Sunday 3 February 2013

Darussa12daga rayuwar Imam Husain [AS] 2


Har yanzu muna cikin wannan wata na juyayi,ba}in ciki dama kuka,musamman ga mabiya Ahlulbayt [AS],saboda yadda ake keta mutuncinsu da kuma alfarmar iyalan gidan Manzon Allah [S] a cikin watan,wato akasin yadda wasu sashen ‘yan uwa musulmi na madrasah ]in Ahlus-Sunnah suka ]auke shi wata na farin ciki da kuma yalwata wa iyali
,har ma suna ma watan la}abi da watan cika ciki,da kuma wani wasa da ake yi a cikin watan mai suna wasan shara,da dai sauran abubuwa makamantan haka.Alhali wani abune wanda yake tabbatacce kuma bayyananne cewa wa]annan ‘yan uwa musulmi na Ahlus Sunna basu jahilce wannan cin mutuncin da kuma keta alfarma da akayi wa iyalan gidan Manzon Allah [S] a wata ]in ba,wato ranar Ashura.Ko kuma ace sun sani,amma suna shakka akai.A’a wani abune wanda sun sani kuma basu shakkar cewa ko ya auku.
Domin yana cikin littafansu na tarihi daban-daban,wanda in mutum ya auna da hankalinsa.Misali ace yanada mata kuma yanada mahaifa,suna raye wato uwa da uba,sai matan nan tasa,  a cikin wata rana daga ranaku sai ta haihu,har ila yau a dai ranar da ta haihu sai wa]annan mahaifan nasa Allah [T] yayi musu rasuwa,wato abubuwa guda biyu sun ha]u;]aya murnar haihuwa,]aya kuma gefen juyayin rasuwar mahaifansa.To,a nan mutum ya tambayi kansa a cikin wa]annan abubuwa guda biyu, wannene zai rinjaya a zuciyarsa? Wato murna ko juyayi? Labudda juyayi shi zai rinjayi tunaninsa,ba murnar haihuwa ba.To,ballantana ma wa]anda akayi wa wannan abu,matsayinsu ya wuce ka kwatanta su da mahaifa ga mutum.Zuriyar Manzon Allah [S] akayi wa wannan abu fa!Domin a rana ta ashura,wa]anda suka fi kowa kusanci da Manzon Allah[S]wato kusanci na jini,sun kasance a muhallin karbala.Alal misali, mafi yawan ‘ya’yan  Imam Ali[AS] da sayyida Fatima[AS]da Imam Hasan da Imam Husain[AS] mazansu da matansu duk suna wajen.Haka nan ‘ya’yan A}il da Ja’afar duk suna wajen.A ta}aice dai babu wani gida daga cikin gidajen bani Hashim wanda babu nashi a wajen.To a ranar ashura a karbala,babu wani daga cikin wa]annan gidajen da aka ambata, dama wa]anda ba a ambata ba,wanda ba a kashe masa wani nashi ba agidan.Har Sayyida Zainab[AS] ‘ya’ya biyu aka kashe mata da kuma mijin ‘yarta.To saboda Allah mutum ya auna da hankalinsa ace ranar da akayi ma zuriyar Manzon Allah[S] wannan aika-aika ta kasance ranar farin ciki da kuma yelwa wa iyali?! Anya mutum ko kunya ba zai ji ba? Ta Manzon Allah[S]. kuma ranar }iyama da wace fuska zai dubi Manzon Allah.Ace ranar da akayi ma zuriyyarsa wannan mummunan aiki,shi murna yake ba ba}in ciki ba.
