayan shahadar su Imam Husain
[AS] har ya zuwa dawowar su madina.Ga kulasar matsalolin da suka fuskanta tun
daga ranar Ashura har zuwa dawowar su madina,sai dai abubuwan suna da sosa rai
da kuma ta da hankali.Bayan da aka kashe dukkan sahabban Imam Husain [AS] da
kuma Bani Hashim,ya zama yanzu babu wani namiji babba daya rage face Imam
zainul Abidin [AS],shi kuma bai da lafiya,da kuma mata da yara,sai Imam Husain
[AS] ya tafi domin yayi bankwana dasu.Abu na }arshe daya fa]a wa Imam zainul Abidin [AS] da yayi bankwana dashi
shine yace masa; “Ya kai ]ana! Ka isar da
sallamata ga shi’ata [wato mabiyana] kace masu,babana an kashe shi yana ba}o.saboda haka kuyi juyayi,kuyi
kuka”.Bayan nan ya tafi hema wato tanti nasu zainab [AS] domin yayi bankwana dasu.Ya
kira sunansu ]aya bayan ]aya; “Ya Sukaina! Ya Fa]ima! Ya Zainab! Ya Ummul kulsum!” Haka ya
kira su dukkan su yace masu “Amincin Allah ya tabbata a gare ku,wannan itace }arshen ha]uwa ta daku”.Wato a wannan gida na duniya.Jin
haka nan take dukkan su suka fashe da kuka.Yace masu; “kuyi shirin fuskantar
jarabawowi.Amma ku sani Allah [T] zai kiyaye ku,zai kuma kiyaye mutuncinku,kuma
zai tseratar daku daga sharrorin na ma}iyanku”. Kuma in muka
duba mutum zai ga cewa wannan abin ya tabbata,wato duk da yadda suka kasance a
hannun ma}iya masu busassun
zukata da kuma yun}urin da Ibn Ziyad
yayi na ya kashe zainab [AS],da kuma wanda yazid yayi na ya kashe Imam Sajjad
[AS],duk Allah ya kiyaye su, dama yun}urin da wani mutumin sham yayi a fadar yazid na
cewa a bashi Fatima ‘yar Husain [AS],shima Allah ya kiyaye.Wahalhalu kam sun
sha na yunwa da }ishin ruwa da
duka na tafiyarsu daga karbala zuwa sham.Amma kisa da ta~a mutunci,Allah [T] ya tsare kamar
yadda Imam Husain ya shaida masu. }arshen abinda Imam Husain [AS] yace wa zainab
[AS] a wannan bankwana shine yace mata; “Ya ‘yar uwata kada kimanta ni a sallar
dare [wato sashi cikin addu’a] domin yazo a tarihi cewa Zainab [AS] hatta ranar
Ashura da daddare bata bar sallar tahajjud ]inta ba,duk da ko gashi a daren Ashura sun
kwana suna ibada,a ranar Ashura kuma ga abubuwan da suka faru,amma duk da
haka,haka tayi sallar dare amma a zaune saboda gajiya da yunwa da }ishi.Shine har Imam zainul Abidin [AS] yake
tambayar ta dalilin sallar a zaune tace masa; “wallahi }afafuwana basu iya ]auka ta”.Bayan haka Imam Husain [AS] ya fito
zai wuce ya duba dama ya duba hagu ba kowa yace; “wa zai kawo min doki na?” Da Zainab [AS] taji haka,ta fito taje ta zo masa da dokinsa [AS],ya hau ya
tafi fagen fama. Abubuwan
da suka faru ,suka faru marasa da]in ji da karantawada kuma rubutawa,wato na abubuwan da shimr [LA] yayi
masa.Can bayan wani lokaci sai ga doki ya dawo zuwa tantin su zainab [AS] ba
Imam Husain [AS],wanda abin da yake alamta an kashe Imam Husain [AS].Wannan
dokin ainihinsa dokin manzon Allah [S] ne,amma ikon Allah yayi masa tsawon rai
har zuwa lokacin, wato bayan shekaru 50 da rasuwar manzon Allah [S] yana
raye.Bayan wa]annan la’anannun sun kashe wa]annan bayin Allah sai suka bisu suna ]a]]ebe masu tufafin jikinsu suna rabawa tsakanin su.Haka suka barsu ba tufafi a