Domin in mutum bai sani ba ya sani,su jagororin da suka jagoranci wannan mummunan aiki,suka kuma bada umarnin ayi,sun yine da nufin ]aukar fansa na iyayensu da kakanninsu da aka kashe a ya}o}in da Manzon Allah[S] yayi kamar ya}in Badar da makamantansu.In mutum kuma yana ganin ba  haka  bane,to ya tambayi tarihi,wato ya karanci littafan tarihi,bama wa]anda malamam shi’a suka rubuta ba.a’a,wa]anda malaman Ahlus-sunna suka rubuta.kamar littafin Tarihi na [abari,Ibn Kasir da dai suransu,ya duba ya gani wannan abu haka ne ko ba haka ba?Misali anan shine abun da Yazidu ]an Muawiya ya fa]a lokacin da labari ya same shi cewa an kashe  Imam Husain da mafi yawan wa]anda suke tare dashi,shine a lokacin ya raira wasu baitoci na wa}e,yana cewa,kaico!Ina ma dai kakanninsa da aka kashe a Badar zasu ga wannan ]aukar fansa? To,irin wadannan jagorori na ]aukar fansa su suka sa  aka }ir}iro Hadisai masu yawa,wa]anda suka siffanta ranar Ashura,ranar farin ciki da kuma yalwata wa iyali.Kuma }ago Hadisi da yi masa isnadi a jingina shi ga Manzon Allah [S] wani tabbataccen abune daya gudana a daular bani umayya.Domin a zamanin banu umayya a }ago hadisi a watsa shi,ko kuma a jirkita shi aba wani,ko kuma sukar da Manzon Allah [S] yayi wa wani a canza ta, ta zama wani abu,duk wannan ba wani ba}on abu bane.A lokacin har ta kai ma ~angarori na jama’a daban daban suna iya sawa a }ago masu hadisi kan abinda ya shafe su.                                                                                                                             Ta wani ]an kasuwa shi mutumin Akka ne,sai ya kawo albasa a makka,sai bai samu ciniki ba,abin duk ya dame shi sai ya ha]u da wani yake shaida masa ga albasar nan yazo da ita amma bai samu ciniki ba sai mutumin yace,kaje a yi maka hadisi a kai mana.ile kuwa,sai ya tafi aka }ir}iro masa Hadisi akayi masa isnadi da kuma matani: “An wane,an wane yaji daga Manzon Allah yace duk wanda yaci albasar Akka a makka yana da lada kaza”.Jin hadisin nan take aka saye masa albasa.Mu duba fa mugani.Bacin gudun fita cikin maudu’in, da an kawo misalai da yawa irin wannan.                                                                                                             Kuma mu }addara wannan hadisai na cika ciki da kuma yalwata wa iyali ranar Ashura ingantattu ne,ashe abinda akayi wa zuriyar manzon Allah [S] a ranar ta Ashura bai isa yasa a jingine cika ciki da kuma yalwata wa iyali a ranar ba? Ballantana ma wadannan hadisai kago su akayi.Mutum ya karanci tarihi ya gani,ranar da za’a iso da kawukan wa]annan bayin Allah da aka kashe a karbala zuwa garin sham,wato inda fadar yazidu take a lokacin,sai da aka }awata garin da ado,akasa mutane suyi ado su fito ganin abinda suka ambata wai,nasarar yazidu akan wa]anda ba suyi masa bai’a ba.A ]aya gefen kuma sauran zuriyar manzon Allah [S] da suka rage,wato mata da yara,suna ]a]]aure da sar}o}i,kawunan wa]annan shuhada’u suna tsittsire a masu,an tasa su a gaba maya}a na biye dasu.Haka aka shiga dasu garin sham,har ya zuwa fadar yazid.Yazo akan cewa lokacin daya hango su,kafin su iso fadarsa ya soma nuna farin ciki da murna yana rera baitoci na wa}e,da suka iso aka ]auki kan Imam Husain [AS] aka kai masa, wa]annan bayin Allah [T]wato  su Zainab [AS] suna bayan sa,yazo akan cewa a lokacin sai da Zainab [AS] tayi kuka,saboda abinda yazidu yayi a wannan lokacin.                                              Daga cikin abubuwan da yayi,akwai sanda a hannunsa a lokacin sai ya dinga zunguran bakin Imam Husain [AS] yana yi yana wa}a.A lokacin akwai wani sahabin manzon Allah [S] da ake cewa Abu Barzata Al-aslami yana wajen,sai yace wa yazidu “Kaiconka ya yazid! Da sandarka kake zungurar Husain [AS] [an Fatimah? Tabbas na shaida naga manzon Allah [S] yana sumbatar bakinsa da kuma bakin ]an uwansa Hasan yana cewa,kune shugabanni samarin Aljannah”.Da yazidu yaji haka sai ya fusata yace ayi waje da shi.Haka aka ja shi ta fuska aka fita dashi.Bayan haka sai yazidu ya dubi Imam Zainul Abidin [AS] yace masa, “Alhamdu Lillahi da Allah ya kashe Babanka.” Sai Imam Zainul Abidin [AS] yace masa “Allah ya tsine wa wanda ya kashe Babana!” Sai yazidu ya fusata yace,aje a sare wuyansa.Allah bisa ikonsa ya kare shi.                                                                                                                                                                                                      Dadai abubuwa na cin mutunci da kuma zarafi da wa]annan bayin Allah [T] mata da yara suka gani a fadar yazidu,wanda wa]ansu abubuwan suna da sosa rai da kuma tada hankali.To,mu duba fa sashen abubuwan da akayi wa wannan gida na manzon Allah [S].Wa]annan abubuwan da aka ambata da wa]anda ba’a ambata ba suna nan  rubuce a littafan tarihi,mutum yaje ya bincika ya gani.Saboda haka,kamar yadda aka fa]i a baya,za’a sake maimaitawa cewa ranar Ashura rana ce ta ba}in ciki ba farin ciki ba,sai dai in mutum na shakkar cewa wa]anda akayi wa wannan aika aika a wannan ranar ba Ahlulbayt [AS] ]in manzon Allah [S] bane.Ga wasu Hadisai da aka samo daga manzon Allah [S] dake bayani dangane da Imam Husain [AS] da kuma matsayinsa:                                                                                                        An samo daga Ya’ala [an Marra yace; “Manzon Allah [S] yace “Husain [AS] daga gare ni yake ni kuma daga Husain nake,Allah yaso duk wanda yake son Husain.”                                                                                 An samo daga Bara’a [an Azib yace; “naga manzon Allah [S] yana ]auke da Husain ]an Ali a kafa]arsa yana cewa ‘Ya Allah ni ina son sa ka so shi’.                                                                                                                      Haka nan kuma an samo daga Salman Alfarisi [RA],yace “Naji manzon Allah [S] yana cewa “Hasan da Husain ‘ya’yana ne.Duk wanda yake son su,to yana sona,duk kuma wanda yake sona,Allah zai so shi,wanda Allah yaso shi zai shigar dashi Aljannah.Duk kuma wanda ya }isu ha}i}a ya }ini,duk wanda ya }ini Allah zai ]ishi,duk wanda Allah ya }ishi zai shigar dashi wuta.”                                                                                        Har ila yau an samo daga Abdullahi ]an Mas’ud [RA] yace ‘manzon Allah [S] yace dangane da Hasan da Husain wa]annan ‘ya’yana ne,duk wanda yaso su ha}i}a yana so na,duk wanda ya }isu ha}i}a yana }ina.”                                                                                                                                                                                                         A kuma wani Hadisin manzon Allah [S] yana cewa “Duk wanda yaso ni yaso Hasan da Husain,yaso mahaifinsu,yaso kuma mahaifiyarsu,zai kasance tare dani a matsayina ranar }iyama.”                   A kuma wani Hadisi wanda aka samo daga Salmanul Farisi [RA] yace “Husain ya kasance akan kafa]un manzon Allah [S] yana sumbatar sa yana cewa ‘kaine shugaba [an shugaba,Baban shugabanni.Kai Imam ne,[an Imam,Baban Imamai.Kai Hujja ne,[an Hujja,Baban Hujjoji.” Da dai sauran Hadisai da yawa wa]anda ba za’a iya kawo suba saboda gudun tsawaitawa.                                                                         Sai kuma abinda ya shafi wa]ansu ~angarori na rayuwar Imam Husain [AS],domin su kasance Darussa a cikin rayuwarmu.Yana da gayar muhimmanci ya kasance duk lokacin da ake tunawa da wa]annan munasabobi na wafati ko wiladar A’imma [AS],mutum ya dinga kwatanta rayuwarsa da kuma rayuwarsu,yaga ya yake wajen kwafar su da kuma koyi dasu.Domin mustahili ne,ba zamu iya kai wa kamar suba.Amma ya hau kanmu muyi iya kokarin mu wajen misaltuwa dasu.Kuma haka suka bukata daga wajenmu.A nan ke nan zamu iya fahimtar cewa,lallai idan muka bibiyi rayuwar Imamai [AS],sannan kuma muka zo muka kwatanta da rayuwarmu,zamu ga cewa akwai gi~i babba dake tsakani:                                                    IBADARSA.
Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan ibada da kuma mujahada.Ga misalan wasu daga cikin ibadodinsa:
A.      Sallolinsa:Imam Husain [AS] ya kasance a kowace rana yana sallar nafila raka’a dubu,to mu kwatanta wannan da rayuwarmu wajen tsayuwa da raka’a 51,kamar yadda yazo a Hadisi da aka samo daga Imam Askari [AS] cewa,daga cikin siffofin Muminai yin sallah raka’a 51 kowace rana.kwatanta raka’a 51 da kuma raka’a 1000.
B.      Karatun Alkur’ani:Imam Husain ya kasance mai yawan karatun Alkur’ani ne,ya ma zo a tarihinsa cewa a watan Ramadan kowace rana yakan sauke shi,wato kenan sauka 30 a cikin watan.To,mutum ya kwatanta da kansa,sauka nawa ya keyi a watan Ramadan,da kuma sauran watanni?
C.      Azuminsa:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan Azumi,yama zo a tarihi cewa mafi yawan ranaku yana Azumi ne.Akwai ma wani da yayi masa shaidar cewa,bayan da yaji an kashe shi,wallahi sun kashe shi alhali ya kasance mai yawan Azumi a ranaku,mai yawaita tsayuwa da daddare.
D.      Hajjinsa:Imam Husain [AS] yayi Hajji a rayuwar shi ]ai ]ai har guda 25,kuma dukkansu a }afa ya taka tun daga madinah har zuwa makkah,wato ba tare daya hau dabba ba.Idan Allah ya na’imta mutum ya tafi aikin Hajji yayi tunanin nisan dake tsakanin makkah da madinah,amma haka Imam Husain [AS] yake kama hanya tun daga madinah har yazo makkah,ba sau ]aya ba ko sau biyu,a’a har sau 25 ba kuma saboda ba dabbar da zai hau bane.
E.       Addu’oinsa:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan Addu’oi,akwai malamai da yawa daga madrsah ]in Ahlulbayt [AS] da suka tattara addu’o’insa suka mai da littafi.Alal misali,akwai sahifatul Husainiyyah,wanda baki ]aya addu’o’in Imam Husain [AS] ne,banda kuma malaman da suka yi sharhin addu’arsa ta ranar Arfa.Wanda wannan addu’ar tasa taska  ce babba  ta ma’arifa wanda koda ace ba wani Nusus,wato aya ko Hadis dake bayanin matsayin Imam Husain [AS],to wannan addu’ar tasa ta ranar Arfa ta isa ta bayyana matsayinsa.                                                                                                 A ta}aice dai Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan Ibada.Yama zo akan cewa lokacin da Umar ]an Sa’ad, shida rundunarsa su kayi yun}urin su kai masa hari a yammacin Tasu’a,wato tara ga wata,sai Imam Husain [AS] ya aika da ]an uwansa Abbas [AS] yace masa yaje wajen su domin ya shawo kansu su jinkirta zuwa gobe,saboda muyi salloli da addu’o’i da kuma Istigfari a wannan daren.Imam Husain [AS] yaci gaba da cewa; “Allah yasa ni ina son salla gare shi da kuma biya littafinsa [wato Alkur’ani] da yawaita addu’o’i da kuma Istigfari; Haka ko wannan al’amari ya auku Abbas yaje ya shawo kansu, domin sun so suyi wannan aika aikan da su kayi ranar Ashura tun a yammacin Tasu’a,saboda haka a wannan dare na Ashura kamar yadda yazo a tarihi cewa Imam Husain [AS] da sahabbansa,sun shafe daren baki ]aya ba suyi barci ba suna ibadodi wannan na salla wannan na karatun Alkur’ani,wannan na addu’o’I dadai sauran su na ibadodi, shi yasa yazo akan cewa daga cikin abubuwan da ake son yi a daren Ashura akwai raya daren da ibadodi domin koyi da Imam Husain [AS].