jikinsu.ya mazo akan cewa kasantuwar Imam Husain [AS] yasan haka zata auku,da
zai fita bayan yayi bankwana dasu Zainab
[AS] ya samu tsofaffin tufafi wanda mutum ma ba zai yi sha’awarsu ba
yasa.Saboda wannan mummunan aikin da zasu yi.Haka bai ishe su ba,sai suka bi su
suka sassare kawukansu daga jikunansu,shima suka raba kawukan tsakanin su.Daga }arshe wanda ya jagoranci ya}in baki ]aya ya basu umarnin dasu hau dawakansu suyi sukuwa akan
jikkunan wa]annan bayin Allah!! Haka ko suka aikata wannan
mummunan aikin. Bayan haka
sai suka tafi hemomi na mata da yara da suka rage suka kwashe masu kayayyakin
su !! Kai
hatta ]an kunne na mata
da ababen hannu irinsu warwaro basu bari ba. Wani
ma da yaje hemar da Imam Sajjad [AS] yake ciki yana jinya,shimfi]ar da Imam Sajjad
[AS] yake kai,ya fisge ya jefar da Imam Sajjad [AS] a }asa.Ana cikin haka sai ga shimr ya zare takobi
zai sara wa Imam Sajjad [AS],sai Zainab [AS] ta fa]a kan Imam Sajjad [AS] tace sai dai akashe ta
kafin a kashe shi.Nan dai wasu suka bada baki cewa a }yale shi,shine shimr [LA] yace masu ai kun san
abinda Ibn Ziyad ya bada umarni akan cewa akashe duk ‘ya’yan Husain [AS].Allah
[T] bisa ikonsa ya tsare. Bayan
sun gama wannan aika aika na kwashe kayayyakin wa]annan matan da kuma yara,sai suka cinna wa tantunan
wuta.Shine Zainab [AS] ta samu Imam Sajjad [AS] ta shaida masa ga abinda mutanen nan sukayi nasa wa hemomi
wuta.Meye abinyi ? Imam Sajjad [AS] yace su fita daga cikin hemomin su
gudu.Bayan da suka gama wannan aika aika na }one tantuna,Zainab [AS] ta sake tattara wa]annan bayin Allah [T] da yara a waje ]aya.A cikin wannan yanayin ne aka samu yara
biyu suka rasu ‘ya’yan khadija ‘yar Imam Ali [AS],sakamakon yunwa da }ishi da kuma firgitar da yara da sukayi.Haka wa]annan bayin Allah suka kasance a filin
Allah [T] har wayewar gari.Haka Zainab [AS] ta kasance lokaci bayan lokaci tana
bi tana dudduba su.Saboda a wannan rana ta Ashura bayan shahadar su Imam Husain
[AS] mafi yawan wahalhalun da wa]annan bayin Allah suka fuskanta,Sayyida Zainab[AS] ce tafi kowa shan
wahala a cikinsu,saboda yazo akan cewa sun dake ta ba ka]an ba,don ko duka za’a kaiwa wani cikin
mata da yara ita take karewa da jikinta.Haka suka kwana a daren 11 ba abinci,ba ruwa,ba kayansu da suke amfani dashi
yau da kullum,duk an }wace.
Bayan
haka washegari, wato 11 ga wata bayan zawal na ranar suka sa wa wa]annan bayin
Allah sar}o}i suka tasa su gaba zuwa Kufa tare da kawukan Shuhada tsire a
masu!! Suka bar jikkunan wa]annan bayin Allah da suka kashe a fili a nan
Karbala. A wata ruwaya an ce kwanansu uku a wannan filin, sannan wasu bayin
Allah (T) suka zo suka yi jana’izarsu.
ISAR
SU ZAINAB KUFA: Lokacin da labari ya iso ga Ibn Ziyad cewa an iso da wa]annan
bayin Allah Kufa, sai ya ba da umurnin cewa kawukan Shuhada da Ibn Sa’ad ya
aika da su a soke su a masu a ]aga a kuma zagaya da su a kan tituna da kasuwar
Kufa tare da wa]annan mata da yara domin mutane su gani.
Bayan an gama kewayawa da su aka
kawo su fada wurin Ibn Ziyad maganganu marasa da]in ji da izgili suka gudana
daga wurinsa, Zainab (AS) ta mayar masa, shi ne ya fusata wai zai kashe ta. Shi ne wasu na fadar suka ce masa "haba! Ba ka ganin
mace ce?" A nan Zainab ta yi jawabi mai tsawo, wanda yake cike da balaga
da kuma fasaha.
Bayan
wani lokaci aka kama hanya da su zuwa Sham. Haka suka kama hanya da su daga
}auye zuwa }auye, birni zuwa birni, har suka isa Sham. A kowane }auye ko birni
da suka isa sai a yi yekuwa ga mutane, domin su zo su gan su. Kazalika duk wata
ko wani yaro da ya yi kuka sai su dake shi. Abinci kuwa sau ]aya suke ba su a
yini a cikin wannan tafiya tasu. Ya zo a kan cewa Zainab (AS) wani lokaci nata
abincin takan }ara wa yaran, ita kuma ta ha}ura. Haka suka rika yi masu a
hanya har suka isa Sham.
Ya zo a kan cewa sun isa Sham
ranar farko ga watan Safar, dubi adadin kwanakin da ke tsakanin ranar Ashura da
1 ga watan Safar? Za ka ga kwanaki 20 ke tsakaninsu. Sa'annan mutum ya yi
tunanin matsalolin da wa]annan bayin Allah (S) suka fuskanta a cikin wa]annan
kwanakin. Da suka iso Sham sun iske mutane a yanayi na murna da bukuwa na
wannan abin da ya faru. Abin nufi a
nan shi ne su mutanen Sham suna da bambanci da mutanen Kufa. Mutanen
Sham suna da bambancin tunani da kuma asasin abin da suka ginu a kai da mutanen
Kufa. Misali mutanen Sham ba su san su waye Ahlul-Baiti (AS) ba, ballantana su
san matsayinsu, sa~anin mutanen Kufa su sun san su waye Ahlul Baiti (AS), sun
kuma san matsayinsu. Domin Imam Ali (AS) a nan ya zauna har ya zuwa shahadarsa,
sa~anin mutanen Sham, Mu’awiyya (LA) ne ya zauna da su, har ya zuwa mutuwarsa.
Shi ya sa idan mutum ya yi nazarin jawabai da hu]ubobi wa]anda Zainab, Ummu Khulsum,
Fatima ’yar Imam Husain (AS) tare da Imam Zainul Abidin (AS) suka yi a Kufa,
zai ga akwai bambanci da wa]anda suka yi a Sham. Kuma ma in mutum ya duba zai
ga cewa lokacin da aka shigar da wa]annan bayin Allah (T) garin Kufa, galibin
matan, wa]anda suka yi wannan aika-aikan sun fito suna kuka ne sa~anin ko Sham
sun samu mutane suna ki]e-}i]e da raye-raye na murna da farin ciki.
Da suka iso Sham abubuwa da yawa
munana sun faru gare su, wato tun daga isar su garin har ya zuwa isar su fadar
Yazidu. Amma daga baya abubuwa sun canza sakamakon abubuwan da matar Yazid ta
yi da kuma bayyana matsayinta kan wannan aika-aika da aka yi, wanda wannan
‘mau}if’ ]in nata ya sa ala dole Yazid ya canza usulubin fuskantar wannan
al’amarin. Wannan abin yana da ban mamaki ta wata fuskar, ta wata fuskar kuma
babu mamaki. Wato na mau}if ]in matar Yazid. Ya zo a tarihi cewa ita wannan
mata ta Yazid sunanta Hindu ’yar Abdullahi ]an Amir, lokacin da aka kashe
Babanta sai ta dawo gidan Imam Ali (AS) da zama tana hidima a gidan. Bayan
shahadar Imam Ali (AS) sai ta koma gidan Imam Hasan (AS) da zama, kuma ta ci
gaba da hidima a gidan. Kamar yadda ya zo a tarihinta takasance ma’abociyar
kyau, a kan asasin haka ne Mu’awiyya ya nemi aurenta ga ]ansa Yazidu, aka ba
shi. Bayan da aka yi auren ta koma Sham da zama tare da
Yazidu. Amma duk da haka lokaci bayan lokaci idan ta ji wasu sun zo daga Madina
takan bincika domin ta ji labarin su Imam Hasan da kuma Imam Husain (AS). Lokacin da
aka kashe Imam Husain (AS) ba ta da labari. Bayan da aka kawo su Zainab Sham,
sai wata mata ta same ta ta ce mata lallai an zo da wasu ribattatun ya}i ko za
ta bincika ta ji daga ina aka kawo su. Amma akwai }ishin-}ishin asalin su daga
Madina suka fito.