                2.ILIMINSA.
Imam Husain [AS] ya kasance a wannan fage na ilimi a zamaninsa babu wanda yakai shi ballantana ya wuce shi.Ya mazo a tarihinsa cewa manya manyan sahabban manzon Allah [S] sukan zo gare shi dangane da tambayoyi na mas’aloli na addini ya kuma basu amsa,kuma tsawon zaman sa a madina ya kasance yana karantarwa ne a masallacin manzon Allah [S].Akwai ma wani da yazo ya sami wani yana tambayarsa ina zai ga Husain [AS] yace masa kaje masallacin manzon Allah [S] idan kaga wata hal}a ta mutane wa]anda kai kace kawukansu akwai tsuntsaye [wato saboda natsuwa a wajen karatunsu],to,zaka samu Husain anan.A ta]aice dai manyan sahabbai da ‘ya’yansu da kuma Tabi’ai sun amfana da iliminsa.                                                                                 3.AKHLAK [INSA.
Shima a wannan fage na Akhla}, kamar sauran fagage babu wanda ya kai shi a zamaninsa.Ga misalan wasu daga cikin Akhla} ]insa:
A.      Kyautar sa:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan kyauta,yama zo akan cewa akwai wani ba}auye da yazo madina,sai ya tambaya a garin wa yafi kowa yawan kyauta? Sai akace masa Imam Husain [AS],sai yaje wajensa.Ko da ya isa sai ya samu yana salla,sai ba}auyen ya tsaya ya kama raira wa}o}i na yabo.Bayan da Imam Husain [AS] ya sallame salla sai ya bashi kyautar Dirhami dubu hu]u.                                                                                                                                                                        Haka nan akwai lokacin da Imam Husain [AS] yaje gai da wani da bai da lafiya,ana ce masa Usamatu ]an Zaid.Sai Imam Husain [AS] ya same shi cikin damuwa da ba}in ciki.Ya tambaye shi dalilin haka,sai yace masa bashi ne yake kansa wanda yakai Dirhami dubu 60,000.Sai Imam Husain [AS] yace zai biya masa.                                                        Haka nan kuma akwai wani Ansar daya ta~a zuwa yana so ya tambayi Imam Husain [AS] amma yana jin kunya,sai Imam Husain [AS] yace ya rubuta a takarda sai ya rubuta.Yace “Ya Aba Abdullah,wani ne yana bina bashin Dirhami 500,kuma ya matsa min in biya,sai nace masa ya saurare ni zuwa wani lokaci”.Lokacin da Imam Husain [AS] ya karanta wannan takardar sai ya shiga gida ya fito da Dirhami 1000,yace masa “Dirhami 500 ka biya bashinka,sauran kuma ka biya bu}atunka na yau da kullum”.                                                                        Haka nan yazo akan cewa,bayan shahadar Imam Husain [AS] a ranar Ashura,sai aka ga kanta kanta a bayansa.Sai aka tambayi Imam Zainul Abidin [AS], sai yace wannan ya kasance ne saboda kayayyakin abinci da yake ]auka zuwa ga gidajen miskinai da kuma matayen da mazajen su suka rasu.