Jin haka matar Yazidu ta ]aukar wa
kanta ta je ta bincika da kanta. Ta shirya
domin ta tafi sai ta shaida wa Yazidu ga inda za ta je. Jin haka
Yazidu hankalinsa ya soma tashi, saboda ya san mau}if ]in matarsa dangane da
Ahlul Baiti (AS) don ta zauna gidan. Amma kasantuwar tana da sul]a a kansa,
wato bai tsallake maganarta ko kuma abin da take so kamar yadda ya zo a tarihin
zamantakewarsu. Saboda haka sai ya }yale ta ta tafi. Saboda haka ta fita tare
da ’yan rakiya da masu yi mata hidima. Lokacin da suka kusa isowa inda su
Zainab suke, Zainab ta hango ta ta gane ta, Ummi Khulsum na kusa da ita, ta ce
mata kin gane waccen matar da take zuwa? Ta ce
ba ta gane ta ba. Ta ce; “Hind ’yar Abdullah ce mai yi mana hidima”. Jin haka
sai Ummi Khulsum ta sunkuyar da kanta. Haka nan ita ma Zainab ta sunkuyar da
kanta. Lokacin da ta iso sai aka aje mata kujera kusa da Zainab take cewa;
“Zainab ya na ga kin sunkuyar da kai?” Sai Zainab ba ta amsa mata ba. Sai ta
sake tambayar ta cewa; “Daga wane gari aka kawo ku? Zainab ta ce daga Madina.
Jin cewa daga Madina. Sai nan take Hind ]in ta sauko daga kujerarta, ta zauna a
}asa. Shi
ne har Zainab take tambayar ta na ga kin sauko }asa Hind? Ta ce saboda girmama
ma’abocin Madina (wato Manzon Allah(S)). Sai Hind ta ce wa Zainab; “Ina so in
tambaye ki wani gida a Madina?” Zainab ta ce; “Tambayi abin da kike so”. Ta ce;
“Ina tambaya dangane da gidan Ali [an Abi [alib”. Sai Zainab ta ce mata; “Ina
kika san gidan Ali?” Jin haka sai Hind ta fashe da kuka ta ce; “Na yi hidima a
gidan”. Sai Zainab ta ce mata; “Wa kike tambaya a gidan?” Ta ce; “Ina tambaya
dangane da Husain da ’yan uwansa da ’ya’yansa da dai sauran ’ya’yan Ali. Haka
nan ina tambayar ki Shugaba ta Zainab da ’yar uwarta Ummi Khulsum”.