B.      AFUWARSA:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan afuwa.Akwai wani cikin bayinsa daya ta~a yi masa laifi,wanda ya kai ayi masa horo akai.Sai shi wannan bawan yace; “Ya shugabana! Masu ha]iye fushi [wato ya janyo ayar da tayi Magana akan haka]”.Sai Imam Husain [AS] yace,ku }yale shi.Sai kuma bawan yace “Ya shugabana masu afuwa ga mutane”.Sai Imam Husain [AS] yace “nayi maka afuwa”.Sai bawan ya sake cewa “Ya shugabana! Allah na son masu kyautatawa”.Sai Imam Husain [AS] yace “ka tafi na ‘yanta ka saboda Allah [T].                                                                                                                                                                        Akwai wani mutumin sham daya ta~a zuwa madina sai yaga Imam Husain [AS] sai yace masa,kaine ]an Abu Turab,wato fa]i na izgili.Sai Imam Husain [AS] yace masa,na’am.Jin haka sai shi wannan mutumin sham ]in ya dinga fa]in maganganu munana na zagi da kuma cin mutunci gare shi da kuma babansa,wato Imam Ali [AS].Sai da ya gama Imam Husain [AS] ya dube shi dubi na tausayi,ya karanta masa wasu ayoyi na Alkur’ani da kuma wa]ansu Hadisai na manzon Allah [S].Bayan haka yayi masa maganganu lausasa,har ma yace masa in yana da wata bu}ata ya fa]i a biya masa,in kuma bashi da masauki yazo za’a bashi,dadai wasu maganganu kyawawa na akasin abinda shi yayi.Jin haka sai shi wannan mutumin sham,kunya da kuma nadama suka kama shi.Sai Imam Husain [AS] yace masa kada ya damu,Allah ya gafarta masa.Sai mutumin yace,sai naji }unci kamar na nutse a }asa.Shine daga }arshe yake cewa; “Duk a doron }asa ba wanda nafi so kamar kai da Babanka ”.Wannan kenan shima a ta}aice.
C.      TAWALI’UNSA:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan tawali’u,yazo akan cewa wata rana yana tafiya sai ya ha]u da miskinai suna cin abinci,sai yayi musu sallama,sai suka ce yazo yaci,sai yaje ya zauna.Sai yace masu,da ba domin sadaka bane da naci.Sai Imam Husain [AS] yace masu ku tashi mu tafi zuwa gidana.Da sukaje ya basu abinci da tufafi da kuma ku]a]e.
D.      TAUSAYINSA:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan tausayi,hatta ga wa]anda suka munana masa ko kuma suka zalunce shi.Yazo akan cewa ranar Ashura kafin shahadarsa,an ga yana hawaye aka tambaye shi dalilin hakan,yace yana tausayin wa]annan mutane ne,saboda wannan aika aikan da zasuyi zai kai su ga wuta.
TSORON ALLAH:Imam Husain [AS] duk da matsayin da yake dashi a wajen Allah ya kasance mai yawan tsoron Allah.Akwai ma wata rana da akace masa,me ya kai gayar tsoronka ga Ubangijinka? Sai Imam Husain [AS] yace,ba wanda zai amintu ranar }iyama sai wanda yaji tsoron Allah a gidan duniya.Ya mazo akan cewa Imam Husain [AS] idan zai yi alwala akan ga launin fuskarsa ya canza kuma ga~u~~ansa na makyarkyata.Sai aka ce masa,me yasa haka? Sai yace; “Dolene ga wanda zai tsaya gaban Allah [T] launin sa ya canza,ga~o~insa suyi makyarkyata”.                                                                                                                                                                    Insha Allah sauran darussan a wata munasabar za’a ]ora.                                                             

No comments:

Post a Comment