Jin haka sai Zainab ta yi kuka,
kuka mai yawa. Sai ta ba ta amsa da cewa; “Tambayarki dangane da Husain (AS) ga
kansa can gaban Yazid. Dangane da Zainab kuwa ni
ce Zainab, wannan kuma ita ce Ummi Khulsum”. Lokacin da matar Yazid ta
ji haka, sai ta fashe da kuka tana fa]in “Wa Imamah! Wa Sayyidah!! Wa
Husainah!!” Ta ce kaico! Da a ce na makance, gabanin wannan ranar ban ga
’ya’yan Fatima a irin wannan halin ba." Aka ce haka ta dinga dukan kanta har sai da ta suma. Lokacin da ta farfa]o
Zainab ta ce mata; “Ki koma gida. Ina ji maki tsaron mijinki Yazid”. Hind ta ce
ai ba zan koma gida ba sai tare da ku. Daga nan ta kama hanya kai tsaye sai
zuwa wajen Yazid, ta ce masa "yanzu kai ka ba da umurnin a yi wa Hasan
haka, kuma a yi masu irin wannan cin mutunci? Shi ne ya yi waje yana ce mata;
“Ai Ibn Ziyad duk shi ya aukar da wannan abu na kashe shi, Allah ya tsine masa”,
in ji Yazid. Wato don ya kwantar mata da hankali. Shi ne matar tasa ta ce; “To
ka sani wallahi ba zan shiga gidanka ba sai tare da su. Jin haka
sai Yazid ]in ya ce to, shi ke nan, tana iya shiga da su. Aka shiga da su
Zainab gidan aka aje su a sashin aje ba}i. Aka ce a nan suka yi zaman makoki na
kwana uku. Daga baya Yazid ya fahimci zaman su hatsari ne a wajensa domin
mutanen gidansa da kuma mutanen gari sun soma samun canjin tunani sakamakon
bayanin da suka ji daga su Zainab da kuma Imam Zainul Abidin (AS). Shi ne wani
na kusa da shi ya ba shi shawarar cewa mafita gare shi ya mai da su Madina. Shi
ne ya shirya a mai da su Madina. Saboda wauta irin ta Yazid, da za su tafi sai
ya ]auko ku]i mai yawa ya ba su, wai ga wannan kan abubuwan da aka yi maku. Shi
ne Ummu Khulsum ta dube shi ta ce lallai Yazid ba ka da kunya, kuma ka cika mai
tsaurin ido, ka kashe ]an uwana da Ahlil Baiti ]ina, wai ka ba mu wannan
makwafin haka? Suka watsar masa da ku]insa, ba su ]auki komai ba.
Bayan kuma haka aka kama hanya da su
zuwa Madina. Da suka iso Madina, inda Zainab ta fara zuwa shi ne Masallacin
Manzon Allah (S). Da ta iso Masallacin ta dafa }ofar Masallacin ta ce; “Ya
Kakana! Ina yi maka ta’aziyyar ]an uwana Husain. Sannan ta fashe da kuka. Bayan
haka ta wuce gida.
Wani tambihi a nan shi ne mutum ya
auna ya yi tunani lokacin da su Zainab suka bar Madina tare da Husain (AS) da
wane da wane, amma yau ga shi sun dawo Madina birnin Manzon Allah (S), ba Imam
Husain (AS), ba wane ba wane. Hatta ita Zainab ’ya’yanta biyu aka kashe. Mutum
ya duba ya gani, ya tunanin wa]annan bayin Allah zai kasance lokacin da suka
iso Madina suka wuce zuwa gidajensu. Bayan isar ta gida matayen Madina suka
cika gidanta. Shi ne Zainab ta yi masu bayani sanka-sankan abubuwan da suka
faru a Karbala a Kufa da kuma Sham, matayen suka yi ta kuka. Da suka koma
gidajensu suka fa]a wa mazajensu abubuwan da suka faru, wato kamar yadda Zainab
ta yi masu bayani, ]an lokaci ka]an labari ya cika Madina, da yawa suka yi wa
Yazid tawaye. Shi Gwamnansa na Madina ya aika masa cewa in yana da bu}atar
Madina, to ya kori Zainab daga cikinta. Shi ne
ya aiko da sa}o a fitar da ita daga cikin Madina. Zainab ta ce ba inda za ta
je. Shi
ne wasu daga cikin mataye na Bani Hashim suka same ta suka ba ta shawara a kan
ta bar Madina. Suka ce Yazid zai iya yin komai, a kan haka yana iya maimaita
wata Karbala a nan. Kuma su ba za su yarda a
ce za a zo a fitar da ita da }arfi ba suna gani su }yale sai dai duk abin da
zai faru ya faru. Jin
haka sai Zainab (AS) ta yanke shawarar ta bar Madina zuwa Misira.
Wannan ke nan a ta}aice. Ga mai
bu}atar ganin wannan, musamman ma na al’amarin matar Yazid da aka kawo na
mau}if ]inta ya duba littafi mai suna Zainabul Kubra minal mahdi ila lahdi na
Sayyid Mahammaf Kazim.
Daga }arshe babu abin cewa face
“Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya Zainab, ranar da aka haife ki, ranar da
kika yi wafati da kuma ranar da za a tashe ki.”
No comments:
Post a Comment